Sashe 15
Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umma da na gama lectures nazo inda yake ajiye motar sa, nayi ta jiran sa ban gan sa ba, Kuma na Kira layin sa a kashe a tunani na wani abun yake na shiga neman sa kawai sai na ganshi da wata suna hi....... "
kukane yaci karfinta ta kasa karasa maganar dake bakin ta.
Umma ruko hannun ta tayi suka dawo parlor,zaunar da ita tayi ta sa ta a gaba tana kallon ta , ita ko Ma'isha kukan ta to ta Rai rawa "lallai abinda nake zargi ya tabbata Soyayya ce a tsakanin yaran Nan tunda gashi har kishi take" zancen zuci take
A bayyane Kuma gyaran murya tayi Tace "Daughter ki daina kuka wa ya gaya miki ana wa na miji kuka kiyo shiru ki daina kuka sai ya raina ki,kuma ma naga ai shi ya Miki laifi so shi ya kamata ya baki hakuri ba ke ba."
Cikin shesshekar kuka Tace "A'a umma Ni na Masa laifi, da ban jira shi ya gama abinda yake ba, ni nayi tunanin kashe wayar sa yayi Ashe ba chajine, Kuma ku ma na tada muku hankali Dan Allah kuyi hakuri" ta karasa maganar tana kuka Mai tsuma zuciya.
" Yi shiru daughter yi shiru tunda kin dawo ai Shikenan, duk tunanin mu wani abun ne ya same ki har shi kanshi Haisam d'in ya damu don yafi kowa ma damuwa 'bacin Raine kawai Amma zai huce ki daina kukan haka, zo muje kitchen ki tayani aiki."
Riko hannun ta Umma tayi suka nufi kitchen, Nan ta Fara Taya ta wanke wanke da sauran abubuwan da ya dace.
Haisam kuwa tunda ya Shiga cikin d'akinsa ban d'aki ya fad'a ya kunnawa kansa shower ba tare da ya cire kayan jikinsa ba, tsantsan 'bacin Rai da Jin haushin abinda tayine ya sa shi hakan, sannan ya kunna shower d'in ne don kar yaji kukanta, sabida bazai iya jure Jin kukan ta ba, Dole ne ya horata.
"Ayra kiji tsoron Allah ki fad'a min abinda kuke shiryawa da mahaifinki, Ayra Ina guje miki abinda zai je ya dawo"
"Uhmn Umma Kenan Amma kin San Daddy bazaiyi abinda zai cutar dani bako?"
"Hakane nasan da hakan Amma ina so ki fad'a min abinda kuke shiryawa"
"Mamy kiyi hakuri bazan iya fad'a miki ba , sabida daddy fa gargad'i yamin akan kar na kuskura na sanar da kowa Shirin mu"
" Amma ai ni uwarkice ina da hakki Akan ki"
"Shima Kuma yana dashi a kaina, please Umma ki fita daga cikin maganar nan, daddy yaki fad'a miki ne sabida yasan baza ki bada had'in Kai akai ba"
" Hakan shi zai tabbatar da tsiya kuke Shirin aikatawa, ina so duk abinda zakiyi a rayuwar ki sa tsoron Allah a zuciyar Ayrah, shifa rayuwar Nan gajera ce, mahaifin ki bazai tab'a fahimtan hakan ba sabida shi na mijine ciwon 'ya mace na 'ya mace ne"
Mikewa Ayrah tayi tare da fad'in "Kar ki damu Mamy nasan Kina Sona Baki son abinda zai cutar dani insha Allah Babu abinda zai sameni"
"Ayrah Ni ba take nake ba, in tunanin abinda kuke Shirin aikatawa nee, Kar ki manta Haisam d'an uwan kine mahaifiyar sa Kuma kamar uwa take a gare ki, kamata ai idan Kika ga wani zai cutar dasu ki Kare su Amma ke da kanki?"
