← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 83

Sashe 76

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

" mama sunfita itada baffah, ummi Amarya kuma kanta ke ciwo ta kwanta, Anty Mamie tana d'aki itama."
Batareda yace komaiba yanufi d'akin Anty Mamie, saida yay knocking tabashi izinin Shiga sannan yatura k'ofar yashiga da sallama.
Da Aysha yafara cin karo zaune kusada Anty Mamie tana bata dambu abaki.
Suduka idonsu nakansa, duk suka masa sannu da zuwa.
A sanyaye ya amsa yanamaijin k'aunar mahaifiyarsa har cikin ransa. K'arasowa yayi ya zauna d'ayan gefen Anty Mamie shima.
"Babana andawo?".
Kansa ya jinjina mata, ya d'ora kan nasa agefen kafad'arta yana kallon Aysha, yace, " Mamie kidaina shagwa6a yarinyarnan, jiyafa ta6ara taitamin iri-iri."
Aysha tad'an murgud'a masa baki, tana fad'in "jealousy kawai".
Anty Mamie kam 'Yar dariya tayi, " babana aidolene Na shagwa6ata, bakaga ba ita kad'ai baceba, yanzu hakama abinci taci tayi amansa, shine matar zunnurain tayi dambu takawo mata, inad'an lalla6atane tanaci".
Rankwashi khaleel yamata agefen kanta, takuwa kware baki ta zabga k'ara tareda dafe kanta.
Da sauri Anty Mamie ta rungumota jikinta, shima tamasa rankwashi biyu akansa.
Dafe wajen yayi yana fad'in "uchhhh, dazafi wlhy Mamie".
" oooh kasan dazafin amma kama yarinyata? duk wata mugunta ka iyata babana salo-salo ko?".
"ALLAH Anty Mamie yarinyarnan batada kunya, kigafa murgud'en takemin harda gwalo? kibarni kawai Na caskalata".
Cikin 'Yar dariya Anty Mamie tamik'e daga tsakkiyarsu, ''kunga kutashi kuje 6angarenku, bazan iyaba dawannan rikicin, kuje wajan Ammah Tamuku shari'a".
" uhm tab, lallai Anty Mamie, yanzu naje wajan jar wuya aii bakina saiyaje gate, dama haushina takeji nak'i saya mata mota.
"Hhh kunfi kusa aii".
Jakkarsa Aysha tad'auka tafita tana dariya, tabarsu dansud'an gana.
Binta khaleel yayi da kallo yana murmuahi da jinjina hankali irin nata, yamaido kallonsa ga mahaifiyar tasa, wadda itama ayshan tabi da kallo murmushi d'aukeda fuskarta.
Khaleel yamatso kusada Anty Mamie, hannunta Na dama yakama ya sumbata, sannan yad'auki hannun yad'ora bisa kanta, murya amarairaice yace, " Mamie Na kisamin albarka, a office an za6eni cikin wad'anda zasu gana da shigaban k'asa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma nine shugaban dazai jagoranci kwamitin ma, wlhy duk fargaba tacikani, tunda safe naketa tattara bayanan dazanyi agaban shugaban k'asa ina kwancewa, narasa wanne zan d'auka, gashi inason kai kukana akan manyanmu danake zargi da hannu a k'ungiyar su momy."
Murmuahi Mamie tayi, tashafa fuskarsa da d'ayan hannunta, murya a sanyaye tace, ''karkakji tsoro babana, nasan kaid'in jarumine kuma jajurtacce, kasaka aranka CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI, shugaban k'asa mutumne kamar kowa shima kuma yanada sauk'in kai, danhaka karkaji tsoro ko shakkar ganawa dashi, katuna bayaune kafara ganawa da shugabannin k'asashen duniyaba."
"Duk inda kake addu'ata nabiye dakai, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, yatsareminku aduk inda kuka tsinci kanku, kaje kayi wanka kahuta danka samu isashshen lokacin kanka".
" idonsa cikeda kwallah yace amin Mamana, farincikina, haske mai haska rayuwata, ALLAH yak'ara tsawon rai mai amfani da ingattacciyar lafiya", 'yak'are maganar da sumbatar hannunta'.
Jiki a sanyaye yamata sallama yafice.
Hawayenta tashare, tana murmushi, ahankali tace, "ALLAH Na gode maka".

6angarensu yanufa, dan baiga Aysha ananba, yasan tawuce.

