← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 83

Sashe 67

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka tace, "bazan ta6a nutsuwaba ya khaleel, sai mahukuntan k'asarnan sunyi tsawatarwa akan 6arnar dake faruwa ga mata, gidanjen aure bamu tsiraba, kullum mace tana fama da damuwa, idan zaka zauna da mata dubu to wlhy d'ari tara acikinsu dukzasu fad'a maka suna zaman aurene saboda 'ya'yansu, ammafa badan jindad'i agidan aurenba, kullum mace saidai ta karanta tattali da soyayya a cikin novels, shiyyasama wasuma suke ganin zak'ewar writers wajen rubuta yawan tattali da soyayya anovels, sabida su basa gani agidajen aurensu, shiyyasa mata sukafi kowa yawan kallon films, saboda anan kad'ai suke ganin ana sayyaya maiban mamaki, ba'a barmu agidaba, ba'a barmu amakarantaba, lectures da students 'yan uwanmu kullum suna farautar mutuncinmu, sunsan dukkan hanyoyin dad'in baki dazasubi domin janye hankalin yarinya su lalatata, lectures kullum suna kadamu a jarabawa idan mun hanasu kammu, sukan bama wadda tabiya buk'atarsu koda bata cancanci samun wannan makinba, ta wannan hanyar anruguza rayuwar wasunmu bada sonsuba, a offices ba'a barmu ba, kullum manya nasama damu farautar rayuwarmu sukeyi, idan kin bada had'inkai a k'ara miki girma, idan kin bijire a k'ask'antar dake ko'a koreki daga wajen aikinma gaba d'aya. K'ananun makarantu Na primary da secondary nanma mata basu tsiraba, komin k'ank'antarki sai'an samu malamin dazai dinga bibiyar mutuncinki, kan hanya kullum taremu ake ana mana fyad'e, yaranmu da manyanmu, amma koda ankai kotu babu wani Abu da alk'alan sukeyi, k'arshema sai a koro k'arar ace bakuda shaidu, idan kuwa an yanke masa hukuncin to bazai wuce Na shekaru uku ba, kuma harda tara, daya biya taran shikenan sai'a sakeshi ya tsira, itakuma ya haddasa mata bak'incikin dahar tamutu bazata ta6a mantawaba, hakama iyayenta, yanzu kuma abin bak'inciki anmaidamu tumakin ciniki akowacce kasuwa, daidai farashinka daidai aljihunka, dakabiya saika kama, shikenan kasamu dabban tirkawa, kullum kabata dusa domin tattalinta, itakuma yunwa da kwad'ayi yasakata lashewa, ribarka sada ita kazuba kud'in aljihu, kokuma kaita ga mahauta su yanka maka, aimaka filla-fillah da namanta kazo ka soya kanaci ahankali kana nishad'i.
Haba ya khaleel, shin maza sunmata uwace ta haifesu? Inhar uwa nada daraja a idanunsu baikamata sudunga keta mutuncin sauran mataba, kosun manta sun haifi 'ya'ya matane? Sun manta matane abokan rayuwarsu? Sunmanta Nana Aysha macece? Sun manta Aminatu (mahaifiyyar Manzon ALLAH s,a,w) macacece? Sun manta Nana Maryam macece?, sun manta Nana fad'ima macece?, sun manta Nana khadeejah macece? Sun manta..... Sun manta dayawa?, shin miyasa darajar kimar mata tafad'i awannan zamanin???.
Mata wannan tanbayar daku nake, kune yadace Ku amsata ba mazaba, domin kune lalacewar kanku, banta6a ganin gidan karuwai Na mazaba, banta6a ganin namijin da suturarsa ta mutunci ta banbanta data banzaba, haba mata, atunaninku shigar banzace wayewa? Atinaninku tallata kankune mutunci?, kwad'ayine da son asani yajefa mata duk cikin wad'anna had'arin Na rayuwa, kuzauna kuyi tunani, kuyi tunanin gyarawa sannan maza suji Shankar keta mutuncinku, kucirema zukatanku kwad'ayi dason burga inhar kunason tsira da muncinku wlhy, idanfa 6era nada sata, daddawafa nada wari, sai bango yatsage k'adandagare kesamun gurin kwana, duk Wanda yakwana lafiya shiyyaso, wani lokacin laifinmu yafi namazan yawa, bazaki ta6a ganewaba saikin nutsu akan kura kuranki..............

