← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 55

Sashe 14

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga gida d'akin ta ya nufa ya tura yaji a rufe, d'akin mummy ya nufa ya ga bata Nan, da sauri ya fice ya nufi part d'insu da sallama ya Shigo a tsatsaye ya gaida su yace "Mummy Ma'isha fa?"

Cike da mamaki suke kallon sa Umma Tace "Lafiyan ka kuwa meya same ka Shigo a rud'e Haka?"
"Umma banga Ma'isha ba, na d'auka ta dawone Kuma ban ganta ba"
Mikewa Umma tayi Tace "Shirmen banza Kenan dama ta tab'a dawowa ba tare da Kai bane?"

"Umma wall....... "
Mummy ce ta katse shi da fad'in "Son kasan dai baza ta 'bata ba ko? Ka Kira wayar ta man"
"Wallahi mummy wayata ce ta d'auke to nafi sa ran ta kirani ne bata same ni ba"

Umma ce ta zaro wayar ta dake chaji ta Shiga dialling number ta Amma switch off kallon Haisam tayi Tace "A kashe"

Kallon ta kawai yayi ya ma rasa abin fad'i,kana ganin sa Zaka gane Yana cikin tashin hankali, Ya dad'e a tsaye mummy Kam kallonta ta cigaba dayi yayin da Umma sai safa da marwa take tana Kiran layin Amma haryanzu a kashe.

A tsawace Tace "To uban me kake jira anan? Kana ji an Fara Kiran sallar maghrib yarinyar Nan bamu San a wani Hali take ciki ba ka fita kaje ka Nemo min yarinya,Kuma wallahi kar ka kuskura ka ka dawo gidan Nan ba da daughter na ba kaji na Gaya maka."

jiki ba karfi ya Shiga d'akin sa , cable d'in wayar sa ya d'auko ya fice ya fad'a motar sa, wayarsa ya zaro daga aljihun wandon sa kana ya sa a chaji, zaro Ido yayi don ganin fuskar wayar tasa da kyau a bayyane yace "15 percent to ya akayi wayar ta d'auke?"
Tsaki yayi ya kunnata ya Shiga dialling number ta haryanzu a kashe, jaan motar yayi ya fita Masallacin unguwar su ya nufa yayi sallah, bayan sun idar ne ya Kama hanyar makaranta, duk inda yasan Ma'isha ke zuwa babu inda baije ba Amma Bata Nan, duk da cewar dare ne Amma Akwai student a school d'in.

Haisam hankali a tashe ya Shiga motar sa ya nufi gidan su Ameerah, Ameerah qawar Ma'isha ce tun a secondary school yakan kaita gidan idan sun gama hirar su ya koma ya d'auko ta, Kiran layin Ameerah yayi da yaw Isa kofar gidan su.

Mamaki ma abin ya bata sabida ba ya kiranta haka kawai sai da dalili, picking tayi bayan sun gaisa yake fad'a Mata yana waje had'e da tambayar ta suna tare da Ma'isha ta tabbatar Masa da rabuwar ta da ita yafi 2 weeks tun bikin kawar su da suka je yace "Ya Salam"
Cike da kulawa tace "Lafiya kuwa? Wani abun ne ya Faru?"
"Lafiya lau, sai anjima bari na wuce"
"Baza ka Shigo ku gaisa da Mama ba? "
"Zanzo wani lokacin ki gaishe ta" kitt ya katse wayar.

Ma'isha kuwa tana chan tana ta baccin ta, da sallati ta farka ta kalli agogon dake d'akin ta taga karfe 7 saura mikewa tayi ta watsa ruwa kana ta tayi alwala tayi sallah wani uban yunwa take ji hakan yasa ta nufi kitchen food flask ta bud'e, farar Shinfa ta gani ta bud'e d'ayan taga stew tsaki tayi Tace "Mutanen gidan Nan da shinkafa nifa in ba tuwo ba duk shirme ne" plate ta d'auko ta zuba, kujerar dake Kitchen d'in ta samu ta zauna sai da ta cinye abincin Tass har ta Kara tasha ruwa tayi hamdallah, tasa Kai zata fita suka ci karo da Mummy Tace "Sorry mummy ban ganki ba ne"
cike da mamaki mummy Tace "Ma'isha kece?"

"Eh Mummy"
"Yaushe Kika dawo?"
"Tun kan la'asar"
Mummy ta Shiga ta yarfa hannu Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Amma Ma'isha Allah ya shirye ki,Ashe dawowa kikayi Kika sa Yayan ki wahalan neman ki yanzu ga chan Umman ku ta Hana shi zaman gidan na tace kar ya kuskura ya dawo ba tare dake ba Ashe kina Nan kina ta baccin ki"

Turo baki tayi tace "To ai mummy...... "
"Ai mummy me ke? Ki fita daga idona Ma'isha wannan wani irin rashin hankaline, me ya sami wayar ki mukayi ta Kira a kashe?"
"Kashe nayi" Kai a kasa Tana wasa da yatsunta.

