← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 55

Sashe 36

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meerah Tace "hmm And what if we decide not to Forgive? Look idan baku da abin fad'a muna da abinyi"
Ayrah Tace "Meerah ko kad'an Banga laifin ki ba, kina da right d'in da zaki Fad'i ko ma mene ne sabida an cutar dake, har ga Allah ko nice aka min haka da na dad'e da d'aukan mataki akai but please have a second thought on this"

Mardiya Tace "Hakane zancen ki gaskiya ne Ayrah, and Isha please Kar laifina ya shafi Yayan Wallahi yana cikin wani hali bazai jure rashin ki ba"
Murmushin gefen baki Isha tayi kana Tace "Da nayi niyar fasa auren nasa Amma zuwan ku yasa na Canza shawara zan auri Yayan ki Amma fa da sharad'i idan kikayi abinda nake so ina mai tabbatar miki da cewar bakina da Ma'aruf ranar Friday mai zuwa babu abinda zai sa a fasa shi sai dai in bana numfashi"

Ajiyar zuciya Mardiya tayi kana Tace "Insha Allah Koma mene ne zanyi Wallahi"
Meerah Tace "har da rantsuwa da dai ki bari kiji bukatar ta kamun nan ki rantse ko da yake ma baki San illan sa ba mtsww"
Ayrah Tace "Isha Insha Allah zamuyi dukkanin abinda kukace muyi, ina da na sanin abinda na aikatawa d'an uwana na jini, na bi hud'ubar mahaifina sannan nayi amfani da maganganun sa na karya da gaskiya, a dalilina Ya Haisam ya kusa rasa ransa yana neman Almost 3 years kenan a kwance, bazan tab'a yafe wa kaina ba" ta karasa maganar cikin kuka.

Isha Tace "Uhmn Haka Allah yaso kuma shima insha Allah zai farka ko ba yanzu ba"
Ayrah Tace "Allah yasa"
Duk suka amsa da ameen.

Mardiya Tace "Isha ina sauraron ki mene ne sharad'in naki?"
Isha kallon Meerah tayi, Meerah ma ta kalle ta Yar karamar dariya sukayi Wanda na kasa gane dalilin dariyar tasu, hankalin Ayrah da Mardiya yayi mugun tashi, kallon Kallo suka Shiga yiwa juna, Turo kofar da akayi ne yasa dukkannin su kallon kofar don ganin Wanda ya turo kofar.

Kuyi hakuri da wannan please,ba yawa,haryanzu jikin ne ba dad'i, dakyar nake samun Daman typing d'in, nagode sosai da Addu'oin ku.
_________________________
Masu tambayar complete d'in littafin Nan babu sabida 6th/01/2022 na fara typing, sabon littafine am just typing it.
Ina Jin dad'in yanda kuke son book din Allah ya bar Kauna.

Milhaat ce
Yar Terawa
[7/7, 10:02 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page

