Sashe 26
Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar daga sama Momy tafad'o d'akin ko sallama babu, kunyace tad'an kamata, dataga ansakama ya khaleel k'arin ruwa, amatsayinta Na mahaifiyarsa bashida lafiya har haka amma batazo ta dubashiba, alhalin kuma tasani sarai, ko yanzun zuwa tayi tamasa fad'a akan wai yak'i yaje inda take saboda yayi aure, saikuma tazo ta taras Ashe jikin nasane.
Batareda Aysha ta kalletaba tace, "Momy ina kwana".
Harar Aysha Momy tayi, batareda ta amsaba tamatso kusada khaleel, cikin d'an rikicewa tace, " Ibrahim! Dama bakada lfy amma aka gaza sanarmin? Tunkafin ayi nisa son rabani dakai akeyi kenan?".
Aysha data fahimci zancen Momy tsaf da ita take, saitayi murmushi, tana cigaba da goga towel a goshin ya khaleel tace, "uhmm to k'ila laifin Anty shukurah ne, Dan itakam jiyama kusan anan tawuni tareda kowa na gidannan, Momy inagama dai kekad'aice bakizoba sai Anty zuwairah dasu mufeedah".
Ya khaleel najinsu, amma kokad'an bai fahimci bak'ar magana sukema junaba, musamman yanda yaji Aysha nama Momy magana cikin girmamawa.
Magana Momy zatayi ya khaleel yabud'e idonsa, shiru Momy tayi tadawo da hankalinta kansa, saitakama borin kunya wai ank'i sanar mata.
Murmushi kawai yamata, amma baice komaiba.
_____________________________
Anty zuwairah dai tun jiya tawuce, Anty shukurah kam baffah yahana, yace tayi zamanta har mijinta yazo.
Hakan da baffah yayi yakuma hasala Momy, amma bata nunaba.
Wajen 3pm saiga hajia khaltum a rikice tazo gidan, ko gaisuwa basuyi da momyba tace, " Aminiya yanzunan ankamasu gwaska shine baki sanarminba".
Wata zabura Momy tayi tareda fiddo ido waje, tace, "kamarya? Ban ganeba?".
"Hummm kina bani mamaki wlhy wani lokacin, abinda yasa tun jiya banzoba wasu yarane muka tura k'asar Dubai amma aka kamasu suda Ruth d'in, gabad'aya hankalina atashe yake, shiyyasa ban maida hankali akan su gwaska ba, ni duk azatona yarinyar tana hannunsu, sai yau naje gidan gwaska wani yaronsa ke sanarmin ankamasu agidannan daren jiya, shima abinda yasa yatsira ba'aje dashi baneba, sunbarsa tsaron gida".
Sosai naga tashin hankali da rud'ewa tattare da Momy, tama rasa abin fad'a, komai ya kwace mata, suna cikin wannan tararrabi aka kira number hajia khaltum, wai ankama Alhaji bishasha.
😆 kuttt saida hajia khaltum tashiga bayin Momy, dama ita akwai tsoro, sai tsageranci fal cikinta kuma😄.
Momy kamar zatayi kuka tace, " hajia khaltum nafara jin tsoro gaskiya, yanzu kuma suwaye suka kama Alhaji bishasha?".
"Wai sss tareda police Interpol ".
"to ammah Ibraheem yana gida kwance babu lfy aii".
" da gaske".
"ALLAH kuwa, tun jiyama bashida lfy, kama su gwaska ma saidai idan wasu yasaka"..
......jinjina kai hajia khaltum tayi tana fad'in "dolene k'ungiya tahad'a taron gaggawa kuwa, bara naje, zamuyi waya"....
Momy dai takasa cewa uffan, ita gani takeyi haryanzu tanada mafitar kare kanta wajen ku6uta.
Nace hummm.
____________________________
Aysha zaune kusada ya khaleel tana had'a masa shayi, shikuma ya tsareta da idanu ko k'yaftawa bayayi.
Tad'ago danufin bashi tea d'in saitaga ita yake kallo, kunyace takamata, asanyaye tace, "ga tea d'in".
Kar6a yayi batareda yace komaiba, wayarsa tafara ring.
"hello Taheer! Ya garin?".
"Alhmdllh sir".
Yanda yaji taheer yanutsu saiya gane kiran bana fannin abokantaka baneba, Na aikine.
Shima saiya nutsu yaci serous.
Taheer yace, " sir idan babu damuwa zanzo gida saboda namaka bayanin wani aiiki".
"OK babu damuwa, saina ganka", ya yanke wayar.
