← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 83

Sashe 43

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

__________________________
Biki bidiri bired'e, gidafa Alhmdllh yacika da al'ummar Annabi, dangi tako ina sun cika gida, yo kikam harfa 'ya'yan mutum hud'u, momy zata aurar da mufeedah, Anty Mamie, Ramadan, zunnuarain, Amal. Ummie amarya, Shahudah, sai matar uncle ma'aruff k'anin baffah, Naseeba da Hamdiyya, (Dan itama nangidan tadawo za'a had'u waje d'aya ayi kawai.
Aikam gida dai ba'a magana, mama ma dabazata aurar dakowaba danginta dank'am da gida, su Yaya fadeelah, hafsat, Ummah, Anty nasarah matar ya Qaseem duk suna nan, harda matan kawu bilyamin, da babbar 'yarsa, saikuma Rufaidah da Safiya amare, kowacce da cikinta, su Rufaidah anata zubar da yayu.
Aiko Aysha tatasosu gaba da dariyar mugunta, wai daga yin aure harsun sami ciki.
Yaya Hafsat tayi dariya tana kallon ayshan, tace, "hummm Aysha kema wannan k'yawun naki aii inkaji gangami da labari, kinga yanda kika k'ara 'Yar k'iba kuwa, harda wasu hips na musamman, gawani bala'in k'yau dakikayi, anya ya khaleel Na kallonki kuwa?.
Kwa6e fuska Aysha tayi, tatashi daga d'akin mama tafice, dama anan suke hirar, tun isowar mutanen kanon da safe Aysha tadawo tsakkiyarsu anatashan hira, tayi kewarsu sosai.
Maganar Yaya Hafsat tasakata fita, danta Sosa mata inda yake mata k'aik'ayi, tun jiya yakamata ya khaleel yadawo gidan, amma shiru, har tayata su maleeka sukayi tagyara 6angarenta, suna shirya masa abinci. Amma har dare babu labarinsa, tasha kuka kuwa da daddare, da safennanma haka tatashi cikin bak'in rai, zuwansu yaya fadeelah nema yasakata d'an sakin jikinta.
Tunani yatafi da hankalinta wata duniyar baki d'aya, jitayi anyi sama da ita kawai.
Zaro idanu tayi waje, cikin matuk'ar firgita, wanene ya d'auketa, jikinta sai 6ari yakeyi takai dubanta kansa.
Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki, ''sadauki! Yaushe kadawo?".
Kashe mata ido d'aya tayi, yana wani k'asaitaccen murmushi, saida yatura k'ofar 6angarensu yashiga sannan yabata amsa.
"Yanzunnan nadawo".
Shiru tayi bata tankaba, saima hawaye data kamayi.
Harsuka isa 6angarensu tana kuka, shikuma baice mata komaiba, tana rik'e a hannunsa yasaka key d'in yabud'e k'ofar falonsu.
Bai ajiyeta a faloba yanufi d'akinsa kai tsaye da ita, yasan yayi laifi dolene yayi lallashi.
Ko ina tsaf yanata tashin k'amshi, saboda gyaran dasukayi masa jiya, kuma yauma batareda sanin Aysha ba Anty Mamie ta turo tasleem takuma gyara Inda k'ura ta sauka.
Saman gadonsa kawai ya d'ireta, takara k'arfin kukanta tana bubuga k'afafu yanda yara sukeyi Idan ansakasu kuka.
Bai kulataba nanma, yaje ya kulle k'ofar yahau cire kaya, Aysha kam bata gajiba tacigaba da ta6ararta😜.
Toilet yashiga, kusan 20minute yafito d'aure da towel, alamar wanka yayi, jikinsa kawai ya goge yad'an fesa turare yasaka boxer ya haye gadon.
Jawo Aysha mai kukan shagwa6a yayi jikinsa, tanata tureshi itakuma alamar karya ta6ata.
Cikin sigar tsokana yace, "o, Sholyn sadaukinta bagani nadawoba to, kema kinsan aikina aii, sai kinamin uzuri, haka Nike kullum tamkar kud'i, koda yaushe acikin yawo nake".
" amma inda bakada mata kake wannan yawon, aii yanzun saika tuna Kannada ita ko......
"Umh hakane kuma, yakatseta da Sauri, zata k'ara magana ya d'ora bakinsa akan nata🤫...
🏃‍♀🏃‍♀.

