← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 55

Sashe 50

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Isha yayi sai ya maida kallon sa ga Mummy alamun kisa baki Mana, Murmushi Mummy tayi tace "Maman Yara ayi Hakuri a barta ta kula da Yayan ta"
Umma dariya mummy ta bata data Kira ta da Maman Yara , sunane da suke Kiran junan su ita da Mami, Abba yace "To tunda Tace zata iya a barta Mana, ko ya kace Yaya?"
Yana maganar Yana kallon Daddy, Daddy yace "eh a barta kawai"

Umma Tace "Kuna biyewa yaran Nan Wallahi, Shikenan nayi shiru tunda kunfi karfina" duk sukayi dariya.

Daddy ne ya fara magana, "Son Bayan kwanciyar da kayi ajiyar ka da ke wurina nayi amafani dasu wurin gina maka asibiti, sannan na zuba maka ma'aikata aciki Ana gudanar da aiki yanda ya Kamata, a gaskiya Haisam ka samu aboki na Kwarai, da taimakon Farukh ne komai ya tafi dai dai tun Bayan wannan lokacin shi yake kula da komai, a halin Yanzu asibitin yana d'aya daga cikin manyan asibitocin da ake ji dasu a garin gombe, sannan na gina maka gida, na zuba maka dukkanin abubuwa na more Rayuwa"

Mikewa Haisam yayi ya rungumi daddy yana kuka kamar wani karamin yaro Yana ta Nagode Allah ya saka, daddy Murmushi kawai yake Yana d'an bubbuga Masa baya alamun rarrashi, Umma ma godiya ta Shiga Masa, tana Kara godewa Allah da Ma'isha sabida itace silar komai, shiysa take matukar son Isha, fiye da ka yadda take son Haisam d'in, Abba yace "Kan mu shigo, mun biya gun Dr Ali yace anjima da Yamma za'a sallame ka"

"Alhamdulillah dama Wallahi na gaji da asibitin Nan, Yamma tayi ai Abba"
Duk dariya sukayi.

Suna cikin maganar ne sai ga shigowar Dr Ali, Bayan sa biye yake da wata nurse hannun ta Kuma rike yake da patient file, Bayan sun gaisa ya Shiga Duba Haisam, Bayan ya gama ya rubuta Masa magunguna da za'a saya ya mikawa Ma'isha had'e da fad'in "Pharmacists a samawa patient magani" Karb'a tayi tana dariya tace "Ai na samu hutu"
" Yet ke staff d'inmu ce"

Charafff Haisam yace "She was dai, don Canza mata wurin aiki zanyi" girgiza Kai Isha tayi Dr Ali yace " Fatan alhairi" sai ya fice nurse din tabi Bayan sa.

Tattara kayan su Umma da Mummy suka farayi Isha ma bata zauna ba da ita ake had'awa su Daddy da Abba Kuma suna Kai kayan mota, farin cikin da Umma take ciki bazai misaltu ba yau Bayan shekaru 4 d'anta zai Koma gida, har kuka Saida tayi mummy na ta aikin rarrashin ta. Bayan sun gama kai tsaye gidan Umma suka nufa Haisam zai zauna a gunta Kan ya gama murmurewa, Isha dama already tana gidan Umma, Ni ko nace Anya zaman Isha, Haisam ga Kuma mardiya zaiyu kuwa a gida d'aya?
Muje zuwa.

Mardiya Bayan ta koma gida ta shirya cikin doguwar rigar atamfamfar ta, Atamfa less ne, brown an Masa Flowers da kallan ja da yellow sannan less d'in Jikin farine hakan yasa tayi Rolling da d'an figegen gyale fari hannun ta Kuma rike yake da labcoat d'ayan hannun ta Kuma fashion bag d'intane shima fari Sannan takalmin ta ma fari, a gogon hannun ta take Kallo sai Kuma tayi Tsaki , a bayyane Tace "wannan Wace irin Rayuwa ce, a gaskiya zan d'auko mota na tun d'azu nake ta jiran abun Hawa Amma babu."

Wata dankararriyar mota ce tazo ta faka a gaban ta, ta kawar da Kai Jin an Kira sunan ta Yasa ta kalli Wanda taji ya Kira sunanta Tace "Laaaa Adnan"
Murmushi yayi yace "Mardiya manyan gari ana ganin ku dama?"
Itama Murmushin tayi Tace "Gashi kuwa"
"Hakane, ina zaki ne haka?"

"Gun aiki ina ta jiran napep Amma ban samu ba"
"Hoop In Mana mu rage Miki hanya"
Ba musu ta bud'e gidan baya sabida daf take da yin latti,jaan motar yayi yace Mata
"Wani asibiti kike aiki?"
"Specialist hospital"
"Okay "
Babu Wanda yace komai sai chan yace "Wannan abokina ne sunan sa Abdallah"
"Barka"
Shima ya amsa da yauwa barka,nan suka fara hirar yaushe gamo,suna Isa specialist hospital har ta bud'e marfin motar Tace "Baka tambayeni mutuniyar ka ba?"
Sai da yaji kirjin sa ya fara duka uku² cikin rawar murya yace " Wa Kenan?"
"Ayrah Mana"
"Ummmm...... Ya take ne? Tayi aure ko?"
" Wai kana nufin baka ji abinda ya same ta?"

