← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 83

Sashe 41

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin takunsa Na jarumta da isa yake tafiya, yanayinshi kawai zaka kalla kagane ransa a 6ace yake, sunshiga inda akan ajiye gawawwakin wad'anda wahala tasakasu mutuwa, ko aka kashesu, kokumadai Abu mai muhimmanci yasaka aka ajiye gawar tasu, Dan ayi bincike akanta.
Ma aikatan wajen sai k'amewa sukeyi, kasancewar suma police ne, amma likitoci.
Bakai tsaye su ya khaleel suka shiga wajenba, saida aka basu wata Riga suka saka, suka rufe dukkan jikinsu👨🏻‍🚀, har hannayensu da hanci sannan suka shiga, doctor Sadam mai bincike akan gawar David yabud'e abinda aka lullu6eshi, bayan anjawo gawar daga cikin wani glass, fitulu aka kunna saitin gawar David.
Doctor Sadam yabama khaleel wata fitila mai haske🔦, suna haska damtsen hannun David Na haggu saiga hoton kunama🦂.
Hoton wajen Joseph ya d'auka har sau biyu sannan suka fito.
Ahanya khaleel kecema Joseph, ''wato da muna aikine a birkice, ko kad'an mun Gaza samun bakin zaren matsalarmu sai a yau, tabbas akwai masu laifin dake da alak'a da juna a setetion d'innan, amma wad'anda suka kashe David basusan wannan sirrinba, mu kanmu bamusan da hakanba, wannan tambarin kunamar yana nufin tambarin wata k'ungiyane kenan?".
Maganarka gaskiyace sir, amma ya akayi kagane wannan tambarin kunamar?".
Ya khaleel bai bashi amsaba har suka k'arasa office d'insa, yacema Joseph kiramin Taheer, youseef. Adams, & Solomon".
☎duk yagama kiransu cikin mintuna k'alilan.
Babu dad'ewa saigasu sunzo.
Yana shan shayin daya had'a suka shigo, kowa yazo saiyayi gaisuwa sannan ya zauna, kowa yayi shiru yana sauraren boss.
Khaleel yamik'e hannunsa d'aukeda mug d'in tea yanasha a hankali, idonsa a kansu, "kunsan dalilin kiranku?".
Atare sukace a'a sir!.
Remote yad'auka, ya danna TV d'in office d'in, saiga hoton kunamar dasuka d'akko ajikin gawar David, "wannan kunamarce, ita wannan kunamar takasance tambarin nawata k'ungiya, kuma nasameta ajikin David, ranar Taheer kasanarmin kana zargin alak'a tsakanin David da barau modibbo ko?, to yanzu inason abinciki wannan kunamar ajikinsa, bama shi kad'aiba, harda duk wasu criminal's da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi kamar David, sannan David yana safarar yara shima, kenan dukmai alak'a dashi akan bigire d'aya suke?".
"Zamu gudanar da aikinmu da lura, shiyyasa Na taraku kud'in amintattuna, bana buk'atar asaka wasu yara a aikin, dakanmu zamuyi, saboda akwai magoya bayan su David acikinmu, wannan ne yasakasu kasheshi dankar yafad'a mana komai".
Gaba d'ayansu suka jinjina kai.
Adams yace, " sir!, aikuwa akwai wannan hoton kunamar a hannun Moxies".
"Da gaske"?.
" am telling you sir".
"Kenan Moxies yanada alak'a da David?".
" zamu iya cewa hakan".
To inkuwa hakane, Ku bincikamin Ruth da aka kama da yara a air port zataje Dubai, sannan Solomon miye labari gameda bincike Dana sakaku akan email d'in sirri da'aka turo sunayen su Ruth aciki?".
Sorry sir, munata k'ok'ari, amma gaskiya mai email d'in mutumne mai wayo, Dan saida yabi matakan Kare kai daga binciken kwankwanto kafin yafara aikinsa, kuma tabbas yasan computer sosai, inhar ba k'arya zan makaba zan iya cewa bamu samo komai game dashiba, saidai kuma yin maganar kunama mai tambarin k'ungiya yatunamin dawani Abu, tabbas mai email d'in yasan wani Abu dangane da wannan k'ungiyar, domin duk sak'on dazai turo akwai hoton k'aramar kunama da bindiga kusada ita, bara kaganai". 'Solomon yay maganar yana bud'e laptop d'insa, mik'ewa yayi yay connecting da TV d'in office d'in, tana gama searching saiga jerin sakwannin mai email d'in sirri, acan gefe mak'ale kunamar take, 🦂🔫, sannan an nuna kunamar da bindiga.
Huci mai zafi ya khaleel ya furzar daga bakinsa, ya ajiye kofin hannunsa tareda matsawa jikin tvn, nazarin komai yakeyi cikin kwarewar aiki, saikuma ya jinjina kansa, yajuyo yana kallonsu youseef, ajerin sunayen damai email d'in yaturo guda biyar, macece ta uku, kuma yabamu tabbacin zata sauka Nigeria aranar 17-ga watan 4, watan dazamu Shiga kenan, zata tasone daga k'asar Malawi, ta sauka Dar es salaam, babban birnin Tanzania, washe garine zata k'araso Nigeria. Jirginta zai sauka a Kano state ne, daganan yabamu za6in kamata a Kano, kokuma a Abuja, acewarsa wannan yarage namu, shi yagama nasa".
Gaba d'ayansu sunyi shiru, kowa da abinda yake tunani, ya khaleel yakatse shirunsu dafad'i "so ina jinjina kwakwalwar mai email d'innan, koda criminal ne shi tabbas yanada kwakwalwa, kamar yanda yabamu satar amsa akan kama Moxies haka yabamu akan wannan matar, saidai bazamu saki jiki kai tsaye da bayaninsaba, saboda tsaro".
Youseef, kaida taheer Ku tattaramin bayanin David, da Moxies awaje d'aya, tunda sunada alak'a da juna, Joseph kaida Faruk da Mahfouz kucigaba da bincikamin Duk wani mai wannan tambarin dake a setesion d'innan, Solomon kanemi su Kausar acigaba da bibiyar mai email d'in sirrinnan, nasan dolene watarana yayi kuskuren dazamu samu wani bayani akansa".
"Nida Adams da Samuel Zamu cigaba da farauta".
" komai yazama da kula, banason kuskure kuma kunsani, duk Wanda yamin wasa da hankali acikinku koyaci amanata wlhy dakaina zan fasa kwakwalwarsa da bullet, koda kuwa cikinsu youseef".
Ku kula da k'yau, Adams ina buk'atar Ak'ilu Abbas agabana yanzunnan, kukuma zaku iya tafiya".
Atare suka mik'e baki d'aya, duk sukayi salutes d'insa, murtani ya maida musu, sannan yakoma kujerarsa ya zauna, sukuma duk suka fice.

