← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 83

Sashe 72

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tunda khaleel yadawo daga sallah bai koma barciba, Dan yau yakeson komawa bakin daga.
Aysha daketa kurin aiki itama antashi anyi shiri.
Yana tsaka da shiryawa cikin uniform d'in aiki saiga Aysha tashigo d'aukeda tire.
Ta madubi yake kallonta yana saka ma6allan rigarsa.
Mamaki ya kamasa harya d'an juyo ya kalleta itada tiren, sannan ya juya yacigaba da saka ma6allan.
"Wai daga ina haka da tire?".
''Daga kichin mana, kad'anyi breakfast kafin kafita".
Turare yad'auka yad'an fesa sannan yajuyo gareta gaba d'aya, kusada ita ya zauna akan sofa tana juya tea daketa turiri.
Kumatunta ya sumbata, yana magana yana saka sock's da takalmi.
" humm, nifa mamaki kike bani wlhy, wai dama ba barci kikeyiba ne?".
"Lallai sadauki, inani ina barci yau Monday, insha ALLAH saina koma aikinnanfa, kamata yayima ka dinga k'arafamin guywa aii, saurafa wata biyu kacal nagama, nasha wahalar watanni goma, saida aski yazo gaban goshi sainayi sakaci kuma?".
''Inafa zan yarda Maman babies na, gara kigama kizo kinutsu wajen yimin tarbiyyan yara".
" tab aikinfa?".
"Gashinan zakiyi agidan mijinki". 'Yay maganar yana d'aukar doya yasaka abaki'.
" sadauki banfa ganeba".
Saida ya k'ur6i tea sannan yace, ''aii dama bazaki gane cikin sauk'iba, d'akko agogona gashi can saman mirror ki sakamin, nakusa makara, kuma inada meeting 8:0am wlhy".
Tashi Aysha tayi tad'akko agogon, tadawo kusadashi ta zauna, hannunsa takamo tamaido saman cinyarta, tana d'aura masa agogon tana juya maganganunsa aranta, idonta nakan zara-zaran yatsun hannunsa masu dogayen farce dake a tsaftace kuma a yanke, kamar yanda addininmu ya koyar damu, (sa6anin samarin yanzu da 'yan mata dake barin farce wai danufin gayu, yo gayu kokuwa bama shaid'anu mafaka😏).
Tana d'aura masa yana shan tea d'in a hanzarce.
Tsaf ta d'aura, yadace da chocolate d'in skin nashi kuwa.
Sauran tea d'in yakai bakinta tareda fad'in sha kema.
Kauda kanta tayi gefe, "uhm uhm sadauki, banajin shan tea wlhy, zanje cikin gidane k'ila sunyi kunu saina sha."
''Kenan batare zamu fitaba?, dankuwa su Adams Na hanyar zuwa d'aukana, shima yafara koyan latti nakula".
"Kaikam ya khaleel amaryafa gareshi, da shikad'aine, amma yanzu saiyad'anyi lallashi, saikuma an tsareshi yasha tea kamarkai".
Dariya maganarta tabashi, ya ajiye cup d'in tareda jawota jikinsa ya sumbaci cikinta da goshinta, ahankali yace, "I love you so much cuty na, ked'in badai iya tsara zanceba." 'Yay maganar yanajan karan hancinta'.
Kunya saita kama Aysha, tasaka hannu tarufe fuska tana murmushi.
Shima d'aukar jakkarsa yayi yana murmushi, yace, ''bye, akula sosai, banda magana da maza wlhy, inhar batazama tilasba, daga wajen aiki kar acemin kinje koda gate, idan time d'in tashi yayi ki kirani zan turo a maidoki gida. kije zaku fita tareda ummi amarya."
Baijira cewartaba yafice.

Da kallo Aysha tabishi, batareda ta iya cewa komaiba harya fice.

********
Kamar yanda suka saba, cikin girmamawa suketa salute nashi da k'amewa, tuni Adams yatareshi ya kar6i kayan hannunsa, Samuel yabud'e masa motar da sauri.
Shiga yayi ya zauna abaya cikin k'asaitarsa, suma sauran securitys d'in duk suka shiga.
Saida suka fara tafiya sannan Adams yace, "sir! Akwai maganar kama guy d'inanfa Manner, kuma nasamu labari a majiya mai k'arfi yashigo Nigeria adaren jiya."
Bud'e idanu khaleel yayi yana kallon Adams, yace, ''aikam zuwa Kano yakamamu dole a yau, domin Sa'eed ya tabbatarmin inhar yazo Nigeria to washe gari a Kano yake kwana, kaga kuwa yau kenan zaije Kano, idan mukayi saken har zuwa gobe to tabbas zamu rasashi, kuma guy d'in yanada muhimmanci akan bincikenmu, ta hanyarsane kawai zamu iya sanin wanene Alhaji Anas Jalingo, gashi kuma meeting d'inan zai kaini kusan awanni 8, Dan sai 1 zamu fito".
Cikin huro iska abakinsa yace, ''yakake ganin za'ayi kenan?, ko shigar dare zamuyima Kano d'in?".
"Duk yanda kace sir, kaga idan mun ajiyeka saimuje airport muyi biking jirgin yamma."
"Shikenan, damun Isa kad'auki file d'in bayanan Alhaji Anas d'in ka kaima Basheer office yasaka hannu, sannan inaga kawai numbers d'in duk kan yaran Alhaji Anas ahannun Solomon, saiku duba number d'in Munner awajen, sannan su Solomon su bibiyar mana inda yake ta hanyar layinsa, dakuma duk indama zaije ayau har zuwa dare".
" kukira Mustapha yabibiyeshi, kakuma gargad'esa akan karyamin wasa a aikina, idan yakuma kuskure irinna last time wlhy saiyayi nadama."
"OK Sir! Babu damuwa".

