Sashe 57
Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
_Awannan ga6ar kam zan baku hak'uri, amin afuwa sosai, nasan wasu basajin dad'in yanda sukemin comments a groups amma bana magana, wlhy abubuwan yawa sukemin, zaka kula da Oga da safe, kafin yafita, yana fita aikin gyare-gyare zakayi, sannan nafita islamiyya, nadawo 12, wlhy ina dawowa typing kawai nake zaman yimuku, wahalar typing takan d'aukemu lokaci mai tsawo, saboda abune Na nazari, wani lokacinma saikin kusa gama page kiji baiyiba, ki goge kiyi wani kuma, kunga kafin mutum yagama kansa yad'auki zafi, sauri kake kagama ka fuskanci aikin gida kuma, wani lokacin kiyi bak'i, ko fita takamaki kekanki, ALLAH akullum ina gamo da messages Na PC samada 150, rasama ta ina zan fara nakeyi, gakuma Na groups, groups yakai 40 wanda nake a ciki, wasu kunyarsu take hanani fita kawai wlhy, lokacin dazan gama typing kaina yad'auki zafi sosai, saina dingajin gandan duba sakwannin PC, amma dankarkuga kamar inamuku wulak'anci nake daurewa naduba, shiyyasa nake d'auke idona ana groups, amma wlhy inajin dad'i sosai, kuna sakani farinciki ainun, badankuba banga amfanin rubutubba, tunda bazan rubuta danna karanta nikad'aiba, duk inda masoyina yake nima ina matuk'ar sonsa da alfahari dashi, babu abinda zance daku saidai ALLAH yabar zuminci, k'aunarkuce ke sakani wajen 6ata lokacin yin typing kullum da siyen data, I love you so much my fans, babu marubucin dabaison masoyinsa, duk muna k'aunarku wlhy💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤❤._
Amin afuwa please, kuna raina wlhy👁💘.
3⃣9⃣
Su khaleel sunada yawa sosai, amma dukda haka su hajia babba sunfisu yawa, danma ankama wasu aciki, sauk'in d'ayane bakowa keda makami acikinsuba.
Dukda jikin ya khaleel a sanyaye yake, kuma baisan daliliba, amma hakan baihanashi aro jarumtaba ta musamman ya k'arfafawa kansaba, daboda gudun Matsala.
Acikin kwarewar aiki suke shiga wajajen, duk wanda akayi karo dashi kuwa cikin dabarar aiki suke gamawa dashi, basuda mafitar data wuce kashesu, saboda suma suna samunsu kashesun zasuyi tunda akwai nakamai a hannunsu.
Bawai k'aramar k'ungiya baceba, k'ungiyace data tara manyan mutane, masu muk'amai kala-kala, ga dukiya sun tara, saboda business kala-kala dake gudana cikin k'ungiyar, kuma Na manyan kud'i.
Karya wuyan wani da khaleel yayi bayan nannad'e kansa aleda yasakani rintse idanu, sosai tsoro yashigeni, danganin yanda zukatansu khaleel suka gama bushewa, basajin komai wajen kisan garatan nan.
Matsalar da aka samu shine cctv camera dake aiki acikin d'akin taron, wadda su khaleel basusan da itaba.
Wad'anda suke kulada cctv camera d'inne suka ankarar da 'yan k'ungiyar.
Tashin hankali kenan, wai Wanda ba'a saka masa rana, kusan shekaru 29 k'ungiyar Na aikinta. Amma basu ta6a gamo da makamancin tashin hankalinnanba, saidai amusu tsinci d'ai-d'ai badai gaba-da gababa, don ko kad'an basu aminta wani yafidda sirrinsuba, komai cikin ilimi ake yinsa.
Hargitsewa hall d'in yayi, masu makamai suka fara d'ana kunamin bindugu, irinsu Momy kam sai neman wajen 6uya.
Musayar wutane yafara gudana a tsakaninsu, bakajin komai sai k'arar harbe-harbe.
'Yan jarida kam dasu khaleel sukazo dasu sai d'auka sukeyi, lamarin kaikace film ne wlhy.
Shirin ma'aikaci da d'an ta'adda bazaizo d'ayaba, dukda gawurtar k'ungiyar su hajia babba takai taringa bama matasa training saboda gudun zuwan rana irin wannan ta kota kwana.
Tiyagas su khaleel suka fara jefawa cikin hall d'in, dama su sun d'auki matakan kare kai, dandanan wajen yakacame da tari da atshawa, gashi hayak'in yana saka hawaye, masu ciwon asma kuwa saidai addu'a kawai.
Jefa tiyagas yaba su khaleel damar shiga hall d'in, dukda haka akwai masu taurin zuciya dake harbi har yanzun.
Amma haka su khaleel sunata samun nasarar cafke wasu, Dan k'ungiyar ta tara maza da matane, harda wad'anda tunaninka bazai ta6a kawo maka ganinsuba awajen, saboda Girman milki ko dukiya.
Akwai k'ofofin fita da dama acikin hall d'in, wannan ne yabama wasu dama sulalewa, amma ina, wannan shine angudu ba'a tsiraba, dankuwa cikinsu khaleel wasu sun bisu.
Acikin masu guduwa kuwa harda hajia khaltum da hajia babba.
Lamarifa yaci tura, komai yagama hargitsewa, acikinsu khaleel dayawa sun sami harbi, 'yan k'ungiyar kam ba'a magana, bayan wad'anda aka antaya barzahu akwai masu harbi a sassa daban-daban.
