← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 83

Sashe 79

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai a lokacin Anty Mamie takai labari cikin gida.
Aifa kowa yarud'e da murna, Dan danan suka cika d'akin, jariri d'an dangi, harfad'an wazai d'auka akeyi.
Suna tsaka da murnarsu ya khaleel yashigo, babuma Wanda yalura dashi, sai Aysha dake kwance akan gado tana kallonsu cikeda jin dad'i.
Yunk'urawa tayi zata tashi zaune Dan ganin ya khaleel, amma saiya dakatar da ita, tareda zama kusada ita abakin gadon ya kamo hannunta yahad'e danasa.
"Sholyna sannu da k'ok'ari kinji? babudai inda kemiki ciwo ko?".
Akunyace ta jinjina masa kan, dansu ummi Amarya suna d'akin, ga matansu ya mujahedeen mamadai batazoba, Anty Mamie ma batadawoba duk sunama ummi amarya kara.
Yasan sarai mitake jima kunya, amma yak'i sakin hannun.
Ammah data shigo d'aukeda kofin tea ta balla masa harara, shima hararar tata yayi yana kauda kai.
" yo iro, iyakarkadai hararar tawa, amma babu yanda ka iya dani, ka harareni son ranka, nasan yanda zanyi maganinka agidannan".
Shiru yamata, yacigaba dama Aysha magana.
"Yo karka tankamin d'in, dama masana sunce dogo da hankali dacene, mtsoow".

Shi dariyama takoma bashi, amma saiya k'iyi, ya shareta.
Kowa ad'akinkam fad'an nasu dariya yake bashi, kowa kuwa yana darawa k'asa-k'asa, Anty Mamie da ummi amarya ne kawai tasu tafito fili.
Ummi amarya tamik'o masa jaririn tana fad'in kaga bar Ammah kaji babana, sotake kawai tabaka haushi. Ga maigida kamasa addu'a.
Sai yanzune zai d'auki yaron, bakinsa d'aukeda addu'a yad'aukeshi, wani farinciki yaratsashi, wai wannan nasane, kai 'ya'ya k'yautar ALLAH, ya mannashi da k'irjinsa tareda lumshe manyan idanunsa.
Ummi amarya dukta kad'a Kansu suka koma falo, akabar Ammah dasu ayshan kawai ad'akin.
Cikin mamaki Ammah da Aysha suke kallon khaleel dake rungume da yaro yana hawaye, bakinsa yana d'an motsawa ahankali, dagani kasan ALLAH yakema kirari da godiya, yakai tsawon lokaci ahaka sannan yabud'e idanunsa akan yaron, yashiga sumbatarsa kuma.
Ammah dai da Aysha sunzama 'yan kallo, Dan sun sakin baki sukayi suna kallonsa.

🤔kai masu karatu, lallai khaleel yanason yara, nifa harma narasa yanda zan musalta muku farincikin dayake aciki.

Bayan Aysha tad'an huta khaleel yakaisu asibiti itada Ammah Dan a duba lafiyarsu data jariri maikama da babansa sak👍🏻.
Ya khaleel an.......🤭koda yake bara nayi shiru kawai.😎

Alhmdllh, maijego da jariri lafiyarsu lau sai wasu magunguna da doctor Faisal yabasu susaya Aysha tasha, shima jaririn saboda 'Yar mura dayazo da ita anbasu Wanda zasuna bashi.
Daganan suka dawo gida.

Kasancewar haihuwar yammace, dare yafarayi makwaftane kawai suka shishshigo sukayi barka daganin jariri.

__________________

Bayan sallar isha'i Baffah yashigo shima ganin jinjiri, daduk samarin gidan, yanata barcinsa aka kawoshi.
Cikin tsokana baffah yace, "iye, kaga d'an gayu, barcima kakeyi? Idon maza biyu kaikuma naka arufe?".
Dariya aka sanya gaba d'aya, zunnurain yace, " a'a baffah karfa kace haka, yarona jarumine, ba barci yakeba likimo yayi dai".
Suka kuma tuntsurewa da dariya, baffah nata tsokanarsa sukuma suna kare masa, ya khaleel dai baicewa komai sai dariya.
Addu'a baffa yamasa, sannan yad'ago yana kallon khaleel, "mu'azzam kamasa hud'uba ko?".

" a'a baffah, kaidama ake jira".

Baffah yay murmushi, yasan dama za'a rina, Dan ya khaleel tun yana yaro idan yasamu Abu, kafin wani yagani, koyayi amfani dashi saiya kaima baffah.
Baffah yace, "wane suna kakeso?".
K'asa khaleel yay dakansa yana murmushi, " baffa duk Wanda kaza6a masa shine dai-dai".
Nanma baffa murmushin yayi, sannan yafarama yaron hud'uba.
Yana gamawa yamik'ama Ramadan dake kusadashi yaron yana fad'in "ALLAH ya raya Takwarana Abdallah".
Masha ALLAH Sukaita fad'a, kowa ya yaba da wannan suna.
Haka sukaita d'aukarsa d'ai-d'ai suna masa addu'a amatsayinsu Na iyaye.
Khaleel da farinci ya isheshi, dama sunan dayake burin sakama yaron kenan, gashi tunaninsa yazo d'aya dana baffah, dad'i yaji sosai, mik'ewa yayi yashiga d'aki yakira Aysha.

