← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 55

Sashe 24

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta Isa asibitin na had'a su duka tayi ta masifa Banda hakuri Babu abinda suka ce mata, haka Umma ta kwana ba ta haihu ba sai uban wahalar da take Sha, har gari ya waye sai abin ya tashi ya sake kwanciya.

Ganin har karfe 8 tayie bata Haihuwa ba Umma Tace su koma guda Ma'isha ta had'o musu breakfast ta kawo, a gidan Umma Haisam ya ajiye ta ya Koma gida yayi wanka ya dawo gidan Umman sai da ya karya Ma'isha ma tayi wanka suka koma asibitin.

Abba na Abuja ji yake kamar ya dawo Amma ba hali kasantuwar washe gari yana da meeting da zasuyi, Daddy Kuma yana bauchi yaje yin wasu harkokin sa a Chan, anan asibiti sukayi sallar azahar, Haisam banda matsar kwalla ba abinda yake yi Mummy da Isha Kuma sai aikin rarrashin sa suke suna kwantar Masa da hankali Likita ce ta fiti fuskanta d'auke yake da Murmushi gunsu ta nufa Tace "Alhamdulillah Allah ya sauke ta lafiya, ta Samu Twins duka Mata"

A tare su Umma suka Shiga hamdallah, Likita kuwa Tace "Amma ta zubar da jini sosai Gaskiya tana bukatar jini"
Haisam a rud'e yace "To a d'i a nawa mana"
Hannu ta d'aga Masa had'e da fad'in "Come with me." Yabi bayanta.

Sai da aka gyara su tsaf da jariran ta Mummy da isha suka Shiga suka gansu Yara kyawa Masha Allah, wayar Ma'isha ce Fara ringing picking tayi ta dafa Kai "Tace am sorry wallahi yanzu haka ina specialist ne mom d'ina ce take labour, Amma gani Nan zauwa yanzu"

Mikewa tayi Tace "Mummy zan tafi ni na manta ma yau afternoon nake karfe biyu ya kamata na karb'e ta gashi har quarter to 3 yanzu"
"Yi maza kije Allah ya tsare"
Ta amsa da "Ameen Mummy" sai da ta d'auki hoton jariran kana ta fice, napep ta Tara ta koma gidan Umma ta d'auko lab coat d'inta kana ta d'auki motar ta ta wuce asibiti, tana Isa wacce zata karb'e ta, ta tafi, wayar ta ta zaro ta turawa Daddy da Abba hotunan, Abba na gani ya kirata
Yace "Dama ta haihu ne babu Wanda ya fad'a min"

"Eh Abba d'azun Nan ta haihu"
"Amma shine baku fad'a min ba tun d'azu hankali na a tashe yake"
"Yi hakuri abba wallahi Mun shafa'a ne, Kuma ance tana bukatar Karin jini"
"Subhannallahi an samu an Sa Mata?"
" Ban sani ba wallahi nima yanzu ina bakin aikine"
"okay bari na Kira su naji"
Ya katse wayar Murmushi tayi Tace "Lalllai Abba bai ma damu da yaran ba matar sa kawai ya sani" Nan ta cigaba da aikin ta.

Haisam kuwa jinin sa bai Dace da na Umma ba sai da suka saya sannan aka sa mata, bacci Tasha sosai har sai yamma lis ta farka, Murmushi kawai tayi ta yi, tana kallon 'ya'yan ta.

Mummy kanta ne ya kulle ta rasa yadda zatayi , Ma'isha na gun aiki gashi suna bukatar abinci yau ga ranar Yar aiki, Kiran abba tayi ta rarrashi shi cikin ikon Allah ya amince dama akwai wacce take son Fara aikin a gidan mummy Amma ya Hana, Mummy ba tayi kasa a gwiwa ba ta kirata, ta fad'a mata Duk abinda zatayi tana zuwa Mai gadi ya bud'e mata gate ta shiga sabida mummy ta Riga ta fad'a Masa hakan yasa bai tsaya tambayar ta ba.

