← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 55

Sashe 32

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meerah Tace "Ni zan fitar da Kai daga cikin duhu ko Kuma ince zan kunna maka haske,in dai Wannan yarinyar kanwar kace Wallahi Sam bakayi dacen kawa ba sabida wannan da kake gani tafi bakar macijiya mai mugun dafi"
Isha Tace "Please Meerah maganar nan ta wuce, please kiyi hakuri ki manta komaai dan Allah"
"Isha ke Shaida Ce kin San halin da suka sa na shiga, Duk duniya zan iya yafe komai Amma banda abinda Sukayi min"
Ma'aruf yace "Isha please Kar ki hanata Dan Allah, Meerah Sanar dani me Kanwata ta Miki?"

Mardiya kuwa duk da AC da ke d'akin bai hana jikinta jikewa da zuwa fa, sai rarraba idanu take, juyawa tayi da niyar fita daka Mata tsawa ma'aruf yayi yace "Dawo Nan"
Jiki Sim sim ta dawo ya nuna mata kujerar dake gaban sa yace "Zauna anan" sai da ta zauna ya maida kallon su ga Meerah da Isha yace "Please ku zauna, Meerah ki Sanar dani abinda ya kamata na sani"
Kallon Kallo Meerah da Mardiya suka shigayi wa juna.

Ana wata sai ga wata shine mene ne wannan abun da Mardiya tayiwa Meerah?
Ku cigaba da bibiyata, don Jin yanda labarin zata kasance.
_____________________________
Ina Jin dad'in comments d'inku Group d'in Dangin Uban dama sauraun groups d'in, bana samun damar yi muku reply Amma ina gani sannan hakan na faranta min Rai nagode Sosai Allah ya bar Kauna.

Please kuyi min sharing sannan ku cigaba da Sharhi ni Kuma na Rika yi muku typing

Milhaat Ce
Yar Terawa
[7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page

47&48
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

_Continuation......._ Ma'aruf ganin sunyi shiru ya Kuma cewa "Meerah kinyi Shiru, Ina sauraron ki, Dan Allah ki Sanar dani Kar ki boye min komai"

Ajiyar zuciya Meerah tayi kana Tace "Na San ka San kawancen dake tsakani na da Mardiya Bayan Isha bani da wata kawa da ta wuce Mardiya"

Kai ya d'aga had'e da fad'in "Wannan Hakane"
"Mardiya tayi amfani da yardar da na Mata ta cutar dani" gyara zama tayi kana Tace "Bayan na gama secondary school, ina burin Shiga School of nursing Amma Abba yaki ya fi so sai na yi aure in yaso na cigaba da makarantar, Already dama ina da saurayin da yake son Aurena Mai suna Bashir, Bashiir mutum ne mai bala'in kishi, Kuma yana yawan fad'in shi idan ya auri mace ya same ta ba a budurwa ba zai rabu da ita"

Ma'aruf yace "Ina sauraron ki"
"To akwai wani d'an unguwar mu , Kama sanshi sunan sa Usman ana Kiran sa da Usu"
"Eh na gane shi"
"Akwai wata rana Mardiya ta shigo gidan mu ta zo take min labarin sa, akan yana da kirki Kuma yana Sona, sai nace Mata kina da shirye me wallahi an fa Riga da ansa ranar biki na Nan da yan satikai Kuma kike min maganar wani, sai Tace min "Ai ba a d'aura ba tukunna ai ansha yin hakan"
Nace Mata "Bana so ayi hakan akai na gaskiya kima bar maganar Nan kawai."

sai ta Ciro wasu kud'aden da ni ban San adadin su ba, Wai Usu ne yace a bani, babu yadda batayi da ni ba naki karb'a, a haka ta maida masa, ba shine na farko kuma ba shin na karshe ba tana yawan kawo min maganar sa Duk da na nuna Mata Bana son hakan.

Sau dayawa takan kawo min kud'i da turaruka akan shi yace a kawo min ban tab'a sa hannu na karb'a ba, tunda bana son sa bazan so abin hannun sa, akwai wata rana ana saura 5 days da bikina tazo gidan mu nace "Mardiya ya batun lalle ne, wa Kika Sanni wacce ta iya, don Gaskiya ina so a fitar Dani"
Tace "Eh akwai wata mata da take yi gidan ta bayi da wani nisa sai muje a Miki,Amma fa sai munje Mun tambaye ta,ta San da zaman ki"

"To yaushe kike ganin zamuje?"
"Zuwa gobe,idan Baki da abin yi"
"Okay zan fad'a wa Mama Sai muje,zan ma Kira Isha sai muje tare"
"Ki bari ranar lallen sai muje tare da Isha d'in tunda yau ai tambayar ta zamuyi ko?"

"Eh to da Wannan ma, Allah ya Kaiimu goben" Nan muka cigaba da hirar mu, washe gari Bayan sallar azahar sai ga Mardiya ta shigo gidan mu,dama na sanarwa Mama inda zamuje tana zuwa na Sanar da ita zamu fitan, ta min a Dawo Lafiya Kuma tace Kar ka na dad'e,muka tafi, napep muka hau wani gida d'an madaidaici muka nufa, kusa kan mu mukayi muka Shiga ciki Bayan mun Shiga har parlor muka zauna.

