← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 55

Sashe 26

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza Kai kawai yayi ya Koma kusa da ita ya zauna ya sanya hannunta a cikin nasa Yana ta kallon ta, sai yamma ya tuna bai Kira su Mummy ba, Nan ya kirasu ya Sanar dasu, ba dad'ewa Mummy da Daddy suka zo, mummy na ganin halin da yarta ke ciki ta Shiga rera kuka dakyar daddy ya samu ya rarrashe, a takaice dai Ma'isha a haka ta kwana bata farka ba ta kwana ta wuni tana bacci, sai yamma lis ta bud'e idon ta haisam da kanshi ya duba ta, ya mata alluran da ya kamata, aiko ta sake komawa bacci.

A takaice dai Ma'isha Kwanan ta uku a gadon asibiti, sai da ta d'an Samu sauki aka sallame ta, a cikin Yan kwanakin Nan ta rame ta lalace Kamar ba ita ba, kuka kuma sai abinda ya karu,mummy da daddy sunyi rarrashin sunyi fad'an Amma taki fad'a musu, mummy Tace "Ma'isha idan baki fad'an min damuwar ki ba wa Zaki fad'awa umm? Ki duba kiga yanda kika lalace fisabilillahi baki kyauta wa Kanki ba wallahi"
"Mummy nifa ba abinda yake damina"
"Idan babu abinda ke damin ki me ya kawo miki ciwon zuciyar?"
"Uhmnn mummy ciwo ne kawai daga Allah ba wani abinda yake damina"
"Toh naji kukan da kike Kuma fa? Ki duba abincin Nan da sadiya ta kawo miko tun na safe baki ma tab'a shi ba"
"Zanci Mummy"
"A gaskiya Ma'isha bana Jin dad'in ganin ki a haka Dan Allah........ "

Sallamar da akayi ne ya katse ta amsawa tayi had'e da kallon kofar don ganin wane ne, Murmushi Umma tayi Tace "Ameerah kece?"
"Eh Mummy ina wuni?"
"Lafiya lau ya gida ya su maman naku?"
" Suna lafiya sunce a gaishe ku da maie jiki"
"Allah sarki muna amsawa , sannu Ameerah Allah ya biyaki sai faman wahala kike "
"Aaaa haba Mummy nida Isha ai Mun Zama d'aya nima idan hakan ta same ni nasan zata min fiye da hakan,fatan mu shine Allah ya bata lafiya"
"hakane Allah ya bar zumunci"
"Ameen Mummy"
"Please kiyi Mata magana ta fad'a miki abinda ke damin ta, Kuma taki cin abinci, rabonta da abinci tun jiya da dare"
"Kar ki damu mummy zataci insha Allah"
Mummy fita tayi ta barsu da ga ita sai Isha, plate da d'auka tasa abincin d'an dai dai ta ajiye Sannan ta zaunar da ita ta Shiga bata a baki ba musu ta karb'a.

Cike da kulawa Tace "Haba Isha, Isha so kike ki kashe Kanki?wannan fa ba alkawarin da Kika d'aukan min ba Kennan, kin zabi ki mutu Kennan?"

"uhmn zan mutu idan kwana na ya kare,kema kin San da hakan ko?"
"Amma kuka ai gangancin kine zai saka ki rasa ran naki tun kwanakin ki bai kare ba, wallahi Isha na gaji da ganin ki a Haka, a gaskiya lokaci yayi da zan fad'a Masa da dasu mummy"
"Meerah please ki tuna alkawarin, Duk Wanda ya karya alkawarin to ba Makawa alkawari zata cishi, kin fiso a rasa rayuka biyu ne?"
"Ban gane a rasa Rayuwa biyu ba, wa Dawa Kenan?"
" Ni da Ya Haisam, wallahi farin cikinsa matters allot to me, bazan juri ganin sa a cikin damuwa ba, moreover ba Sona yake ba"
"Shima Kuma bazai tab'a jin dad'in abinda kike Shirin aikatawa ba, ko da ace baya sonki na tabbata zai so ki Nan gaba"
Maganar Meerah a kunnen Haisam ya sauka, turo kofan yayi ya shigo gaisawa sukayi kana Meerah ta Mike Tace "Zan wuce asibiti dama nazo  na duba jikin nakin ne, sai gobe zan dawo insha Allah, Allah ya baki Lafiya"
Suka amsa da ameen tayi ficewar ta, tana fita ta nufi gun motar ta Muryar Haisam taji yana kiranta a hankali ta juya tana jiran sa.

