Sashe 31
Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*******
Kiran wayarsa da'aka k'arayine yasakashi yin k'aramin tsaki, batareda yaduba mai kiranba ya d'auka yasaka a kunne yanayin sallama, yayinda hankalinsa kenan aiki a laptop.
"Ibraheem Aleeya ta saukafa, tace tanata kiran wayarka Baka amsaba".
" wlhy Momy aiki yamin yawa a office, please ki aika driver ya d'akkota mana, kokuma cikinsu Muhseen idan wani yana gida yaje ya d'akkota".
''ni babu wasu su muhseen dazan saka, dadai zaka daure saikaje ka d'akkota minti nawane kwata-kwata".
"Hummm Momy bazaki baneba wlhy, kinganni kuwa a office?, yanzu haka sallah nakeson natashi nayi nadawo kan aikina, kisankusa kwanaki goma bana office, please amin afuwa Dan ALLAH driver ya d'akkota".
Shikenan bara nama driver magana, sai suje da 'yan biyu".
OK saina shigoto, baijira cewartaba ya yanke wayar yana mita.
"kajiminfa Momy dawani zance, ita hartakai Isar dazanje airport d'aukarta, haba saikace wani lusari, mtsoww, wlhy kemafa Momy kinada matsala, haba kullum zance d'aya, yay maganar yana mik'ewa saboda Kiran sallah da akayi Na azhur.
Wayar yad'auka yaduba number data kirasan, saiyaga harda miss call d'in Aysha, itacema tafara kira, saikuma Na Aleeya guda biyu.
Kansa yadafe, Dan baiyi tunanin kiran nataba, yama manta yanada number ta, yakar6ane wajen mama tun lokacin gabatowar bikinsu data tafi Kano, tunda yakar6i number ma baita6a kirantaba, ita kanta ayshan batasan yanada number d'intaba.
Massage d'in da'aka turo yaduba Dan ganin number ayshane.
_"Sadaukina ya aikin?, kakasance cikin farinciki da kwazon aiki irinnan gwarazan sadaukai mijina"._
*_Sholynka Ce_*😘
Murmushin dabai niyyaba ya su6uce masa, yakuma maimaita massege d'in, aransa yana jinjina baiwar Aysha, gata 'Yar k'arama sai wayon tsiya.
Masallaci yafice Dan gabatar da sallah.
Bayan idar da sallah suka had'u dasu taheer. Cikin tsokana Taheer yace, "kai alhaji kaga kuwa k'yawun daka k'ara? Lallai ango kana kwasar amarci yasin".
" mtsooww! ALLAH ya shiryeka Taheer, kaidai bazaka ta6a canjawaba ko? To dan k'aniyarka muni kakeso Na k'ara saboda nayi aure?".
Cikin dariyar shak'iyanci youseef yace, "A'a bak'inciki yakeson maka, k'ilan soyay kadawo aiki wujiga-wujiga ko? Katina lokacin daya dawo hutun angwanci, ALLAH Taheer harwani yallew-yallew yakeyi saboda gara daya kwas.........."
.......Bai k'arasaba taheer yakai masa rankwanshi.......
Youseef yamatsa yana dariya. "Kai Malam ALLAH ka rankwasheni ramawa zanyi, koka manta Na girmeka tunda narigaka aure?".
"To uban 'yansan girma, munji karigamu aure saime to? abinda kake tak'amar kasani mumadai yanzu mun sanshi koko Taheer?".
" A'a j bakada bakin maganama kaikam, tunda kaine auta acikinmu".
"Kuttt ammafa ka sameni, d'an iska zan ramane, nakula tonon silili zakamin cikin yara, bara nawuce office aiki nacan jingim yana jirana, ni dama banje wannan hutuba".
" hhhh tab wlhy ganganne, muzaka saka a kwali, kagama dirzar amarci da young girl d'inka kazo kanawani daddojewa🤣".
"Banza d'an iska banida lokacinka, kagama tafiyata", 'ya khaleel yay maganar yana barin wajen, fuskarsa d'aukeda murmushin iskancin da youseef kemasa'.
Suma dariya sukayi, youseef ya kalli taheer, "d'an uwa Alhmdllh, kagafa j yasamu kwanciyar hankali wlhy, gaskiya Na yarda aure na k'arama mutum daraja arayuwa".
"Hakane youseef, kagadai kamar wasa duk munzama masu iyali, ga matarka harda ciki, kai Alhaji kaimafa shegen samane, kafayi aiki alkur'an".