__________________________
Biki kam dai ba'a cewa komai, gida yagama. rikicewa, baka ganin kowa ba'a ganinka, duk son d'aukar rahotona Na tsiya dole Na hak'ura, nakoma gefe nazuba idanu.

Karfe 10am aka d'auro auren Zunnurain da Amaryarsa Maryam, sannan aka d'unguma misali 11am aka d'auro Na zunnurain da amaryarsa Samha.
Tom angwaye saimuce ALLAH ya sanya alkairi😂😂😂.

Misalin 1:30pm bayan idar sallar Azhur aka d'aura auren mufeedah & Ameenudden, sai Hamdiyya & Abdul-Hakem, Amal & Adams, Shahudah & Anwar, Naseeba & Najeeb, ubangiji ALLAH ya sanya alkairi amare da angwaye, su babban Yaya ya khaleel sai baza babbar Riga akeyi, angwaye kam aii ba'a cewa komai, su Adams da ya Ramadan baki kamar ya yage😂, hakama amare sunsha k'yau acikin gida, kamar zasuje gasar sarauniya k'yau.lol.
komai yana cigaba da gudana cikin tsari, acikin gidama mata nata shigi da fici da shagalinsu.
Amma banda Aysha da zazza6i yarufe, su Rufaidah na 6angarenta tun jiya, a can suka kwana, hirar family d'insu sukeyi, dauriya kawai Aysha dake kwance a 2seat takeyi tana jefa magana a first tasu, Sadiya ce ta fahimci kamar ayshan batada lfy.
Tace, "Aysha lfy kike kuwa?".
" eh mana sadiya mikika ganine?".
"Naga sai hura hanci kikeyi, kamar kuma a wahalce kike magana?".
''A'a wlhy, kawai gajiyar aikice".
Hararta Sadiya tayi, tace, " aikinmi kikayi agidannan Aysha?, tun d'azun kina like da ya khaleel a d'aki, sai 9 kuka fito, kijimin 'Yar rainin senses ".
Dariya duk sukayi. Amma banda Aysha data harareta itama, to gwaggo mai tsari, sokike nabarsa shikad'ine? Ke haka kikema mijinki da har kika k'unso ciki?".
Hhhhhh mi kowa zaiyi ba dariyaba, dama Aysha da sadiya inhar suka had'u sai anyi tsiya, kamar sakone da sako aii (like nida Anty Ruk'ayya maikan goruba😜😂🤭).

Abinci suketaci, Aysha na kwance tana kallonsu, babu abinda ke bata sha'awa a abincin, sai wani kallonsu takeyi a yatsine kamar taga gotta.
"K dallah malama kidaina mana wannan yatsine-yatsinen, idan bazakici bane babu dole, ki d'auke kanki mana". 'Rufaidah tayi maganar tana harar Aysha'.
Baki Aysha ta ta6e, ta kauda kanta daga kallonsu, tajuya kwanciyarta tama basu baya.
Babu Wanda yasakebi takan Aysha, sukaita shagalinsu da abinci. Ita daga nanma barcine ya kwasheta.
An idar da sallar la'asar ya khaleel yashigo gidan, bayan yasamu mutane sund'an lafa musu, saidai cikin gidan dank'am yake da mata, har 6angarensu dayake anan 'yammatan amare suke, 6angaren ya sultan, danshi yad'anfi sauk'in kai, mujahedeen ma halinsa d'aya da ya khaleel, shiyyasa basu cika sakewa a wajensaba, balle yau yana gida.
Babu wacce ta isheshi kallo yashige 6angarensa, su Rufaidah suna bedroom d'in Aysha, wasu na sallah wasu na gyara kwalliyarsu.
Aysha na falo tana barci, Dan basu tada itaba, tunda sunga tanajin dad'in barcin.
Harya wuce zai shiga d'akinsa ya hango Aysha na Neman fad'owa daga kujera.
Da sauri yak'araso cikin falon, ahankali ya d'auketa gudun karya tada ita, yana jiyo hayaniyarsu maleekah ad'akin Aysha, saikawai yawuce d'akinsa da ita, ya shinfid'e agado yana mai kallon face nata, mamakin irin kyawu da farin da ayshan tak'ara yakeyi, yakai hannu yana shafa sumar kanta ahankali, gashin gaban goshinta kwance luf-luf, cikin tsanaki yakebin dukkan illahirin jikinta da kallo, shi saiyagama kamar tad'an k'ara k'iba, ga fatarta harwani k'yalli takeyi, gashi gazar-gazar duksun fito taciki k'ofofi dasuka k'awata shek'in fatarta.
"Sholyna wane irin k'yawune haka?, ga jikinki akwai d'umi kamar bakida lafiya". 'yay maganar yana sumbatar goshinta'.
Kusan mintuna 12 ya lalata wajen k'arema Aysha kallo, sannan yamik'e ya canja kayansa zuwa k'ananun kaya, wani d'an aiki yakeson fita shi kad'ai.
Harya gama kimtsawa yafice tanata barcinta.

