← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 83

Sashe 35

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sungama kimtsawa yabud'e k'ofar, aii Aysha tarigashi fitowama, ta tarar zeenatu tafita, amma ankawo break fast an jera a dinning table.
Tana cikin bud'e abincin yafito, dining d'in yak'araso, yaja kujera ya zauna, batareda ya kalletaba yace, "had'amin abinci yunwa nakeji".
Yanda yay maganar yana wani cin d'aci sai abin yabama Aysha dariya, tasaki murmushin daya bayyana jerarrun hakwaranta farare tas, batace dashi komaiba tanufi kichin.
Bin bayanta yayi da kallo shima yana murmushi, yana kallon sanda tasaki murmushin d'azun, bayansa ya jingina da kujerar yajawo wayarsa yakira Taheer.
Babu dad'ewa yad'aga, suka gaisa.
" hummm sannufa da k'ok'ari j!, kace jiya operation d'in dare kafita?, nakulafa mai email d'in sirrin nan dagaske yake taimakonmu zaiyi".
"Hakane taheer, dama nace inhar muka kama mutum uku acikin sunayen biyar daya jero, tom tabbas da gaske yakeyi, amma ina mamakin waneneshi? Miyasa kuma ya 6oye mana kansa?".
" hakane j, wlhy nima tambayar dakemin yawo kenan kullum arai, amma ko wayema insha ALLAH zai bayyana mana kansa k'ila anan gaba kad'an".
"To ALLAH yasa".
" Ameen to, kana inane?".
"Ina gida wlhy, sallar asubahice ta kwacemin shine nakoma gida nayi wanka nayi, amma zuwa kamar 1 zanzo office, akwai wasu files dana sakama hannu please kad'auka ka kaima Oga, kaima Na ajiye wasu takaddu kad'aga k'ark'ashin files d'in da youseef yakawomin ranar Friday Na d'ora kwalin pen akansu, saika d'auka kadubasu, idan kagama kabama Solomon".
"Ok, shikena saika shigo".
"Ok".
Duk agaban Aysha yayi wayar, jitake wani uban dad'i Na ratsata, tamkar ta taka rawa Dan murnar ganin aikinsu Na tafiya dai-dai, lallai bud'e email d'in sirrinnan bak'aramin sauk'ak'a musu aiki yayiba, ALLAH mungode maka, kubrah kece next😆, insha ALLAH". 'Tayi maganar tana dariya a zuciyarta'.

Abincin tahad'a masa, yanda take komanta cikin nutsuwa da Jan aji sai ta burge ya khaleel, harya shagala da kallonta tun yana waya da taheer, harga ALLAH yanson mace mai nutsuwa, kai shi harma namijin, yanason mu'amulla da nutsatstsun mutane.......
Sai magana take masa, tagama, amma yana wata duniyar, cikin mamaki Aysha tace, "naga ta kaina, mikuma ya khaleel yake tunani? Ko har yanzun giyar bata gama sakinsa bane?".
Karaf sai a kunnensa, ya fesar da iskar bakinsa, sannan yakamo hannunta ya zaunar kan kujerar dake kusadashi, "A'eesha! Kalleni nan".
Babu musu Aysha ta kallesa, amma bazata iya jure kallon tsakkiyar idonsaba, saboda kwarjinin dake cikinsu Na kamala da nutsuwa, tajanye idanunta akansa, amma dukkan hankalinta na kansa.
" miyasa kika rainani wai?".
"Lah nifa ba rainaka nayiba".
" uyim to miye? Inba rainiba".
"Shikenan to, kayi hak'uri bazan sakeba".
Idanunsa ya lumshe, batareda da sake tankawaba yagyara zamansa, abincin yad'iba yakai bakinsa, lumshe ido yayi Dan dad'i, yasandai wannan girkin kodai mama kokuma Anty Mamie, Dan sune keciyar dasu bbinci mai dad'i da gamsarwa.
Yad'iba yakai bakin Aysha, bata bud'e bakinba, saidai d'ago ido tayi ta kallesa, ya harareta, babu shiri tabud'e bakin azuba mata.

