← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 83

Sashe 78

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bak'inciki tamkar yakarsu, wai wannan 'Yar yarinyarce ke fad'a musu magana haka?, kai kaiconsu dawannan rayuwa.

Khaleel kam kasa cema momy komai yayi, saidai kallon kallo tsakaninta dashi, a yaukam wani matsanancin tausayinta yaratsa zuciyarsa, amma yanaso tad'anyi zaman prison d'in koda Na wattannine ta d'and'ana taji, kodan zuciyarta takuma nadama da sassautowa, Kodan masu hali irin NATA karsuji sha'awar yi.
yaja hannun Aysha sukabar wajen.
Aysha tajuya tana musu gwalo😜..

Ho sholy, ho sholy🤣🤣🤣🤣🤸🏻‍♀

__________________________

Kulli nafsin za'ikatul maut...

Sakamakon abinda yafaru zuciyar innah jummai tabuga da ajali, fad'uwar datayi ko shurawa batayiba awajen, koda sukaje asibitima dubwar farko doctor Faisal yace saidai hak'uri tarasu.
Wayyo Ammah tasha kuka kuwa, itakad'ai gareta 'Yar uwa gashi tatafi tabarta, d'iya d'aya tilo data haifa kuma tak'are agidan prison, saidai jikoki da ALLAH yay nufin zata bari.
Zuwan su khaleel gida dai-dai dakawo gawar innah jummai.
Anmata suttura tareda sallah aka mik'ata makwancinta, sauran bayani yarage tsakaninta da ubangijinta.

Mudai namu ALLAH yajik'anta, Dan babu maishiga tsakanin bawa da ALLAH.😊

********

Bayan kai innah jummai kuma sai mufeedah tafara nak'uda, babu shiri aka kwasheta zuwa asibiti itama.
Tasha bak'ar wahala kam, harma anfidda rai daita saikuma tahaihu, amma d'iyar batazo da raiba, wannan yasaka aka mata allurar barci domin tahuta.
Sannan doctor yazo yasanar musu halin da'ale ciki.
Aunkar6i jariri k'yak'yk'yawa, kamar mai rai, sukaje aka binneta itama.

Mufeedah kuma tacigaba da jiyyar sati d'aya a asibiti, sannan aka sallamota.

Zancen yanke hukuncin su momy yazagaya ko ina acikin duniya, gidajen jaridu da redio, TV, social media daduk wata kafar yad'a labarai, akuma lokacinne khaleel yayarda 'yan jaridu sukai hira dashi.
Suma sauran jami'an tsaro d'innan anyanke musu hukuncin kisama a kotunansu.

__________

Alhmdllh hankalin khaleel ya kwantakam yanzu sosai, saidai 'Yar damuwa daba'a rasaba, Dan haryanzu yakasa mantawa da momy, shak'uwar shekaru talatin dawani Abu bawasaba fans, saidai kawai hak'uri dayawan addu'a.

Yanzunkam rayuwa tana cigaba da gara musu cikin farinciki, khaleel yana bama Aysha kulawa tamkar tsoka d'aya amiya, hakama su Anty Mamie, ammah jar wuya kam aiba'a magana, kayanta takwaso tadawo tana kwana 6angaren su khaleel, darana saita koma 6angarenta, duk tanayine dankar nak'udar dare takama Aysha, tace ya khaleel bashida hankalin sanin nak'uda🤣.
Aikam yahad'e fuska yana zabga mata harara.
"Yo mikika maidani jar wuya? haihuwarma saina kar6a, saidai kuji kukan jarirai".
" kai da Allah can dogon banza, yo banda rik'e bindiga da makar 'ya'yan jama'a uwarmi ka iya, sai mazurai ko?".
"Wanene zaibarka kar6ar haihuwa kamurd'e kan jaririn tunma baizo duniyaba".

" hhhh amma kinga inda nake barci jar wuya, shikenan duk abinda kikemin abakacin motarki to".
"A'a tsayamana kaji irorona, ainidaka babu haka, kaidai mik'o, indai kasiyi motarnan aizan barka, saina koma kan sultani d'in banzarcan".
" wlhy Ammah ki kiyayeni". 'Cewar sultan'.
"Ank'i kiyayarka d'in d'an kwal uba farin banza, gawasu shegun kunnuwanka falka-falka, gashinan ka gogama Sadiq wad'an nan kunuwan naka (d'ansa🤣)....."

"Nid'in?".
" eh kaid'in, kozakayi wani abune?".

"Hhhh bazanyi komaiba jar wuya, amma nima nafasa miki k'yauta d'innan".

"o, tsaya tsaya mutumina, kaikuma mizaka bani?".
" aina fasa, badai nine Sultani ba, mai falka-falkan kunnuwa kuma?".
"Kai haba, bafa kaiba gaye".

Gaba d'aya falon aka shek'e da dariya, dama suna 6angaren ya khaleel ne sunzoma Ammah hira, tunda idan dare yayi nan take dawowa.