Kusan awanni 3 aka d'auka ana Abu d'aya, lamarin kamarma bazai k'areba, kowa yafita hayyacinsa, Dan babu Wanda baiji jikiba, ansami cafke mafi yawa acikinsu, wad'anda suka samu raunuka akafiddosu waje, gawawwakinma haka duk an fiddosu, wad'anda suke k'alau kuwa handcuff aka saka musu, duk aka fito dasu waje, 'yan jarida sunata aikinsu.
Ya khaleel yafara bin ma'aikatansu yana dubawa, Dan a tantance wad'anda suka mutu, dakuma rauni, duk a wahalce suke.
Khalee yace, "amma akwai wad'anda babu acikinmu?".
''yes Sir! Wasu sunyi yunk'urin guduwane, shine suka bisu".
"OK!, yakamata azuba wad'annan amotocin da aka kawo, suma akirasu aji?".
" OK sir".
Wad'anda basa wajen aka shiga kira, wasu suce sun kamasu, wasukuma suce sunadai binsu binsu abaya har yanzu, amma suna buk'atar k'arin ma'aikata.
Taheer dai cayayi ahad'ashi da khaleel.
Faruk yamik'ama khaleel wayan cikin girmamawa.
A kunne yakara batareda yayi maganaba, daga can Taheer yace, "sorry sir idan bazaka damuba kazo da kanka, wasu mutane hud'u sun shiga gidanka, bazai yuwu mushiga babu izininkaba".
" gidana kuma Taheer?".
"Yes sir?".
''OK ina zuwa, kubani k'ank'anin lokaci".
Saida khaleel ya tabbatar anzuba sauran a mota, wad'anda suke buk'atar k'arin ma'aikata aka tura musu, wasu kuma suka tafi da motocin wad'anda aka kama, ma'aikatasu kam tuni anyi gaba dasu Dan basu taimakon gaggawa.
Ya khaleel kansa yasamu raunuka, amma bai damu da kansaba, Na k'asa dashi kawai yake son abama kulawa.
Key d'in mashin yakar6a ahannun wani ma'aikacinsu, yanufi gida zuciyarsa Na dukan 100-100 saboda fargabar abinda zai Tatar, kenan zarginsa yazama gaskiya, acikin gidansu akwai mai mu'amullah da k'ungiyar? jiyake tamkar zuciyarsa Zata kama da wuta saboda bak'in ciki da fargabar wanda zai tarar amazaunin d'an k'ungiyar.
Ak'ofar gida yay gamo dasu Taheer dake tsaitsaye, basu shiga gidanba, saboda girmama ogansu.
Bai tsaya garesuba, horn kawai yayi d'an gwari yabud'e masa gate yashige da mashin d'in, suna su Taheer duk sai suka shiga.
Tunda su hajia babba suka sami nasarar baro hall d'in kaitsaye nan gida suka nufo afirgice, sunyi imani da cewar idan anan gidan suka fake khaleel bazai ta6a kawosu aransaba, tunda bai gansuba, amma hajia babba da idanunta taga khaleel.
Babu Wanda yasan sun shigo gidan, sai mutane kh'alilan, gaba d'ayansu arud'e suke, hajia babba kuka takeyi da idanunta, takasa zaune takasa tsaye, khaltum kam ba'a magana, dama kunsanta afagen tsoro, sai mutum biyu dasuka gudo tare, suma duk matane, d'ayama budurwace, d'ayar kam zata iya zama sa'ar khaleel.
Ko kafe mashin d'in baiyiba yasakeshi anan, sai cikinsu Taheer ne wani yagyara farking d'in mashin d'in.
Taheer ya nuna masa motar dasu hajia babba sukazo, khaleel baisan motarba, Dan bata gidan baceba, saikace mayunwacin zaki haka yanufi d'an gwari datun shigowar su khaleel yake arud'e, Dan yasan tabbas babu lfy yau agidannan, cikin daka tsawa khaleel ke tambayarsa waye yashigo da motarnan gidannan?!!.
Hargowar khaleel ce tafara jawo hankalin mutanenen gida, suka fara fitowa d'ai-d'ai.
Jikin d'an gwari rawa yakamayi, Dan yasan yau babu wargi ga khaleel, dama can bawasa yakeyi dawani acikinsuba, har taune harshe yakeyi wajen magana saboda tsoro, yace, "wasune, amma suna can ciki".
Shigewa khaleel yayi cikin babban falon gidan, Wanda zai iya sadaka dakowanne part Na masu gidan, hankalin kowa yatashi agidan, Dan sunsan yau khaleel amatsayin ma'aikaci yazo musu ba d'an gidaba.
Kowa yafito amma banda Momy, yagama binsu d'aya bayan d'aya da kallo, kad'anne daga cikinsu babu, kuma yarane, yace, " suwaye suka shigo gidannan awa 1:30 dasuka wuce?!!".
Yanda yay maganar dolene katsorata komin kusancinka dashi.
Hafiz ne yay namijin k'ok'arin fad'in driver yad'akko su Adeel daga school, sannan nima da ya muhseen yanzu muka shigo".
"Saiwa kuma!!?".
Umme Amarya tace, " nima bandad'e da shigiwaba, kusan tare kuma muka shigo da hajia babba".
Arikice ya kalli ummi amarya, "umme acikinku wanene mai farar mota?".
" hajia babba ce sukazo da ita, inaga motar bak'intace".
Wani irin huci mai azabar zafi khaleel yafesar, kansafa yafara juyawa, akid'ime yanufi part d'in Momy, dak'afa yadaki k'ofar, amma yajita a kulle, kuma dukanta yayi, nanma ko gezau.
Dukan k'ofarne ya farkar dasu Momy halin da ake ciki, hajia khaltum tace shikenan laura, dabararki bataciba, matsiyacin yaronnan yabiyomu.