← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 55

Sashe 18

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haisam Bayan yaje Masallaci ya dawo ya koma d'akin sa yayi wanka, wando three quarter baki ya saka sannan ya saka Riga armless Shima baki kana ya fito yazo part d'insu Daddy zaman sa ke da wuya daddy ya Shigo da Baki sun Kai su Shida cikin girmawa ya gaidasu suka amsa, Kai tsaye dinning suka wuce, mummy da Umma suka fito daga kitchen da sauran abincin Nan aka Shiga gaishe gaishe, Bayan sun ajiye suka koma d'akin mummy suka fara hirarsu a chan.

Bayan su Daddy sun gama cin abinci suka d'an zanta har karfe takwas da rabi kana suka gama meeting d'in, fita sukayi duka a tare har wurin motocin su ya raka su duk suka wuce Amma banda mutum d'aya a tare suka sake shigowa a parlor suka zauna Haisam ya musu sannu suka amsa Nan fa daddy suka fara Hira ba kakkautawa da mutumin nan.

Ma'isha kuwa Saida tayi sallar Isha kana ta fito daga d'akin doguwar Riga ce Mara nauyi sannan ta saka baby hijab ta fito parlor ganin su daddy da gudun ta karasa inda suke ta fad'a jikin Daddy tana fad'in "Daddy sannu sa dawo wa"
Ya amsa da "Yauwa Daughter."

Dariya sukayi mutumin nan da suke tare da daddy yace "Oh daddyn ki kawai Kika gani baki ganni bako?"
"Laaah Abba wallahi ban gan ka ba, ina wuni?" Ta d'an duka ya Masa da "Lafiya su Isha manyan mata kaga yarinyar Nan yanda ta girma"

Daddy ya amsa da "Wallahi kuwa kasan girman mace"
"girman mace ai kamar Taki ake saka musu, ya school d'in dai dafatan ana kokari?"
"Eh daddy Alhamdulillah"
"Allah ya taimaka"
"Ameen nagode Abba"

Wanda ta Kira da Abba ne ya Kara maida kallon sa ga Haisam a karo na sau ba adadi ya maida kallon sa ga daddy yace "Yaya ina ta zuci zucin tambayar ka wane ne wannan?"

Murmushi daddy yayi yace "Ai shine yaron da nake baka labarin sa kwanaki"
"Ohhhh" girgiza kai yayi alamun ya tuna kana ya d'aura da fad'in "Haisam ko?"
Yana kallon Haisam d'in, cikin girmawa Haisam yace "Eh yallab'ai"
Murmushin gefen Baki yayi yace "Yallab'ai Kuma Haisam Kuma ka Kira Yaya na da Daddy? Ko Ni ban Kai a kirani da Daddy bane?" Ya karasa maganar a sigar wasa, sosa keya Haisam yayi yace "A'a ba Haka bane"

Gyara Zama Abba yayi yace Sunana Abdallah Aminu Tahir, d'aga Malam Tahir Mus'ab wannan da kake gani.... Yana nuna daddy haisam ya kalli daddy kana ya maida kallon sa gare shi,ya d'aura da fad'in "Yaya nane uwa d'aya uba d'aya muke dashi shi ya sha nono ya bar min kaga Kennan Ni Abban Ma'isha ne zanzo ka Kirani da Abba kamar yadda Isha take Kirana"

Murmushi Haisam yayi yace "Insha Allah Abba"
Daddy Har cikin ransa ya ji daddy, hakan zai tabbatarwa da Haisam ya zama d'an gida.

Daddy yace "Daughter jeki ki Kira su Mummyn ku"
Mikewa tayi had'e da fad'in to, tana Shiga d'akin da sallama ta Sanar dasu cewar daddy na Kiran su a tare suka fito, gaisawa suka Kuma yi Nan sukayi ta Hira tare yayin da Alhaji Abdallah sai Satan kallon Umma yake ta lura da hakan, hakan yasa duk take jinta wani iri, sai da karfe 11 tayi ya mike da zummar zai tafi daddy da mummy sukayi duk yanda sukayi suka sa ya Kwana.

