← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 83

Sashe 80

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanciya khaleel yayi akan gadon yad'ora jenior a saman cikinsa, ya kalli Aysha dake saka kayan barci " shi baza'a masa wankanba ne?".
Juyowa tayi tad'an kallosu, sannan tamaida kanta ga madubi tana tufk'e gashinta, tace, "aii Ammah tamasa tun d'azun bayan anyi sallar magriba".
" OK, Ammah ko fitina, yanzu dai datasan kina d'akinnan dayanzu tashigo, bansan miyasa takemin hakaba?".
Zama Aysha tayi a bakin gadon kusada kan ya khaleel tana 'Yar dariya.
"Kabar Ammah kaji, aii yanzu hira da innah ne ke d'auke mata hankali".
" hakane, amma miyasa taketa wani kaffa-kaffa dake".
"🙈catayi idanfa ina shige maka saika kuma min wani cikin, waikuma ga jenior k'aramine".
Bashiri khaleel yatashi zaune yana 'Yar dariya, ''kai amma dai tsohuwarnan ta rainani, to bansan kina jego bane komi? Tama maidani wani bunsuru alkuran".
Dariya Aysha taita masa harda tuntsurawa.
Tuni dariyar ta Aysha tafara narkar da ya khaleel, dama gata acikin kayan barci, jegon kuma yasakata yin shar, takuma murjewa da 'yar k'iba, kasa hak'uri yayi, ya ajiye jenior agefe yamatso kusada Aysha.
Tashagala cikin masa dariya taji ya kwantota jikinsa, kafin tayi yink'urin kwacewa kam bawan ALLAH ya had'e bakinsu waje guda.
Tunfa Aysha nad'an tittirjewa sai jikin mutuniyar taku yasaki🤣, tafara badakai😎.

Sun lula wata duniya kukan Abdallah yadawo dasu hayyacinsu, yaro kamar yasan mi'akeyi ya daddage ya callah kuka😂🤣.
Dole suka saki juna suka dawo gareshi, kunya dukta ishi Aysha, khaleel yad'akkosa yad'ora mata acinya yana murmushi.
''Inagafa yunwa jenior yakeji".
Kan Aysha ak'asa takar6esa tafara shayar dashi, cikeda sha'a khaleel yake kallonsu, jiyake tamkar ya had'iyesu donsi, waya yad'auka yamusu pic, sannan yamatsa tareda rungumo Aysha jikinsa ya manna mata kiss akumatu yad'aukesu ahaka.

Nida nake ala6e nace "lamarin zaaaaam fans😂🤙🏻".

Ranardai haka ya khaleel ya yaudare Aysha takwana d'akin, dukda baimata komaiba tasha jagwalgwala.

Nace, "Ashe dai gaskiyar Ammah😱".

_______________

Washe gari kuma bak'i sukaita tafiya d'ai-d'ai.
Cikin kwana biyu kowa yakama gabansa, kaikace gidan baitara kiwaba, daganan kuma sai bikinsu musleem.

Ammah tace sai Aysha takoma 6angarenta kokuma d'akin ummi amarya.
Khaleel yay tsalle yadire akan bai aminceba, Ammah kuma tace bai isaba.
Ankai ruwa rana kam kafin ya yarda dan dole Aysha takoma 6angaren Ammah, saida baffah yasaka bakima sannan.
Aikam yayta fushi dakowa agidan, harma ita ayshan kanta.
Daga k'arshema wani aiki yataso masa yashirya yatafi France, headquarter d'insu dake birnin Lyon.

Bayan sati uku da haihuwar Abdallah (jenior).............✍🏻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*😭🙏🏻
[10/26, 4:30 PM] Aysha Galadima: *_📲Typing_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASS......._*
_(Home of expert and perfect writers)_

*_part 2_*
_(littafi Na biyu📙)_

_alkairin ALLAH ya iso gareku kuma, bilyn Abdul bata manta dakuba._
*DUNIYAR MAKARANTA group & ATK hausa novels, Momiskoh hutu.*

5⃣1⃣

Kwana biyu kenan da dawowar khaleel Nigeria, har yanzu kuma fushi yakeyi da Aysha, zaidai shigo yad'auki junior yafita, Ammah ma baya kulata, yana dai gaisheta amma babu hira.

Yau takasance monday, dawuri khaleel yay shirin office, ko cikin gida bai shigaba yafice da hanzari.
Adams yabud'e masa mota yashiga, bayan sunyi salute nashi.
Tafiyar mintuna k'alilance takaisu.

Zamansa babu dad'ewa a office saiga kira yashigo wayarsa, dubawa yayi kasancewar wayar office ce, ganin ogansa yasakashi d'agawa da hanzari.
Cikin girmamawa ya gaidashi.
Saikuma naji yana fad'in "OK sir, ganinan zuwa to".
Yana Yanke wayar yamik'e yad'auki wasu takardu yafice.
Saida yayi knocking aka bashi izinin shiga sannan yatura k'ofar yashiga, ya k'ame tareda salute na ogansa.
Fuskar Oga d'aukeda murmushi yanuna masa wajen zama bayan yamaida masa murtanin salute d'in.