Da sauri yatareta tafad'o jikinsa, saboda juwar datayi hajijiya da ita, ak'asa suka zube, rungumeta yayi dak'au yana shafa bayanta, muryarsa a tausashe yace, "kiyi hak'uri hakanan A'eesha, tabbas da ace mata nada irinki dabasu tsinci kayinsu ahalin dasuke cikiba yanzu, namiki alk'awari insha ALLAH zanyi amfani da aikina wajen kawo gyara, koda ban gyara dukaba zanyi iya bakin gwargwado, nasan baza'a rasa mai irin burinaba dazai d'ora daga inda natsaya, ki kwantarmin da hankalinki, kinga bake kad'ai baceba, banason babyna yafara fuskanta damuwa tun yana ciki kema INA buk'atar lafiyarku kinji.
Kanta ta jinjina masa, tana cigaba da zirar da hawaye, shikuma yana share mata, saida yaga tadawo cikin 'Yar nutsuwa sannan yad'auketa suka nufi d'akinta, shirin barci sukayi suka kwanta bayan khaleel yamusu addu'a, dukda yana buk'atarta haka ya hak'ura danya kula yau masu rigimarne akusa, shi baima ta6a tunanin haka A'eesha takeba, Ashe itama akwai zuciya, jiyayi k'aunarta nakuma ratsa dukkan sassan jikinsa da 6argo, ya furzar da huci tareda k'ara k'ank'ameta😉💋.

_____________________________

Kwance take tana kallonsa haryagama tsane ruwan jikinsa, ya d'akko mai yadawo bakin gadon kusada ita ya zauna, idonsa akanta yad'ora hannunsa Na dama bisa gishinta.
"My sholy tunda zazza6in ya sauka kidaure kitashi hakanan kiyi wanka ko?."
Yatsine fuska Aysha tayi tana d'ora hannunta kan nasa, murya a sanyaye take magana, ''ALLAH Sadauki banajin tashinne, bank'i nawuni kwanceba batareda nayi komaiba, gaba d'aya sainaji jikina a kasalance."
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ''karki damu komai zai dai-daita idan cikin yay kwari kamar yanda Amman tace, amma kuma ahaka da kikemin kurin komawa aiki?".
"ALLAH sadauki sonake nagama bautar k'asana cikin salama, kagafa wata biyu kacal ya ragemin".
" hakane, insha ALLAH kuma zaki k'arasa kinji. tashi muje namiki wankan mu shirya, karya zam mukad'ai ake jira kuma".
"Kai sadauki, ina zamujene haka wai? Kuma duk mutanen gidan?".
" basai nafad'aba, kedai kawai tashi Na shiryaki zaki gani aii."
Batace komaiba ya taimaka mata ta sakko, kayanta tacire ta d'aura towel.
Yace muje to.
"A'a kayi zamanka Na hutashsheka, gamma naringa k'arfafa jikina, yanzu kwatsam tafiya ta taso maka wazai dinga tattalina haka? gamma Na daureda koyaya inayin wasu abubuwan ko?."
Kansa ya jinjina mata yana murmushi, azuciyarsa yana jinjina wayo da hikima irinnan Aysha, ita komai nata dabanne.
Mai shima yashafa, sannan yafice d'akinsa domin shiryawa.
Itama Aysha bata 6ata lokaciba tafito, adaddafe dai tad'an shafa mai, tasaka doguwar riga ta material, kayan sunmata k'yau, ta d'aukko madaidaicin gyale tayi rolling, tsaf tafito kamar wata balarabiya, tana cikin zuba d'an abinda zata iya buk'ata koda sun fita a jakka ya khaleel yaturo k'ofar yashigo da sallam.
Bata d'ago ta kallesaba amma ta amsa masa sallamarsa. tsaye yayi abakin k'ofa ya jingina da bango yana kallonta, tamasa k'yau sosai, hardai yakasa hak'uri ya tanka.
"Yanzunan da wannan shigar zaki fita?".
d'agiwa tayi ta kallesa, sanye yake cikin uniform d'in aiki, sunyi masifar zaunamasa ajiki, tajanye idonta ahankali ta maida kan jikinta, " haba sadauki miye aibun wannan shigar tawa?, ko inafa Na jikina arufe yake, tafin hannuna da fuskatane kawai ake gani.
Guntun murmushi yayi, yatako ahankali har zuwa gabanta, jawota yayi jikinsa ya rungumeta, a cikin kunnenta yace, "bazaki ganebane kedai, ina kishin aganemin wannan k'yak'yk'yawar surarne sholyna, ALLAH ya halicceki domin nine kad'ai, danhaka Na haramtama kowa ganeminke."
Cikin jin dad'in kalamansa tashafo fuskarsa, akasalance tace, "ngd Sadaukina, bara Na canja to".
''No barsu, amma next time akiyaye".
"Angama boss", tafad'a tana kanne masa ido d'aya, da salute nashi".
Shima k'amewa yayi yay salute nata.
Atare suka tuntsure da dariya, yakama hannunta suka fice suna cigaba da dariyarsu, idan kagansu dolene su burgeka.
Cikin gida suka shiga, afalo duk suka tadda ahalin gidan, sunyi cirko-cirko suna kallon innah jimmai daketa zuba tsiya, ajiya labari ya isketa, da yamma ta'iso Abuja, saita kwana gidan wata mata dasuke mutunci, shine yau ta k'araso nan gidan domin jin ba'asin kama mata d'iya da'akayi.
Daga Aysha har ya khaleel, babu Wanda ya kalli ko inda take, khaleel ma saiya nufi dining inda su sultan ke zaune suna breakfast shida muhseen da Ramadan.
Duk gaidashi sukayi, muhseen yace, "ya khaleel wai baffah yahana atakama tsohuwarnan birki, please, kamana maganinta mana".
d'an ta6e baki khaleel yayi, yad'au mug d'in shayi yana k'ok'arin had'a shayin, " to inbanda abinka muhseen, tunda baffah yace abarta, aii sai kowa yazuba mata Na mujiya, lokacintane tayi, anjima kad'an koda kud'i aka had'ata tayi tari bazatayiba. kaga mik'omin kularnan tagabanka Ramadan, minene aciki?."
"Fankasunefa yau Anty Mamie tayi agidan, ALLAH nifa banason abinnan".
" saika zauna da yunwa aii, koka saka matarka ta girkamaka wani abun, ai su Mamie nema suka barku, kunyi aure amma har yanzun kuna nane dasu suna wahalar girka muku abinci, Ni kaga Zubamin guda uku".
Dariya mujahedeen dake k'ok'arin zama yayi shida Sultan, Sultan yace, "to ya khaleel kaimafa kana cikinmu, tunda gakanan a tebirin gandu".
Guntun murmushi yayi yana kur6ar tea, idonsa akan Aysha dake zaune kusada Anty Mamie tana 6ata fuska, Anty Mamie nabata abinci abaki, da'alama tsareta akayi kawai.
Ya kauda idonsa yamaida kan Sultan, " aini kasan lalurace yaro, dan matana batada lfyne kawai, amma soon bazaku ganniba anan".
Dariya sukayi gaba d'aya, wadda tak'ular da innah jummai, azatonta da'ita suke.
Dawowa tayi Inda suke tana zaginsu, babu Wanda yama kalli inda take acikinsu, bare tasamu amsa, saima cigaba da firarsu sukayi suna dariyarsu hankali kwance.
Sai kawai innah jummai tafashe da kuka, wai baffah da Ammah Nagani su Khaleel Kecin zarafinta, dama tasan Ammah Ba sonta takeyiba, kaza......kaza...haka taita surutai marasa d'ad'inji, babu Wanda yay koda tari barema ya tanka mata.
Har kowa ya kammala abinda yakeyi suka fito, motoci duk suka shishshiga, ganin haka itama innah jummai tabi ayari.🤣👍🏻

