← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 55

Sashe 49

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

71&72
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

```Continuation.......``` Isha Murmushi kawai take ta kasa bata amsar tambayoyin ta, mardiya sakin Isha tayi hawayen fal a kwarmin idanun ta, Tace "Allah ya sauke ki lafiya"

Duk suka amsa da Amin, Farukh ne ya zauna kusa da Haisam musabaha sukayi, sannan ya tambaye shi ya Jiki, hiran su suke hankali kwance, yayin da Meerah da Isha ma tasu hirar suke, Mardiya kuwa ta yi saye tana kallon su kamar gunki, kallon ta Farukh yayi yace "Hajiya ki zauna Mana" kamar dama jira take ta koma mazaunin ta Jiki a Sanyaye.

Farukh yace "Baby ya Kamata mu tafi fa, kin San akwai wuraren da bamu je ba tukunna"
Mike wa Meerah tayi fuskar ta d'auke yake da Murmushi, kallon ina zakuje Isha take Mata, hannu tasa a jakar ta ta cire IV (invitation card) ta zaro su dayawa bata San Guda nawa bane ma ta Mika wa Isha had'e da "fad'in tare ya Kamata mu raba, amma Kuma kina tare da patient, ga wa'annan ki bawa Wanda ta dace"

Kallon kati Isha tayi tana Murmushi Tace "Kai Masha Allah, katin yayi kyau, ikon Allah baikin saura 1 months" ta karisi maganar tana kallon Meerah, Murmushi tayi Tace "Eh."

Gyaran Murya Haisam yayi kana yace "Amarya to ni ina katin nawa ko baza a gayyace Ni bane?"
Yar karamar dariya tayi kana Tace "Ai sai dai kayi gayya ba dai a gayyace ka ba"
Faruk yace "You're right kaifa babban abokin angone"
" Isha Kuma babbar kawar Amarya ba, an bata Amma Ni ba'a bani ba" a Shagwab'ance Haisam yayi maganar kamar karamin yaro.

Isha dariya ma ya bata ta Mike ta Mika Masa Tace "Gasu Nan Yaya"
Meerah Tace "Bakwa gajiya da drama, to ai Ishan ba nata bane na bata ne don tayi gayyar ta itama"

" To Nima a bani tawa" ai kuwa da sauri Meerah ta Sanya hannu a jaka ta miko Masa masu yawa, dariya ya shigayi had'e da fad'in "Ni Wallahi zolayar ki nake, Allah ya nuna Mana ranar"
Suka amsa da Amin.

Mardiya kuwa ji take kamar ta Burma musu huka, ta tsani taga Meerah na cikin farin ciki duk da ta kasance kawarta ce tun na yaranta, mardiya irin mutanen ne masu bakin hassada da Kuma kyashi.

Meerah da Farukh suka nufi hanyan fita, sai Meerah ta juyo kamar tayi mantuwa, inda Mardiya take ta nufa,ta zaro kati d'aya ta Mika mata had'e da fad'in "Be my guest" kallon katin ta tsaya yi kamar Mai tunani kana tasa hannu ta Karb'a, ta mata Kirkirerren Murmushi da duk Wanda ya gani yasan a iya fuskane kawai, Meerah da Farukh sukayi ficewar su.

Shiru d'akin yayi sai kara IV da Isha take ta kallo, Haisam yace "Ya dai Princess?"
"Me ka gani?"
"Naga sai kallon katin kike tayi, ko dai.....? "
" Ko dai me?"
" Baaaa......buuu" yace babun yana jaan sa, girgiza Kai Isha tayi ta mike had'e da ajiye IV d'in a Kan kujerar da ta tashi, yace "Ina zaki?"

"Toilet, alwala zanyi"
Yace "oh" ta shige toilet ba tare da ta ce masa komai ba, shiru sukayi kowa da abinda yake tunani ransa, Haisam tunani yake Akan yadda zai kula da Isha ya gyara dukkanin abun da ya 'bata ya sani da ace baiyi na'am da Ayrah ba da Yana Nan tare da ishan sa, idan bai zame mata farin cikin ta ba Tabbas Hakkin soyayyar ta (sunan book d'ina na gaba *HAKKIN SO*) bazai barshi, a Yanzu ya shirya zama da Isha ko ta halin Kaka ne,sabida yana matukar kaunarta, a ranar da ta gaya masa cewar tayi aure kwana yayi baiyi bacci wani irin wutar kishi ne take tashi a zuciyar sa, Amma daga bisani yace haka Allah yaso.

Mardiya kuwa tunani take ta ina zata bullo wa al'amarin Auren Meerah sai ta gama da ita tukunna ta Dawo Kan Isha da Haisam, baza ta tab'a bari Isha tayi farin ciki ba in ta kuskura Tace zatayi aure.

(Oh ni milhaat ina mamakiin karfin Hali irin na Mardiya, ita idan baza ta samu Abu ba to gara kowa ya rasa, muna da ire iren mardiya a cikin al'umar mu Wanda they can even do worst ya Allah ka Shiga tsakanin mugu da na gari, Amin).

Bayan Isha ta fito daga toilet ta kalli Haisam da ke kallon sling na d'akin yayin da Mardiya kuwa tana kallon kofar d'akin, dukkanin su sunyi nisa a duniyar tunani, gyaran Muryar da Isha tayi ne yasa duk suka kalleta ta, a lokacin ta d'auko prayer mat ta shimfid'a, ta hau kai ta tada sallarta.