Karasowa yayi yace "Meerah wane ne Wanda Ma'isha take so?" In a serious tone yake tambayar ta, mamaki ma ya bata don ita ta manta ranar da ya Kira Ma'isha da sunan ta in bata manta ba tun suna school, ajiyar zuciya tayi Tace "like I said to you ban sani ba ni kaina taki ta fad'a min, sai anjima Kar na makara" ta shige motar ta har ta fice daga gidan Haisam na tsaye yana nazarin maganar ta a bayyane yace "Dole na sanarwa su Mummy sabida jinin ta sake Hawa yake Yi"

Ya shige ciki ai kuwa Yana shiga har d'akin mummy yayi zama yayi ya Sanar mata da halin da Ma'isha Ke ciki tace "yanzu Isha dama akan na miji ne ta kamu da ciwon zuciya?"
"Wallahi mummy Ni kaina abin mamaki yake bani"
Daddy ne ya shigo Zama yayi Bayan sun gaisa ta Sanar mishi da halin da Isha take ciki Murmushi irin tasu ta manya yayi yace "Habae biri yayi kama da mutum, Dole mu nema Mata farin ciki ta samu abinda take so, koma wane ne zan Nemo shi sanan Nan da sati uku za a d'aura musu aure"
"Haba alaji ko waye fa kace idan Kuma ba mutumin kirki bane fa?"
"I trust my daughter baza ta tab'a son abinda bayi da kyau ba."

Uhmnn kawai mummy Tace Haisam yace "am in full support Daddy Dole a nemo shi ko ina yake don wallahi idan bata Samu abinda take so ba zamu iya rasa ta"
Daddy yace "Insha Allah, zan mata magana."

Mummy ta ce "Amma ya kamata a bita a hankali gudun kar rashin Lafiyan nata ya kuma tashi ya kamata ace tana samun kulawa ne"
"kar ki damu insha Allah zan San yanda zanyi ta fad'a min."

Mikewa daddy yayi ya nufi d'akin ta babu yanda baiyi da ita ba ta fad'a masa Tace Masa "Babu wanda nake so Daddy." Matsa mata yayi Sosai daga bisani ta fashe da kuka daddy ransa a mugun 'bace ya bar d'akin.

'Dakin mummy ya nufa ya tarar haryanzu Mummy da Haisam maganar suke,hushi yake Yana fad'in "Taki ta fad'a min,ban san wani irin taurin kai Isha take da shi ba,tana chan tana kuka don kawai na bukaci ta fad'a Mana gaskiya"

Mummy mikewa tayi Tace "Ka gani ko Alhaji,sai da fad'a maka mubi ta a hankali" tana kai Nan ta fice da sauri tayo d'akin Isha.

Haisam shima mikewa yayi yace "Daddy kawarta fa tasan komai"
Kallon sa yayi kana yace "Wacce kawarta Kenan?"
"Daddy ai kawarta d'aya ce Ameerah,I over heard them suna maganar sa but na bita ta fad'a min Taki ta Sanar dani"
"Ta kwana gidan sauki,Ni zan same ta da kaina kasan inda zamu same ta?"
"Eh har gidan su na sani,Kuma Nurse d'in mu ce"
"Shikenan idan Allah ya kai mu gobe sai muji"
"Allah ya Kaiimu" sai ya fice.