Sallamar su mufeeda ne yasakasu d'ago ido suka kallesu, Aleeya da mufeedah ne, wadda Aleeya tamatsa sai an rakota wajen ya khaleel d'in sun gaisa, shine momy tasaka mufeeda ta rakota.
Ya khaleel kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa, yad'ibi abinci Yakai bakin Aysha, itako Dan kawai ta k'ulal da mufeeda takar6a a yangance.
Aikam ba mufeeda kawaiba har Aleeya sak'on Aysha ya iso gareta, mufeeda falo taje ta zauna, bayan ta gaida ya khaleel da ko kallonta baiyiba, itakam Aleeya dining d'in tak'araso, taja kujera tazauna.
Da mamaki Aysha take kallonta, ya khaleel baima nuna yasan da zamantaba.
"my boo... Good morning".
Maimakon shi ya amsa sai Aysha ce tace, " tofa, kajimin wani sabon salo, boo...kuma? Babbar magana, su gwaggo daga ina? Dan nikam kin wucemin Anty saidai gwaggo, Dan nakula kinkai haihuwar kamata".
Bak'aramar dariya Aysha tabama ya khaleel ba, amma yadake bai yiba, sai guntun murmushi, yakula yarinyarna akwai rainin wayon tsiya, Ashe rainashin datayima k'aramin alhakine, inbanda wulak'anci dai yaza'ayi takalli Aleeya tace mata wau tama haifeta, kajifa iskanci, hardama kiranta gwaggo......
Tea d'in da Aleeya tad'auka agabansa tana sha wanda Aysha ta had'a masa yasakashi juyowa ya kalleta, tamasa fari da idanu.
Janye idanunsa yayi yamaida kan Aysha, wadda tacika tayi fam daboda rainin wayon Aleeya, gashi Aleeya tak'i tanka maganar da Aysha tamata.
Amma itama sai cakud'a maganar ayshan takeyi cikin zuciya, tarasa abin da zata cema Aysha ne shiyyasa taza6i yin shiru tashare maganar, batareda ta maida murtaniba, saidai tunani takeyi akan badai Aysha bace matar khaleel?.
Wani tea d'in Aysha tahad'ama ya khaleel, batareda takuma kallon ko Aleeyar ba, yauce rana ta farko da Aysha tamasa Abu mafi mamaki, Wanda baita6a zaton tsaurin idonta yakai nanba, dukda hakan yasaka takuma birgeshi da k'ara kima a idonsa, domin ta nuna martabarta ta d'iya mace mai aure.
Humm. Koda Aysha tagama had'a tea saita kar6i cokalin hannunsa, bai hanataba, yabata yanamai kallonta da mamaki fes a fuskarsa, soyake yaga mizatayi....
Baikai k'arshen tunaninsaba yaji lallausan tafin hannunta a face d'insa, kuma fuskarta d'aukeda murmushi, tad'age gira d'aya sama kamar yanda yakeyi sannan tazuba masa abinci abaki.
Shikansa batareda yasaniba yabud'e bakin😂, Dan salon Aysha yagama kashe masa jiki murus.
Aleeya dai da mufeeda kallonsu sukeyi cikeda bak'in ciki, har Aysha tagama ciyar da ya khaleel abinci, shima kuma yaciyar da ita dariya kuwa nata cinsa azuciya, wai wannan 'yar yarinyar tasan kishi.
Kamar wasa aleeya takamo hannun ya khaleel, cikin shagwa6a tace, "haba my boo...wajenkafa Nazo mu gaisa, tunda kagama break fast d'in saika juyo aii muyi hira".
"Kambu tak'ashin ubankiiii Aysha tafad'a azuciya, tayi kwafa aziciyarta tana fad'in yau zan nuna miki Na haddace karatun Anty glory Ashe, sannan inasamun ilimi wajansu Lola da Lyn.
Kawai ya khaleel nashirin juyawa yama Aleeya tatas saikawai yaga Aysha bisa cinyarsa, kutttt🤥, baikai k'arshen mamakinsaba tafara shafa fuskarsa tana fad'in cool dawn Sadauki na, kasanfa 'ya'yan tasha ako ina sai sun nuna hali, naga ranka zai 6aci abanza akan shakatafin gwaggon nan, kwantarmin da hankalinka mana sadauki na", 'tayi maganar tana shafa k'irjinsa'.
🤣su ya khaleel an suma alkur'an.
Lallausan murmushi yasakar mata Wanda bai shirya yinsaba, saidai kawai birgeshi datayi, ita kuwa Aysha ganin tasamu goyon bayansa saita kashe masa ido d'aya, zuciyarta Na dukan uku-ukun tsoron tahad'e bakinsa danata".🙀
Sassanyar Ajiyar zuciya kawai ya khaleel yasaki, aransa yace ya salam zata kasheni🤣.
Kawai saiya bada kai bori yahau, yakuma tallafota da k'yau jikinsa suka cigaba da faranta ran juna😝.
Mamaki yakama mufeeda dakecan falo tana hangosu, dama yarinyarnan haka take?.
Aleeya kam aii mutuwar zaune tayi, tuni zuciyarta tafara tafarfasa kamar talgen tuwon dawa, dak'arfi tabuga table d'in dining waidan su tuna akwaifa mutane a falon, amma ina ko gezau basuyiba, su ya khaleel anyi nisan kiwo.🤭
Da sauri mufeeda tataso tazo takama hannun aleeya dake hawaye sukabar falon🤣🤣🤣.