"Ka jimin ja'irar yarinya ki tadawa mutane hankali ba gaira ba dalili, dama kije ki Kira shi yanzu, tun d'azu yaron Nan baya gida gashi tun safe bai sa abinci a cikin saba kuka tafi makaranta ke Kuma kina Nan kin zauna Kinci abincin ki in ba mugunta ba"

"Mummy kiyi hakuri Dan Allah, wallahi na Kira layin sa ban same shi ba Kuma na gaji da jiran sa shiysa,Kuma na dawo a gajiye shiyasa fa na dawo gida Amma kiyi hakuri please"

"Dallah gafara ki bani wuri ko na had'a kanki da ginin Nan Mara hankali kawai"

Ficewa tayi da sauri don taga alama mummy zata iya buga Kan natan ta dad'e bata ga 'bacin ran mummy irin haka ba, da gudu ta Shiga d'akinta tana matsar kwalla, tana kunna wayar shigowar kiran Haisam ne ya shigo.

Haisam a kishingid'e yake a cikin motar, parking motar yayi a kofar gida ya kasa shiga cikin gida don bai San irin masifar da zai Sha a gun sa ba, ta dad'e baiga umman sa a cikin irin 'bacin ran Nan ba.

Jin Kiran ya Shiga ya zauna cike da kulawa yace "Princess Lafiyan ki kuwa? Kina ina nazo na d'auke ki?"
Cikin sanyin murya Tace "Ina gida"
Cike da mamaki yace "Gida wani gidan? Yaushe Kika dawo?"
"Gida man Ya Haisam akwai wani gidane bayan namu? Kuma tun kan la'asar nake gida"

Kashe wayar yayi, yayi horn Mai gadi ya bud'e Masa, Yana Shiga ya kashe motar ya fita ba tare da ya Kai motar parking lot ba, ya shige cikin gida da sauri, d'akin ta ya nufa, kofar d'akin ya tura da d'an karfi ganin ta Akan gado ya d'an ji sanyi a ransa sai Kuma ya fice daga d'akin tana Kiran sunan sa yaki kulata.

*FEDERAL LOW-COST*
Ayra kwance take Akan lallausar katifan ta, da sallama daddyn ta ya shigo tana ganin sa ta tashi Tace "Sannu da zuwa daddy Ashe ka dawo?"
"Eh Yar daddy na dawo tun d'azu mummyn ki Tace min kina school, ya school d'in dai?"
"Lafiya Lau daddy"
"Komai normal ko?"
"Eh Daddy"
"Masha Allah, to ya maganar mu ta kwana? Da fatan kin Fara aikin da na saki?"

"Hmm daddy Kennan ka kwantar da hankalin ka alkawari na maka sai na Kai makiyin mu kasa ko ta wace hanyance Kai dai kawai ka tayani da addu'a"

"I trust you Yar daddy, I trust you shiyasa na saki wannan aikin sabida nasan Zaki iya but mind you kibi a hankali kar kaikayi ya koma Kan mashekiya"
"hahaha insha Allah ba za'ayi hakan ba daddy your girl is very smart"
"Allah ya dafa Miki"
"Ameen daddy nagode, Ina tsarabata?"

"Yana Nan Zo muje ki karb'a"
Cike da murna ta Mike ta bi bayan sa.

Bayan ta karb'o ledan da ya Mika ma ta ta nufo d'akin ta, ji tayi an Kira sunanta cikin sauri ta juya don ganin Wacce ke kiranta ganin mahaifiyar Tace tayi Murmushi Tace "Na'am Mamy"
"Zonan ina da magana dake" tana Kai Nan ta shige d'akin ta Ayra ma tabi bayanta.
__________________________
Please comment sharhi, ku duba yawan typing da nayi Amma wasu thanks kawai nake Samu please kuyi min sharri sannan kumin sharing.

Milhaat ce
Yar Terawa

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

*DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

25&26
..................Da gudu tabi bayansa , ya nufi part d'insu da gudu ta Sha gaban sa "Yaya Dan Allah ka saurare Ni"
Kallon ta ya tsaya yi kamar zai tanka mata sai Kuma ya kauce ya Shiga cikin gida da sauri, d'akin sa ya nufa Yana Shiga ya sa key ya rufe kofar Yana ji tana Kiran sunan sa had'e da bubbuga kofar tana fad'in "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi kuskure aka Samu, bazan sake ba"

Umma jin Karan buga kofa ta fito daga kitchen cikin sauri hannun ta d'auke da cokalin Miya alama tana girki ne, kofar d'akin Haisam ta nufa ganin Ma'isha na bubbuga kofar tana kuka Tace "Daughter lafiya? Ina Kika Shiga ne Kika tada Mana hankali iye?"

Cikin kuka tana share hawayen da ke sauka a kuncin ta Tace "Umma ina Nan fa tun d'azu"
"Ban gane kina Nan tun d'azu ba, bayan Haisam shi kad'ai ya dawo Kuma yana neman ki, hankalin mu ya tashi sosai sabida a tare kuka Saba dawo wa"
Chapter 14 · 0% Book details