___________________________

"Aminiya agarin Yaya kikayi sakaci baici maganinnanba?, anya kuwa kinsan bala'in dake tinkaromu?, kekankifa kinama cikin saka idanun k'ungiya, dansu gano cewa Ibraheem d'ankine, kuma shine yake mana tsinci d'ai-d'ai, k'ungiya ta bada date d'in daza'ayi zama Na musamman domin Ibrahim kai tsaye, Alhmdllh munsami damar ku6tar da talatuwa daga hannun police, Dan munyi gamo da d,p,o kwad'ayayye, yanzu haka talatuwa Na gida".
"Alhmdllh, naji dad'in hakan, sannan karki damu aminiya rashin cinsa bashi yake nuna ya tsiraba, Dan nakafa masa wani tarkon ma, k'ungiya kuma zan fahimtar dakowa komai kai tsaye, Dan banason d'ana yafuskanci wani Abu daban, inasonsa fiyeda tunanin mai hakali".
" tsaki kawai hajia khaltum tayi, amma batace komaiba".
Hajia babba tace, "aminiya zan kashe matar Ibrahim".
" miyasa? aminiya, ita mitamiki?".
"Kinsani aii".
Dariya hajia khaltum tayi, tace, " bazan hanakiba aminiya, dama a k'ungiyance kisa yarinyar ya cancanta agareta, saboda gudun tonuwar asirinmu, dannasan wani daga cikin sirrinmu. Damacan ina shirya abubuwa akanta tuni, sonake sai mungano Inda meerah take, kisan Aysha tamkar munkashe macijine bamu sare kansaba, inhar meerah Na numfashi a duniya, wannan ne dalilin dayasa nabar Aysha bansake waiwayartaba".
"Shikenan aminiya nabar komai a hannunki".

