← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 83

Sashe 77

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aysha Na zaune afalo zama da k'yar tashi da dabara, dukda cikin nata bawani uban girma yayiba, kunsan cikin fari dama bakowanne keyin k'atoba.
Sallamar ya khaleel yasakata d'ago ido ta kalleshi.
Cikin murmushi tace, "sannu da zuwa sadauki na, yau da wuri haka?".
Kusada ita ya zauna yana murmushin shima, yadurk'uso ya sumbaci cikinta, " babies na inafata kuna cikin k'oshin lfy? Injidai maah-maah tabaku abinci?".
"Tab abinma dariya, ALLAH Sadauki idan kana wannan abun dariya kake bani, waya gayamaka yara biyune to?."
Matsawa yayi sosai, ya mannata da jikinsa, acikin kunne yarad'a mata abinda nima banjiba.
Aysha ta tureshi tana fad'i ''kai kai ALLAH nidai babu ruwana, saima Na fad'aka da Ammah".
"Hhh dubeta kamarma zata iya".
" OK haka kake zaton bazan iyaba ko? Kajira sammaci". 'Tayi maganar tana komawa k'asa'.
K'afarsa takamo tafara k'ok'arin cire masa takalman.
Shikuma yana fad'in "kibari kawai, kinma tunamin wlhy, wai shegen alk'alinnan dukda hujjoji da lauyanmu yabayar yad'aga zaman kotun nan harsai next week".
" to aii babu komai sadauki, dayau da wani satin duk d'ayane, insha ALLAH za'a yanke musu hukunci dai-dai dasu, wahalarmu bazata tafi abanzaba aii, mugodema ALLAH ma da nasarorin daya bamu duk aka kamasu".
"Hakane kuma sholyna, su john ma k'asarsu hukuncin kisa ta yanke musu".
" woow! Dan ALLAH da gaske sadauki!?".
"I'm telling you".
" kai alhmdllh, amma naji dad'i sosai wlhy, nasan Anty meerah saitafi kowa farinciki dahakan, tsinanne, dama dukmasu hali irinnasa k'arshensu kenan, sugama tara dukiyar kuma daga k'arshe tazama mara amfani agaresu, saidai wasu suci kuma".
"Hakane wlhy sholyna, gadai su momy nan inda suka k'are, ita wannan ciwonma data tsinci kanta kad'ai ya isheta, munyi magana da Anty zuwairah akan dukkan kud'ad'e da kaddarorin momyn, kawai zamu kaisu gidan marayu, danbanga amfaninsuba, baffah yace babu Wanda zaiyi amfani dasu agidannan".
''Hakan shine dai-dai aii sadauki, to Amma su Lola fa? naga suma sakasu akayi bashiga sukayiba".
" eh, hakane, amma kinsan mutanenmu da bushewar zuciya, dukda sunga an hukunta wad'annan bazaisasu dainaba suma, sunrigada sun saba da iskancin, dakuma kama kud'ad'e masu nauyi, yanzu koda an sakesu suma tasu dabar zasuje su kafa. Amma dai munan muna tattaunawa akansu, sauran yaran kuma duk mun maidasu hannun iyayensu".
"Aii kunyi dai-dai wlhy, jaridun k'asarnan gaba d'aya wannan satin labarinkune kawai aciki, nasan gaba d'aya idanun al'ummar Nigeria Na kanku yanzu, kai duniyama baki d'aya, jira kawai akeyi aji irin hukuncin daza'a yankema wannan k'ungiya".
"Hakane wlhy, yanzufa da k'yar Na kufto daga hannun 'yan jarida, Taheer nabar musu nagudo, saiya bar wajen yayta tsinemin azuciya d'an iskan".
Dariya Aisha tayi, tace, " aiini wlhy birgeni kukeyi, yanda kuke tafiya da rayuwarku a tsari, idan fannin aiki kuke komai cikin girmamawa suke makashi, basa kallon kaid'in abokinsune, hakama idan aka dawo fannin abota kashige cikinsu kuyita barkwanci, baka kallon kai ogansune awajan aiki, lamarinku daban dana sauran jama'a sadaukina."
"To miye duniyar Sholyna, watarana komai saikiga yazama tarihi, saidai atuna sunanmu badai mud'inba, su Youseef mutanene masu kwazo, kinga tunda nabasu shawarar mukafa k'ungiya taimakon matasa babu musu suka amincemin, yanzu haka nake fad'a miki mun samama matasa kusan 200 aiki wlhy, banda wad'anda muka samama sana'oi, dakuma wad'anda suka koma makaranta, aikinga wannan nasarace, watarana basaikiji sunkai irin dubu biyar d'innanba, inaga hakane yakamata masu kud'in k'asarmu sunayi, musamman ma 'yan arewa dan mutanan kudancin k'asarnan tuni sun waye da irin wad'annan taimakon, amma 'yan arewa ina, kowa burinshi akirashi wane, zakiga kowanne banki mutum yanada kud'i, gawasu agida, motocin hawa Na alfarma, saka manyan kaya masu tsada, agogo wannan saikiji Na million d'aya ahannunsa, 'ya'yansa kowanne yanada account nakansa, ga hannun jari a ma'aikatu daban-daban, shin dukmi zakayi dasu?, kasan dai baza'a gina rami arufeka dasuba ko?, kiga mutum yak'are rayuwarsa kaf aneman dukiya, babu kwakwkwarar ibadar dazai rik'e tazame masa guzurin shiga kabari, wlhy kaiconmu dawannan makauniyar rayuwa, bazakasan kana cikin babbar asaraba sai mala'ikin mutuwa yazo kanka, lokacin babu tsumi babu dabara kuma?".
"Wlhy hakane Sadauki, ai gaskiyafa 'yan arewa muna cikin halin hau, kowa dagashi sai 'ya'yansa, shiyyasa kullum kuma mune abaya, masu k'aunarmu da gaskiya dason dawomana da martabarmu irinsu BUHARI kuma toshewar basira tahanamu ganewa, munfison awatsa mana tsaba mu tsatstsage alokacin, batareda munyi tanadi wa gobenmuba, inhar za'a cigaba da tafiya haka aii wataran sai'an shafe tarihin arewa da al'ummar cikinta, shiyyasa nake tausayin 'ya'yanmu wlhy".
" dolene subaka tausayi, ayanzuma jibi yanda duniya take walagigi, inaga nanda shekaru 20 masu zuwa, ALLAH ka gafarta mana dai kawai."
"Ameen to". 'Aysha tafad'a tana yunk'urawa zata tamik'e'.
Saida ya taimaka mata sannan tasamu tatashi.
"Sannu sholyna kinji, insha ALLAH saura kad'andai ki juyomin babies d'ina ki huta muma mu huta".
"ALLAH ya kaimu, dama nagaji nikam, tashige kichin".
Shima mik'ewa yayi yana dariya dafad'in ''k'ya gaya musu yarinya, kina juyewa zankuma ajiye wani aii".😂😜