Cikin ladabi ta durk'usa gaban baffah tana gaidashi, ya amsa da kulawa, yana tambayarta jikinta.
Kasa amsawa tayi saboda kunya, takumayin k'asa da kanta tana d'an murmushi, baffa yanata zubamata addu'oi da albarka, ahankali take amsawa da ameen, su Muslim natayata.
Muslim azuciyarsa yana tuna dayanzufa shi aka haifama yaronnan, wayyo ALLAH ya khaleel yamasa kwace😂😜.

Bayan tafiyarsu baffah ma Anty Mamie da mama suka shigo sukaga jariri, suma sunmasa addu'oi.
Nace, "kaga yaro d'an gatan dangi😃👍🏻.

_________________________
Washe gari aiba'a magana, gida yacika da 'yan uwa da abokan arzik'i, su Amal amare, kowacce danata cikin, matansu Joseph suma da 'yan yaransu abin sha'awa, Anty zuwairah ma saigata tabiyo jirgi, danta kasa hak'uri, su Anty Shukurah ma anzo, 'yan Kano dai sai nanda kwanaki uku, ammafa tuni sunga hotunan baby da'aka tura musu, Anty Amatullah ma pictures d'in baby tuni suncika wayarta, kowa yagani dole yayaba.
Fans ma pictures duksun zomuku nasani😉😃🤚🏻.

🤣🤣
Ammah tayi karnene ad'aki tahana khaleel sakewa, Bai isa yak'e6e dagashi sai ayshaba, daya shigo zatazo ta zauna itama, idan zaicika d'akinnan da harara bazata kulashiba.
Takuma hana Aysha shiga d'akinsa.
Haushinta sosai khaleel yakeji, yarasa kuma yanda zaiyi da'ita, duk wani motsinsu akan idon Ammah ne😂.

Kai Ammah jidalice fans🤣🤣.

********
Masha ALLAH Abdallah yayi yayi goshi, kayan barka ba'a magana, baffa yayi nasa, Anty Mamie danata, mama danata, ummi amarya danata, to ballantana kuma iyaye su ya Sultan, duk basu manta rawar gani da d'an uwansu yataka anasu haihuwar 'ya'yanba, harma da bikin nasu, kowa saida yaymasa hidima ta bajinta, hakama Anty Zuwairah wannan karon tayi hidima kodan tawanke laifinta nabiki dabatama ya khaleel komaiba, kayan baby 'yan ubansu haka tahad'o, banda Na Aysha dashi khaleel d'in kansa, Anty shukurah, Anty Amatullah ma duk ba'a barsu abayaba.
Abin tamkar fariyya, ya khaleel maiyine, shiyyasa shima ba'aji k'yashin masaba, koya kukace fans🤷🏽‍♀.

Kumafa nasan kunan kuna shirya gifts😉😂.

_____________________

Kwanaki hud'u da haihuwa saiga Anty Fadeelah da Anty Hafsat, sunyo gaba daga Kano.
Zokaga murna wajensu dasukaga jariri.
Aysha taji dad'in ganin 'yan uwanta, sunzo dakayan arzik'i suma, daga kawu bilyamin, Na Ummah ma daban, haka su ya Qaseem.
Aikam ranar ansha hira.

Ana gobe suna kuma su ummah suka iso suma, harda matar kawu Ahmad da Ummulkhairi autarsu Aysha dake hannunsa, yarinya tayi girma sosai, zasu iya zama sa'anni da ummunoor, bana zata jss 1 secondary, gwaggo Asma'u ma tazo daga katsina, da Matan su ya Qaseem, matan kawu bilyamin ma da 'ya'yansa, su Rufaidama ba a barsu abayaba, sunzo da 'ya'yansu masha ALLAH dunsunyi wayo.

To saikuma ga 'yan jigawa, harda inna tsohuwa mairan k'arfe, dukda tasan duk abinda yafaru hakan bai hanata shan sabon kukaba ta rungume khaleel tana fadin "dama tanaji ajikinta khaleel jinintane, ba'a banzaba take k'aunarsa kamar tsoka d'aya amiya😂, shikansa saida kwalla ta tarumasa agefen idonsa.
Matan uncle ma'aruff ma duk sunzo, da gayyar dangi Na 6angaren Ammah da Anty Mamie, gidafa yacika kaikace biki akeyi. Kowa burinsa ya kwatanta alkairi ga ya khaleel koda baikai Quarter d'in Wanda shi yake musubama.