*TSOKACI*
```Shin wane ne Alhaji Mus'ab Aminu??```

Alhaji Mus'ab Aminu d'ane ga Alhaji Tahir Mus'ab da Hajiya Maryam Muhd, Tahir Mus'ab cikekken bafulatanin Gombe ne gaba da baya, shaharen Mai kud'i ne Wanda yayi suna a fad'in Nigeria suna da 'ya 'ya biyu dukka maza Mus'ab Wanda yaci sunan mahaifin sa sai kanin sa Abdallah sun taso cikin gata dukkanin su kuma sunyi karatu ne a kasan waje Sannan dukkanin su Business suka karanta, Bayan Mus'ab ya gama karatu a India ya dawo gida Nigeria, Bayan ya dawo ne ya da Yan kwanaki karayar arziki ya Kama mahaifinsa kasantuwar asarar da yayi zuciyar sa ta buga.

Tun daga sannan mahaifiyar su ta kwanta rashin Lafiya yau da lafiya gobe ba lafiya a haka har ta shekara daga bisani ita ma ta rasu, da Taimakon Allah da na Mus'ab ya farfad'o da business d'in mahaifin nasu har ya samu Abdallah ma ya Zama mutum Shima ya fara business d'in.

Tare suke koman su har suka samu sukayi aure, a Rana d'aya suka yi aure, Shi Mus'ab Yar Gombe ya samu ya aura Mai suna Maryam, shi Kuma Abdallah a yawon business d'insa ya had'u da fauziya, fauziya bahaushiyar kano ce, Bayan shekara biyu Fauziya ta haifi d'a na miji sai yayi wa Yayan sa Mus'ab takwara, Bayan shekaru uku ta haifi Yan biyu dukka mata wata hassana da Hussaina,daga Nan suka koma Kano da Zama sabida ya cigaba da lura da business d'insu na Kano d'in.

Maryam hankalin ta kullum a tashe yake bata da wani buri da ya wuce ta samu ciki, kullum cikin kuka take Mus'ab shine Mai rarrashin ta.

Cikin Muryar kuka Tace "Mus'ab Zaka rabu har dani ko? Ko Zaka karo min kishiya"
Rungumeta yayi tsam a jikin sa yace "Bani da wacce ta fiki maryam, bazan tab'a miki kishiya ba insha Allah, kullum ina fad'a miki ki daina tada hankalin ki shi fa Haihuwar Nan na Allah ne"

"Amma ai ganan Fauziya a Rana d'aya akayi auren mu yanzu yaran ta uku yanzu haka tana d'auke da cikin wata hud'u Ni ko 'batan wata ban tab'a yi ba, sama da shekaru 7" ta karasa maganar cikin kuka.

Bubbuga Bayan ta yake yace "Amma ai ba dabarar ta bane Kuma kema ba laifin ki bane, tunda munsha zuwa asibito ci da dama har kasar waje munje duk zancen d'ayane dani dake duk bamu da matsala Kinga Kenan lokacin Haihuwar ne bata Zo ba, ki daina tada hankalin ki mu cigaba da addu'a"

*AFTER 10 YEARS*
Maryam ta tashi da zazzabi Mai zafi banda amai babu abinda take, cikiin tashin hankali ya kaita asibiti, Likita ya Sanar dashi labari Mai dad'in da ya dad'e yana son ji, farin ciki fal ransa ya Kira Abdallah ya Sanar dashi, dashi da Fauziya sunyi muran matuka, Bayan wata 9 Maryam ta sami yarta, yarinya kyakkyawa kama take sak da ubanta Amma da d'auki hasken fatar Maryam, kasantuwar Mus'ab ba wani haske yake dashi sosai ba.

Abdallah najin labarin Haihuwar ya sa suka shirya dashi da matar da yaran sa hud'u , Mus'ab, hassana da Hussaina sai Autan su Faisal, Wanda a lokacin Mus'ab nada shekaru 10, Hassana sa Hussaina 8 years sai Faisal a lokacin bai cika shekaru 4.