******

Rana bata k'arya.......

Yaukam kotu tacika dank'am da jama'a, su Kansu 'yangidansu ya khaleel kwansu da kwarkwata sun halarci zaman, harda innah jummai datak'i komawa Jigawa har yanzun🤣, saboda tsoron dariyar mutane, da anamusu fafa su masu kud'i.🤪
Tunda hajia babba taga gayyar 'yan gidansu taketa zubda hawaye, tama kasa had'a ido da kowa awajen, su kansu duk hankalinsu nakanta, ko kad'an Aysha bataji tausayin kowaba acikinsu, musamman ma hajia babba da hajia khaltum, glory, kubrah. Saima d'an karan dad'i dake ratsa zuciyarta da ruhinta, yauga mak'iyanta gurfane agaban kotu, abinda bata ta6a zaton zai faruba ko a mafarki, dantasha jin labarin makamanta wannan cases d'in natafiya abanza, batareda ankama koda masu laifinbama bare agurfanar dasu gaban kotu.

Kotu tayi tsit ana sauraren jawabi daga lauyoyin na 6angarori biyu, lauyan gwamnati yakawo kwararan hujjoji, tareda manyan shaidu irinsu ya khaleel, wad'anda ganaune ba jiyauba.
Shiru nawani lokaci Alk'ali yana bincika hukuncin dazai yanke.
Alfarma hutun mintuna talatin aka d'auka, Alk'ali da jama'arsa suka shiga wani d'aki domin tattaunawa.

Kusan mintuna talatin saigasu sun shigo, alk'ali ya zauna, bayan wasu 'yan mintuna yad'ago idonsa dake sakaye acikin glass yana kallon jama'ar kotu, yay gyaran murya tareda gyara zamansa.

"Wannan kotu mai alfarma tayankema wad'annan mutane hukuncin dai-dai da laifinsu, saboda fasa kaurin miyagun kwayoyi dasukeyi, dakuma safarar yara mata, tawani fanninma harda makamai, laifinsu yahad'u dayawa, wannan yasaka bamuda kwakwkwaran hukunci, bisa nazari dawannan kotu tayi, da taimakon manyan lauyoyi anyankema dukkan wani dake cikin wannan k'ungiya hukuncin d'aurin shekaru 40 babu Tara, sannan babu wani dakeda lasisisn fitar dasu koda wata gewamnati tazo annan gaba, akwai horo mai tsananin gaske da azabtarwa da'aka tanada musu agidan kaso.
Mutun uku acikinsu basuda isashshiyar lfy, d'aya tasamu sauk'i, za'a wuce da ita gidan kaso, amma akwai alfarmar idan anga ciwonta yatashi amaidota asibiti tacigaba da kar6ar magani, idan tasamu sauk'i sai'a maidata cikinsu.
Guda biyukam abarsu a asibiti sucigaba dashan magani harsu sami sauk'i sannan asakasu cikin 'yan uwansu.
Akwai jami'an tsaro 26 acikinsu, wannan kotu tamik'a nasu case ga hukumominsu, zasumusu hukunci a cotes nasu, ga sunayensu kamar haka.........
Tsaf Alk'ali ya lissafoau, harda Ak'ilu Abbas, dakuma wani ogan khaleel Wanda khaleel yata6a fad'a masa saiya binciko dukmasu hannun alamarin, dawasu k'ananun ma'aikata.
Sai tsine musu akeyi, khaleel yay murmushin jin dad'i tareda fad'in Alhmdllh, yakai dubansa ga momy wadda itama shid'in take kallo, idonta cikeda kwallah, kasa jurar kallonta yayi, domin haryanzu tanada kima a idonsa, dukda tareneshi akan wata manufa tata tadaban, shi kallon uwa yake mata har gobe.
Daganan kotu tatashi.