"A, yoni Na wasane aka gaya maka?, inagamafa matar Joseph itama takamu, dan jiya nakirasa yakecemin sunje Asibiti madam babu lfy, nikuma d'an mutuncin bansake kiraba, gashi yau tun safe sukatafi Zamfara shidasu Zakariyya".
"ALLAH ya inganta mana to, baka saniba, dolece tasaka Joseph zuwa Zamfara d'innan wlhy, dan babu yanda zai kaucene".
"aini tunda naji jiya j yayi maganar naketa addu'a kar sunana yafito amasu zuwannan wlhy, haka kawai, bakagama amarciba asambad'aka daji".
"Hhhhh wlhy kaji haushi taheer, aikam saina zugashi ansaka sunanka a masu zuwa Lagos insha ALLAH".
" munafiki basai kabadaba".
Cikin dariya youseef yabar wajen, dan yasan Taheer ya shak'a.😆.lol.
Sai kusan 6 ya khaleel yadawo gidan, yaukam motocin har cikin gida suka shigo, saboda sun saka mai gadi suma.
Kamar yanda aka saba Adams yarakoshi da kayansa har barandar 6angarensu.
Anan ya kar6a, "uhmm Adams inagafa yau munada fitar dare gaskiya, dan d'an iskannan Moxies ancemin yana 9ja, nagane club d'in dayake zuwa, tom inaga dolene daren yau mu ziyarci club d'in, ni da kai kawai zamuje, saimunga yanda wajen yake sannan inma muna buk'atar wasu saisuzo, tunda bamusan yawan yaransaba da mabiya, so ka sanarma su Samuel, suzama cikin shiri".
"OK sir ALLAH ya kaimu daren, amik'amin gaisuwa wajen antynmu".
" Zataji tunda dai kak'i zuwa ka gaidata".
" ayi hak'uri boss insha ALLAH Wannan weekend d'in zan shigo".
" ALLAH yasa to".
Sukayi sallam ya khaleel yashiga ciki.
Babu kowa a falon. Saidai yanata tashin k'amshi, ko INA k'al-k'al yake, yayinda karatun alkur'ani ke tashi cikin sifikun, wata nutsuwa yaji ta saukar masa, dukkan gajiyarsa tatafima baki d'aya.
d'akin Aysha yalek'a, saiyajiyo motsinta ruwa a toilet tana wanka, "badai sai yanzu yarinyarnan tadawo aiikiba?", 'yay maganar yana kallon agogon hannunsa'.
Babu mai bashi amsa, danhaka yajuya zuwa nasa d'akin danya d'an watsa ruwa............✍
Wayyo kaza zanci😩🤧👻
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
[9/23, 8:35 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 2_*
(littafi na biyu📕)
2⃣2⃣
Babu dad'ewa Aysha tafito daga wankan, simple makeup tayi tasaka wandon jins blue dawata lemon green d'in riga wadda Tamata masifar k'yau, ta gyara kanta ta d'aure, bawai Aysha Nada wani uban gashi baneba, amma daidai gwargwado yanada tsayi.
Kasancewar ba sallah zatayiba tafito falo, kwanciyarta tayi saman doguwar kujera tana sauraren karatun alkur'anin data saka, kokad'an tunaninta bai kawo ya khaleel yadawo gidanba.
Shima a d'akinsa wanka yashiga, ya d'auro alwala yafito, jikinsa kawai ya goge da k'aramin towel ya zira jallabiya blue black ajikinsa, turare yafesa kad'an sannan yafito zuwa masallaci.
Ganin Aysha a kwance idonta kuma alumshe saiyayi nufin tsokanarta, cikin sand'a yak'araso kusada inda take, k'afarta datad'an lek'o Yakama babban yatsanta yaja, da sauri yaduk'e bayan kujera.
Kawai Aysha jitayi an matsa mata yatsan k'afa, aiko tamik'e a firgice tareda kwallah k'ara, sosai ta firgita, ta wawwayga kuma bataga komaiba, hakan yakuma tsoratata, sai tasaka kuka da kiran mama ta shiga uku, anturo abu zai kasheta.
Yanda take dire-diren k'afafu da kuka tamkar taga dodo ido da idone abin yabama ya khaleel dariya, duk k'ok'arin rik'ewa dayakeyi Baisan dariyar ta kwace masaba.
Aysha takuma tsorata, saida taji muryarsace sannan tagane shine.
Yafito daga wajen 6uyarsa yana cigaba da dariya sosai.
Tunda Aysha take bata ta6a ganin dariyar ya khaleel irin hakaba, saita samu kanta da shagala kallonsa.