A Ranar suna Mus'ab ya Sanar musu da yarinya taci sunan mahaifiyar su wato Maryam Amma ana Kiran ta da Ma'isha, tun da sassafe suka shirya suka Kama hanyar Gombe a hanyar su ta zuwa gomben sukayi hatsari,Fauziya da 'ya'yan ta duk 4 suka rasu,yayin da Abdallah ya bugu sosai Yana kwance a asibiti Rai a hannun Allah.
________________________
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa

🍃*DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

31&32
_Continuation........_ Tun daga Nan Abba yake kwance a asibiti, Rai A hannun Allah buguwar da yayi ne ya sa bai farka ba yayi dogon Suma, Satin sa d'aya a kwance.

Su Fauziya Kuma da 'ya'yan ta tun a ranar aka kai su makwancin su, bayan ya farfad'o mutuwar tasu ta girgiza shi Kennan, tun daga Nan ya ji baya bukatar aure sabida gudun kar ya sake rasa su, hakan yasa ya bar kasan gaba ki d'aya ya Koma dubai, Yana kula da harkokin su na chan,sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa duba su, Nan ma kwanaki biyu zuwa uku kawai yake musu ya koma,wani lokacin Kuma ya kwana hotel.
Wannan Kenan.

*CIGABAN LABARI*
Abba ba don yaso ba ya Kwan,washe gari kuwa Ma'isha Bata sa Lectures a ranar akayi sa'a Haisam ma bayi da shi, a tare sukayi breakfast karfe 10 na safe flight d'in su Abba zai tashi.

Bayan sun gama karyawa Abba yace dasu su fito waje akwai abinda zai nuna musu,Bayan sun fitane ya zaro key a aljihun sa ya mikawa Ma'isha, sa hannun tayi ta karb'a had'e da fad'in "Abba ajiye maka zanyi?"

Yar karamar dariya yayi yace "A a My Isha,Taki Ce na Saya mikine sabida kokarin sa kike a school" Benz Ce baka sidik sai sheki yake wani uban ihu tayi had'e da salle,da gudu ta rungumi Abba had'e da yi Masa godiya "Abba Thank You Thank you"
Shima rungumeta yayi Yana "fad'in mention Not Daughter, ki dai Kara kokari akan Wanda kike yi kinji?"

Ta amsa da toh da gudu ta nufi gun Mummy tana nuna Mata,Duk sukayi Masa Godiya, Sannan suka koma cikin,Abba lokacin tafiyan sa ya kusa Amma bai ga Haisam da Umma ba,cike da kulawa yace "Yaya ya Banga sauran mutanen gidan ba?"

"Eh suna part d'insu Amma yanzu nasan zasu Shigo" Aiko Yana rufe baki sai ga shigowar Haisam cike da girmawa ya gaidasu Duk suka amsa.

Ma'isha da saurin ta Tace "Yaya ka gani Nima an Saya min mota babu ruwana da jiran ka bare ka jaa min ajii"
Murmushi yayi yace "Masha Allah , congratulations gaskiya na tayi ki murna"

Mikewa tayi Tace "Kazo muje kaga motar" wucewa tayi shi Kuma ya bi Bayan ta mummy girgiza Kai tayi Tace "Alhaji bari na Shiga daga ciki" ya amsa da "Toh."

Ya rage daga Abba sai daddy a parlor ,gyaran murya Abba yayi yace "A gaskiya Yaya bazan yi shiru na cuci kaina ba Umman Haisam ta kwanta min a Raina,da fatan zaka bani auren ta?"
Chapter 18 · 0% Book details