Sashe 13
Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushin yake tayi Tace "You're safe Mana Yaya, kawai dai naga sai aikin kallon ka take Kuma bata ji dad'in bani abinci a Baki ba, nayi tunanin ma itace auntyn tawa"
Dariya yayi yace "Haba princess ai da kece Zaki Fara sanin hakan,ni ba Soyayya muke da ita ba,hasali ma ban tab'a zaman minti 30 da ita ba"
"Amma fa Yaya Na lura Kamar son ka take"
"ah haba Dan Allah?"
"Allah kuwa"
"Lalle d'an Ni d'in Nan?"
Murmushi kawai tayi yace "Well bani da wannan lokacin Yanzu idan na tashi soyayyar ma ke zansa ki nema min Matar aure"
" Kamar dagaske"
"Allah kuwa dagaske nake miki na rantse miki da kauyen kakana"
Dariya tayi sosai Harda tafi, a Haka suna Hira har suka Isa gida.
Har cikin ranta taji dad'i ko ba komai hankalin ta ya kwanta, tunda tasan ba sonta yake ba, Bata da sauran damu sai na soyayyar sa da fatan ya fahimci hakan.
Suna isa gida suka tarar da su Mummy da Umma shigowar su gidan Kenan Suma, bayan sun gaisa ta wuce d'akin ta Shima Haisam ya wuce nasa d'akin, dake dukkanin su biyu suna da assignment basuyi kallon da suka Saba ba, hatta chat d'in ma basuyi ba.
Haisam na zaune akan gadon sa yana browsing yaga shigowar Kira ba wayarsa kallon time yayi yaga Karfe 11:38pm a bayyane yace "Aysha da Daren Nan?"
Picking yayi ya Kara a kunnen sa daga d'ayan 'bangaren tace "Barka da war haka yallab'ai"
Murmushi yayi yace "Yauwa Barka dai Yallab'iya"
Yar karamar dariya tayi Tace "da fatan dai ba bacci Kake ma tashe ka ba?"
"umm umm ba bacci nake ba, assignment nake yi"
"Oh so sorry na dame ka,duk da ma na ce ka Zama Tutor d'ina kaki ko?"
"No Kar ki damu, ba ki nayi ba ai na fad'a miki idan kin shirya ki Sanar dani"
" To na shirya gobe idan Allah ya Kaiimu"
"To Allah ya Kaiimu"
Ta amsa da "Ameen ya Allah"
Yace "ya kike d'azu kawai Kika tafi ba sallama"
"Uhmnn gani nayi ka fad'a lambun soyayya baka ji baka gani"
Dariya yayi yace "Soyayya Kuma Ni d'in?"
"Eh Mana Kai da princess d'inka harfa abinci naga kae Bata, nace lallai kud'in masoyan asaline"
Girgiza Kai yayi Kamar tana gaban sa yace "Ni ba Soyayya nake ba"
"Kiyayayya Kake yi Kennan?"
"Hahaha a a, to Shima dai d'an uwan soyayyar ne, amma taya za'ayi nayi soyayya da Kanwata?"
Cikee da farin ciki tace " Au dama kanwar kace? "
"Eh kanwatace da me Kika d'auka?"
"Na d'auka budurwar ka ce"
"To ki ajiye Kanwata ce,ai Ni bank da budurwa ban ma tab'a soyayya ba"
"Na dai ji ban yarda ba"
"Allah kuwa trust me ba wasa nake Miki ba,sai dai idan ke zaki nema min Yanzu"
"A a idan Kuma na nema maka waccce Bata maka ba Kuma fa?"
"Zata ma yi insha Allahu"
"To Insha Allah zan nema maka waccce zata dace da kai"
"Da kuwa naji dad'i sosai"
Nan sukayi ta hirar su kusan na mintuna 20 kana ta Masa sai da safe suka sauke wayar a tare, kwanciyar ta tayi yayin da Haisam ya cigaba da abinda yake yi.
________________________
Ba na ganin comment d'inku
Please kuyi sharhi sannan kuyi sharing.
Taku a kullum
Milhat
Yar Terawa
🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
23&24
*...............WASHE GARI*
Kamar kullum a tare suka shiga school tun karfe 7 na safe, Yau Haisam ya Riga Ma'isha Gama lectures hakan yasa ya zauna zaman jiranta a Mango garden na cikin School.
Kiran Aysha ne ya Shigo wayar sa, picking yayi da sallama daga d'ayan 'bangaren ta amsa da "Wa'alaikassalam yallab'ai kana lafiya?"
"Ina lafiya ke fa?"
"Nima haka"
"Masha Allah ka Shigo kuwa?"
"Eh na Shigo"
"Ok please kana ina ne nazo na same ka"
"Ina mango garden"
"Okay muna kusa ma gani Nan karasowa"
Ya Masa da " okay" ya kashe wayan.
Girgiza Kai Aysha tayi Tace "Qawata Kinga bawan Allan Nan, Yana da wani habit d'in da bana so wallahi"
"Me Kenan fa?"
"Bai tab'a Kirana ba tunda Amma idan na kirasa shi yake fara cutting call d'in which is very bad" ta karasa maganar kamar zatayi kuka.
Mardiya Tace "It's not a big deal qawata tunda in Kika kirasa yana d'agawa Kuma yana sauraron ki ai Shikenan Kuma Nan gaba da kansa zai Rika neman ki"
Huci tayi tace "Shikenan tunda kince Haka shiyasa a ko wani lokaci idan ina bukatar shawara Kai tsaye ke nake nema nasan zan samu solution"
" I will always be here for you Qawata,yanzu dai tashi kije ki same shi before it's too late"
Aysha tace "I thought tare zamu"
"A a kaaai, kamata ai daga ke sai shi zaki fi fahimta" ta kashe mata Ido d'aya,duka Aysha ta Kai Mata ta kauce.