**********

Tafiyar mintoci kad'ance takawosu station d'in su khaleel, kowa yayi mamakin miyasa ya khaleel zai kawosu nan?.
Ganin ya khaleel ma'aikatan wajen sukayo caaaa akansa, sai k'amemasa sukeyi da Salutes nashi, suna tambayar ya jikinsa.
Su Aysha dai sai kallon ikon ALLAH sukeyi da girmamawar da khaleel kesamu daga ma'aikata nak'asa dashi, kuma sunsan wannan yana cikin adalcinsa da sassauci.
Su Kansu sai gaidasu akeyi cikeda girmamawa, kuma abin birgewa musulmai da wad'anda ba musulmanba kowa girmamasu yakeyi.
Ana cikin haka saiga Adams, saida yafara k'amewa da salute Na ogansa sanann Yakoma kan surukansa, ya gaishesu cikeda girmamawa.
Suma cikin fara'a suka amsa masa, da tambayarsa yadawo aiki?.
Yace eh.

Su Joseph ma duksun k'arasu, sun gaida su baffa sannan suka maida hankalinsu wajen khaleel dake magana.

Adams akaisu hall d'incan su zauna, ina zuwa, youseef ina buk'atar ganawa da momy".
Yay maganar cikin d'acin murya.
"OK sir".
Youseef yafad'a a girmamame.
Chapter 67 · 0% Book details