← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 83

Sashe 66

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_ya khaleel mata suna cikin bak'incikin rayuwa a nahiyar Africa, wad'anda suka samu damar yin aure basu tsiraba, matar k'auye kullum tana cikin wahalar bautar mulkin mallaka na d'a namiji, abincin kirkima baigama isartaba, basuda aiki saina d'aukar ciki da haihuwa, gashi babu wani tallafin da yaran ke samu, sukan saka namiji makaranta, amma mace data tasa sai aimata aure, shekara d'aya saikaji ayuriyiri ta haihu, kafin wata shekarar tadawo ankuma samun wani cikin, shekaru uku kad'ai zakabata agidan mijin idan kakoma bazaka ganetaba, saboda tagama lalacewa tafita hayyacinta, babu abinci babu kwakwkwarar kulawa gamijin, daganan sai afara kiranta tsohuwa, itakanta zuciyata ta raunana, atunaninta shikenan tagama yayinta, saikuma 'ya'yanta, musamman idan yakasance 'yarta tafari macece, saikaji ana fad'in kwana nawane itama tazama surukar wani. Hummm._
_Dazaka duba, duk k'auyancin k'auye saika samu mai suyar kifi, mai tukubar nama, sannan tebirin mai shayi, kuma kowanne saiyayi sana'arsa arana kuma tak'are._
_shin abin tambayar anan, suwaye ke siye tulin bread da indomin tebirin mai shayi? Harda kwai. Sannan suwaye kecinye gasashshen naman tukubar mai nama?, sannan suwaye kecinye kifin tebirin mai kifi?._
Amsar d'ayace, mazan k'auyen.
_kullum da an idar da sallar isha'i saika gansu zagaye dawad'an nan tebiran, k'ilama harda k'arin mai soya doya da kwai da kaji agarin, amma kafin safiya duk ancinye, amma dazaka bincika babu matar mutum d'aya acikinsu dataci wad'annan kayayyakin, watama masarar tuwo ko dawa kad'ai aka bata, ita tayi wahalar k'ud'in nik'a dana daddawa dad'an barkono, koda babu manja da isashshen magi haka zata kad'a miyar suci itada yara su kwanta, mijin yadawo yana mazurai, bayan yagama kacaccala arayuwarta a tukubar mai kaji._
_da'an kwana biyu kuma yahango wata saikaji zancen zai k'ara aure, sukuma iyayen babu tunanin komai sud'auka su bashi waidon suhuta daganin wannan d'iyar tasu tana yawo agari ana zaginsu, kaico dawannan bahagon tunani._
_da tsautsayi zai gifta yasaki matar tasa, kwana biyu takoma gida saikaga tamurje takoma d'as yarinya d'anya sharaf da ita, da tsohon mijinta yaganta saiya rikice dafara hura hancin son komawa cikin masu takarar Neman aurenta._
" kasan miyasa hakan ke faruwa kuwa?".
Kamar sakarai khaleel ya jinjina mata kai alamar a'a.
Murmushi Aysha tayi, tacigaba da fad'in.
''Alokacin aii ya gama durk'usar da waccan amaryar daya aura yasaki wannan dominta, itama ya maidata tsohuwar k'arfi dayaji, kaga dole yakoma hange-hangen watakuma, koda ace waccan tsohuwar matar tasa bata koma garesaba, zai nemi auren wata kuma, dawad'annan abubuwan kullum aketa kashe rayuwar matan k'auye, da'an samu mai raunin zuciyata saita 6alle tazo takafa dabar 6arna da jagorancin tarwatsa rayuwar sauran 'yan uwanta dasuka tsinci rayuwarsu arin halinta.