Shikam baimasan tanayiba, yaga mugunta dariya ta tik'eshi, ya zauna kan kujera yana dariya.
Saida yayi mai isarsa sannan yad'ago yana kallon Aysha wadda ta cuno baki gaba saboda jin haushin dariyar dayake mata.
"Wai dama haka kike da tsoro? Hhhhhhh, wlhy kinbani dariya, to dakika tashi ina zakije ne?".
"Cikin shagwa6a Aysha tace, " yoni wlhy nama rikice, narasa INA zan dosa, d'aki ko waje, towai yaushe kadawo ban sanibane?".
"Kina wankafa nashigo, harnayi wankama, masallaci zanje kawai naganki kwance ido arufe, shine naji sha'awar tsokanarki, kinzata miye to?".
" yo aljani mana".
"kinajin karatu wane aljani ya Isa zuwa kusadake, kedai shegen tsorone dake, saikuma tsiwar tsiya fal kanki".
"Wlhy bazaka ganeba ya khaleel, natsorata wlhy, kaikuma kanatamin dariya, dama haka ka iya dariyar mugunta?".
Bai bata amsaba yamik'e, ''kinga bara naje massalaci karna lalace anan ashiga sallah".
Binsa kawai Aysha tayi da kallo tana murmushi dajin dad'in ganin dariyar mijin NATA murd'ad'd'e, dama yana dariya har haka? Oni shatun mama, su ya khaleel an iya mugunta.
Saina rama aii Nima".
Lallai yarinya zaki rame dai, naje madallaci".
To adawo lfy.
Saida akayi sallar isha'i yadawo gidan aysha takawo masa ruwa ya kar6a yana fad'in "thanks", yana gama sha ya ajiye cup d'in yana satar kallon Aysha k'asa-k'asa, kwalliyar tata tamasa k'yau, amma dayake ya khaleel akwai iya shariya, bazaka ta6a zaton yama damu da itaba.
Danne-danne kawai yakeyi a waya.
Aysha tace aranta aljanun miskilancin sun motso kenan?......
Maganarsace takatse tunaninta, tad'ago tana kallonsa, Dan bataji miyaceba sosai.
"Kin tsareni da idanun kinnan, canayi ki dafamin shayi".
Kad'an Aysha ta murgud'a Baki, azatonta baya kallonta, Dan haryanzu waya yake dannawa, tanufi kichin tana 'yan k'unk'uni.
Yana kallom murgud'a bakin data masa, dakuma k'unk'uni datakeyi, saidai bayajin mitake fad'a, ransane ya6aci, "shin mi yarinyarnan ke nufi? Kodan taga Na sake mata ina wasa da ita?", kwafa yayi yacigaba da danna wayarsa.
Kusan mintuna 10 Aysha takawo masa shayin, tasha jinin jikinta dan ganin fuskarsa cid'in-cid'in ad'aure, duk kuma saitaji babu dad'i, koba komai tana shiga farinciki idan taga ya khaleel Na walwala.
Kofin tea d'in ta mik'a masa, batareda ya kalletaba ya kar6a, baisake bi ta kantaba, yacigaba da shan tea d'insa yana danna waya.
Itama Aysha tayi shiru cikin kujera tana kallo, amma duk Rabin hankalinta Na Kansa, sai satar kallonsa takeyi.
Ahaka hasnah tayi sallama tashigo ta samesu.
Aysha ce kawai ta amsa mata, amma Oga ko ido baid'ago ya kallesuba.
Hasna sai Harar Aysha takeyi, yitai tamkar batasan tanayiba, Dan bata gabanta, arantama sai ayyanawa takeyi, yarinriya da uwarki laura zanyi badakeba, danke kinmin kad'an a filin daga.
Kusada ya khaleel hasnah ta k'arasa, ta rissina tana fad'in "'ya khaleel Momy tace kazo tana kiranka".
Saida ya6ata mintuna biyu sannan yad'ago ido ya kalleta, "naji to, inazuwa, kinzo kinmin tsaye akai". 'Yak'are maganar da hararta'.
Fita tayi tana tutura Baki wai ya dizgata gaban Aysha.
Bai fitaba saida yagama shan shayinsa.
Fita yayi batareda ya kalli ko inda Aysha takeba.
Aysha ta ta6e baki cikin hanlin ko inkula, yana fita takira Rufaida da Sadiya a waya, tahad'asu waje d'aya suna hira, dayake shashashune kowacce k'uruciya Na d'ibarta, sai sukaita bama juna labarin first night d'insu.
Nace, "ALLAH ya shiryaku".😏