Duk abubuwan da Mummy ta fad'awa Sadiya duk tayi su kasantuwar ita d'in Mai nutsuwa ce, Bayan ta gama ne ta Kira Hajiya ta Sanar mata akan ta gama, Mai gadi mummy ta Kira tasa ya kawo ta asibitin ta kawo musu abinci da duk da duk wani abun da zasu bukata.

Kwanakin su uku a asibitin aka sallame su, a ranar Kuma Abba ya dawo, bakin Nan a wage an kasa rufe shi, Mummy Kam gaba ki d'aya ta dawo gidan Umma tana kula da ita, bayan Nan mummy tasa Dole sai da aka samawa Umma ita ma Yar aiki, sai Bayan suna Mummy ta koma gida kasantuwar Daddy zai dawo, Twins kuwa Ana Kiran su da Aaima da Aymana.

Sosai suke samun kulawa a gun familyn gaba ki d'aya kun San Twins da Shiga Rai musamman ma ace identical Twins ne.

Kwan a tashi ba wuya a wurin Allah, Haisam ya samu ya gama makarantar sa sabida good Results d'insa ma Asibitoci da dama suna son su d'auke shi aiki, Amma Isha ta kafa ta tsare Dole ya karb'a a inda itama take aiki, acikin shakara d'aya komai ya canza, Haisam kuwa dama a kage yake ya gama don ya samu damar mallakar Aysha, Ma'aruf kuwa Ma'isha ta kaishi sun gaisa da su Daddy an San da zaman shi, komai tafiya normal yake sai godiyar Allah.

Haisam ne zaune shi daddy suna Kallo a parlor sai yayi Kamar zaiyi magana sai Kuma ya kasa, mummy Ce ta fito hannun ta rike take da Plate fruits ne a ciki ta ajiye a gaban Daddy, Kallon Haisam tayi Wanda ya Shiga duniyar tunani, Kiran sunan sa da tayi "Son!!! Ne ya dawo da shi daga tunanin da ya Lula ya amsa da "Na'am Mummy"
"Lafiyan ka kuwa?"
"Lafiya Lau Mummy"
Murmushi daddy yayi yace
"Tun d'azu na lura dashi Akwai abinda yake damun sa amma yayi shiru, ka fad'a Mana Son me ke faruwane? Ko dai matsalar daga gun aikine?"
"A a daddy dama.... " Sai Kuna yayi shiru yana Sosa keya daddy yace "Feel free man, ka Fad'i Duk abinda kake so ni Kuma na maka alkawari zan maka shi in bai fi karfina ba"
"Umm dama... Dama Akwai wacce Muke soyyaya da itane , to ina so a nema min auren tane"
Murmushi mummy tayi Haka shima daddyn yace "Wace ce Kuma Yar gidan wace ce?"
"Sunanta Aysha,Amma Gaskiya daddy tun da muke ban samu damar ganin mahaifin ta ba, Amma na San gidan su"
"Toh Shikenan ba matsala, sai ka Sanar da ita su sa mana Rana"
"Daddy Kuna iya zuwa gobe ma don munyi magana da ita"
"To Shikenan dama Abban Kuma yana gari kaga sai muje goben kawai"
"To Shikenan Allah ya kaimu."

Mummy tunda Haisam ya ambaci sunan wata ba sunan Ma'isha ba sai taji ba dad'i Haisam mikewa yayi ta Shige d'akin sa, mummy cikin damuwa Tace "Alhaji wallahi na d'auka yaran Nan soyayya suke"
Cikin rashin fahimta yace "Wasu yaran Kenan?"
"Ma'isha da Haisam Mana Gaskiya na dad'e ina burin naga an had'a su aure"
"hmm bake kadai ba har Ni kaina na yaba da halin yaron Nan, Amma tunda ya ce ga wacce yake so ai baza mu Masa Dole ba ita Ma'ishan sai ta fad'awa wannan yaron da yake zuwa gun ta ya turo Iyayen sa sai a had'a ayi rana d'aya."