Agurguje😎

___________________

Washe gari su khaleel suka samu damar ganawa da shugaban k'asa, sunsami tarba mai k'yau daga fadar shugaban k'asa, sunkuma tattauna muhimman abubuwa dazasu kawo cigaban k'asa, dakuma yanda za'a dak'ile ta'addancin dake faruwa ak'asarnan.
Sund'au tsawon awanni kusan 5 taredashi, tarema sukayi lunch da president da tawagarsa, yamusu jinjinar bangirma tareda k'yaututtuka masu k'yau, musamman ma khaleel saboda k'ok'arinsa, sannan suka gana da 'yan jaridu Na awa d'aya.
Sunyi sallama da shugaban k'asa suka tafi, bayan khaleel yabama wani makusancin shugaban k'asar short note domin yabashi.😎👍🏻

________________

Akwana atashi babu wahala wajen ubangiji, kwanaki Na Sauri sati Na gudu, watani tamkar sati ya koma.
Acikin wannan gudun fanfalak'e da suniya takeyi yau ga cikin Aysha yashiga watanni takwas.
Abubuwa masu yawan gaske sunfaru awannan tsakanin, ciki harda kammala bautar k'asa da Aysha tayi, (Nysc) Alhmdlh tagama cikin nasarori.
Rufaida da sadiya duksun haihu, Aysha kuma taje har Kano suna, kwannta 8 a can, saboda khaleel baya k'asar alokacin, amma da k'yar yabarta taje.
Matar youseef ma ta haihu baby boy itama, hakama bishirah, ta haihu, da k'yar khaleel ya yarda Aysha tabi gwaggo bintu sukaje suleja suka mata barka.

Mufeedah ma baiwar ALLAH, anata Jan ciki, ita harma tashiga watan haihuwarta.

Ansaka bikinsu hasnah, watanni hud'u kacal, harda musleem dasu maleekah ma, baffah yace gwamma ya aurar dasu kawai yahuta baki d'aya, yazauna da 'yan k'ananun 'ya'yansa su ummunoor.

*******
Momy dai ana nan anata shan jinya, amma jikin NATA da sauk'i, saboda tana samun kulawa, Idan tayi magana anaji yanzu, sannan tana motsa hannunta kad'an-kad'an.
da k'yar khaleel ya yarda yashiga ya ganta tana barcima lokacin, danhaka batasan yajeba, yafad'ama su baffah suma sunje sun ganta.
Babu wanda bai zubar mata da kwallaba ganin yanda duk ta lalace, ta canja kamanni kamar ba itaba, k'ibarnan dukta zube.
Hawaye taita zurarrwa saboda ganinsu, magana take amma basajin mitake fad'a, dole suka hak'ura.

Saida Baffah yayta lallashi daban magana sannan khaleel yayarda yasakko innah jummai, amma da yasaka anyi rammm da ita a station d'in su, yace anan zata k'are sauran rayuwarta.
Saida k'yar da lallashi yayarda yasakota.
Rasa inda zata nufa tayi kuwa, doledai tadawo gidan mak'iyar tata Ammah, suna zaune awani yammaci kawai saigata tamkar an jehota.

ALLAH Sarki d'an uwa mai dad'i, saiga Ammah takar6eta da hannu bibiyu, suka rungume juna suna kuka, daneman yafiyar juna.
Annan innah jummai tazauna sabodama batada isashshiyar lafiya, ciwon k'afa da hawan jini.😏

____________

Su khaleel duksun gama shirye-shiryen kai k'ungiyar su momy kotu, sunsami nasarar cafke sauran mutanen dasuke zargi, dakuma kar6o Na k'asashen k'etare, ciki harda manya-manyan mutane wad'andama bazaka ta6a tunanin akwai saka hannunsuba............✍🏻

🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀kumuje zuwa yanda zata kaya a kotu, dolene masu laifi su kar6i hukuncinsu ahannu😎🖐🏽.

🤕yanzu saboda buk yazo k'arshe, ankama muku hajia babba shine babu comments ko, aiko zan ajiye nak'i k'arasa typing d'in😎, rashin comments d'inkuma yasakani jin gandar typing d'in wlhy,☹.
Idan naga ruwan comments yau, kwaji yanda takaya gobe, idan naji shiru, nima nawuni barci abuna yafimin dad'i😏😏.

Yawan comments, yawan girman hukuncin su hajia babba😎😎😎👯‍♀

*_I love you all_*💋💋💋💋
[10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_

*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

_ina kike *Asy khaleel*?, wanga page nakine, babanki khaleel namik'o gaisuwa ta musamman, taredani bilyn Abdul😊._👍🏻

Kuma banmanta dakuba wlhy.

Fatima Abubakar, Ummi Alhassan, Rabi Sanusi, Aaliyah, Fatima, Zainab Ahmad, Xeety, Sameera Bello.

Alkairin ALLAH ya iso gareku💋💋💋💋❤🤝🏻

4⃣9⃣

*_Monday morning_*
_Cote_.

A yau ranar litinin 8/9 aka shiga shari'arsu momy, abbabban kotun k'asa da k'asa ta Abuja.
Anyi zammne misalin 10am, tareda lauyoyi masu kare gwamnati dakuma lauya mai kare 'yan ta'addar wannan k'ungiya.
Bayan Alk'ali ya saurari k'arar dakuma jawabai abakin lauyoyin guda biyu.
Am fafata sosai, amma ba a yanke hukuncinba, sai azama Na gaba insha ALLAH.

Ran khaleel yad'an 6aci, soyayi ayita kawai yau ta k'are, amma babu komai, ALLAH ya kaimu randa alk'alin yasaka.
Chapter 76 · 0% Book details