(ho Aleeya kinyi gamo da sholyn sadauki😹)

Suna fita Aysha tacire bakinta dagana ya khaleel tana sauke numfashi, yunk'urin tashi tayi daga jikinsa, yay saurin janyota yamatse, murya awahalce yace, "aibaki isaba yarinya, zaki tadamin hanakiline abanza kigudu, kinci bulus kenan?".
Hawaye Aysha tafarayi, "please ya khaleel wlhy bakina yakusa daina aiki, kaji kuwa zugin dayakemin, kaima baka iya con kwan makauniyaba, daga tayi saika nemi zarmewa acinye dakai".
" koma miye kekika Sani, wayace ki kawo kanki". 'Yay maganar yana d'aukarta cak yanufi d'akinta'.
Wutsil-wutsul taketayi da k'afafu da kukan bashi hak'uri, amma ko'a kwalar rigarsa.

(Nikam bilynku dariya kamar ta karni🤣🤣🤣🤣, maganin sholy kenan aii, waya gaya mata barno gabas takene?, ta6o su ya khaleel aiba wasan yara baneba🤣🤣🤣, gashinan wajen maganin aleeya, ita ya khaleel zaiyi maganinta😆.
gobema tak'ara aii.🤣
su ya khaleel ba'a gayyacesu bama sunzo🤧, bare ankawo musu goro🤐.

______________________________

Da kuka aleeya tashiga 6angaren Momy, babu kowa saisu kad'ai, Dan su husna suntafi makaranta, Momy kuma tatafi aiki bayan fitarsu.
Lallashin Aleeya mufeeda taitayi.
"Humm bazaki ganeba mufeey, waini yau wannan 'Yar yarinyar zatama bariki?, tasan koni wacece kuwa mufeey?, shi yarasa wadda zai aura sai wannan tatsitsiyar abar, miyagani to ajikinta? Ko farar fatar da wad'an nan kwala-kwalan idanun nata uwa Na mujiya?".🦉
" wlhy Anty aleeya muma ba k'aunarta mukeba, shima bawani sonta yakeba baffah ne yahad'a auren".
"Baya sonta ya biye mata?".
" lallai Anty aleeya, bakisan shaid'aniyar yarinyarcan baneba kawai, shiyyasa nak'agara ayi bikinku da ya khaleel kije ki gayarama shegiya zama, wlhy natsaneta itada uwarta, jinake kamar Na cinna musu wuta su k'one k'urmus wlhy".
"Wayyo, dad'ina da gobe aii saurin zuwa, kubarni da ita, tunkan nashiga gidanma zan fara saitata narantse".
" Yauwa auntynmu kina wuta wlhy hajiyata🔥🔥".
Aleeya akayi wani far da ido ita an fasa mata kai.

Hummm🐺

____________________________
🤣🤣🤣
Aysha ido yayi gwale-gwale, a hannunsa ya khaleel, yasha ALLAH ya Isa tafi cikin drom.🤣

Suna zaune afalo kowa yacanja shiga, kan Aysha abud'e tabarsa yasha iska, saiwata roba da k'aramin hanky a cinyarta tana d'ebo ruwan zafi aroba tamatse saita gasa bakinta, bak'aramin ciwo da rad'ad'i yake mataba, sai k'un k'uni takeyi kuwa, ya khaleel yana kwance a doguwar kujera yana kallonta, dariya sai cinsa takeyi arai yana dannewa.
Zuwa can yatashi zaune yana fad'in, "zona taimaka miki Na gasa miki bakin".
Harara ta balla masa,🙄 amma batace komaiba, tacigaba da gasawa tana hawayenta.
Yataso yadawo kujerar datake zaune yana dariya k'asa-k'asa, wayyo harfa ya kumbura sholyna, kai sadauki baka k'yautaba, irin wannan aika-aika daka tafka".
Ture hannunsa dake shafa la66anta tayi, takuma tunzuro bakin gaba, aii wlhy sai ALLAH ya sakamin, kaima za'ama 'yarkane". 'Tak'are da ziraro da hawaye'.
Yanzukam sosai yake tuntsura dariya, aiko Aysha takuma k'ulewa tafashe da kuka🤣...........✍🏿

Wayace kikawo masa kanki sholy?.😆😆😆😂🤪

💓💓💓💓💓💓❤❤❤❤❤❤❤❤❤🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀.

*_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

*_part 2_*
(littafi na biyu📕)

2⃣5⃣
Chapter 35 · 0% Book details