Aysha dake bayan windown hajia babba tazaro ido, danjin maganar su momy, dasauri tabar wajan tana sauke numfashi, tabbas maganar su tadaki zuciyarta, amma bata tsorataba, haka takoma 6angarensu tana juya maganganunsu, takira Anty meerah ta zayyane mata komai.
" lil sholy kibani kwanaki biyu zanyi tunani, kema kiyi tunanin mafita saimu had'a tunaninmu waje d'aya muga miya dace muyi".
"Shikenan Anty meerah babu damuwa".
Yauwa ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH babu abinda zai cutar damu, kisa aranki *_CIKI DA GASKIYA..._* wuk'a bata hudashi da yardar ALLAH".
" To Anty meerah ngd".
"Aha saimunyi waya".

Bayan Aysha ta yanke wayar takwanta taci kukanta, da mamakin hatsabibanci irinna momy da hajia khaltum, lallai tasan zukatansu sun gama bushewa.
Dama dawowarta daga aiki kenan, driver ya ajiyeta saiga hajia khaltum, shinefa tabi bayanta ta mak'ale ta window hartajiyo abinda suke tattaunawa.
Saida tagaji da tunane-tunane sannan tatshi tayi wanka, kichin tashiga ta tanadarma ya khaleel abinci kafin yadawo, dukda batada tabbacin zai shigo gidan dawuri, tunda wani lokacin yakan kai 10 Na dare a office ma.

_______________________
A d'arare Ak'ilu Abbas yashigo office d'in, shima sanye yake da uniform na police Interpol, saida ya k'ame tareda salute d'in khaleel sannan yabashi izinin zama.
Ya khaleel yad'ago manyan idanunsa ya sauke akan Ak'ilu Abbas, shikuma saiyayi k'asa da nasa idon, Dan mara gaskiya baya iya kallon ya khaleel ido cikin ido.
Murmushi ya khaleel yayi, yajawo iPad d'insa yamik'ama Ak'ilu Abbas.
Kar6a yayi cikeda mamakin mizaiyi da itane?.
"Nasan kana mamakin mizakayi da ita ko?, akwai game aciki, kuma shikad'aine, inaso kaje kayishi, iya inda kasamu game over kakawo min, idankuma kawuce abinda kasamu har sau uku to zan gane zaka iya tafiya".
Cikin rawar murya Ak'ilu Abbas yace, " sir? Nikuma miye had'ina da game?".
''Basai kasaniba, banason yawan surutu jeka".
Duk Ak'ilu Abbas ya rikice, baisan dalilin yin hakanba gareshi, tabbas yasan wanene j!, kuma baya Abu saida manufa.
Koda yak'arasa office d'insu su kusan 20 aciki, sai yake gayama abokinsa wanda sukafi shak'uwa.
"Tab wlhy Ak'ilu kashiga tarkon Oga kawai, shiyyasa naita kwa6arka al0kacin amma kak'i, yanzu wa gari ya waya".
" please Sha'aibu kabani shawara mana".
"Yoni shawarar mizan Baka?, kayi abinda yace kawai".
Shiru Ak'ilu Abbas yayi, Dan yasan shi'aibu ma mutumne mai gaskiya, aransa yace shikenan nashiga uku nikuma, anbani kud'i Na aikata abinda zaiyi sanadin k'ask'antuwata, gashima kud'in harsun zama labari, tunda naje karuwai sun cinye .............✍🏿

Nidai nace, " hummm".

*_Ayya my sweet Xoxo, ALLAH yabaki lafiya, yasa kaffarane, yatashi kafad'a, fan's Ku had'o kayan dubiya tawan babu lafiya😞._*

*_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_

*_part 2_*
(littafi na biyu📕)

2⃣9⃣
Chapter 41 · 0% Book details