← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 55

Sashe 43

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    "To ai rashin Jin Faisal ne ya ja mana hakan, gashi Nan Yana chan a tsare na tabbata ba sake shi zasuyi Nan kusa ba"

   Nabila Tace "Nifa yamin dai dai Wallahi"
Sunusi yace "To yanzu wa gari ya waya? Kin San dai hukunci Wanda ya kashe shine a kashe shi ko?"

    Cikin Muryar kuka Ayrah Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan masifa dame tayi Kama?"
Sunusi girgiza kai yayi ya fice abinsa , Nabila ganin Ayrah ta Shiga tashin hankali sosai Tace "Sister ya labarin Adnan ne Kam?"

     Hannun tasa ta share hawayen dake fuskan ta kana Tace "Yana Nan, kin San tun lokacin da yaji labarin aurena da Haisam ya rikice babu yanda baiyi dani ba Akan Kar na Masa hakan, na so na Fad'a Masa plan ne Amma na kasa gudun karya tarwastsa Mana shiri"

   " To yanzu ya ake ciki?"
" Ya daina kulani babu yanda banyi dashi ba Amma yaki kulanai shiyasa na hakura Amma to my surprise jiya ya turo min da wani sakon da ya tsorata ni"

Zaro wayar ta tayi a d'an karamin purse d'in dake hannun ta ta Shiga text d'in ta Mika wa Nabila ta fara karanta shi kamar haka.

"Na tabbata kina cikin tashin hankali Sabida iftila'in da ya dirin muku a gida, Allah Kenan baki ga komai ba this is just the beginning"

Nabila kallon ta tayi kana Tace "Me yake nufi da hakan?"
Tab'e bako tayi Tace "I don't know Wallahi, and I love this guy so much"

    Muryar Mamy taji tana fad'in "Kwarai kuwa baki ga komai ba ko ince bamu ga komai ba, Ai Allah ba azzalumin bawan sa bane ba, sai Wanda ya zalunci kansa bare Kuma Kun tab'a maraya, yau tsawon shekara nawa haisam yake kwance rai a hannun Allah, ai naso da yana Raye yaga halin da mahaifin ki ya shiga kuma Wallahi masifa da bala'i yanzu kuka Fara gani, gashi chan Faisal shima taurin Kan Nasa abinda ya jaa wa kansa"

    Nabila Tace "Haba Mamy maganganun ki sunyi tsauri dayawa Kar ki manta fa ke uwace, Mamy idan uwa tana yawan sawa d'anta Albarka tab'arbarewa yake bare kuma kin Masa mugun fata Dan Allah, Mamy ki Mana addu'a Allah ya Kawo Mana d'auki"

    " Ni bazanyi musu mugun baki ba, Sannan ni bazan musu addu'a ba" tana kaina ta fice daga gun, ta shige d'akin Malam Hassan, hawaye ne ke gangarowa daga idanun sa kallon sa tayi ta jaa wani uban tsaki Tace "Nasan maganar da mukayi ne da yaran Nan yasa kake kuka to Wallahi baka ga komai ba, Duk Wanda yaci Amana to ba Makawa amanar Allah zata ci shi." Ta jaa kujera ta zauna ta d'aura kafa d'aya akan d'aya ta Shiga danna wayar ta.

Malam Hassan kuwa tunda wannan abin ya same shi ya daina magana, sai dai Ido kawai.

Tun daga Wannan ranar Isha da Ma'aruf wani soyyaya mai karfi ya shiga tsakanin su kullum a like suke da juna idan kaga sun rabu to ya fita office ne, a haka har suka gama cin amarcin su, har ta koma bakin aikin ta, sannan lokaci zuwa lokaci ta kan je gidan Umma ko kuma gidan Mummy wasu lokutan Kuma tare da Ma'aruf d'in suke zuwa.