Sai wajen 5 Aysha ta farka, sai zubama su Rufaidah masifa takeyi wai basu tasheta tayi sallah ba.
" yo aii bamu kad'ai zakiyima jarabarba, saiki bari ya khaleel ma yadawo ki had'a dashi, tunda shiyya d'aukeki daga falon yamaida bedroom, amma bai tadakiba, kujimin yarinya kai, kodanmu kin gama rainamune?".
Banza Aysha tama sadiyan, tasan inta biye mata bazata huta da surutuba.

____

Zuwa 9pm duk angama kai amare d'akunansu, ankawo nasu Ramadan 6angarenda su ya khaleel suke, suma anan aka musu gininsu.
Babu inda Aysha taje, Dan ya khaleel yahana, yana gida yakasa ya tsare, dole ta hak'ura, Dan itama batajinma dad'in jikinta sosai.

*_ABINDA KA SHUKA........._*
(sabon buk d'ina mai zuwa insha ALLAH)😉.

Masu iya magana kance abinda ka shuka shizaka girba.
(Wannan batu haka yake)
Asafiyar litinin misalin 11:30am bak'i wasu duksun tafima, wasu kuma na haramar tafiya kamardai mutanen Kano, dake shirin tafiya amma amai da Aysha tawayi gari tana shek'awa yasakasu dakatawa.
Ana tararrabin ciwon na Aysha wadda yasaka ya khaleel rikicewa saiga mufeedah da 'yan rakkiya har mutum uku, tana rusarkuka.
Cirko-cirko kowa yayi, a tsakar gidan, Dan ya khaleel ne d'aukeda Aysha zai saka amota zasu tafi asibiti, yunk'urin amai datakeyine yasakashi sauketa k'asa, yana rik'e da ita tana tsaka da kwara a man m
ne motar 'yan rakiyar mufeedah tashigo gidan, ananne wasu suka raba hankalinsu biyu lokacinda akaga mufeedah tafito a motar tana sharar kwalla🤐...................✍

*_"yaro bari murnar karenka Yakama zaki"._*👉🏻🐅😱

*_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_

*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

_hummm kunata yad'a jita-jita feedohm tarasu, inaga wataran sai wata tace agabanta aka saka gawar wata writer a kabari, to da ranta, haka kawai kudinga jamata bala'i, wai tayi had'arin mota, please mana, haka babu k'yau, duk masoyinka Na kwarai bazai gizganya masifa a kankaba, mutuwa dolece, kokun fad'a kobaku fad'aba zamu mutu aii, amma adaina jamana masifa please._
*duk wadda ta rubuta kuma ALLAH ya shiryeta, ammafa jakace wlhy tunda ta d'auki alhakin mutane, mtsoow.*

3⃣0⃣
Chapter 43 · 0% Book details