___________________________

Khaleel Na kwance afalo, hannunsa rik'eda hisnul Muslim yana dubawa, Aysha tafito daga kichin tana tafiya ahankali, daka ganta kasan batada isashshen lfy, dauriyace kawai irin tata.
Ajiye kayan hannunta tayi bisa table d'in tsakkiyar falon, tad'an jawoshi gaban khaleel.
Sai asannan yad'ago ido yana kallonta, "A'eesha kina lfy kuwa?".
Murmushin yak'e tamasa, " mikagani Sadauki?, lafiyata lau, ciwon bayannan ne kawai, shikuma kasan kullumne babu fashi".
Littafin ya ajiye yatashi zaune sosai, har lokacin idonsa akanta, yakamo hannunta yazaunar da ita kusadashi.
"Kifad'amin gaskiya sholy, tunjiya da daddare nakula bak'yajin dad'i, mutsu-mutsufa kikaitayi awajen barci, nikaina banyi wani barcin kirkiba saboda motse-motsenki, hakama da safennan bakiyi barciba sosai, kodai wani gu namiki ciwo kuma?".

Fuskarta d'auke da murmushi tace, " a'a, ka kwantar da hankalinka, inhar naji ciwon aii zan fad'a😊".
"Shikenan my Angel". 'Yak'are maganar da furzo huci abakinsa'.
Itakuma tafara k'ok'arin bud'e masa fruit d'in dayasa ta yanka masa k'anana.
" gashi kasha, bara nak'arasa aikin danakeyi".
Harta yunk'ura zata mik'e yaruk'o hannunta, "kinga zauna ki huta, idan nagama zanje nak'arasa".
" kad'anfane aikin, kabarni ina motsa jikina, kaifa kayi komai d'azu da safe, please kahuta, bara nak'arasa, aii motsa jikin yanada k'yau shima."
Jin jina mata kai yayi sannan yasaki hannunta.
Tadafashi tatshi.

Akichin tana aiki tana cije le6e, idan azabar ciwo ta isheta kuma tatsaya, sai zufa takeyi, amma taurinkai irinna Aysha tak'i fad'ar batada lafiya.

***********

"Wlhy sainakeji kamar Aysha batada lfy". 'Anty Mamie tayi maganar tana kallon baffah'.

'Dan murmushi yamata, yace, " kai Bilkisu sarkin son 'ya'ya, ba mijinta Na nannaba agida?".
''Yana nan baffansu, ammani shirmen yarannan nake tsoro, zata iya kasancewa cikin ciwo tak'i fad'a, shikuma babana yakasa fahimta. tun ajiya nafara fahinmar tana nak'udar tsaye wlhy baffansu. kaga baradai naduba ko hankalina zai kwanta".
Guntun dariya yamata, "to saikin dawo, ALLAH yasa muji alkairi".
" ameen". 'tayi maganar tana saka takalmanta tafice da hanzari kuwa'.

*******

Hankalin khaleel kasa kwanciya yayi, yanashan fruits d'in amma zuciyarsa nakan Aysha dake kicin, baiyarda k'alau takeba.
Ajiye cokalin yayi yamik'e.
Shikagarsa kichind'in dai-dai da sakin wani marayan kuka da Aysha tayi saboda wani juyi da abinda ke cikinta yayi.
Da sauri nak'arasa yana kiran "A'eesha! A'eesha!! Lfy kuwa?..."

Ina Aysha batasan yanayiba, ya tallafota zuwa jikinsa, saiga Anty Mamie tafad'o falon.
Maganar khaleel tajiyo a kichin yana kiran A'eesha.
da sauri tak'arasa kichin d'in, salati Anty Mamie tafara, dukta rikice, tak'arasa inda suke.
Ya salam, babana garin Yaya haihuwa gadan-gadan amma bazaku iya kiran kowaba?".
"Wlhy Anty Mamie bansan haihuwa baceba, Na tambayeta tacemin lfyarta k'alau, Anty Mamie numfashinta baya fita da k'yau, a d'akko Mota.......

" ina, saidai akira Ammah, d'auketa kakaita bedroom, haihuwar tarigada tazo aii, maza da sauri.....
Da hanzari khaleel yad'auki Aysha daketa nishi da cije la66a.
Anty Mamie kuma takira Ammah arikice.
Mintuna baifi 5 ba saiga Ammah.