Ma'isha ce ta Shigo cikin parlor bakin ta d'auke da sallama da kayan aiki ajikin ta da alama daga asibiti take Zama tayi a Kan kujerar da yake fuskantar su Daddy a kasalan ce ta gaida su suka amsa daddy yace "Yauwa daughter kin dawo a dai dai, ki fad'awa wannan yaron da yake zuwa wurin ki ya turo magabatan sa in har da gaske yake sai a had'a Rana d'aya da na Yayan ki shima gobe zamuje mu nema Masa aure"

Zumbur ta Mike Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Aure Kuma? Yayan aure zeyi?"
Mummy cikin fad'a Tace "Ke Lafiyan ki kuwa me haka?"
Jiki a sanyaye ta d'auki Jakarta ta haura sama da gudu tana kuka, Daddy yace "Meyasa Kika yi Haka?"
"Alhaji me Kuma nayi?"
"Baki San ma me kikayi ba?"
"Umm to Alhaji maganar aure fa akayi, sai kace zancen mutuwa akayi, Kuma Alhaji ban ma San nayi hakan ba,Amma Alhaji nifa ina ganin yarinyar Nan tana son Haisam"
"Kamarya Kenan fa?"
"Baka lura da hakan ba yanzu fa maganar auren sa da kayi ne ya razanar da ita yanzu Nan tabbata kuka takeyi"

Ajiyar zuciya daddy yayi yace "Maybe shakuwa ce kawai ba soyayya bace , Amma shekaru nawa sukayi suna tare a gidan Nan ai in da Soyayyar ce da mun sani ko? "
"Hakane Kam, to Allah ya tabbatar da Alhairi"
"ameen."

Kamar yadda mummy Tace Isha kuka take tun da ta shiga d'akinta take aikin kuka Haisam kuwa Yana kwance hankalin sa kwance Yana waya sa masoyoyar sa, ya sanar da ita su daddy zasu zo gobe, tayi murna sosai harda Yar tsallen ta, Tace "Yanzu bari naje na fad'awa Mom ta sanarwa da Daddy"
"Toh ki bari mu gama wayar Mana tukanna"
"Aaa wallahi za dai muyi waya anjima zanje na fad'a mata"
"Uhmn habibty zumud'i Kenan?"
Cikin muryar Shagwab'a Tace "Toh habib ranar da nake jira Kenan fa kaga zumud'i dole, so kar kaga laifina"
"A a Banga laifin ki ba ko kad'an ni kaina na kosa goben tayi, don a gaskiya ban so auren mu ya wuce Nan sa da 3 Months"
Zaro Ido tayi kamar yana kallon ta tace "Har 3 Months Gaskiya yamin Nisa Habib"
"A hakan yayi nisa? To ya ya kike so ayi?"
"Nan da 2 months dai,kaga dama muna Shirin Exams ne zamu samu hutu Mai d'an tsayi kawai sai ayi"
"To Shikenan hakan za'ayi zan Sanar wa su Daddy idan sun amince Shikenan"
"Zama su amince,yanzu dai bye naji kamar daddy ya Shigo"
"Bye" ta katsewayar, da kanta ta Sanar da dad halin da ake cike Murmushi yayi yace "Yaran zamani ba kunya wato ma zan yi baki Shikenan Allah ya Kai mu goben sai sun Zo"
"To Daddy."

Ma'isha kuwa sai da tayi kuka Mai isarta kana ta fito parlor mummy Tace "Dama yanzu zan Shiga na duba ki Lafiyan ki kuwa?"
"Lafiya Lau Umma"

"Ya naga idanun ki sun Kumbura?"
"Bacci nayi Mummy,an gama abinci?"
Ta fad'i hakanne don ta kawar da maganar ba don tana Jin yunwa ba.
Mummy ta amsa da "Eh an gama,Yau anan Zaki Kwana ba gidan su Abba ba?"
"Eh Mummy sai jibi zan koma chan d'in"
"To Shikenan Allah ya kaimu,zo muje dining d'in."
Chapter 24 · 0% Book details