Bayan duk an fito khaleel yaja tawagar 'yan gidansu har inda hajia babba take akan keke ana turata, saboda bata iya tafiya.
Cikin takun k'asaitarsa da jarumta tareda izzar kwarjini Na nutsuwa da cikar kamala yake nufota, kallonsa takeyi wani tuk'uk'in bak'inciki Na azabtar da ruhinta, saidai babu damar koda magana.
Baice komaiba yaja gefe yatsaya, tareda jingina da bango ya hard'e k'afafunsa da hannayensa ak'irji.
Baffah ne yake magana cikeda 6acinrai, tunda abinnan yafaru saiyau bakinsa zai furta wani Abu kuwa.
"Laure kinga k'arshen mutum mara godiyar ALLAH ko? Kinga yanda rayuwar mutum mai buri da hassada take k'arewa, komi katara, komin k'arfin ikonka saika dawo k'asan k'asa, mutum mak'ask'anci, shin miye ribar dakika samu laure?, nasan ko alhakin raba d'a da mahaifiya bazai k'yalekiba, ga alhakin salwantar da rayuwar yara masu d'unbin yawa dakikayi, kinmanta dacewa UBANGIJI Na gaggawar kar6ar addu'ar Wanda aka zalinta koda baiyiba."
"Aike koda babu wani hukunci da'aka miki kin tsinci abinda kika girba tun adiniya dagake har aminiyar taki, kalli k'afar khaltum yanda take fidda tsutsotsi saboda ru6ewa datayi, kekam kalleki dukkin lalace, ga 6arin jiki baya aiki, ga hawan jini ga ciwon zuciya, ga 'ya'yanki sun tsaneki, zuwairah saboda halinki tace bazatazoba, Dan bata buk'atar ganinki, hakama shikurah, kinraba khaleel da mahaifiyarsa, kekuma ALLAH yarabaki danaki 'ya'yan, hummm bara nabarki haka, kije Na sauwwak'e miki aurena, dan bazan iya cigaba da kallonki amatsayin matata ta sunnaba, tabbas kinci amanata dayawa Laure, amma darajar 'ya'yan damuka Haifa dakuma zumincin iyayenmu, kije nayafe miki, ALLAH ya shiryi zuciyarki idan kinada rabon shiriya."
Da k'arfi hajia laurah ta kwallah k'ara, wadda rabonda aji muryarta haka har an manta, kuka takeyi harda kururuwa, tana kiran tashiga uku ta lalace, Dan ALLAH amata rai, baffah yayi hak'uri, ya yafeta, karya saketa, wlhy tana sonshi har yanzun, innah kin cuceni, bazan iya yafe mikiba, kin tagayyara rayuwata tareda salwantar da'ita saboda son duniya da hassada akan abinda ALLAH ne kawai keda ikonsa, inama bakece uwataba innah, kaiconki innah keda masu hali irin naki, ALLAH ya Isa tsakanina dake da khaltum, kuncuci rayuwata, Khaltum kema ALLAH ya tsinemiki, yacigaba da tagayyara rayuwarki khaltum, insha ALLAH bazaki sake jin dad'in rayuwarkiba khaltum, innah sai ALLAH yamana hisabi nida k........
Maganarta takatse lokacin dasukaji fad'uwar Abu, koda suka waiga saiga innah jummai kwance wanwar.
Tashin hankali kenan, aii sai hajia babba takuma rikicewa da ihu, cikin gaggawa aka d'auketa zuwa asibiti.
Aysha tamatsa kusada su kubrah tana musu kallon raini, "manyan mata haka kuma rayuwa tak'are?, aiduk ABINDA KA SHUKA, SAIKA GIRBESHI glory da kubrah, ai babu mai babbar asara sama daku, garama su hajia khaltum, su sun haihu, kuko aurenma bakuyiba bare kubar Wanda zaimuku addu'a, ALLAH karabamu da asararriyar rayuwa irin taku dai, kud'in antara kuma babu amfanin cinsu, idan Na haihu zankawo muku babie har prison kukagani kunji😂👎🏻.
Chapter 77 · 0% Book details