Sashe 3
Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Banda tari babu abinda mahaifiyar Haisam keyi, cike da tausayi yace "Ki kimsa ta ku fito" hannun Haisam ya riko, sannan ya cewa Ma'isha "Daughter zo mu jira su a mota" ba musu ta bi bayansu,suna isa inda motar take yace haisam ya zauna a gaban motar,shi Kuma ya zauna a gun zaman driver,Ma'isha Kuma tazauna a baya.
Bayan mummy ta gama gyara ta, da taimakon Mummy da Ma'isha suka sa Umma a mota, Kai tsaye asibiti suka nufa, likitoci sunyi matukar jajincewa wurin kula da ita hakan yasa acikin Yan kwanaki ta samu sauki kamar ba ita ba.
Wata rana Mummy ta kaiwa Umman Haisam ziyara, zaune suke suna Hira zuwa yanzu sun saba sosai, Nan take tambayar ta dalilin da yasa haryanzu bata biya wa haisam Kud'in WAEC ba, Bata 'boye mata ba ta Sanar da ita cewar Mijinta guba aka sa Masa a abinci da yanda kanin sa kwace Masa dukiya, ta tausaya musu sosai, a haka har suka gama hirar tasu ta dawo gida.
Cikin dare ta kasa bacci, tashin Daddy tace "Am sorry na katse maka bacci" Zama yayi cikin muryar bacci yace "Kar ki damu,me ya Faru?" Nan ta shugay fad'a Masa Labarin da Umma ta bata, bayan ta gama basa Labarin ne tace "Darling ina so mu taimaka wa haisam da mahaifiyar sa"
"Ina sauraron ki"
"Me zai Hana tunda Boys Quarters d'in Nan babu kowa aciki a Basu part d'aya su zauna, Naga jikin nata bai gama warwarewa ba, sannan Ina so a biya wa Haisam WAEC"
Murmushi yayi ya riko hannun ta yace "Madallah da samun mace kamar ki a rayuwa, tabbas ke d'in rayuwa tace, Maryam Allah ya Miki Albarka, a irin Rayuwar da muke ciki yanzu kowa kansa ya sani Amma ke kullum cikin taimakawa na kasa dake kike"
Murmushi tayi Tace "To mijina mene ne amfanin Kud'in namu? Idan baza mu taimakawa na kasa damu ba,Kuma na lura Ma'isha tana so a taimaka musu ne kuma ina matukar son farin cikin ta,nasan idan taji Haisam zai dawo gidan nan kuma taji za a biya Masa WAEC zatayi matukar farin ciki"
" Hakane Yar Albarka,Halin ki ta d'auko tana da tausayi sosai,ga son mutane"
"Kaji ka da wani zance kai ta d'auko dai"
"Zancen kike so,yanzu dai naji dukkanin maganar ki, Kuma zanyi yanda kike ce, Kuma Insha Allah zan rike Haisam tamkar d'ana, da niyata gidan nasu nake so a gyara musu"
"A a tun da ga nan Kuma gidan ya mana girma mu kad'ai, su dawo Nan kawai"
"To ba matsala, idan Allah ya Kai mu gobe zanje makarantar tasu na biya Masa, sannan ina so kije gidan ki d'auko mahaifiyar Haisam d'in, ban yarda ta 'dauko komai ba, Zan tura miki Dubu d'ari biyu, ki saya mata kaya, idan na nadawo zamu fita da Haisam d'in Shima na Masa sayayya"
Farin ciki da Murna yasa ta rungumi mijinta had'e da yi masa godiya, a haka sukayi bacci.
Washe Gari
Daddy Kan yaje gun aiki ya biya ta makarantar su Haisam ya biya masa Kud'in WAEC harda NECO.
Mummy na fad'a wa Ma'isha maganar da suka tattauna Akan Haisam da Umma tayi farin ciki sosai harda tsalle, tayi ta musu godiya da musu addu'a Wanda ya dace d'a yayiwa iyayen sa.
Tana Isa school a kusa sit d'in Haisam ta zauna, tunda ta lura shi d'in ba mai son magana bane Hakan yasa sai ya kulata take kulashi.
Principal ne ya shigo yana Kiran sunan wa'anda basu biya Kud'in WAEC d'in su ba, ga mamakin Haisam har aka gama ba a kira sunan sa ba, hannu ya d'aga yace "Excuse me sir!!!
Yace "Yes"
Mikewa yayi yace "I haven't paid and you didn't call my name"
Cike da mamaki yace "You didn't pay? What's your name?"
"Haisam Ahmad Umar"
Ya shiga dubawa Bai ga sunan Haisam ba Yana duba list d'in wa'anda suka biya yaga sunan Haisam yace "Mr Man you already payed"
Cike da mamaki yace "I payed? But sir please can you check the date of the payment for me?"
"Sure"
Yana dubawa ya Maida kallon sa ga Haisam yace "It was payed today"Yana Kai Nan ya sa wa'anda basu biya ba a gaba har Saida ya kai su bakin gate ya jaddada wa Mai gadi Akan Kar ya bari su shigo ya koma ciki.
Haisam mamakine ya rufe, a zuciyar sa yake fad'in "Wa ya biya min Kud'in nan?" Da sauri ya d'ago kansa ya kalli Ma'isha ita ma kallon sa take, murya kasa kasa "kin San wani abu Akan haka ko?"
Kai ta girgiza Tace "Ni ban sani ba" ta karasa maganar tana rufe bakin ta alamun dariya take son yi.
Cikin sanyin murya yace "Ma'isha Please"
Tace "Daddy ne ya biya"
"Dan Allah dagaske?"
