Sashe 33
Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji nayi kukan ma na kasa yi ina kallon su baki a bude nace "Yanzu akan kud'i? Akan kud'i Kika min Haka kefa kawatace?"
"mtssw Wannan kuma ke ta shafa na samu kud'i na babu abinda ya Sha min Kai, Kuma idan Kika kuskura kikace Zaki Kai karan mu, ina mai tabbatar miki da sai Bashiir yaji labari, Kuma idan yaji kema kin San ba zai tab'a auren ki ba"
Ayrah dariya ta Shiga yi Tace "Sunan wani abu wai fanko, anyways kar ki damu baza mu fad'a Masa ba , Amma idan Kika kuskura muka ji maganar nan a wani wuri sunan ki Sorry, Kinga Nan" wayarta Ciro a jaka ta nuna min Video d'ina da na Usu Ashe sunyi Mana video yanda yake lalata dani, ta d'aura da fad'in "Nasan Mardiya baza ta rasa number sa ba zamu tura Masa"
Mardiya Tace "Idan kunne ya ji?" Had'e da rike kunnen ta, Ayrah ta karasa mata zancen nata da "Jiki ya tsira" suka yi dariya had'e da barin d'akin na dad'e a tsaye agun kukan da nake yi ma na kasa yi.
Zama nayi na had'a Kai da gwiwa ina kuka Jin an turo kofar ne na yi shiru had'e da d'ago kaina don ganin Wanda ya shigo ina ganin Isha ce ta nufeta da gudu na fad'a jikin ta ina kuka, Allah sarki Isha kawar arziki Nan ta zaunar dani tayi tayi ta rarrashi na, Bayan na fad'a mata abinda aka min har ta fini Shiga tashin hankali, tashi tayi akan zataje ta sanarwa su Mama don a bi min hakki na, na hanata sannan na fad'a mata dalili na da farko taki Amincewa bayan hakurin da nayi ta bata ta fasa fad'a musu ba don ta so ba.
Ana saura kwani hud'u bikina Bashir yazo gidan mu, ina ganin yanayin sa, sai da naji gaba na ya Fad'i dama a parlor baba muke Hira Bayan Mun gama gaisawa sai nace "Kana Lafiya kuwa,naga fuskar ka wani irine"
"Lafiya na Lau,akwai maganar da nake so muyi dake ne"
Na amsa Masa da "ina sauraron ka"
yace "so nake ki rakani wani wuri yanzu"
Zaro Ido nayi nace "Yanzu da daren nan? A a gaskiya Ni ba inda zanje Mama ba za ta bari na fita ba yanzu"
Murmushin gefen baki yayi yace "Amma Kuma kin iya zuwa 'dakin samari ko?"
Cikin rashin fahimta nace "Ban fahimce ka ba"
Yace "Kar ki rainawa kanki hankali don wallahi kinyi kad'an ki rainan hankali" wayan sa ya ciro ya nuna min Video nan, kuka na fara yi ina fad'in "Wallahi ba da sani akayi ba" Amma yaki yarda da magana ta mikewa yayi yace "A Daren nan Nima ina so ki bani abinda Kika bashi in ba Haka ba goben Nan zan turo a karb'a min kayana da na kowo gidan ku"
Durkusawa nayi a akasa da gwiwowina ina rokon sa "Dan Allah Bashir Kar ka min haka, Dan Allah da wanne zanji Dan Allah ka rufa min asiri."
Yace "Idan kina so na rufa miki asiri kiyo yadda nace kawai" ganin dagaske yake hakan yasa na share hawayena na Mike had'e da fad'in "Bashir idan baka fasa aure na ba kai ba d'an halak bane, kayi Duk abinda zakayi Amma Ni bazan bika"
Cike da mamaki yace "Oh haka kikace, kinje ki ba wa wani ni da zan aure ki ne baza ki bani ba?"
"Tunda aure na zakayi sai ka jira idan aka d'aura auren sai na baka kaina Amma wallahi bazan tab'a aikata abinda kake so na aikata ba"
Yace "Allah ya sauwake na had'a jini na da Yar iska karuwa"
"uhmn naji na gode Amma Allah Shaida nane ban a hayyacina aka yi hakan ba"
"Dallah gafara makaryaciya inda fyad'e aka miki ai da kin fad'a a gida ko ni Nan bazan bari ba, bare ma karya kike da son ranki akayi hakan"
"Ban fad'a wa kowa bane sabida sun tsoratani Akan zasu nuna maka, shiyasa na yi shiru"
"Makaryaciyar banza, Ni zaki kalla ki fad'awa hakan an gaya miki ni yaro ne, Wallahi Meerah idan baki biya min bukatata ba zan fasa auren ki"
"Sai akace maka Ni d'in wawiyace ko? Oh in baka kaina ka yi yanda kake so dani sannan kaki aure na, Ni ba mazinaciya bace, sannan na tabbata bani da zunubi a agun mahaliccina, sabida haka kazo ka karb'i kayan ka mtssw" tafiya nayi na barshi a gun baki a bud'e shikan sa yayi mamakin yanda akayi ban amince da bukatar sa ba Duk da dama niyarsa ko da kuwa nayi abinda yake so bazai aureni ba.