A dai-dai lokacin suka iso, bayan Adams yabud'e masa yafito, yakar6a wayarsa a hannunsa da lap-top, wad'annan akaisu office kawai, ka d'auki wasu files nanan a kan desk, nad'ora kamar wani book ne akai, nadai manta, kabama Samuel yakai office d'in Oga Victor, kace yatsaya yaduba yabashi ya maido maka, kaima kasamin hannu sannan kakaima Taheer akwai abinda zaije Ku bincika kaidashi da faruk da zeenatu a d'akin bincike, kafin nafito a tattaramin bayanai, bara naje suna jirana."
"Afito lfy sir!".
Kansa kawai ya jinjina Adams tareda d'aga hannu yanufi inda zasuyi meeting d'in, iyasu manya-manyan jami'an police Interpol, tareda wasu daga cikin immigrations da Customs, harma dawasu manyan ainahin police d'in, zasu tattaunane akan aikin had'aka dasukeson gudanarwa domin cafke wasu masu laifi dake k'asashen k'etare, dakuma goyon bayan wasu manya dake cikin Nigeria..............✍🏻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🤚🏻✋🏻._*
[10/26, 4:28 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_

*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

*_Bilyn Abdul bata manta dakuba, kunan acikin ranta zaune daram wlhy. Ina k'aunarku fiyeda tunanin mai hasashe._*

Bilkisu saddiku shona, Asmeey*Jibreen, Zee*Matorh, haleemerh💖, Aysha*Bose, Sakinat Baba Didi, Hafsat I kari, halima, Shahida ibrahim, Khady fulani🐄, Sumee qasarawa, Saddiqa Dahiru. Zaynab, Maman Umar, Aysha Maman ta, Maman HAIDAR, Maryam Adam, abdullahi 002. Marcy bintu Muhammad Maman waleed maman shaheed. Ameera, Samina sulaiman lambu. Mmyn xahra. Ramlart ma'aruf.. Binta garba sakawa. Rukkyh Rky . Mrs uthman. Ummi haidar. Ummu Mahmud. Balkisu sulaiman . rashidart Abubarkar sultan. Khairat. Mom ismart, Rumanatobbr, Zainab Atiku, Auta nijar, Sameeran gaya, Hanan yusuf, Mardiya, Jamila sule, Zahra eabrahim, Farida ridwan, Mmn walida, Pherteemah, Maman islam, Anuty, Momy, Fancy honey, Khadeeja dantsoho, Hafsat wali, Aysha wali, Hussaina idiris maman amira. naima nura. hauwa umar. abubakar. nafisa yunusa
saratu k, Muhammad habiba khaleel, Maryam, umar musa, Jamila Muhammad Adam, Zainab, Maman khalifa, Maman sudais, Ummu, abudull, Maman sajida, Farida gamco, Firdausi kabir, Momin Abdul malik, Momy zuwaira, Rukaiyya aliyu, Aysha m bello, Rahila abba, asiyya muregi, Fatima garba sule, Ummu ihisan, Ummu salma.

_Na gaisheku ababen alfaharina😂👍🏻❤❤😍😍😍😍😍._

4⃣6⃣

Dole likitoci suka rufu kan hajia babba, dukda ba'a bama wani criminal kulawa kamar haka, saidai inhar suna buk'atar wasu bayanai awajensa, amma darajar khaleel Taheer yace abama hajia babba kulawa, Dan lamarin yawuce k'aramin Abu, Amman jini taketa zazzagawa. Innah jummai sai kuka takeyi. Kusan awanni biyu likitoci natareda momy, bayan wasu 'yan mintuna saigasu sun fito, kowa yana yarce gumi.
Sai hura hanci sukeyi.
Taheerne ya tambayesu abinda ke faruwa?.
Dr Abraham yace sir, akwai matsala, zuciyar matarnan ce tabuga gaskiya, shine dalilin aman jinin datakeyi, saidai munsami nasarar ceto rayuwarta, yanzu hakama tana barci, maganar gaskiya kuma, bamuda tabbacin tashinta normal.

"Miyafaru da itane?".
" uhm, inagafa tasamu paralysis, 6arinta Na dama munga duk jijiyoyin sun saki".
" Ya salam!". 'Taheer yafad'a yana shafa kansa da huro iska abakinsa".
Gaba Dr Abraham yayi abinsa.

Nidai bilynku nace magana ta girma😱.

_________________________________

Tunda khaleel yashiga office saiya kulle kansa, inda kujeru suke agefen office d'in yaje ya kwanta, Dan anhad'a wajenne tamkar falo.
Idonsa alumshe suke, amma hawaye Na zurara.

Yabani tausayi ainun, domin bansan mike k'ona zuciyarsa hakaba harta kaisa ga yawan kuka.😢

Haka yayta zama cikin office d'in, saidai yatashi daga nan Yakoma nan, saikuma sallan data zame masa tilas, komin knocking d'in da akamasa k'in bud'ewa yakeyi, su Taheer basusan yana nanaba, duk zatonsu yatafi gida.

___________________
Chapter 72 · 0% Book details