Mardiya kuwa,tun ranar da ta kai musi abinci bata sake Shiga part d'insu ba,idan sun had'u a gun Mom sukan gaisa, kawancen nata da Ayrah tayi baya sosai ba kamar da ba kasantuwar Ayrah idan bata gun aiki to tana gun mahaifin ta, Itace Kad'ai take kula dashi Mamy kuwa da ta gaji da jinya gidan su ta koma, Ni ko Nace Anya Mamy bata d'auki zafi dayawa ba kuwa?

*AFTER SOME MONTHS*
Meerah ce ta Kawo wa Isha ziyara , Bayan sun gama hirar su ne suka fito tare har gun motar ta ta rakata, suna tsaye suka hango motar Ma'aruf parking yayi ya fice a motar yazo inda suke, Bayan sun gaisa ne ya ce "Barina na shiga part d'insu mom Dad ne ya dawo"

"okay Nima gani Nan shigowa yanzu"
"Okay ya shige ciki"
Yana wasa da key d'in motar dake hannun sa,Isha binsa tayi da Kallo tana Murmushi , Meerah Tace "Wannan kallon fa?"
"Hmm Bangane ba mijina ne fa"
    "Oh sai yanzu Kika San cewa mijin kine ko?"
    " Tun da dad'ewa Nasan da hakan"

"Uhmnn manyan Mata, Amma naji Dad'i Gaskiya da Kika kwantar da hankalin ki no wonder Mana Naga sai Fresh kike kina kyau, Anya ma ciki kike dashi ba?"

    "Dallah malama bana son sa Ido...... " Motar  Mardiya ce ta shigo ta faka, Bayan ta fito wurin su ta nufa, Isa wurin su ke da wuya suka jiyo wani uban Kara, juyawan da zasuyi suka hangi part d'insu Mom ne yake ci da wuta ga Warin gas ya maimaye gun gaba ki d'aya.

Dukkanin su babu Wanda ya Isa mosawa a gun, suna Tsaye suna kallon ikon Allah, Mai gadi be ta fito daga ban d'aki hannun sa rike yake da buta yana kokarin d'aure mazargin wandon sa, Yana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, ba kowa a ciki ko?"

   Nan ne fa Isha ta d'aura hannu a kai ta kwarma wani uban ihu, ta yanke jiki ta Fad'i , Mardiya kuwa suman tsaye tayi daga bisani ta Fad'i sumammiya, Meerah kuka ta shigayi tana nemon taimako.
________________________
Rashin comment d'inkune yasa jikina Duk ya mutu da typing d'in,Dan Allah ku bani had'in kai Nasan Kuma Kun kosa da kuji yadda labarin zai kasance

Please Comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa

63&64
'''Continuation.....'''  da gudu Mai gadi ya nufo su, Yana ta ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Nan da Nan jama'ar unguwa suka Fara shigowa cikin gidan kowanne da abinda yake tufawa.

      Fire service aka Kira ,basu d'au wani lokaci Mai tsawo ba suka iso , suka Shiga kashe wutan, Isha da Mardiya kuwa a motar Meerah aka sasu sai asibiti.

    Bayan wutan ya d'a tsagaita suka Shiga ciki don duba 'barnan da wutan yayi, Mutum uku suka gani a parlor, Mutum biyu suna zaune a kujera Wanda Mom da Dad ne, yayin da d'ayan Yana kwance a kasa shine Ma'aruf. Nan aka Shiga fitar da gawakin su a waje kowa ya jinjina al'amarin cike da tausayi suke ta kallon su,yayin da masu saurin kuka Kuma sai kuka suke suna yabon hayyyan su musamman ma Dad da Ma'aruf.

      Bayan sun Isa asibiti, taimakon gaggawa aka Basu, yayin da Meerah ta Kira Dad ta Sanar dashi abinda ya faru, anyi sa'a Yana gari, a lokacin suna gidan Umma shi da Mummy, a razane ya mike zufa na keto Masa, mummy da Umma a tsorace suke tambayar sa abinda ke faruwa, Daddy kallon Abba yayi kana yace "Zo muje" ya fice Abba kuwa yabi Bayan sa ba tare da yaji inda zasuje ba, bin Bayan su sukayi suna tambayar ko Lafiya.