_Macen binni kuwa zaka sameta daci dasha, da suttura, amma babu kwanciyar hankali, koyaushe miji namata dodorido da sake auro irin jinsinta na mace domin k'untata, sannan yanacan awaje yanacin zarafin mutuncin 'Yar uwarnan tata mace a hotel ko'a office. datayi maganar Neman 'yanci yace zai saketa yamaye gurbinta da 'Yar uwarta mace, kullum mazan birni cikin had'a wutar masifa suke a tsakanin mata, dakaga mace tadage tana haki da hura hanci da taune harshe wajen tanki intaka to akan namijine._
Sannan kuma sai'a ringsla samun mata 'yan jari hujja irinsu hajia laura da hajia khalum suna safarar matannan domin kaisu k'ashen duniya amatsayin hajar siyarwa mafi tsadar farashi da yalwatuwar riba mai tsoka.
Karka d'auka gwamnatin k'asashen Africa da jami'an tsaronmu basusan da wannan gur6atacciyar sana'arba.
Sun Sani sarai, sunkuma son anayi.
Kasan miyasa suka gaza d'aukar mataki kuwa?.

Tasaki guntun murmushi mai ciyo, sannan tacigaba.
Sungaza hanawane saboda suma suna amfanuwa da wannan kasuwancin, Koda amfanuwa ta fannin aljihu, kokuma amfanuwa ta fannin biyan buk'atunsu, da wannan kud'in cin zarafin Matan suke yima matayensu nagida hidima, dasu suke ciyar da 'ya'yayensu dake killace agida, dasu suke jar fata da mazurai acikin al'ummarsu, sannan dasu suke amfani wajen keta martabar sauran Matan dasuke killace agidajen iyayensu ko mazajensu, tunda anmaishe da mata 'yan tsaki, da'an watsa mana tsaba saimu fito muna tsatstsaga.
Abin bak'in cikin bamuna tsatstsagar tsabar bane domin son murayu cikin salama, kosan mu k'arfafa rauninmu wajen Neman 'yancin ketama Junanmu mutunci, a'a muna tsatstsagar wannan tsabarne domin gyara halittar jikinmu ta daidaita mu burge mazajennan dasuka watsa mana tsabar, munyi hakane domin gobe mufito cikin nagartar burge wad'annan mazajen, haka zasuyita watsa mana wannan tsabar munaci nuna gyara kammu dominsu, ahaka har rayuwarmu ta lalace mukoma jagororin ingiza saida mutuncin sauran mata nak'asa damu.
Inda za'a zauna tebirin tattaunawa saikaji ance mata sun lalata duniya, mata sunfi shaid'an shed'anci, shin idan mace shaid'aniyace? Dawa take shaid'ancin? Kuma danwa take shaid'ancin?.
Wad'annan tambayoyin nakeasn duniya damazan duniya subani amsarsu😭.
Ya khaleel Kasan kuwa d'umbin mata dake rayuwa cikin k'unci da bak'inciki kuwa?, kullum ana k'wasar yaranmu ana kaiwa saudia cibiyar addinin islama dasunan aiki amma hajace ta tallatarwa wa mazan wannan k'asa, kaimu akeyi domin k'ask'antarwa da tozarta Kimar 'ya mace da mutuncinta, ana amfani da rauninmu wajen wargaza dukkan martabarmu, shin bakwa tunanin raunin mazajen k'asarmu wajen sakacin rik'e mata agidajen aure yake kawo wannan kwad'ayin na mata Masuson tafiyar wasu k'asashe bayan angama yaudararsu?.
Kuje kuga Matan dake zuwa saudiyya danufin aiki acan, a k'ask'ance suke, marasa daraja ake kallonsu, kullum cikin mulkin mallaka aikatau da fataucin mutuncinsu ake, (ita batayi zaman aureba, bakuma tayi bautar ALLAH ba cikin nutsuwa) haka ake binsu kamar tumaki dagudu ana kamawa, why? Ya khaleel. Mata why dabazaku farkaba?.😭
Inhar k'asa irin saudiyya bazata San mutuncin daraja rayuwar 'ya'ya mataba to bansan ina mace zataje tasamu mafakaba aduniya ya khaleel, inhar za'a iya tarwatsa mutuncin mace a k'asa mai tsarki to tabbas babu wata k'asa da 'ya mace zataje ayi tunanin dawowarta da mutuncinta.
Inhar dagaske kakeyi ya khaleel, inhar da gaske kaid'in ka banbanta da sauran jami'ar tsaro dake k'asarnan to katashi domin ceto rayuwar mata dayawa da'aka salwantar da sanin iyayensu koda rashin saninsu, da yardar Matan koda tilastawar azzalumai 'yan jari hujja irinsu hajia laura, ninan namaka alk'awarin taimakonka da sirrika masu yawa danake dasu batareda sanin kowaba😭😭😭😭😭😭.