Dafe kanta tayi Tace "Ya Rasullullah, Mamy wai wa yace miki cutar dasu zamuyi after all haryanzu ban shirya abinda nake sonyi ba, amma wallahi sai ya d'an d'ana kud'ar sa na wulakanta min mahaifi da yayi" tana Kai Nan ta d'auki ledar ta da ta Shigo dashi ta fice daga d'akin.
Mamy Tace "Allah kana gani nayie iya bakin kokari na wajen ganar dasu Kuma sunki saurarata Allah ga bawan ka Nan Haisam bawan Allah da mahaifiyar sa ka kare su daga sharrin su, sannan ka Kare Musulmi a duk inda yake, ya Allah ka Shiga tsakanin mugu da na gari" Ni ko na amsa da ameen.
Da guda na koma gidan su Haisam don ganin Wace wainar ake Toyawa.
Bayan Umma da Ma'isha sun gama girki suka zauna zaman ci, Umma da kanta taje ta Masa magana Akan yazo suci abinci yace Mata ya koshi, ta dawo abinta Ma'isha kuwa duk yanda take son Tuwo ta kasa ci , gashi Nan tuwon shinkafa sukayi da Miyar alaiyahu yaji gyad'a sai zuba kamshi yake. Har karfe 9 Haisam yaki fitowa hakan yasa tayi wa Umma sai da safe ta koma part d'insu.
Mummy da Daddy ta tarar a parlor ta musu sannu ta Shige d'akin ta Bata zauna sukayi Hira ba kamar yadda suka saba, gyara Zama daddy yayi yace "Hajiya baki lura ba kamar yarinyar Nan akwai abinda ke damin ta"
"Na lura da hakan ya wuce ita da Yayan nata?"
"hmm Haisam da Ma'isha Kenan wannan karon Kuma me ya Faru"
Nan mummy ta Sanar dashi abinda tayi, tsaki yayi yace "Ni kaina ta 'bata min Rai banji dad'i ba bare shi da akayi wa, ko da yake zasu shirya kansu"
Mummy Tace "Sanin hakan ne yasa ban Shiga cikin maganar tasu ba, sun fi kusa" Nan suka cigaba da kallon su suna Hira, daga bisani suka kashe TV suka koma d'akin su.
"Allah kawata kice kin kuntata mata yau?"
"Trust me mana, nice fa Kuma kin San me abun burgewar?"
"A a sai kin fad'a"
"A lokacin da na kashe wayar naga kiranta ya fara shigowa na kashe , bayan Nan kusan thirty minutes sai na hango ta tsaya tana kallon mu sai ta juya ta tafi"
Wata irin shu'umin dariya Mardiya Tace "That's my girl idan kina haka Zaki Shiga tsakanin su a saukake ba tare da sun gane ba"
"Hmm ke dai bari zan so da Kinga fuskar ta d'azu Amma Anya Qawata yarinyar Nan ba son shi take ba kuwa?"
"Haba ke kuwa ya za'ayi ta so shi bayan d'an uwan tane?"
"Ina ta tunanin hakan Amma zan Kara tambayar sa nayi don ina tunanin na uwa d'aya uba d'aya suke ba, babu yanda za'ayi suna uwa d'aya uba d'aya su shaku har haka"
"Da wannan ma to ki kirashi Mana tunda kuka rabu kunyi waya kuwa?"
"A a 'bata min Rai yayi Kinga wani saurin da yake ya barni a gun kamar wata wawayi yasa aka tsaya kallona"
"Fushi fa ba naki bane ki kirashi kawai, don na tabbata tana fushi dashi Kinga kin samu damar waya dashi ko ba komai zaiji dad'i"
"Wannan hakane, bari na kirashi"
Sai da safe sukayi wa junan su, Aysha wanka ta Shiga abinta Akan in ta fito tazo kwanciya sai ta kirashi.