Mummy na Shiga d'akin Isha ta tarar da ita kuka take Sosai rungume ta tayi tana rarrashin ta amma Taki yin shiru, ganin Kamar numfashin ta na kokarin tsayawa ta shiga kwalla wa Haisam Kira, Haisam kuwa dama yazo fita ne yaji irin kiran za take masa, da gudu ya dawo ya Shiga d'akin, Daddy da sadiya suka shigo a tare.

Duk kanta suka nufa Haisam kuwa Bayan ya duba ta d'akin sa ya Koma ta d'auko first aid box ya fara duba, Duk abubuwan da yakamata yayi Mata kana ya mata alluran bacci, mummy kuwa kuka take Sosai daddy na rarrashin ta, sadiya kuwa tausayin Ishan ce ya kamata sai matsar kwalla take, sabida Isha ta kasance tana kyautata Mata.

Haisam ne yace "Mummy!! daddy!! Ya kamata mu bar ta ita kad'ai ta samu damar bacci, mummy Dan Allah ki daina kukan hakan Nan, Kar kema ki jaa wa kanki wata matsalar please."

Hannun ta daddy ya rike suka fice daga d'akin,sadiya tafita, Haisam kuwa kallon ta ya tsayayi na d'an wasu lokuta kana ya fice daga d'akin.

A hanyar sa ta fita ya jiyo Muryar Umma da Abba a parlor da sauri ya karasa Bayan ya gaida su ya Mika hannu ya d'auki kannen sa wata Aaima da Aymana,  mummy dai haryanzu kukan take Umma hankalin ta tashi yayi ganin mummy a Haka, cikin Muryar kuka Tace "Dama jikin Daughter yayi tsanani har hakane? Nifa tun a asibiti da na ga har munyi Hira na d'auka taji sauki Sosai."

Ajiyar zuciya daddy yayi ya Sanar Mata abinda yake damin ta dama sun 'boye Mata Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ciwon zuciya a d'an karamin shekarun Nan nata? Kuma akan na miji? Dan Allah wane ne shi? Ni zanje na durkusa har gaban sa ya aure ta" ta fashe da kuka, cikin Muryar kuka Mummy Tace "Bamu San shi ba, Taki fad'a mana Wanda take so"

Daddy yace "Yanzu kukan da kuke me zai amfane mu dashi? Dan Allah da wanne zamuji?" Tsaki yayi ya fice daga gidan, Abba ma yabi Bayan sa, a garden suka zauna suna ta tattaunawa har Abba ya bukaci da a d'aga auren daddy yace "A a Abdul baza a d'aga auren Nan ba"
"Amma Yaya ka duba halin da isha ke ciki, shi Karan kansa baya cikin hayyacin sa"
"Uhmn bikin Nan fa saura 4 days, 4 days kawai me zamuce wa jama'a?"
"Amma Yaya Ana uzuri ko?"
"Eh Ana uzuri, Amma baza a d'aga bikin Nan ba, ranar jumma'ar Nan za'a d'aura auren.

Abba ganin Daddy dagaske yake hakan yasa ya bar maganar suka Fara maganar kasuwancin su, Haisam kuwa Zama yayi dasu mummy Yana Basu hakuri had'e da wasa da kannen sa, sun girma sai wayo idan sukayi wata maganar zakace fad'a musu akayi, dab da sallar magrib Abba ya Shigo akan su koma gida.

Umma ta kekashe Tace babu inda zata je anan zata kwana sabida ta kula da Ma'isha, Dole daddy ya hakura, Daddy ne yace "To kaji, kaima sai ka kwana anan, tunda gidan babu kowa baza ma kaji dad'in gidan ba."

Murmushi yayi irin nasu na manya yace "To ya na iya da garen da ba wuya? Dole nima na kwana"
Daddy ne ya maida kallon sa ga Haisam yace "Toh masu kanne taso muje Masallaci" suka wuce.
Sosa keya Haisam yayi ya bi Bayan su.
Chapter 26 · 0% Book details