" J! Ya iyali?, da abokina Abdallah?".
Murmushi ya khaleel yayi, yace, "yana nan lfy sir".
" to ALLAH ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa yafika jarumta da kwazo".
Murmushi sosai khaleel yakumayi, Wanda har hakwaransa suka bayyana, yanason ayaba masa d'an Abdallansa😃👍🏻.
Yace, "to ALLAH ya amince sir".
Oga yay 'Yar dariya, tareda mik'ama khaleel wata Leda mai azabar k'yau.
"Ga wannan j!, gobe idan ALLAH ya kaimu su zaka saka, kuma kaida madam zakazo".
Cikeda mamaki khaleel yakar6i ledan, yad'an lek'a cikinta sannan yakalli ogan nasa.
" sir! wani abune za'ayi?".
"A'a, kaidai kasaka kawai, kuma sai around 11 za'azo a d'aukeku insha ALLAH".

kasa cewa komai khaleel yayi, sai jinjina kai yake tamkar k'adan gare.
Oga yayi murmushi, tareda basar da zancen yace, " so ina takardun danace kazo dasu?".
Mik'a masa khaleel yayi.
Oga yakar6a yad'an dudduba, sannan yad'ago yakalli khaleel d'in, " ehm j akwai wani aiki daya taso mana again, so zamuyi meeting akan batun next week insha ALLAH, kuma aikin gaskiya dolene kaine keda zarrar yinsa, Dan wad'anda za'a kamad'in saida irinku awajen, amma gawad'annan kaduba wani 6angarene nabayanan, zan turo maka sauran ta network".
"OK sir!".
" zaka iya tafiya abinka".
Mik'ewa yayi tareda k'amewa dayin salute na ogan, sannan yafice.

**********

Tunda yadawo office yaketa juya maganar ogan nasu, baidai bud'e kayanba, yamaida hankalinsa akan binciken bayanan da oga yabashi akan aikin kuma dayake tunkarosu.
Yaja tsawon lokaci a binciken yaji alamar shigiwar massage a wayarsa.
Kamar bazai dubaba dai yad'auka.
Number Aysha yagani, yasaki guntun murmushi sannan yabud'e sak'on.

_"Amincin ALLAH ya tabbata agareka yakai sanadin farincikina, inafatan kana cikin kwanciyar hankali da walwala ahalin yanzu?, Alkairin ALLAH yacigaba da yalwatuwa aduniyarka, ALLAH yatsareminkai daga idon mata🤕, masu k'arema mazan mutane kallo😏."_
_"junior yace dadynsa yakasance cikin kwazon aiki da farinciki, gefe kuma yaringa tuna mamansa, yamata uzuri, adaina fushi da ita, ba laifinta bane, itama tana kewar bakandamiyar rayuwarta Abban junior💋."_

Baisan sanda wani murmushi ya su6uce masaba, yakuma maimaita sak'on sannan ya tuntsure da dariya, kai yarinyarnan sai'a barta, 'yar k'arama da ita ta'iya kishi.
Cikin lumshe idanu ya sumbaci massage d'in, shikansa fushin dayakeyi dauriya kawai yakeyi, amma yana kewarta, yanaso kod'an kissing d'inta yayai, amma Ammah takafa tatsare.
Bud'e idanunsa yayi, sannan yay dealing d'in number d'inta, harta katse bata d'agaba, kasa hak'uri yayi yakuma kira, bugu biyu kuwa tad'aga.

Murya can k'asan mak'oshi tace,
"Hii my lollipop".
Lumshe idanun yakumayi, da k'yar ya iya furta " A'eesha kin rainani ko? kimin laifi amma kimaidashi wasa?".
_"Ooo! my god, ni na'isa wasa da jarumi mai zarrah irin j!, karfa ka manta j! Ne, kuma j!! Bayason raini, amin afuwa, komai akaga nayi, akan kuskurene, amma bazan sakeba, junior nataya Amminsa bada hak'uri, kagama kuka yake shirinyi, harya fara ta6e baki"._
"Kai haba dai?".
" ALLAH kuwa". "tayi maganar tana kara wayar kusada Junior".
Aikam tamkar jira yake yafashe da kuka😂

" kai, dama da gaske kikeyi? Please banason jin kukansa, kibasa abincinsa".
Shagwa6e murya Aysha tayi. tace, "to kadaina fushin dani please?".
" ai wancan laifin daban, bamu abincinmu kuma daban".
"Naji, to amma naci albarkacin junior".
" sarkin wayo, shikenan na yafe miki, komai yawuce, amma saiki shirya tarbata yau ko?".