Haisam har karfe goma ya kasa bacci sai juyi yake , Yana ta jiran Kiran Ma'isha Amma Bata kirasa ba a bayyane yace "wato ma baza ta iya Kirana ba ta bani hakuri bayan tasan tamin laifi"
Yar karamar tsaki yayi ya d'auki wayar sa ya Shiga kiran Aysha, fitowar ta Kenan daga wanka jikinta sanye yake da bath robe, Murmushi tayi Tace "Alhamdulillah"
Picking tayi cikin sanyin Murya ta Masa sallama ajiyar zuciya yayi ya amsa kana ya Shiga Bata hakuri Akan tafiyar da yayi ba tare da yayi Mata sallama ba, ta nuna Masa ba damuwa.
Nan tayi ta jaan shi da Hira har ya manta da Yana cikin 'bacin rai, suna cikin wayar ne yaji shigowar wani Kiran dubawa yayi Yana ganin sunan *Princess* yayi Yar karamar tsaki.
Aysha Tace "Lafiya kuwa ya da tsaki?"
Yace "Wani ne yake ta damina da call"
"To ka d'aga Mana"
"Kar ki da mu it's not important, Uhmn kina bani labari"
Yar karamar dariya tayi Tace "Yauwa bayan na gama......" Nan ta cigaba da bashi labarin shimen ta shi Kuma ya biye mata, har wayar ya Kai awa d'aya yanke ya Kuma kiranta suka cigaba da hirar su, Ma'isha Kuma ta Kira yafi sau ashrin idan taji yana waya sai ta katse, har karfe Sha biyu na dare suke waya jin ta Fara hamma ya mata sai da safe ya katse wayar missed call 57 na Ma'isha ya gani da message guda d'aya
_"Yaya Dan Allah kayi hakuri, na yi ta jiran ka baka Zo ba Kuma wayar ka akashe bayan naje neman ka Kuma naga Kuna Tutorial da Aysha shiysa na dawo gida don kar na katse ku am sorry please"_
Bayan ya gama karantawa tsaki yayi ya ma kashe wayar Baki d'aya ya yi baccin sa, Ma'isha ta sake Kira taji switch off kukane Mai karfi ya kwace mata tana fad'in "Shikenan Shikenan dama na San Yaya ba so na yake ba ni kad'ai ce nake hauka na, insha Allah daga yanzu na cirewa kaina soyayyar ka"
Kasa bacci tayi yanda taga rana haka taga dare, idan tayi kukan ta gajie sai tayi shiru tana tuna abinda ya mata Kuma sai ta fashe da kuka a Haka har gari ya Waye, tana Jin an Kira sallar asuba ta Mike tayi wanka sannan tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta nufi kitchen breakfast ta d'aura bayan ta Gama ta dawo d'akin ta ta Fara Shirin school.
Bayan ta gama ta d'auki Jakarta ta fice daga d'akin, dinning ta nufa ta tarar da su Mummy da Daddy na karyawa cikin girmamawa ta gaishe su suka amsa.
Ta sa wa kanta abincin ta hau ci bayan ta gama ci ta musu sai ta dawo, tayi ficewar ta Mummy da Daddy kallon junan su sukayi yace "Haryanzu fa Basu shirya ba"
Mummy Tace "zasu shirya don na tabbata yana waje yana jiranta"
Haka kuwa akayi tana fita ta hangosa a mota Yana jiran ta, Kuma waya yake hankalinsa kwance da kamar baza ta Shiga ba sai Kuma ta fasa ta bud'e gaban motar ta Shiga Kallo d'aya ya Mata ya cigaba da wayar sa.
Ya d'auki tsawon minti uku Yana waya kamun Nan yace "karfe nawa Zaki Shigo?" Daga d'ayan 'bangaren ta ce "Karfe 4,kaifa?"
"Ni bani ma da Lectures yau"
Cikin wani irin murya Tace "Yau bazan ganka ba Kenan?"
" Me zai hana idan kina son gani na zaki ganni, Kuma kinsan Dole na Kai princess makaranta"
"Albarkacin ta zanci Kenan"