Bayan Mun Zauna ne naga wani Saurayi ya fito daga shi sai gajeren wando da singlet, Ya mana Sannu kana ya wuce, Yana fita nima na miki na Fara masifa ina fad'in "Dama Nan gidan zaki kawo ni, gidan maza, kince Nan gidan mai lalle ne Amma Banga mace ko d'aya ba tunda muka Shigo" hannu na ta rike Tace "Haba Meerah Nan gidan Mai lallen ne wallahi tana ciki shi Wanda ya wuce d'an tane fa" Kan na bata amsa wata budurwa kamar sa'ar mu ta fito Hannun ta d'auke yake da drinks da ruwa ta Shigo da sallama, tace "Sannun ku da zuwa,tana wanka zata fito yanzu" sai ta fice, jin hakan sai naji hankali na ya d'an kwanta, sai na samu wuri na zauna.

Mardiya da kanta ta zuba min a kofi na karb'a nasha Sannan ta d'auki d'ayan ta bud'e ta zubawa kanta ta Sha, nace Mata "Big cola ne fa, ai da baki bud'e wani ba"
Sai tace min "Eh Wallahi kan ne ba dad'i kin sanni da shirme" girgiza kaai kawai nayi na shanye Tass, kasantuwar ni masoyiyar coca cola ce.

Tunda na Sha Wannan naji idanuna sun fara rufewa tun daga Wannan lokacin na manta kaina ban San a Ina nake ba Kuma ban san a wani Hali nake ciki ba, ji nayi na farka a razane d'ago kaina da zanyi na gan ni a kwance a jikin Usu, a razane na Mike nayi kokarin d'aga kafana naji sun min nauyi kallon kafan nawa nayi naga jini na bin kafana.

Usu kuwa Kallo d'aya yamin ya kawar da kansa a kaina hakan ne ya tabbatar min da Usu ya min fyad'e, kuka na fara yi ina ja Masa Allah ya Isa shi da Mardiya bazan tab'a yafe musu ba, hijabi na d'auko Nasa ina tafiya da kyar har na fita bakin fate napep na Tara ya kaini gida, ina Shiga gida naci sa'a Mama na d'akin ta hakan yasa na Shiga ban d'aki na gyara jikina.

Fitowa ta Kennan daga ban d'akin Mama ta Shigo d'aki na, ganin irin tafiyar da take ta tsaya Kallo na Tace "Me ya same ki a kafa na ga kina limping?"

Cikin inda Inda nace "Mun dan yi accident ne a hanya na sai na d'an buga kafa na"
Tace "Subhannallah Baki ji ciwo Sosai bako?"
"Eh d'an bugewa nayi kuma nasha magani"
"sannu Allah ya sauwaka, Ita Mardiya fa babu abinda ya same ta" ji nayi kamar na fashe da kuka da naji ta anbaci sunan ta amma nayi kokarin dannewa nace "Eh babu abinda ya same ta nice kadai na d'an buge"
"toh Allah ya tsare na gaba"
Na amsa da "Ameen" sai ta fice.

Kwana nayi da zazzab'i chemist d'in unguwar mu na nufa na sayi magunguna nasha shine na samu zazzab'in ya d'an sauka, washe gari kuwa da mamaki na ina kwance a d'aki na ga shigowar Mardiya da Wannan Yarinyar da ta bamu abin Sha.

Mikewa nayi saye cike da takaici nace "Ke me ya kawo ki gidan mu? Ke don ke karamar Mara kunya ce har kin iya tako kafar ki Cikin gidan mu har cikin d'akina?"

Mardiya tace "Kiyi hakuri Wallahi ban San gidan su Usu bane"
Murmushiin takaici nayi nace "Ke d'ince baki San gidan su Usu ba? Bayan gidan su Usu a unguwar nan yake? Mardiya kin cuce ni kin lalata min Rayuwa kin ruguza min tanadin da na dad'e ina yi,laifin me na Miki? Wallahi tallahi bazan tab'a yafe Muku ba"

Wacce suka shigo tare ce tayi duguwar tsaki Tace "To sai me in baki yafe ba, kar fa ki d'auka Mun Zo neman yafiyar kine, munzo gidan ku ne don muga yanayin da kike ciki"

Ji nayi kaina Yana juyawa na rasa abinda yake min dad'i cikin kuka nace "Dan Allah me na muku me na muku"
Mardiya Tace "Wallahi babu abinda Kika Mana, Kin san ance mutunci ya fi kud'i but to me kud'i yafi mutunci, 5 mil ba wasa, zuwa yayi ya same mu, Akan mu taimaka Masa ya cimma burin sa Akan ki, kin San ke d'in akwai kayan Jin dad'i " dariya sukayi suka yi tafi kana ta d'aura da fad'in "Ya mana tayin 5mil each ni ko ina ganin Wannan kud'in bazan bari su wuce ni ba"
Chapter 32 · 0% Book details