← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 55

Sashe 39

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

57&58
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

https://www.wattpad.com/1246873923?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp

```Continuation.......``` cikin Muryar kuka Tace "Mamy Mari?"

Cikin hargitsi da d'agawa tace "Eh Mari idan na kuma Jin makamanciyar maganar nan daga bakin ki sai na sab'a ki wawiya Mara hankali, mahaifin ki kike had'awa da mugun kalma irin wannan"

Ayrah cikin sanyin Murya Tace "Amma Mamy gaskiya ta fad'a Kuma kema kin San gaskiya ne, why won't you fight for your right?"

Mamy tunda Ayrah ta fara magana ta kawar da kanta tayi kamar bata jinta, Ayrah ganin tayi shiru Kuma bata ga alamar zata kulata ba ta Kuma cewa "Mamy Dan Allah kiyi hakuri ha horo Haka Mamy, da wanne zanji Dan Allah da rashin kulani da kike zanji ko kuma da matsalar da take tsakanin ku da Daddy Wanda Nasan duk nice sila"

Ajiyar zuciya Mamy tayi kana fuskanci Ayrah dake tsafe a bayan ta tace "Sam ba Wai bana son kulaki bane sabida abinda kuka aikata da mahaifin ki ba a'a so no na nuna miki kuskuren ki"

Langwabe kai tayi Tace "Mamy Wallahi na gane kure na, 3 years ba wasa ba, Dan Allah mamy ki yafe min Kuma yanzu daga gun Haisam d'in nake ya farka"

Murmushi Mamy tayi cikin Murya kamar dariya tace "Dan Allah dagaske?"
Kai a kasa Ayrah tace "Eh Mamy amma fa bai dad'e ba ya kuma komawa"
"Ban gane ya kuma komawa ba?"
" Ya sake Shiga comma"
Dafe kai mamy tayi Tace "Ai ga irin tanan Wallahi Ayrah kin cuci d'an uwanki kun biye wa son zuciya da uban ki, Dole Mutane suji tsoron *Dangin Uba* kuma Wallahi idan Haisam bai yafe muku ba baza ku tabay ganin rahamar ubangiji ba" tana kaina ta haura d'akin ta cikin tsananin 'bacin rai da takaicin abinda Mijinta da yar ta suka aikata.

Ayrah fashe wa tayi da kuka mai sauti da karfi ta saki jikin ta a kasa ta cigaba da rera kukan ta,da gudu Nabila ta karasa inda take cike da kulawa ta fara rarrashin ta tana tambayar ta laifin da tayiwa Mamy cikin Muryar kuka ta Sanar mata da komai, baki a bud'e Nabila ke kallon ta Tama rasa abin Fad'i hakan yasa ta tsaya kallon Yar uwar tata.

Muryar Faisal sukaji yana Fad'in "Tabbas biri yayi kama da Mutum Wai ace abinda Daddy yake aikatawa Kenan? Taya na za'a ce alhakin su zai barmu gaskiya daddy ya cuce mu"

Sunusi yace "Ka duba kaga ni fa Yaya abin fa bai tsaya Akan sa shi Kad'ai ba harda big sis yayi involving a ciki and abin haushin ma she blindly did what he ask to do"

Nabila Tace "Sunusi didn't you heard the story since from the beginning? Bata fa San komai akai ba, and ni ina blaming Mamy ma for not telling her the truth since from day one"

Sunusi yace "Uhhh here you go again look sis Nabila Mamy bata da laifi had it been lokacin da Dad ya Fad'a mata abinda zatayi ta Sanar da Mamy ai da zata hanata Amma ta boye mata gaskiya"

Faisal yace "Ya Isa please this is not the solution here, fad'in wa yake da laifi ko baiyi da laifi duk bai taso ba, sabida bazai amfane mu da komai let the bygones be gone please" ya karasa maganar yana hard'e Hannayen sa alamun roko.

Shiru Sukayi na d'an wasu lokutan Babu Wanda yace komai sai kukan Ayrah dake tashi a d'akin Faisal ne ya matso kusa da ita ta durkusa, handkerchief ya ciro daga aljihun sa ya Mika mata had'e da fad'in "Please ki daina kuka hakan ya Isa Dan Allah karfa ki ja wa kanki wani matsala"

Cikin shesshekar kuka tace "Faisal idan banyi kuka ba mezanyi kaina ya kulle duk duniyar bata yimin Dad'i"

Yace "Ki fawwala wa Allah komai Insha Allah komai zai dai daita"
Ciza le'be Sunusi yayi yace "Wato a cikin Haram aka Haife mu haryanzu kuma muna cikin ta Allah ya isan mu Wallahi......." kallon da Faisal yayi masane yasa ya shiru.

Mardiya na Isa gida da murna ta Shiga d'akin Yayanta ta Sanar dashi cewar zancen auren sa da isha na nan yace "Idan na Kira ta naji akasin hakan fa?"

