← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 55

Sashe 37

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya tayi had'e da fad'in Alhamdulillah, sauke wayar tayi daga kunnen ta suna tambayar ta Amma ta kasa basu amsa key d'in motar ta fizge daga hannun Mardiya ta fad'a cikin motar baki a bud'e Duk suka tsaya kallon ta, ganin ta tada motar Kuma tana niyar tafiyane sukayiw saurin Shiga motar su ma. Suna Shiga ta fizgi motar da wani mugun speed.

"oyoyo oyoyo Yarana" da gudu suka nufi inda mummy take suka rungume ta , Zama sukayi, Mummy kallon sa tayo Tace "Haba Auta baza kamin magana ba?"

Turo baki yayi kana yace "Ai ni bakya Sona Su Sister Aymana da Aima kawai kike so"
"Kai ma ina sonka nama fi sonka Akan kowa, kazo muje na baka chacolate"
Jin an ambaci sunan chacolate da gudu ya nufi inda take, hannun sa ta rike, d'akin ta suka shiga Aymana da Aima na biye da su chacolate da Biscuits ta Basu kana suka fito, Channel ta Canza musu Tasa Nicklodeon suna ganin favorite channel d'insu ki wannen su ya samu gu ya zauna suka cigaba da kallon su.

Mummy ganin Umma tayi shiru hakan yasa tace "Umman Yara lafiya dai ko? Ya na ganki haka?" Cike da kulawa take tambayar ta.

Gyara Zama Umma tayi kana Tace "Uhmn Mummy Yara ina cikin damuwa Wallahi"
"Sanar dani mene ne kuma ya faru?"
"Yarinyar Nan Ce tazo har gida wajen Daughter"
" Wace yarinya Kenan?" Mummy ta tambaya cikin rashin fahimta.

Umma Tace "Aurajy Yar gidan malam Hassan"
Zaro Ido mummy tayi tace "Ayrah kuma tare da Isha? Amma kin tabbata ita d'in ce?"

"Kwarai kuwa ga Nan kamannin uwarta na gane ta"
"Allahumma ajirni fii musibati, to ita Ma'isha me ya had'a ta da tsinanniyar yarinyar Nan? "
"Allahu a'alam na biyo tane don naji dalilin zuwan ta har gida ta same ta, a ina take nema banji motsin ta?"
"Ha'aa ai na d'auka suna chan sabida ba ta dawo ba"

"Ikon Allah ko ta wuce asibiti ne?"
"Anya yau ai tana off"
"Shikenan Duk inda taje zata dawo ta same ni inji dalilin ta na magana da shaid'aniyar yarinyar Nan, da har zata zauna inuwa d'aya da ita" tana maganar cikin tsananin 'bacin Rai.

Umma Kam kasa magana tayi, don ta ma rasa abinda zatace.

"Rabi Anya kina tsoron Allah kuwa? Anya kina so ki Gama da duniya Lafiya kuwa? Shin kina son Shiga aljanna kuwa? Karfa ki manta cewar aljannar ki a karkashin kafata yake, Wallahi sai in take ta muga yanda zakiyi"

"Mtsww kaga malam Dan Allah Kar ka Dame ni kaji ko kazo ka tsaya akaina kana damina da surutu"

Nuna kansa yayi cike da mamaki yace "Ni Rabi? Ni malam Hassan kike fad'awa haka? Kar ki manta fa ni mijin ki ne"
"Kai ka sani don ni Wallahi na dad'e da daina kallon ka a matsayin mijina idan kana son kwanciyar hankalin ka a gidan Nan ka sauwake min na tafi gidan mu"

"Na fad'a miki bazan sake ki ba, Wallahi ko mutuwa zakiyi bazan rabu dake ba in ko Kika bar gidan nan to ki sani ban yafe miki ba, Wai ma shin kin San hukuncin Matar da ta nemi Mijinta ya sake ta kuwa?"

"Ayyirriiiiiii har Kai ka Isa ka nuna min sanin Allah me ka sani a game da adddin ka, da ka sani baza ka Rika aikata abubuwan da kake ba"

"Oh kina nufin ni jahiline Kenan ko?"
"To me banbancin?"
"Oho Wannan Kuma kai ta shafa, Dan Allah idan ka gama ka fice min daga d'aki"
"Naji zan fita Amma ina bukatar ki yau a turaka ta"
"Allah ya sauwake na had'a jikina da naka, a Bayan ma ban San abinda kake aikatawa bane yasa na saki jikina da kai"

Kasa kasa yayi da murya yace "Rabi kiji tsoron Allah tun lokacin da yaron Nan ya Shiga comma kika kaurace min, ya kike so nayi ne Dan Allah Kar ki manta Ina da hakki fa Akan ki"
"Kaje chan inda aka saba baka karb'a idan Kuma kaji haushi Kaje ka kara Aure mtsww" ta cigaba da kallon da take, kallon ta ya tsaya yi kana yace "Zanyi maganin ki dani kike zancen" Yana kaina ya fita.

Da d'an karfi Tace "Do your worse, d'an halak ka fasa, tasan yaji abinda tace Amma yayi kamar bai ji ta ba, fita yayi daga gidan gaba ki d'aya Bai Kai awa d'aya ba ya Dawo tare da wata yarinya wacce baza ta wuce sa'ar Ayrah ba, a lokacin Mamy ta fito parlor Suna Kallo da ita da Nabila, Faisal da Sunusi kannen Ayrah.