"Kai kajimin sakaran yaro, miye nad'orata kan gado itada take nak'uda, sakkota k'asa da sauri".
Khaleel ya sakko da Aysha k'asa sannan Ammah tak'arasa waje.
Cikin haushi yafita, danyafi son matarsa ta haihu agabansa, amma tsohuwarnan tawani korosa, saboda iyayi😏..............✍🏻

Kutanadi kayan babys🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😜

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu, dadukkan musulmai baki d'aya😭._*
[10/26, 4:30 PM] Aysha Galadima: *_📲Typing_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASS......._*
_(Home of expert and perfect writers)_

*_part 2_*
_(littafi Na biyu📙)_

*_yanda kike tadaban haka gaisuwarki tadabance my dear pinky pinky😜, Anty Zuwairiyya, k'awarki anty zuwairah ta gaisheki🤭. Alkairin ALLAH yakai miki har Kano auntyna ta mutunci._*

💋💋💋💋❤👍🏻

5⃣0⃣

Azaba ta ishi Aysha, duk addu'ar datazo bakinta yitake, tana kiran mama da khaleel suzo su taimaketa zata mutu.
"Wayyo Ammah zan mutu, Dan ALLAH ki ciremin jaririnnan, zai kasheni wayyo Anty Mamie."
"Daure Aysha kiyi nishi da k'arfi kinji, kinga kan yaro gashinan, insha ALLAH kinayin nishi zai fito ki huta, runga addu'a, bazaki mutuba insha ALLAH".
" to Ammah, inayin addu'ar aii, hazbinallahu wani'imal wakil, ya khaleel kana ina?, shikenan kabarni da wahala? bama zakazo ka taimakenib......? kai ya salam, I love you mamana.....wayyo ALLAH Na.

Duk surutannan da Aysha keyi dakiran sunansa khaleel najikin k'ofa yanaji, tausayinta yakuma kamashi, jiyake inama zai iya maido ciwon jikinsa, yanzu nan haka Anty Mamie tasha azabarnan, Amma momy bataji tausayintaba ta d'aukeni batareda ko ganina tayiba, momy kin cutar da Anty Mamie gaskiya, wannan alhakin kad'ai ya isa hanaki zaman lf..........
Tunaninsa yakatse lokacinda yaji kukan babie yacika d'akin, Ammah kuma tana fad'in kai Alhmdllh sannu da k'ok'ari Aysha, masha ALLAH barka dazuwa duniya.......
Waigawa yayi yaga Anty Mamie bata wajen, tana kichin d'ora ruwan zafi, ai baiyi wata-wataba yatura k'ofar yashige.
Ganinsa kawai Ammah tayi yafad'o.
Shikam ko kallo batama isheshiba yanufi inda Aysha take kwance tana maida numfashin wahala da k'yar.
Kanta yad'auka yad'ora bisa cinyarsa, yasaka gefen rigarsa yana share mata gumin fuskarta, sai jero mata sannu yakeyi .
Sannu Humairah na, ALLAH yayi miki albarka, yasaka farinciki arayuwarki, kin faranta min, kema ALLAH ya faranta miki fiye da haka, ya ubangijina bazan daina godemakaba da wannan k'yauta dakamin".
yaduk'o yasumbaci goshin Aysha, datake guntun murmushi idonta arufe.
Ammah dai batama kulasuba, tana gama yanke cibi tamaida hankalinta wajen gogema jariri jiki saboda d'a na fad'owa uwa tabiyo baya.
Muryar Aysha can k'asan mak'oshi tace, ''Sadauki zansha ruwa".
"Ruwa?, tom inazuwa bara Na d'akko miki".
Da sauri yafita, batareda Ammah ta kallesaba ta tuntsure dadariyar tsokana, baimasan tanayiba, Dan tuni yafice abinsa ma.

" a'a babana lfy? Mizaka d'auka? Yama naga jini ajikinka?".
"Anty Mamie ta haihufa, ruwa tace zatasha shine zan d'auka mata."
"Alhmdllh Anty Mamie tafad'a cikin d'aga hannu sama, amma khaleel yabata dariya yanda yarikice, badai tayiba ta danne".
" kaga baruwan sanyi zata shaba, kar6i wannan kakai mata".
Tamik'o masa ruwa maid'an d'umi.

Yana zuwa ya iske Ammah ta kulle d'akin, bugun duniya amma tak'i bud'e masa, haushi ya isheshi, hardai Anty Mamie tafito daga kichin tana tambayarsa lafiya?".
Da hannu ya nuna mata d'akin.
Murmushi tayi, dantasan shida Ammah ne, tunda sunsaba, "kaga kyale Ammah kaji babana, tashima kacire wannan kayan kayi wanka, kaga duk jini ya6ataka ko?".
Kallon jikinsa yayi, shi saima yanzu yalura jinin ya6atashi. mik'ewa yayi yashiga d'akinsa, sai jero tsakin haushin Ammah yakeyi, batama barsa yaga koda jaririnba mtsoow, ALLAH tsohuwarnan tagama rainashi.😂

********

Cikin mintunan dabasufi 30 ba Ammah tagyara maijego da jariri tsaf, d'akinma aka gyarashi, kaikace ba'a haihuba.
6angarenta taje ta d'akko turaren wuta data tanada domin wannan ranar, matan su Sultan ma duk haka tamusu, harda kayan sanyi Na jarirai masu azabar k'yau.
Tazo ta kunna, Dan danan 6angaren Aysha yad'auki k'amshi, aka sakama jariri fararen kayannan Na sanyi, sunmasa k'yau, sai barcinsa yake zubawa hankali kwance, bashida wata damuwar data wuce hakan to🤷🏽‍♀.
Chapter 78 · 0% Book details