Tak'are maganar dafashewa Dama tsanancin kuka mai cin rai da zuciya.
Da Sauri ya khaleel yataso yatareta saboda tangad'in hajijiyar fad'uwa datakeyi.
Cikin kakkasar murya tace, "karka ta6ani saikamin alk'awarin zakayi, saikamin alk'awarin bada kwakkwkwarar gudunmawa, saikamin alk'awarin fara nuna misali akan momy, karka duba wahalar raino datasha akanka, karka duba shak'uwar dake tsakaninka da ita.
Katuna 'ya'yanmu masu tasowa, katuna wannan cikin dake jikina indan nahaifi mace wace irin rayuwa zata tsinci akanta?, katuna da su momy sunci nasarar tarwatsa rayuwata wane bak'inciki zaka tsinci kanka.............?

Bai bari ta k'arasa ba yace..............✍🏻

😱😱😭😭💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤mata ku farka

*_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_

*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

*_kud'in nadabbane agareni, dolene gaisuwarkuma tazama tadaban, ina k'aunarku ainun, domin munzama 'yan uwan juna, ALLAH yabar mana zuminci 'yan group d'ina, my diamonda d'ina, kune gold d'in bilyn Abdul😉😉😉👍🏻👍🏻👍🏻💋💋💋💋😍😍😍😍❤❤❤_.*

hajara gambo (uwargida), fatima Muhammad (mom Ammar), Zainab Zubairu Maitama( Zeezu byr Mytama, Ummu abdulnasirr(Ainah Buhkari), ummul Ahmad momy twice, khadija Auwal(maman Farhan), Hassernath Jalingo, zahra abbakar (Ummu unborn), Sadiya Aminu, 💅🏼teemahcute💅, Aysher Bello, Nanerh🧕, Beentahmk, khadija Muhd (Dee), Deeyerht, NANA YAKAKU, AISHAT UST, preety zee🧕🏼, zainab Gadaka, 👑💅🏼Ummu iman, Mrs usman, Beeky, mummyn ihsan, Mmn zeey baby, rahma salihu, Xynab, Hauwa magaji, Falmata Ibrahim, Falhat, xaenab ibrahim, Mmn walida, Fatee Ibrahim umar, ∂єєנαян✍, Smart lady, maman zeey, Falmata Ibrahim, Maryam Lanko, Zakiyat, Jamila Fika, Saddiqa musa, Aeasher2😍😘, Rukayyah R K Y😍🤝, Nanah😍, Deeyerht, Ameera😘,Rukky, Aysha Mustapha, Aeesha Isah, Zainab Ibrahim, Dr hairas H~, Mmn Khalid da sajida, RUKAYYA BALA SURU, binta a abubakar, Aysha rabiiu, khadija Mustapha, Bilkissu💋💄, Aisha Dantanko, Bilkissi Niger , Maman Umar, Aisha Awais, Meenasko, Maman sudais, Ommeetah, Hafcee, Amina lawal, Bilkis , Maijidda (mamin mua'azzam), Meenasko, Hadiza (mom yasmin), Teemah yola💅🏻, Asmy smiler , Hafsat Ahmad, Akori kishiya Aci daula, Aysher, Mom Afrah😍, Ummun Hajiya, Surayya Auwal, Eashan mamanta😍👸, Hassanat ismaeel🧕, *Muneerah Muhammad (M3)*, Aaeesha, xeeyhert Muhammad , Lawisa sani, Zeetah😘, Mrs Shariff, Mom aysher, faryderh ❣❣, Sadiya abdulwaheed, Deedee gwarzo, Zainab maman zainab.

_bilyn Abdul ta gaisheku k'yauta😉👍🏻_.

4⃣4⃣

"Kinga nutsu muyi magana mana".
Chapter 66 · 0% Book details