Malam hassan har cikin parlor suka Shiga da yarinyar , Mamy ko kallon inda suke batayi ba bare ya dame ta, Nabila ce tabi su da Kallo har suka haura sama sai da suka Shiga d'aki Nabila tace "Mamy Wace ce wanchan suka shigo tare suka da daddy?"
"Kije ki tambaye shi mana, ba uban ki bane"

Faisal yace "A gaskiya Mamy Wannan cin fuskan yayi yawa, har cikin gida daddy ya fara kawo Yan matan sa Bayan maganganun da muke ji a unguwa yana zubar Mana da mutunci Mana"

(Yaran Malam Hassan guda hud'u ne, Ayrah sai Nabila da take binta sai Faisal sannan karamin cikin su Sunusi).

Kallon su kawai Mamy take batace musu komai ba, Nabila Tace "Mamy Yanzu Dan Allah haka zamu zubawa baba Ido yana abinda ya ga Dama a gidan nan?"

"Nabila!!! Nabila!!! Nabila!!! Sau nawa na Kira sunan ki?"
Kai a kasa Tace "Sau uku Mamy"
"Good idan Kika sake min maganar uban ku Wallahi tallahi sai na miki baki, ba ke Kad'ai ba har daku" ta karasa maganar tana nuna Faisal da Sunusi.

Mikewa tayi ta shige d'akin ta, kallon juna su sukayi sannan ko wanne su ya Shiga taitayin sa.

Isha gudu take sosai, tana driving d'inne ta Sanar musu da cewar Haisam ya farka.
_________________________
Please comment and Vote
Milhaat Ce
Yar Terawa
[7/13, 8:42 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page

55&56
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

```Continuation........``` Su Ma'isha na Isa asibitin fita tayi ba tare da ta kashe motar ba, gudu take sosai har ta isa ICU Dr Ali ta gani yana kaiwa yana kawo wa murya na rawa Tace "Dr Ali ina yake? Yana ciki ne?"

Kan ya Bata amsa da sauri ta kusa kanta cikin d'aki Meerah, Ayrah da Mardiya Suma suna kokarin Shiga ciki yayi saurin d'aga musu hannu had'e da fad'in "A a please ku jira ta anan" sai yabi Bayan Isha.

Isha inda ake Canza Kaya ta nufa ta cire takalmin ta,ta sanya Wanda ake Shiga cikin ICU dashi, da sauri tayie inda Haisam yake, ganin Haisam tayi yana rarraba idanu yana son gane inda yake Isha tsuman tsaye tayi tana kallon sa, suna had'a Ido dashi ta masa Murmushi shima Murmushin ya mata sannan ya rufe idanun sa.

A dai dai Nan Dr Ali ya Isa inda suke fuskar Haisam ya kalla cikin kid'ima ya nufi kansa duba nakurar da ke Kan Haisam ya Shiga yi ajiyar zuciya yayi ya fita, Isha ma tabi Bayan sa.

Sai da suka fita waje tace "Dr ya naga Kuma ya rufe idon sa?"
Ya amsa da "I don't know isha, ban San ya akayi hakan ya Faru ba, baifi mintuna 30 da farkawa ba fa, ina ganin ya farka na Kira ki"

Dafe kanta tayi Tace "This is not what I asked you Dr meyasa ya rufe idanun sa?"
Kallon ta yayi kana yace "I don't know and I just told you that, look Isha hakan na faruwa dama Kinga Kenan akwai alamun ya kusa ya Dawo"
Cikin murya Mai d'an kara tace
" What? Kana nufin ya sake Shiga comma ne?"
Kai ya d'aga Mata alamun eh.

Jiki a Sanyaye ta zauna a kasa hawaye d'aya na bin d'aya daga nesa suka hango su da sauri suka karasa gun, Meerah ce take kokarin d'aga ta Amma ta kasa hakan ne yasa Ayrah tayi saurin riko ta, Ma'isha da dukkanin karfinta ta ture ta har sai da ta Fadi a kasa
cikin zafin nama Ma'isha ta Mike cikin tsawa tace "How dare you Ayrah? Who gave you the audacity to touch me?"

Meerah baki a bud'e take kallon Isha don Bata tab'a ganin 'bacin ran Isha har haka ba, cikin sanyin Murya Meerah Tace "Isha calm down please,muna asibiti ne fa ki duba kiga kin sa ana ta kallon mu"

"A kalla Mana I don't care,gara su kalle mu su san cewa akwai Mutane mugaye azzalumai kamar Ayrah a dalilin ta na rasa d'an uwana kuma masoyina ta rabani dashi,Kuma kice min I should calm down?" ta karasa maganar cikin kuka.

Meerah Tace "Na sani Isha Amma kiyi hakuri Insha Allah, Allah zai bashi Lafiya,but ba Kince ya farka ba?"

"Eh ya farka don har na kalli cikin idanun sa Amma ya sake rufe idanun sa,Ayrah bazan tab'a yafe miki ba Idan wani abu ya sami Ya Haisam"
Chapter 37 · 0% Book details