← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 55

Sashe 2

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zane su yayi sosai kana yasa su yanka ciyawa, Ma'isha da kawayenta suka Zo da niyar taimakawa Haisam, Amma yaki yace su taimakawa Haneef sabida shi aka bawa wurin noman dayawa sabida shine silar fad'an Ma'isha Tace "A'a baza mu taimaka Masa ba, shi ya jawo wa kansa jiki magayi, yaron yana da matsala sosai" " Ma'isha ba a Rama mugun ta da mugunta, da babu Wanda zai tuba ya gyara laifin sa, Dan Allah kuje ku taimaka Masa" " okay , zamu taimaka Masa Amma da sharad'i" " What? " " Sai dai idan zaka Bari driver na ya ajiye ka a gida" "Inaa bazaiyu ba, I won't, I can't, can't you see that my uniform is very dirty? " Afnan tace " that's even more you should allow her to take you home, bai kamata ka tafi acikin kaya Masu ditti haka ba" "Okay, agreed, na amince"

Ma'isha da kawayenta sunji dad'i sosai, yanda Haisam yace sukayi hakan sukayi suka taimakawa Haneef, abin ya bashi mamaki sosai, bayan sun gama yaje ya bawa Haisam hakuri, Haneef yace "am awfully sorry for everything, Dan Allah kuyi hakuri, all of you should forgive For all the trouble I caused, Dan Allah ku barb'e ni a matsayin aboki" girgiza Kai Haisam yayi yace "Kar ka damu komai ya wuce" Ma'isha zuwa tayi ta sayo musu ruwan sanyi duk suka Sha sannan suka koma aji..

Bayan an tashe su, Ma'isha babu inda bata duba ba Amma bata ga Haisam ba, taji ba dad'i, shigewa tayi mota ta wuce gida, bayan ta bar gun ya fito ya fashe da dariya "Hahaha come and take me home Mana, so kike kije Kiga gidan mu don ki gane cewar mu talakawa ne, inaa bazaiyu ba" sai da ya tabbatar Ma'isha sunyi nisa da barin gun, kana ya fito ya wuce gida.

WASHE GARI
Ma'isha na Isa school ta tinkare shi "Na tabbata kana sane kake guje min, But Haisam, meyasa kake guje min? Why are you hurting me like this? Bani da kowa shiyasa nake so ka zame min d'an uwa kwalli d'aya, please stop avoiding me Dan Allah."

"Am sorry,kiyi hakuri, forgive me please" " You're forgiven, yau zamu Kai ka gida" "Dan Allah ki bar maganar kaini gida, akwai inda nake zuwa ne Kan na tafi gida" Kan ta bashi amsa principal ya shigo yace "Good Morning class, today is the last day for those who have not paid for thier w.a.e.c fees. starting from tomorrow , personally will be coming to send home any student who comes to school without his or her Money, have I made myself clear?" Duk suka amsa da "Yes Sir" bayan ya fita, Haisam kansa yasa a Kan benci ya shiga tunani mai nisa, har aka tashi bai kula kowa ba tunanin yanda zai samu kud'in ne ke damun sa.

"Yaya zanyi?" Zancen zuci yake "mahaifiya ta bata da Kud'in da zata biya min sannan Dangin Ubana Babu Wanda yake da niyar biya min, Ya Allah ka kawo min mafita" Ma'isha Tace "lafiya kuwa? Haven't you paid the money?" Haisam yace "Eem.....Eem.... Eh but I hope to pay soon" baya cikin yana yin magana da kowa.

Ana tashi ya Kama hanyar gida shi kad'ai yake tafiyar. Ma'isha ta Shiga damuwa ta rasa abinyi daga bisani ta yanke shawarar bin Haisam. Sai da ta tabbatar driver d'inta bai ganta ba a silale tabi bayan Haisam amma Haisam bai San da cewar tana biye dashi ba, yana isa gida ya Shige, Murmushi tayi tace "Finally, yau nasan gidan su. Sai ta juya ta koma makaranta, driver yayi jiran Duniya bai ganta ba hakan yasa ya koma gida.

Ma'isha na zuwa taga wayam ba driver hakan ya tabbatar mata da ya tafi, bata da wani zab'i da ya wuce ta taka da kafa. Kan ta Isa gida mahaifiyarta ta shiga tashin hankali kasantuwar bata tab'a aikata hakan ba, ranta yayi mugun 'baci da driver sabida ya dawo ba tare da Yar ta ba, a tsawace tace "Idan wani Abu ya sami 'yata I'll make sure you spend the rest of you life in jail"

Cikina Rawar murya driver yace "Is not my fault Ma, na dubata ta ko ina a makarantar Amma ban ganta ba, sannan bata makarantar don nine mutum na karshe da ya rage a makarantar, Kuma har na bar gun ban ganta ba"

"Zaka yimin Shiru a wurin Nan ko Sai na buge maka baki? Kaje ka Nemo min 'yata....." Kan ta karasa maganar da zatayi ta hango Mai gadi ma Bud'e gate,Yana Bud'ewa sai ta ga shigowar Ma'isha, da gudu ta nufi inda take.
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
Milhat ce
Yar Terawa
Please comment and share

🍃 *DANGIN UBA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

5 and 6
WASHE GARI
Haisam bai je makaranta ba, hakan ya tadawa Ma'isha Hankali, duk ta rasa sukunin ta a makaranta har aka tashe su. Bayan an tashi musu ta ce wa driver ya kaita gidan su Yar ajin su, ta karb'i assignment ba musu ya amince ta Masa kwatancen gidan ya kaita gidan su Haisam.