53&54
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

```Continuation......``` Da gudu suka shigo d'akin suna fad'in "Umma kin ganta ko, mun fad'a miki bata tafi ba" Aymana da Aima ke Wannan maganar.

Umma dake biye dasu Yar karamar dariya tayi had'e da fad'in "Eh lallai Kun fini Gaskiya" kallon inda Isha ta ke tayi Tace "Daughter Kince min Zaku fita Ashe Kuna Nan?"
"Eh wallahi Umma, munzo fita ne muka had'u da Mardiya da Ayrah"
Umma jin ta ambaci sunan Ayrah hakan yasa tayi saurin kallon inda suke, tana ganin fuskar Ayrah ta gane fuskar ta sabida tana Kama sosai da mahaifiyar ta.

Jiki na rawa suka durkusa har kasa a tare suka ce "Ina wuni?" A d'an yasine ta amsa da "Lafiya" riko hannun Aima da Aymana tayi suka fice daga d'akin, jiki a Sanyaye suka koma ma zaunin su, Meerah dad'i taji wani irin Murmushi tayi Mai d'an sauti.

Isha Tace "As I was saying zan auri Yayan kine on one condition, and the condition is zamuje inda kuka binne Wannan layan ku kona shi da hannun ku"

Ayrah zaro ido tayi tana kallon Isha Tace "Amm.... Amma ai... " Sai Kuma ta kasa karasa maganar da take son yi Isha Tace "Amma me"
Cikin Murya Mai sanyin Tace "Babu komai"
A zuciyar ta Kuma Tace "Ya Rabbi ya zanyi zasu ruguza min shiri gashi yanzu ina son Haisam sosai" muryar Meerah taji tana fad'in "Kunyi Shiru? Bazaiyu bane?"

Mardiya Tace "Me zai Hana yanzu ma sai muje in Kun shirya"
Mikewa Meerah tayi had'e da fad'in "Good Sai ku tashi muje bari na Shiga kitchen nasha ruwa" sai ta fice.

Isha, Ayrah da Mardiya fita sukayi suka tsaya a katafaren compound na gidan suna jiran fitowar Meerah , fitowa tayi hannun ta d'auke da jakar ta tana wasa dashi ta karaso inda suke Tace "Muje ko?"

Tafiya suke ganin Su mardiya da Ayrah sun nufi motar su cikin Muryar fad'a Tace "Excuse me ina Kuma zaku? Wai Kuna nufin motar ku zamu shiga Bazaiyu ba"

Ayrah Tace "Uhmn to kin San inda aka binne abin ne? Idan kin sani to bismillah mu shiga motar taku"
Kawar da kanta kawai tayi Isha Tace "Meerah you know they are right let's use their car"
Meerah Tace "Oh stop it please Duk abinda sukace sai kice they are right? Ai mu ba baki bane a garin ko? Gombe fa garin mune anan aka Haife mu so zamu sani"

Mardiya Tace "zaiyi wuya kusan gun gaskiya Amma babu komai mu yi amfani da motar taku sai na Rika nuna muka hanya"

Isha Tace "A'a ai wannan wahalane goma da ashirin muje kawai" jaan hannun Meerah tayi tana bata hakuri dakyar ta shiga motar, Meerah da Isha a baya suka zauna Mardiya ke jaan motar sai Ayrah a kujerar Mai zaman banza, fice wa sukayi daga gidan suka kama hanya.

Tafiya suke Babu Wanda ke magana da d'an uwan sa, Meerah ganin tafiyar taki karewa Tace "Irin Wannan tafiya haka kamar zamu bar gari are we safe?"

Murmushi Mardiya tayi kana Tace "Of course you're safe, kusa da makabarta ne"
Zaro Ido Isha da Meerah sukayi a tare suka ce "Makabarta dai?"
Ayrah Tace "Eh Makabarta" shiru sukayi basu ce komai ba, ko wacce da abinda take tsakawa a ranta, a Haka har suka Isa gun.

A bakin hanya sukayi parking motar su, kana suka Fara Shiga wani daji sun d'auki tsawon mintuna 20 suna tafiya mardiya ce Tace "Mun iso ganan gun" tana nuna gun da d'an yatsan ta.

Meerah Tace "kin tabbata Nan ne?"
"Eh Nan ne"
Isha Tace "But ya akayi Kika gane gun shekara kusan bakwai Kenan fa ko?"
Ayrah tace "da wannan bishiyar muka gane shiyasa muka binne a karkashin bishiyar"
Isha girgiza kai tayi alamun ta fahimta had'e da fad'in "Oh."

Ayrah Tace "To yanzu ya zamuyi mu tona Ni shaf na manta ma da Mun d'auko ko da wuka ne"
Meerah Tace "Worry Not na d'auko" had'e da zaro wuka a Jakarta ta mikawa Ayrah, Ayrah hannu tasa ta karb'i wukan tana juyashi tab'a Kara kallon wukan tace "Mardiya gashi ki tone"
Tana Mika mata wukan, banka Mata harara tayi Tace "Kila kin manta ko,kece Kika binne Kuma kece zaki tona shi bani ba"

Girgiza kai tayo ta Mika Mata Jakarta da durkusa ta Fara tonawa, tono take yayin da su Kuma suna tsaye suna kallon ta, har sai da ta fara jin alamun abu a kasan ta ajiye wukan ta sa hannun ta tana kokarin cirewa, Isha da Meerah ganin abinda ta Ciro suka jaa da baya a razane, ajiye shi tayi Kana tace "Gashi Nan" had'e da kakkab'e Hannayen ta.

Isha cike da tsoro Tace "Me nake gani haka kamar kad'agare, sannan kamar alluraai ne a jikin sa?"
Ayrah Tace "Eh hakane"
Meerah Tace "Duk tsawon shekarun Nan Amma bai Rub'e ba ya akayi haka"
Mardiya Tace "Eh bazai rube ba sabida abubuwan da akayi amfani dashi, inda ya Rub'e to zai daina sonta ma'ana asirin ya karye Kenan Kuma ba abu bane Mai sauki"

Meerah Tace "Lallai asiri Gaskiya ne"
Mardiya Tace "To gashi nan Mun cire what's next"
Isha Tace "Burn it" Ayrah ji tayi gabanta ya Fad'i, "Bazan tab'a bari ku 'bata min shiri ba" a zuciyar ta take maganar a bayyane Kuma Tace "Dame za'a Kona?"

Mardiya Tace "I wonder"
Ayrah Tace "Mu tafi dashi kawai in yaso idan na Koma gida zan kona"

Meerah charab ta karb'i maganar Tace "Tabd'i kalle mu dakyau ce Miki akayi mu illiterate ne? To da ilimin mu, shiyasa ma na kawo wukan Nan, da Kuma ashana" tana maganar ta sa hannu ta ciro Ashana, ta wurga Mata.

Yar karamar dariya Isha tayi Tace "Inayin ki Qawata" tafi Sukayi suna dariya meerah Tace "Ooops I almost forgot ganan kerosene sai yafi konewa" ta Mika mata dariya suka Kuma yi.

Ayrah gaba ki d'aya taji hankalin ta ya tashi ba don ta so ba jiki na rawa ta zuba Kerosene akai kana ta kunna ashana ta wurga akai sai da ya kone kurmus kana suka bar gun, kan su Shiga mota wayar Isha ya Fara ringing.

Ganin Dr Ali (likitan dake kula da Haisam Kenan) hakan yasa tayi saurin picking murya na rawa ta amsa daga d'ayan 'bangaren yace "Good News,Haisam ya farka Yanzun Nan ya bud'e idon sa."
Chapter 36 · 0% Book details