Bayan na Shiga gida Isha na Kira na Sanar mata da yanda mukayi da Bashir, Isha cike da mamaki Tace "Bashir ya bani mamaki, insha Allah, zai had'u da dai dai shi"
Cikin Muryar kuka nace "Isha yace zai fasa aurena Dan Allah yazanyi ina tsoro Kar ya sanarwa iyayena"
"Kar ki damu, inshallah Allah na tare dake" Nan tayi ta rarrashina, daga bisani ta katse wayar.
Washe Gari
Da safe Bashir ya turo magabatan sa, gidan mu Akan a maida Masa kayan sa, Baba na jin dalili a take hawan jinin sa ya tashi Mama ta Shiga tashin hankali a gurguje aka kaishi asibiti, Bayan ya farfad'owa yayi kuka har ya tsine min Albarka, Albarkacin Mama ita kadaice ta yarda da magana ta.
Baba yafi shekara baya kulani ni kuma ban gaji da bashi hakuri ba duk da ba saurarona yake ba, bayan wasu watanni nayi wani rashin lafiya kamar bazan tashi ba, sanadin rashin lafiyar Nan ne Baba ya saurareni har ya fahimci komai yayi da na sanin fushin da yayi dani sannan ya kudiri aniyar sai yasa an Kama su.
Amma mama ta hana a fad'in ta idan akayi hakan tamkar an tona min asiri ne, dakyar ta shawon Kan Baba ya bar maganar, Bayan na samu sauki ne yasa na Shiga school if nursing, tun daga Wannan ranar da zaran mijin aure ya fito Sai a same shi a sanar dashi Kuma na tabbata aikin Mardiya da Ayrah ne.
'dago Kai tayi tace "Ma'aruf kaji abinda Kanwar ka tamin sabida son zuciya irin nata" ta karasa maganar tana kuka.
Ma'aruf Banda ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un babi abinda yake yace "Mardiya Ashe haka kike? Innalillahi am finding it Very difficult to believe my ears"
Isha Tace "Ya fa Riga ya wuce dan Allah"
Cikin Muryar kuka Tace "Hakika nayi abubuwa da dama Wanda ban tab'a da na sani ba sai yanzu Wallahi nayi na dama Dan Allah ku yafe min"
Isha Tace "Ni baki min komai ba, Meerah kikayiwa Kuma Insha Allah zata yafe miki"
Mardiya Tace "Isha kema na miki laifi kawai dai baki sani bane"
Isha cike da mamaki Tace "Laifin me ni Kuma Kika min?"
*ina masu son koyon humra da kwalacha na jiki da kuma kwalacha na gashi da turaren wuta da kuma kyaran jiki na uwar gida har amarya akan naira #250 kawai, duk mai bukata ya tuntube ni a wannan number 07053599651*
_____________________________
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terewa
[7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*
Page
49&50
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
```Continuation..........``` kallon Yayan ta Mardiya tayi kana ta sunkuyar da kanta kasa tace "Tun ranar da na ganki a cafeteria da Haisam na gane ki, sabida nasha ganin hotunan ki a wayan Meerah, Ayrah ta nuna min tana son sa nice na zugata mukaje gun Boka aka asirce shi, sannan ta bini akan muje mu tona naki, Haisam bazai tab'a son wata ba in har Wannan layan na kasa"
Isha Mikey tayi cikin Muryar kuka tana ambaton sunan Allah tana fad'in "Mardiya why? Mardiya me muka miki haka da kike son ganin mun wulakanta?"
Kai a kasa tace "Meerah Qawata ce tun muna Yara dake unguwar mu d'aya ke Kuma kawar Tace a makaranta, Meerah tana samun Duk wani gata da jin dad'in Rayuwa iyayen ta sunfi nawa karfi bayan hakan Kuma suna sonta sosai kasantuwar ita kadaice Yar su shiysa da Usu ya Zo min da bukatar sa na amince sabida nasan Dole iyayen ta zasu tsane ta, maganar ki da Haisam Kuma hoton ku na gani ke dashi a wayar Meerah sai naji na kamu da son sa ganin irin Soyayyar da kukewa junan ku nasan bazan tab'a samun Soyayyar sa ba, shiyasa na yi kokarin raba ku, duk Wanda ya ganku zai gane Kuna son junan ku Amma, Haisam bai gane ba shiyasa mukayi amfani da wannan damar wurin rabaku,amma Wallahi tallahi ban san Shirin rabuwa take dashi ba plan d'inta ne da mahaifinta Wanda ni ban sani ba, Amma a yanzu nayi na dama kuma na miki alkawarin yau d'in Nan zanje na cire layan Nan"
Cikin Muryar kuka Tace "Kin cuce ni kin cuci masoyina bazan tab'a yafe miki, a dalilin Kune na kamu da ciwon zuciya, sannan a dalilin kune Yayana Yana chan yana kwance Rai a hannun Allah, bazan tab'a yafe muku ba"