Shiru tayi na d'an wasu sakonni kana tace "Ka d'auki Duk matakin da ya Dace"

Yace "Okay" had'e kiran Layin Isha,duka biyu ta d'aga da sallama ajiyar zuciya yayi yace "Na d'auka na rasaki"

"Uhmn baka rasani ba,Ina mardiya ta Isa gida kalau?" Kallon mardiya yayi kana yace "Eh kalau gata Nan ma muna tare"
"Okay ka gaida min ita"
Ya amsa da " tana amsawa" Nan ya fara Jan ta da Hira tun bata kulashi har ta saki jikin ta Sukayi ta Hira.

Da Yamma

Ma'aruf ne zaune da Mummyn sa da Daddyn sa suna ta shirye shirye Don a yau suke so sukai kayan lefe,Daddy tace "Yauwa Babana Nikam ya batun gidan naka ne an gama had'a komai ko?"

"eh dad an gama had'a komai"
Mummy Tace "Dan Allah yallab'ai ka bar min su anan tunda ka chan part d'aya ba kowa su zauna in yaso daga baya su zauna a Chan"

"in dai ya amince da hakan ai bani da matsala"
Kallon Ma'aruf yayi Yar karamar dariya yayi yace "mummy irin wannan Kallo haka?"

"Eh so nake naji ta bakin kane ko bakaji maganar da muke bane?"
"naji Mummy yanda kikace Haka za'a yi"
Murmushi kawai tayi suka cigaba da abinda suke.

Lefe ya had'u iya had'uwa in tsaya muku bayanin sa 'bata lokaci ne sabida haka just imagine it in your imagination,su Umma ne Kan gaba an karb'i baki yanda ya dace sai dai muce Allah ya nuna mana ranar biki.

*WASHE GARI*

Ma'isha tun da ta farka tayi sallah Bata Koma ta kwanta ba, had'a kayan ta tashigayi har sai da gari ya soma haske ta gama ban d'aki ta fad'a tayi wanka a gurguje sabida karfe 8 na safe jirgin su zai tashi, bayan ta gama shirine ta sauko kasa hannun ta rike yake da handbag d'inta d'ayan Kuma d'an madaidaicin akwatin ta take jaa, Driver da tun d'azu ya kai kayan Mummy mota yayi saurin zuwa ya karb'i akwatin natan yasa a jaka.

Mummy da Daddy da hango suna saukowa daga stairs ya rungume ta a jikin sa suna tafiya suna Hira had'e da dariya gyaran murya Isha tayi kana ta sunkuyar da kanta a kasa.

Murmushi daddy yayi had'e da fad'in "Har kin fito?"
Ba tare da kalle sa ba ta amsa da "Eh Daddy Good morning"
Ya amsa da "Morning" kallon Mummy yayi yace "Naso na kaiku Airport da kaina Amma Kuma zamuyi baki Kuma 8 ne yakamata mu had'u"
" Bakomai Alhaji gaba da yawa fatan mu shine mu Isa Lafiya kawai"
" To Hajiya Allah ya kaiku Lafiya ya Dawo daku Lafiya"
Ta amsa da "Ameen"
Ta d'aura da fad'in "Muje ko Isha? Driver na jiran mu dafan ba kiyi mantuwa ba?"
"Eh mummy banyi mantuwa ba, Amma ina Umman take ban ganta ba ko zamu biya mu d'auke ta ne?"

" A'a Umman Ku baza taje ba"
'dan Turo baki tayi Tace "To Amma mummy mai yasa haka bayan tafiyar Nan da ita aka shirya?"

" Gashi Nan ki tambaye shi da Abban kune suka Hana" tana nuna Abba had'e da tab'e baki.
Turo baki Isha tayi had'e da d'an buga kafa tace "Daddy why?" Ta karasa maganar kamar zatayi kuka.

Yar karamar dariya yayi yace "wato Hajiya so kike ki had'a min wuri ko? Daughter idan Umman ku ta tafi wa zai kula da yaran? Abban ku baya nan Kinga bazai yu a bar su da masu aiki bako?"

"But daddy 2 days fa kawai zamuyi"
"Yeah I know kawai kuje da mummyn naku, kinji kiyi hakuri"
Ba don tasa ba tayi shiru bubbuga kafa ta Shiga yi had'e da fita waje, motar ta fad'a, ta zauna had'e da rungume hannun ta sai faman Turo baki take, Mummy a gefen ta tazaun, Driver ya kunna wa motar wuta kai tsaye airport suka nufa, Basu dad'e da isa ba jirgin su ya Lula a sararin samaniya Nigeria to Turkey.

Bayan sun Isa ne a ranar hutawa sukayi basu fita ba sai washe gari suka fita, tun da suka fita basu dawo ba sai yamma liss, washe gari ma hakan Sukayi a takaice dai kwanaki uku sukayi sabida basu samu damar gama sayayyar tasu ba, sai a rana ta hud'u suka koma gida.

Yau saura 3 days biki shiri ake both families, sosai suke shiri ba kakkautawa, Isha dai sunan zatayi aure ne amma Sam bata farin ciki da auren babu abinda tayi na gyara jikin, Umma ce ta zage dantse wurin ganin ta gyara yar ta.
Chapter 39 · 0% Book details