"Lah Sadaukina, banfamuyi arba'inba".
"uhm nasani aii, amma koda bazanje city ba, sai'a barni nad'an rage zafi".
Kamar Aysha na gabansa tarufe idonta, ''kai ya khaleel, ALLAH kaima wani lokacin bakada kunya.
" hhh ko sholyna?".
"Eh mana".
" tom nazama mai kunya, kibarni nayi aiki inba sokike nazabga musu shirmeba wlhy, duk kin wani narkar dani".
"Wata 'Yar dariyar kissa Aysha tayi, tayimasa siririn kiss sannan tayanke wayar batareda yashiryaba, saidai yaji d'iifff."
Da sauri yakalli wayar, yakoma yalafe jikin kujerar yana fad'in ya salam yarinyarnan zata karni wlhy🤦🏻‍♂.

🤣🤣🤣😜.
Kina aljanna sholy, muna binki da addu'a, nida fans🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀.

ALLAH yaba Xoxo irin khaleel kodan........🤭, bazan fad'aba to😜, su o e har an kasa kunne aji kanun labari😏.

_______________________
Sai bayan isha'i yadawo gidan, 6angarensu yashiga yay wanka yakimtsa sannan yazura jallabiya kalan ash, yad'an fesa turare yad'auki ledar da ogansa yabasa dawata ledan dayad'an yima Aysha siyayyar toshin baki😂 yafito.

Da sallama yashiga falon na Ammah, babu kowa aciki sai mufeedah dake barci a doguwar kujera, da'alama bada shiri barcin ya kwashetaba, Dan harda waya a hanunta.
Jiyo Ammah yayi tana karad'i itakad'ai a waya, da'alama waya yakeyi da uncle ma'aruff kokuma wani.
Sad'af-sad'af yashige d'akinta, yana k'yautata zaton Aysha nacan.
Aikam kan gadon AMMAH yahangota zaune tana k'ok'arin sakama junior pampas.
K'ofar yasakama key sannan yak'arasa gareta.
Tad'ago ido tana masa sannu.
Zama kusada ita yayi yana amsawa, tareda saka d'an yatsansa cikin hannun junior, shikam yakama yarik'e gam kamar yasan miye.
"My sweet kawuni lfy?".
Aysha data gama saka masa pampas d'in tad'agosa tad'ora masa acinya tana fad'in " k'alau ya wuni, saidai kewar Abbah ko baffanmu?".
Ya khaleel yakar6esa yana murmushi, ya sumbaci fuskar yaron, "to nima nadawo inata kewarku".
" humm yaronafa sai k'ara k'iba yakeyi, ALLAH nononki yanada k'yau 'yammatana, masha ALLAH, ingani".
'Yay maganar yanakai hannunsa kanta'.
Baya tamatsa tana dariya.
Shima dariyar yayi ya cafkota, jikinsa tafad'o, yana rungume da Junior yamatseta itama, kissing d'in wuyanta yafarayi, bata hanashiba, saima wani salo data fara masa.
Aikam dandanan mutumin naku ya afka.
Suna tsaka da hutawarsu Ammah taita buga k'ofar, shiru sukai mata kuwa, sukacigaba da faranta ran junansu.
Dama tea takawoma Aysha, falo takoma tana mita, saikuma tayi shiru tana d'aga hanci sama, alamar son shinshino k'amshin wani Abu.
Da sauri tace, "tabbas ja'irin yaronnan yazo, gama k'amshin turarensanan".
mik'ewa tayi taje tacigaba da buga k'ofar, nanma shareta sukayi.
Saida suka more iya morewa sannan khaleel yabar Aysha, kunya dukta isheta.
Muryarsa asark'e yace, " nifa gaskiya kuyi ayi arba'in d'inan, akame nake wlhy".
Aysha tayi 'Yar dariya tana kauda kanta gefe.
"Uhmyim, dariyama nabaki ko?".
" a'a fa".
"To inma dariyar nabaki dai, zanyi maganinki, amma bayanzuba, d'auka wancan golden d'in ledan kiduba muga miye aciki?, Ogane yabani a office.........
Yakwashe komai yasanar mata.

'Daukar ledar Aysha tayi tabud'e, tafito dawasu azababbun suit masu taushi da d'aukar idanu, blue da pink d'in riga long sleep, sai kuma gown itama blue har k'asa mai dogon hannu, sai d'ankwali pink.
Aysha tad'ago tana kallinsa, shima idonsa akan kayan.
''Sadauki kodai wani taro suka shiryane akanka baka saniba".
" to wlhy bansaniba sholy, amma bana zaton hakan, saidai giben zamu gani koma miye".
"To ALLAH ya kaimu". 'Tayi maganar tana k'ok'arin maida kayan a ledan'.
"No karki maida duka, cire naki, saiki shirya da wuri karyazam ina jiranku, shima junior kisamu kayan dasuka dace dashi sosai".
" OK''.
Chapter 80 · 0% Book details