Gyara zama yayi ya waigo Yana kallon ta kana yace " A'a me ya same ta?"
_______________________
Please comment
And share
Milhaat ce
Yar Terawa
[8/17, 1:06 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page

73&74
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

```Continuation.......``` Ba Adnan Kad'ai ba hatta Abdallah sai da yaji zufa na sassafo Masa, Adnan kuwa wani abu ya ji ya bi ta makoshin sa ganin irin kallon tuhuma da take masa, Dakyar ya aro jarumta yace "Umm umm bani da labarin komai"

Ajiyar zuciya tayi kana Tace "Ta 'bata ba a San inda take ba"
Gyara zama yayi kamar Bai San komai ba yace "Whatttt!!!! Da d'an karfi kana yace "when, how? Yaushe hakan ta faru,taya ma za'a ce ta 'bata sai kace Yar tsana?"
Ya maida kallon sa ga Abdallah kana yace "kana Jin wani zance ko,wai ta 'bata kamar babyn roba?"

"Wallahi da mamaki Kam"

"Umhn to maganar da ake ma ta kai 4 months ba a San inda take ba"
Adnan yace "Ashhha abu baiyi Dad'i ba, Allah ya bayyana ta"
Duk suka amsa da Amin.

Ficewa tayi daga motar Bayan ta bawa Adnan Number wayar ta, Motar ya tada suka Kama hanya, Abdallah ne yace "Abokina I think is high time fa da zaka bar yarinyar Nan haka ta koma gida, ina gudun abinda zai biyo baya gaskiya"

"I wish zan iya hakan, I wish zan iya cire ta a Raina I wish lokacin da ta nemi mu na shirya na amince da duk ba a Zo Nan ba"
" Bar maganar wish wish d'in Nan ka bar yarinyar Nan haka ta koma gida"
"Bazan iya" Yana maganar ya maida hankalin sa kan tukin da yake.

"Ka fahimce ni Adnan, wallahi idan asirin ka ya tonu abun bazai Mana kyau ba sabida duk abinda ya shafe ka Nima ya shafe Ni"

" Nima ka fahimce ni, wallahi Allah ina son yarinyar Nan har cikin Raina"
"Ita Kuma Tace Bata son ka just let her be"
"Kana ganin idan na barta ta tafi zata rufa min asiri ne?"
Shiru Abdallah yayi na Yan sakanni kana yace "No, I don't think so"

"Good that's my point, ina so na jefi tsuntsu biyu da dutse d'ayane you understand what I mean?"
" Yeah I do, Allah ya shige Mana gaba"
"Ameen"
" But fa ina son kawartar Nan Wallahi"

Kallon bana son rainin hankali Adnan ya Masa kana yace "To wani sabon iskancin naka xaka Fara Kenan"
"A a wallahi tallahi sonta nake Kuma da aure"
"Hmm lallai fa"
" Kana ganin zata amince kuwa?"

"Can't tell, but try your luck"
Bai Kuma ce masa komai ba har suka Isa inda zasu.

Mardiya ce zaune a office d'inta ta Lula duniyar tunani, ajiyar zuciya tayi kana a bayyane Tace "Meyasa nake ji kamar akwai abinda Adnan yake 'boyewa? Anya Adnan baida sa hannu acikin 'batan Ayrah kuwa? Mtswww ko ma mene ne zan bin cika" ta d'auki wayarta ta Fara latsawa.

Bayan ta Dawo daga gun aiki ta tarar da su Umma, abba, Daddy, Isha, Mummy da Twins Sannan da Auta suna dinning suna cin abinci suna Hira, manta jiki tayi tana kallon su, ganin yanda suke farin ciki basu da wata damuwa, tsanar Isha ne ya sake ninkuwa a zuciyar ta.

"You don't deserve to be happy, yayana ya rasa ransa Amma ko kad'an abun bai dame ki ba, hankalin ki kwance dake da ahalin ki, to wallahi Ni zan Zama sanadin rushewar farin cikin Nan tunda Ayrah ta kasa, Allah sarki Mummy da Daddy, Ina kewar ku sosai Yaya kasance kana son farin ciki Isha sama da komai a duniya Amma Bata damu da Kai" magana take a zuciyar ta tana matsar kwalla, batayi aune ba sai jin murya Umma tayi Tace " 'yata kin Dawo?" Had'e da dafe kafad'ar ta.

Umma kallon fuskar ta tayi, cike da tausayi tasa hannu ta share mata Tace "Ki daina Kuka Mardiya, nasan is not easy ki d'auke mu tamkar family d'inki kinji, ki cigaba da musu addu'a kinji"
Chapter 50 · 0% Book details