Haisam karar motar yaji ya tsaya a kofar gidan su hakan ya sashi fitowa don ganin wane ne, ga mamakin sa yaga ma'isha ce. Rai a d'an 'bace yace "me kike yi anan? And how on Earth did you trace my house?"

Ma'isha tace "Am I forbidden from coming to your house? Sannan Kai kuma irin salon naka Kenan na karb'an baki?" " Ba haka bane, kawai ban tab'a sammanin ganin ki anan bane anyway you're welcome" "Thanks, meyasa yau bakaje makaranta ba?" Kan ya bata amsa, yaji mahaifiyar sa na tari da gudu ya koma ciki, Ma'isha bin bayan sa tayi, mahaifiyar sa a kwance tana matsanancin zazzab'i. Ma'isha na ganinta ta gane itace matar da ta sayar musu da kosai ranar. Cike da kulawa tace "Me ke damin ta?" "Ban sani ba tun jiya take fama da zazzab'in Nan" "Ka kaita asibiti kuwa?" Shiru yayi ya kasa bata amsar tambayar sai hawayen da yake zubowa daga idanun sa.

Kan kace me ita ma ta Fara kuka, ta rasa abinyi hakan yasa ta koma cikin mota tana kuka, driver na ganin tana kuka hankalin sa ya tashi, cikin sauri ya Shiga cikin gidan su Haisam a tunanin sa Haisam ya dake tane, Amma yana ganin mahaifiyar Haisam sai jikinsa yayi sanyi, ya fito ya Maida ta gida. Idanun ta a cike yake faal da hawaye suka Isa gida, mahaifiyar ta na ganin ta hankalin ta ya tashi, a tunanin ta wani abun aka mata, tayi tambayar duniyar Nan taki fad'a Mata daga bisani driver ne ya mata bayanin dalilin kukan nata, tana jin haka ta Shiga rarrashin ta.

Tace "Nasan yanda kike ji daughter, Amma Kar ki damu zanyi wa Mahaifin ki magana idan ya dawo, so that we should know how to take your friend's mother to the hospital" ma'isha tayi mutukar farin ciki da jin hakan. Mahaifin ta na dawowa ta Sanar dashi halin da Haisam ke ciki Shi da mahaifiyar sa, ta karasa bashi Labarin cikin kuk,hakika sun bashi tausayi sosai, yace "Karki damu Ma'isha, Babu abinda zai Sami mahaifiyar Haisam, Kuma Kinga gobe Saturday ne Babu inda zanje Kinga gobe da safe sai ki kaimu gidan su Haisam d'in, sai mu kaita Asibiti"

"Thanks Dad, Amma meyasa baza mu kaita Asibitin yau ba, ina tsoron Kar wani ya same ta" "Kar ki damu Insha Allah babu abinda zai sameta, Kuma Kinga dare ta Riga tayie, Amma na Miki alkawari gobe da sassafe zamuje."

Ma'isha na alfahari da iyayen ta ganin yanda suka d'auki damuwarta tasu ce, tasani tunda yace zasuje to tabbas zasuje d'in amma yanda taga rana Haka taga dare, duk a tsorace take, gani take kamar mahaifiyar Haisam zata iya rasa ranta, Kan gari ya waye ta tashi ta Shiga ban d'aki ta d'auro alwala ta jero raka'a biyu kana ta fara rokon Allah da ya bata Lafiya bayan ta idar ne ta kwanta tana jiran wayewar gari,a Haka bacci 'barawo ya sace ta.

Washe gari itace ta Fara tashi duk da ba tayi bacci da wuri ba, jiki na rawa ta gyara gidan tsaf tun kan, Mummy na fita ta rike baki tace "Oh Ma'isha ke da a weekend bacci kike sai nayi da gaske ki tashi yau me ya faru haka?"

"Mummy ina so muje gidan su Haisam da wurine shiyasa, Wallahi Mummy da ita na kwana a rai, gani nake kamar wani abu zai sameta"

Murmushi tayi tace "Inshallah babu abinda zai sameta, Naga kin gama gyara gidan ma"
"Eh Mummy"

"Toh yanzu kije ki shirya Ni kuma Zan had'a mana breakfast, Daddyn ki ma ya na wanka"

Ta amsa da Toh ta shige d'aki bayan ta gama shiri ta fito ta tarda mummy da Daddy suna karyawa, cikin Ladabi ta gaida su, suka amsa, Ma'isha kasa cin abincin ma tayi, wainar indomie da kwai Mummy tayi sabida zaifi saurin gamawa.

Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Haisam, Haisam na ganin su tsuman tsaye yayi cike da mamaki yake kallon su, Yana ganin mahaifiyar ta ya shaida ta, har kasa ya durkusa ya gaida su, cike da sakin fuska suka amsa, Daddy yace "Yaro ina mahaifiyar ka?"

Murya na rawa yace "Tana.....tana.... d'aaaa ki"
Murmushi Mummy tayi tace "To ka kaimu mu ganta ko?"

Jiki na rawa ya shige d'aki Suma suka Mara Masa baya, Ma'isha kuwa sai Murmushi take har cikin ranta take jin dad'in ganin mahaifiyar Haisam na raye, suna had'a da Haisam kuwa kallon tuhuma yake mata,tana ganin haka sai ta Fara dariya kasa kasa.
Chapter 2 · 0% Book details