Haisam ma sauka yayi daga Kan gadon ya nufi toilet din shima da niyar d'auro alwala, mardiya wayan Haisam ta hango a Kan gado a hankali ta Mike tasa hannu ta d'auka tayi sa'a ba password hakan ba karamin dad'in ya mata, sai da ta ji motsin Haisam na kokarin fitowa tayi saurin ajiye wayar a mazaunin sa Takoma ta zauna, Isha taji motsin ta Amma kasantuwar ta juya mata baya bata ga abinda take ba.

'dayan prayer mat d'in ya d'auka ya shimfid'a ya tada sallar.

Su Umma kuwa suna shiga d'akin da Malam Hassan yake, Umma har kusa dashi taje tana Masa ya jiki ya kawar da kanta ya juya mata baya, Nabila har kasa ta duka ta gaida su Mummy da Umma suka amsa ba yabo ba fallasa, ganin Wanda suka Zo gaishe sa bai kula su ba, sukayi hanyar fita, Mami Tace "Dan Allah ku d'an zauna Mana,wurin shiru duk muna cikin kewa"
Ba musu suka zauna suna hiran sama sama,Nabila kuwa tana ta chatting a wayar ta.

Isha Bayan ta idar da sallan ta zauna tana azkar d'in da ta Saba,Bayan ta shafene ta d'auki sallayar ta nad'e kana ta ajiye shi a mazaunin sa,ta koma ta zauna.

Haisam Bayan ya idar da sallar shima ya zauna Yana Addu'oin,ya dad'e Yana rokon Allah yafiya da Kuma biyan bukatunsa na alhairi,yaji shigowar su Abba da Daddy,ganin yana Addu'oin ne Suma suka d'aga hannu a tare suka shafa, fuskar su d'auke yake da Murmushi,gaishe su yayi suka amsa,Isha ma haka, Mardiya kuwa bata ma San da Shigowar su ba,Daddy ne ya mata magana Amma bata ji ba bare ma ta bashi amsa.

Mikewa Isha tayi ta d'an tab'a ta,a d'an razane Tace "Na'am.. "
Isha Tace "Su Daddy na miki magana Amma baki ji ba"
Murya na rawa Tace "Sannun ku da zuwa ina wuni"
A tare suka amsa da Lafiya,Abba yace "Mardiya ki rage yawan tunani gudun Kar ki cutar da kanki, kullu nafsin za'ikatul maut,ko wani rai sai ya d'an d'ani zafin mutuwa muma tamu muke jira,Kiyi ta musu addu'a,Kuma Kinga mutuwar shahada sukayi, insha Allah chan yafi musu Nan kinji" tunda ya fara magana kanta a kasa, tana matsar kwalla,su duk a tunanin su maganar da Abba yake ne yake sata kuka,ita Kuma kukan Nan na haushin Isha ne,ita duk ta d'auki tsanar duniya ta d'aura Mata,gani take kamar ita ta kashe Mata ahalin ta,cikin Muryar kuka Tace "Nagode Abba, Insha Allah zan kiyaye"
"Yauwa Allah ya miki Albarka" ta amsa da Amin.

Daddy ne ya tambaya ina su Mummy suke, Isha Ce ta shaida musu cewar sun je duba Jikin Malam Hassan, kwatancen d'akin suka sa aka musu suka fice a tare, suna fita Mardiya ta Mike tayi hanyar fita Isha Ce Tace "Ina Zaki?"
A zuciyar ta Tace na tsani shisshigi wallahi, Amma a bayyane Tace "Wurin aiki, karfe shida ya Kamata na koma bakin aiki"
"Amma this is just 4:03 ki d'an jira su mummy Mana tunda tare kuka Zo"
"a a akwai abinda zanyi before lokacin yayi, idan su Umma sun shigo kice musu na wuce gida" ba ta jira amsar Ishan ba ta fice, tana fita Haisam yace "kema akwai nacin tsiya Wallahi"

"Me Kuma nayi Yaya?"
"Oho ba'a sani ba"
Murmushi kawai tayi ta cigaba da dannan wayarta, Bayan su Abba sun Isa d'akin Malam hassan suka gaisa da mamy sannan Nabila ta gaida su, har suka gama tsayuwar su malam Hassan bai kula su ba.

Gani suke kamar baya son kula sune Amma shi Kuma kunyace da Dana sani take daminsa , ji yake kamar ya tsaga kasa ya Shiga, shiysa yake pretending cewar baya magana ne.

Sallama suka musu, Daddy ne yasa hannun a aljihun sa ya ajiye musu kud'i masu yawa yace a sayawa Mara Lafiya lemo.
Mami ta masa godiya sosaiii suka fice.

'dakin Haisam suka nufa Umma na ganin Isha a zaune Haisam kuwa sai sharar baccin Sa yake, Umma Tace "Isha kina Nan haryanzu baki wuce bakin aiki ba?"

"Eh Umma"
"Why?"
"Umma hutu na d'auka har sai na haihu, ina wahala sosai wallahi"
"to in ko hakane kin daina Zama akan Haisam d'in Zaki koma gida sai kiyi ta hutawan"

"A a Umma Dan Allah, to idan ta tafi wa zai kula Dani?"
Baki a bud'e suke kallon sa Umma tace " ja'iri dama ba bacci kake ba?"
" A a Yanzu na farka, Dan Allah Umma ku bar Isha anan"
"Lallai Haisam, kai ko tausayin ta ma baka ji?"
Chapter 49 · 0% Book details