Aysha najinsa, bayan ya ajiye wayar yace, "jeki saka hijjab taheer zai shigo".
Ta amsa da "to", sannan tamik'e tanufi d'akinta, shikuma yabita da kallo.
Babu dad'ewa saiga taheer ya iso, yau Aysha taga ikon ALLAH, yanda taheer yawani k'ame tareda salute d'i ya khaleel d'in, shikuma yaci serious, babu ko magana, hannu kawai yad'agama taheer d'in, Aysha a zuciyarta tace Sabon salo, saikace ba abokinsaba? Kai wannan hali Na ya khaleel baiyiba.
Itadai ta ajiye k'aramin tire data d'ora ruwa da lemo agaban taheer, yanda taheer yace mata ya gode cikin nuna girmamawa sai kunya takama ta, takoma gefe ta zauna tana kallon ikon ALLAH.
taheer yamik'ama khaleel laptop dake hannunsa, "sir! Ga jerin wad'anda muka kama tareda Alhaji bishasha, aciki mutum 4 sun rasa ransu, 1 sss ne, 3 kuma yaran Alhaji bishasha, wasu kuma sun sami rauni ta silar harbi da yankan wuk'a, gsky Alhaji bishasha yanada had'ari sosai".
Jin jina kai khaleel yayi, maimakon yabama taheer amsa da turanci kamar yanda yamasa magana, saiya juya da French.
Taheer daya fahimci yayi kuskure yace, "sorry sir".
Dan acikinsu nasan sirri, kuma ga Aysha awajen, baikata kuma tasan wani Abu dangane da aikinsuba, dukda kasancewarta matarsa, saidai baisan Ayshan kuma tanajin French d'inba.
Jin jina kai kawai ya khaleel yayi, yacigaba da magana yayinda yake duba hotunan mutanen, da French yace, "amma taheer wannan guy d'in kamar Wanda muka ta6a kaima hari a Nouakchott ta k'asar Mauritania, shekaru kusan 5 kenan, amma yagudu".
"Yes sir!, nima nayi wannan tunanin wlhy, Wanda muka kama makamai a hannun budurwarsa ko?".
"kwarai kuwa, amma miya kawoshi Nigeria? ".
" yakamata a bincika kam sir".
Ya khaleel ya furzar da huci mai zafi daga bakinsa tareda shafa gemunsa, yamaida yatsansa kan bakinsa yanad'an bugawa a hankali, idonsa nakan laptop d'in yana dannawa da hannunsa d'aya, saida yagama kallonsu tsaf sannan ya kalli taheer, dashima idonsa ke kan laptop d'in, "ummm amma ita wannanfa?". 'Yay maganar yana nuna masa pic d'in wata dattijuwa dake cikin hotunan su Alhaji bishasha'.
"Itama acikinsu take, saidai abinda Na lura dashi, kamar tana zamane dole dasu, bada son rantaba, tama samu harbi a k'afarta, Dr Abraham yayi treatment d'in, yanzu tana nan a clinic d'in setetion kwance, nake ganin zamu samu wasu bayanai agurinta".
"OK, yayi k'yau, amma mi IG yace gameda kamasu?".
"Yanuna jin dad'insa sosai, shinema yace namaido aikin wajenka dukda kana hutu, tunda dama kaika fara".
Nanma ya jinjina kansa.
Cigaba yayi da danne-danne, shikuma taheer yazuba lemo a cup yana sha, shima ya khaleel d'in yanayi yanashan tea d'insa.
Zuwa can yad'ago ido yana kallon taheer, "miye labari gameda mutane 37 damuka tace a contact d'in barau modibbo?".
"Suma Alhmdllh aikin yana tafiya, taheer yad'akko wani files yamik'a masa, ga wannan, bayanaine akan mutane 9 damuka tantance acikinsu, matar data kirashi a waccan ranarma munfara aiki akanta, Dan munkama wata mata dake aiki a k'ark'ashinta zatakai yara 6 k'asar Dubai jiya, nakira phone naka danna sanar maka amma bansamekaba, naturo sak'o kuma baka bada amsaba".
"ban kulaba, Dan jiya ina kwance babu lfy, amma yakamatafa kurufe asusun bankinta, miyasa Solomon baiyi wannan aikinba? Dolenefa kadinga zaburar dasu kamar yanda nakeyi, dukda inagama dole nayanke yawan hutunnan nadawo office, naga aiki yana neman cakud'ewa".