Saikuma ga 'yan Canada kamar wasa su Anty meerah, Aysha batayi zaton zuwan nasuba, aikam kamar ta had'iyesu saboda murna, babyn Anty meerah Raudat tagirma ko INA yawonta takeyi.
Gidakam ba'a cewa komai, ranar kwanan hira akayi, musamman 6angaren Aysha dayazama dabar yaran mata, duk can suka kwana.

Washe gari aka saka suna a massalacin anguwar bayan anyi sallar asuba.
Akaita sakama yaro albarka.

Muma munce ALLAH yaraya Abdallah Ibraheem Abdallah💋.

Dagananfa shagali yadawo Na mata acikin gida.
Aharabar gidan aka shirya walima iya mata zallah.
Suma su khaleel sunyi tasu daga 10am zuwa 1:0pm, saboda abokan aikinsa da abokansa, aikam nasha mamaki, dannaba k'aramin cika akayi awajenba, shi harma mamaki abin yayta bashi..
And'auki Abdallah anje dashi, ALLAH ya taimakesu kuma baiyi kukaba, yanatama barcinsa, kunsan jariri da barci.
Ansha hotuna kam sosai, lamarin harba'a cewa komai.

4:0pm Na yamma mukuma mukayi namu shagalin acikin gida, babu k'arya munfa cashe, lamarin harba'a cewa komai.
Kai fans kunsha casu wlhy, babufa Wanda banganiba, munci rangam munsha zo6o, kowa saida yaciko jakka dakayan alatu, su o e ina kallonta harda guziri tayi a leda bakko😜, bandai fad'i sunaba ehe😏.

Alhmdllh suna yayi suna, Aysha da Abdallah sunsha gayunsu, nimadai nasaka leshina Na k'aramar sallah nayi k'yau😎, ba'a d'aukar rahoto kawai natsayaba ehe😏.

😂😂😂🤣

Su Taheer sun taka rawar gani wlhy, abin arzik'i harba'a cewa komai, lallai Abdallah yayi goshi fans, ALLAH yabamu farar haihuwa irin tasa🤷🏽‍♀👍🏻.

___________________________

Kowa jikinsa yafad'a masa saboda gajiya, Aysha kanta agajiye take, saboda gidan yakuma cika dole tashiga d'akin ya khaleel dantad'an gasa jikinta susamu su kwanta, toilet d'in d'akinta bak'i nata layin shiga.
Batayima zaton yana gidanba.
Aikam babu kowa ad'akin, ta sauke Abdallahd dake goye abayanta yanata barci, Ammah tace dolene taringa goyashi yanajin d'umin bayanta, yanzuma ana kiran sallar magriba tace tad'aukesa tagoyashi, karkuma ta saukeshi sai anyi sallar isha'i, babu yanda Aysha zatayi dole tagoya gudun jarabar Ammah.
Saman gadon ya khaleel ta kwantar dashi, barci yakeyi har yanzu, ta lullu6eshi sannan tashiga bayin. tana shiga kamar jira yaro yafara kuka yana wuntsila 'yan k'afafu sama.

Ya khaleel ne yashigo d'akin danufin d'aukar Abu yafita, dan 6angaren baffa yakwanama jiya.
Da sauri yak'araso gaban gadon yana fad'in ''ya salam, jenior miyafaru kaikad'ai ad'aki? Ina A'eeshan?".

😂ni dariyama yabani, kaikace yaron zai amsa masa tambayoyinsane🤣.

Ya d'aukesa yasaka akafad'a yana jijjigashi, saikiran sorry yakeyi, sorry my Darling, bar kuka kaji".
Aysha Na toilet tana jiyosu, aikam taita dariya, kusan mintuna 20 saigata tafito, bud'e k'ofarne yasaka khaleel juyowa yana kallonta.
"Yanzu dama kina cikin d'akinnan Amma kika barsa yake zunduma kuka haka".
" kai Sadauki, wannanne zunduma kuka? kumafa wanka nayi, ajiyesa kenan nashiga wanka yafara kukan, ALLAH yaronnan yacika wayon tsiya, shikenan dayaji babu motsin mutum kusadashi sayaytama mutane kuka? ALLAH akwai takura, shikenan banida aikinyi saina gadi, yanzuma damutane kenan, inaga kowa yatafi kuma?".

"To minene aikin naki idan ba rainonmuba?". 'Yay maganar yana sakkoda junior daga kafad'arsa'.
Aikam idonsa k'yar abud'e.
Dariya ya khaleel yayi, yasumbaci kumatunsa, ''sholy zokiga abin dariya, waifa idon yaronnan k'yar abud'e".
Dariya itama tayi, tamatso kusadasu.
" to kallafa dan ALLAH, anya bakai jenior yabiyo wayoba".
"Hhhhh, aikema d'in gwanace afagen wayon, kuma aii dama k'yan d'a yagaji babnsa ko".
"Hakane kam".
'Aysha tayi maganar da dariya'.
Chapter 79 · 0% Book details