   Daddy waigo yayi cikin Murya kamar Fad'a yace "Ku koma ciki" Jin yanda yayi maganar Umma ta riko hannun Mummy suka koma ciki, motar daddy suka Shiga.

       Daddy ne yake jaan motar, a hanyar ne yake Sanar dashi abinda ya faru, Banda ambaton sunan Allah babu Abinda yake har suka isa asibitin dasu Isha suke, suna dosan d'akin da Isha take suka jiyo ihun ta cikin Muryar kuka take fad'in "Dan Allah ku sake Ni, Meerah Ma'aruf fa wayyo na Shiga uku" Meerah itama kukan take Amma bata sake ta ba, da taimakon wata nurse suka rirrike ta, Isha na ganin su Abba da Daddy da dukkanin karfinta ture su ta nufi inda suke cikin kuka Mai sautin gaske, tana fad'in "Daddy Mijina na Shiga uku" ta maida kallon ta ga Abba tana fad'in "Abba ya mutu ko? Shikenan Shikenan na shiga uku, yanzun Nan fa mukayi magana dashi, Innalillahi wa ilaihirraji'un"

   Daddy ne ya rungume ta Yana fad'in "Ya isa Isha ki daina kukan hakan"

Amma kamar cewa yayi ta Kara kukan ne, Abba waje ya fita yace su Umma suzo asibitin, Amma bai Fad'a musu dalilin kiran suba.

     Isha tafi Mintuna talatin tana kuka, Abba da Daddy suna rarrashin ta, Meerah kuwa ta rakub'e a gefe itama kukan take sosai, Su Mummy suna shigowa suka halin da take ciki, cike da rashin fahimta suke kallon su.

  Abba ne ya Sanar dasu abinda ya faru, mummy fashewa tayi da kuka da zaran ta kalli Isha sai ta fashe da kuka, Umma ma kukan take, Isha mikewa tayi ta rungumi Umma tana kuka.

   Meerah fita tayi bata dad'e ba ta dawo hannun ta rike yake da goran ruwa Tace "Umma ki bata tasha, ko zata d'an ji sanyi" tayi maganar cikin sanyin Murya da jin tausayin kawar ta.

    Dakyar da makyar kyasa Isha ta Karb'a tasha, bata d'auki mintuna biyar ba ta fara Jin jiri, Umma na ganin hakan tayi saurin kaita Kan gado.

     Nan hankalin su ya Kuma tashi Meerah Tace "Ni Nasa mata maganin bacci zata kwana tana bacci, ina tsoron Kar ciwon ta ya tashi"

Abba yace kin kyauta, Duk suka tsaya zugum suna kallon ta, Nan Abba yace " Meerah ya akayi hakan ta faru?"

   "Abba muna tsaye ne a compound d'in gidan, ya Dawo cikin gidan da fara'a yace ya Dawo ne ya sabida mahaifin sa ya Dawo, yana Shiga cikin gidan bai dad'e ba kawai muka ji wani irin Kara, sai wuta ya kama"

   Daddy yace "Ha'aaah karar me?"
"Ina tunaniin gas ne ya fashe sabida gidan Duk ya d'auki Warin gas" ta karasa maganar cikin Muryar kuka.

     Abba yace "Allah sarki yaron kirki ya mutu da kuruciyarsa da rabon bazai bar baya ba" Yana girgiza Kai, Meerah bayan hannun ta ta saka ta share hawayen dake fuskan ta tace "Ya bari, sabida yanzu haka Isha na d'auke da cikin wata har na tsawon wata biyu"

  Duk da hankalin su ba a kwance yake ba bai hanasu murmusawa ba, suna Mai hamdallah, ganin Isha na bacci hakan Yasa suka fita, d'akin da Mardiya take suka Shiga, tana zaune akan gadon marasa Lafiya tayi shiru bata vko motsi har suka shigo bata sani ba, Umma ce ta zauna a gefen ta Tace "Kiyi hakuri 'yata iyayen ki da Yayan ki sunyi mutuwar shahada, sai dai muyi hakuri"
Chapter 43 · 0% Book details