"Uhmn gashi ka gani"
"Amma....... "
Shigowar malamin sune ya Hana shi karasa maganar da yayi niya, suna fita break ya Shiga neman ta bai ganta ba, Murmushi yayi yace "Alhamdulillah Allah na gode maka, yau Dole. Naje gidan su Ma'isha da Umma muyi musu godiya"
Ma'isha da tun d'azu take tsaye a bayan sa tayi gyaran murya Tace "Anya zuwa gidan mu zakuyi ko Kuma Zaku koma gidan mu?"
"Hmm zuwa Zamuyi dai"
"Za dai ku koma gidan mu"
"Ban fahimce ki ba?"
"zaka fahimta idan driver yazo sannan ko ka gudu zamuje har gida mu d'auko ka" tana kainan ta ruga a guje, Yana Kiran ta Amma ina tayi nisa.
_____________________________
Please comment and Share 🙏🏻🙏🏻
Milhat ce
Yar Terawa
🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
7 and 8
Haisam duk a kage yake a tashi sabida shi Sam bai fahimci Ma'sha ba, bayan an tashe su ne ya shiga neman ta, ai kuwa yana hangota da gudun sa ya nufi inda take Tana ganin sa tayi Murmushi, ya "Ma'isha wai me ke faruwane?"
Cikin muryar dariya Tace "Ga Nan driver yazo" shiga tayi ya tsaya Yana kallon ta, ganin baida niyar shiga Tace " Haisam come in Mana"
Ba musu ya shiga.
Bayan ya gaida driver ya Maida kallon sa gare ta, yace "Ma'isha please tell me Mana"
Dafe kanta tayi Tace "Ya Salam, Haisam Dan Allah ka kyaleni Idan muka je gidan zaka ga koma mene ne."
Gyara Zama yayi yace "Tell me something Ma'isha"
"Uhhmnn ina jinka"
"idan Kika fada min mutuwa zakiyi ne kome?"
"A a ko 'daya baza ka mutu ba"
" So tell me"
" No I won't."
Cikin muryar dariya driver yace "Haisam ga naci, Ma'isha Kuma taurin kai to duk kuyi hakuri in muka koma gidan zakaji Kan zancen"
"Hakan na nufin kaima kasan abinda ke Faruwa kenan ko?"
"A a ba abinda na sani nikam"
Girgiza kai yayi babu Wanda ya furta komai har suka Isa, Kai tsaye parlor suka nufa, Haisam duk ya kasa sakin jikin sa, ganin Umman sa a zaune a gun yasa mamaki ya rufe shi.
Cike da mamaki yace "Umma kina kema Nan aka kawo ki?"
Murmushi tayi, Mummy tace "Eh Nan aka kawota"
Tsosa keya yayi ya durkusa ya gaida su,Daddy dake zaune yayi Murmushi ya amsa ba yabo ba fallasa.
Yace "Tashi ka zauna akan kujera"
Kai ka sa yace "A a Alhaji Nan ma yayi"
Murmushi yayi yace "Haisam wannan umarni ne, ba shawara ba ne ba."
Tashi yayi ya zauna gyaran murya yayi yace "Haisam naji tarihin ka, mahaifiyar ka Bata boye Mana komai ba hakika na tausaya muku, sannan na nemi ganin kune sabida ina so ku dawo Nan da Zama,sannan zan dauki nauyin karatun ka daga yanzu har Allah yasa ka gama"
'daga kansa yayi da sauri ya kalli Daddy sannan ya Maida kallon sa ga Umma, 'daga Masa Kai tayi alamun eh, a zuciyar sa yace "Wato Umma ta ta San da zancen"
Gyaran murya Daddy yayi ya daura da fad'in "Nayi maka alkwarin zan dauke ka a matsayin d'an da na Haifa da ciki na, sannan kofa Bud'e take duk Sanda kake neman wani Abu kar kaji tsoro ko shakkar tinkarata ko Maryam"
" Nagode Alhaji Allah ya saka, ya biya ka da gidan aljanna"
" Umm Haisam, daga yanzu bana so na sake ji ka kirani da alhaji, ka Kirani da Daddy kamar yadda Ma'isha take kirana kaga Kenan Ma'isha ta samu wa"
" To Alhaji, auu daddy nagode"
Duk sukayi dariya, Maida kallon sa yayi ga Ma'isha yace "Daughter kuje kuci abinci, don zamu fita da Haisam din"
Mikewa tayi Tace "Ya Haisam Tashi muje ko?"
Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayanta, Umma tace "Alhaji, hajiya nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, ban San wani irin godiya zan Muku ba"
Mummy Tace "haba ke kuwa tun dazu fa kike ta godiyar nan, ya Isa haka, mu Dan Allah mukayi ba don komai ba, sannan mun lura akwai shakuwa a tsakanin yaran Nan Baki ga yanda ta tada Mana hankali ba nikaina mamaki ne ya kamani"
"Ikon Allah, Amma ni Haisam bai tab'a min maganar ta ba ko da da wasa ne"
"Ai bazaiyi ba don na lura Haisam na da zurfin ciki"
Murmushi tayi tace "haka yake kamar ubansa"
Alhaji dake Danna wayar sa, jin ta ambaci uban sa, yace "Yauwa please a ina baffan Nan nasa yake?"
"Ya Nan cikin garin Nan"
" Kina nufin cikin garin Gombe?"
"Eh"
" Abun zaizo Mana da sauki insha Allah"
Mummy da Umma a tare sukace
" Allahu yasa"
Ya amsa da amin ya daura da fad'in "Maryam ku samu kuje shopping din Nan kar dare yayi, sannan please kar su d'auko komai a chan, za a Saya musu duk abubuwan da suke bukata, sannan idan kudin Bai Isa ba ki Kirani"
Ta amsa da "to Alhaji"