Mikewa tayi ta Masa sai anjimu da jaddada mata idan ta gama zata kirata sai su koma gidan tare,tayi tafiyar ta, ba d'au lokaci mai tsawo ba kasantuwar LT d'in da take da mango garden ba nisa hakan yasa tayi saurin Isa inda yake.
Da sallama ta karasa inda yake bayan sun gama gaisawa Nan ya mata umarnin da ta fito da handouts d'inta, Nan ya zari d'aya ya Fara mata tutorial d'in sunfi awa d'aya yana mata, Amma fa hankalin sa na Kan wayarsa minti minti yake dubawa daga bisani Tace "Akwai abinda kake jirane? Naga sai faman duba time kake"
"Hmmm eh, Time nake dubawa kar princess tayi ta jirana karfe 3 zata gama lectures"
Tab'e baki tayi Tace "Wai dole Kai Zaka kaita gida ne?"
"Eh Mana to wa zai kaita in bani ba?"
Ganin yanayin sa ya canza tayi saurin fad'in "Lallai kana ji da ita sosai Naga karfe 2 yanzu da sauran time ai"
Yace "Eh gashi wayata ta kusa d'aukewa ba chaji Kuma na baro cable a gida Dana saka a mota, kar ta Kira bata same Ni ba"
Ta amsa da "Hakane"
Yace "Anyways mu cigaba ko?"
Ta amsa da "Toh"
Nan ya cigaba da Mata tutorial d'in, ganin hankalinsa yayi nisa a abinda yake koya Mata tasa hannu ta kashe wayar tasa sannan ta maida ta ajiye.
Sun dad'e a zaune a gun ya d'auki wayar sa ya Danna yaga a kashe tsaki yayi yace "Damn it!!!"
Tace "Lafiya kuwa?"
Yar karamar tsaki yayi yace "Wayar ta d'auke"
"In time ne bari na duba maka a wayata"
Yace "Yauwa please duba min."
Aysha na duba time taga karfe 3 da kwata Tace Masa "2:30"
Zaro Ido yayi yace "Wai tun d'azun Nan 30 mints kawai mukayi?"
Tace "Eh"
"Lallai time baya gudu"
"Ko dai ka gajine? Mu bari sai gobe?"
"A a kar ki damu mu cigaba kawai."
Murmushin kyeta tayi ba tace Masa komai ba ya d'aura daga inda ya tsaya.
Ma'isha tafi minti 20 tana jiran sa, Kiran wayarsa take Amma switch off sai ta tuna tana da Number Farukh ta shiga dialling har kusa yankewa ya d'auka cikin Muryar ta mai dad'in sauraro Tace "Ya Farukh ina wuni?"
Ya amsa da "Lafiya"
cikin Muryar bacci, Tace "Am sorry kana bacci na tashe ka ko?"
Yace "Eh wallah but kar ki damu ya akayi?"
"Dama na d'auka kuna tare da Yayana ne"
"A'a mun rabu tun d'azu da mukayi sallar azahar but yace min zaiyi wa Aysha tutorail but ki kirasa ki ji"
"Uhmn number a kashe, Amma Bakomai nagode sai anjima" ta katse wayar tayi ba tare da ta ji amsar sa ba.
Girgiza kai yayi yace "kishi kumallon Mata, Amma guy d'in nan don ya raina min hankali yace min ba Soyayya suke da Ma'isha ba mtss" ajiye wayar yayi ya koma baccin sa, Ma'isha kuwa Mango garden ta nufa dake tasan wurin zaman sa Kenan yawanci.
Tun daga nesa ta hango su suna zaune dai dai lokacin da Aysha take dariyan sunan wani scientist da ya fad'a dariya take sosai Shima ya fara taya ta a Fili Tace "Tutorial d'in kenan" har ta nufi inda suke sai Kuma ta Canza shawara ta koma, gate na makarantar ta nufa tana fita ta tari napep ta wuce gida, ita kanta taji ta wani iri sabida shine karo na farko da ta shiga napep sannan shine karo na farko data Koma gida ba tare da Yayan ta ba.
Kiran sallah da akayi ne Haisam ya Mike a zabure Aysha ma mikewa tayi tace "Lafiya?"
"Kamar kiran sallah fa nake ji?"
"Eh Kiran sallah ne"
Ajiye Mata handout d'in yayi da saurin ya bar gun ba tare da yace mata komai ba, baki bta bud'e ta tsaya kallon sa har ta daina ganin sa bata bar mamaki ba, wa'anda suke zaune a gefen su Kuma suka tsaya kallon ta, tsaki tayi ta wurga musu harara da sauri suka kau da kansu Tace "magulmatan banza kawai Mtssw" ta d'auki Jakarta da handout d'in da Haisam ya ajiye ta bar gun.
Ma'isha na Isa gida ta tarar da su Mummy suna part d'insu Umma, hamdallah tayi ta shiga d'akin ta wanka ta fara yi ta d'auro alwala bayan ta idar da sallah ta kulle kofar d'akin ta kana ta kashe wayarta ta kwanta taso yin bacci ta kasa ta dad'e a haka kamun bacci ya d'auke ta.
Haisam wurin motar sa ya nufa duk a tunanin sa tana jiran sa, ganin bata Nan yace "to ina tayi ne?" Sa hannu yayi a Goshen sa yana ta waige waige bai ganta ba sai Kuma yace "Maybe bata zo ba nasan dai zata jirani"
Daga bisani ya shiga Masallaci don yin sallah, har ya idar ya dawo Bata Nan Zama yayii a motar har wuri ta Fara duhu, tsaki yayi ya jaa motar yabar gun.