"Wlhy yama cakud'e, Kasan kuma yanda suke shakkarka suna aiki da kwazo idan kana nan, basayi idan baka nan, saikaga suna janjani akan aiki, kaga ko sanda aka kashe david kana Mexico ne, sunyi amfani da wannan damar suka kasheshi, kwafa ya khaleel yayi, amma baice komaiba, yacigaba da duba files d'in, saida yagama tas sannan yamik'ama taheer.
Taheer yace, "yakamata kasaka hannu sir".
"OK, amma ya akayi kuka samu bayanai dangane da fita da yara zuwa k'asar Dubai?".
Da sauri taheer yace, "sorry sir, kaga ina neman mantawa, munsami bayanai tawani email ne, amma an6oye kai wajen bayyana sak'on, ma'ana mai email d'in ya 6oyemana kansa, sannan kaga jerin sunayen mutum 5 daya bamu, yakumace muyi bincike akansu, mai email d'in yabamu tabbacin shiba komai baneba, yaza6i bamu bayanaine saboda cutar dashi da mutanen sukayi yunk'urin yi, bazai yuwu ya bayyana kansaba saboda tsaro".
Ya khaleel yajawo laptop d'in, cikin d'aurewar kai yake binciken email d'in, amma taheer kana ganin bawanine yake mana k'ofar ragoba kuwa?, kasanfa bancika son bayanan sirrin nanba, inhar ba irinku Dana yarda bazasu cutar daniba".
"Hakane sir, amma wlhy nayi k'yak'kyawan nazari nidasu Joseph, saimuke ganin kamar gaskiya mai email d'in yake fad'a, musamman idan mukayi la'akari dakama Ruth".
"To shikenan, zanshiga tunanin mai email d'in nima, saiku fara bincike akan mutane 5 d'innan daya turo mana numbers nasu, kasanarma fharuk sukula sosai, idankuma sukaimin wasa nadawo office tabbas zand'auki mataki akan kowa".
" tom shikenan, ALLAH yasa mudace".
"Ameen, yamaganar yaran da aka kama agidannan?".
" yes sir! Suma muna bincike akansu, amma bamu matsantaba sosai, muna jira saika dawo kan aiiki, mun dai kaisu d'akin duhu".
"Ok, kubarsu saina dawo d'in".
Sund'an k'ara tattunawa akan aikin.
Daga baya kuma suka koma tsokanar juna irinna abokai, abinma dariya yabama Aysha, wato idan ana fagen aiki babu wasa tsakaninsu, saidai girmamawa juna, idan kuma aka dawo fannin abota saikaga an canja, afirar tasune ya khaleel yake sanarmasa bashida lfy, nandai taheer ya jajanta masa, harya juyo yana tsokanar Aysha, wai kodai ciwon angon NATA Na wayaune dan a k'ara masa Hutu yasha amarcine?, batadaice komaiba sai murmushi Dan kunyar taheer d'in takeji.
Yace, "su shirya weekend d'innan insha ALLAH zasu kawo musu ziyara suda matansu, dama sund'an basu iskane susha amarci.
Ya khaleel yace, " ALLAH yakawoku to, muna zuba idanu".
''Insha ALLAH zamuzo".
Taheer yad'an dad'e agidan kafin yamusu sallama yatafi.
Cikin matuk'ar farinciki Aysha ta turama Anty meerah sak'o, wai sunci nasara, aikinsu yayi, harma su ya khaleel sun kama k'awar Anty glory Ruth.
Meerah tayi farinciki sosai, Dan kullum burinta dama bai wuce ta rusa k'ungiyar su glory ba..
Meerah ta tabbatar ma Aysha tashirya gobe idan ALLAH ya kaimu zasuzo musu sallam, Dan jibi jirginsu zai d'aga zuwa Canada, dama Dady da maheer tun washe garin d'aurin aure suka koma, maheer zai fara exam ne a school, dady kuma saboda aiki.
Ya naufal kam akwai aikin daya rik'esa anan Nigeria, shiyyasa su meerah suka tsaya jiransa.
Cikin d'oki Aysha tace, "ALLAH ya kaimu lfy Anty meerah na".
Meerah tayi dariya, "oh ke lil sholyna, har yau dai ba'a canjaba, k'uruciya fal ciki, ya khaleel na hak'uri dai".
"Kai Anty meerah, saikace wata jinjira?". 'Tayi maganar a shagwa6e'.
Cikin dariya meerah tace, "sai anjima, kigaida boss".
Bata jira cewar Aysha bata ta yanke wayar.
'Yar dariya Aysha tayi itama kawai, tana fad'in " I love you Anty meerah na, kina sakani farinciki wlhy, ked'in tadabance atarihina😍.