← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 83

Sashe 40

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Afaloma abokan hud'u sun had'e kai suna tattauna zance bud'e k'ungiyarsu ta taimakon matasa, kowa yana kawo shawararsa.
Kiran sallar azhur ne ya tashesu, hakama matan, akabar Joseph da joy kawai.
Duk sai sukaji babu dad'i, abin yata6a zuciyarsu, joy tace, "Sweet! dan ALLAH basu birgeka ba?".
Murmushi yamata, amma baice komaiba, tun tuni idan suna zaune da abokan nasa aka kira sallah suka tashi, saiyaji wani iri babu dad'i, abin na cizon zuciyarsa sosai.
Itama joy shiru tayi. Saitayi tagumi.
Suna nan zaune shiru, har duk suka dawo, Aysha tanufi kichin domin shirya abinci, su Hafeezah duk sai suka bita suka taimaka mata, a falon aka shinfid'a ledar cin abinci, suka shirya abincin akai.
Kowa yana kusada matarsa, sukaci abincinsu, itadai Aysha takasa sakewa taci, dan kunyarsu Taheer takeji.
Ya khaleel na lura da ita sosai, saida yagama cin nasa sannan yamaida hankalinsa kanta, kar6a cokalin yayi ahannunta, Babu musu tabashi, dan batasan mizaiyi dashiba.
Sai kawai taga yad'ebo yanufi bakinta dashi, idanu tazaro waje, "na k'oshi ALLAH sadauki, tayi maganar a hankali".
"Naji kin k'oshi, amma kar6a dai".
rok'onshi zata farayi yadakar da ita, "infa baki kar6aba, ninasan mizan miki yanzu awajennan, dan saina sakaki jin kunyarsu fiye da wadda kikeji yanz....
Bata bari ya k'arasaba tabud'e bakin da sauri ya zuba mata.
Gaba d'aya suka kwashe da dariya, ashe duk suna kallo dajin abinda ke faruwa.
Sinne kai aysha tayi jikin ya khaleel, yayinda shikuma yake murmushi.
Haka sukaci sukasha cikin nishad'i, bayan sun kammala suka taimaka mata wajen gyara wajen tsaf.
Saida akayi sallar la'asar sannan aysha tamusu rakkiya cikin gida, suk saida sukaje suka gaida kowa agidan, saboda aysha ta k'ular da momy saita bar 6angarenta yazama k'arshe.
Aikam sak'on aysha ya isa ga momy. Dan zuciyarta tayi k'unci sosai, aganinta ita ya cancanta sufara zuwa su gaida.
Su Mufeeda sai antayama aysha harara sukeyi, itako ko'a jikinta, su sukaga zasu iya wai sautin mahaukaciya.
Basu wani dad'eba aysha tace sutafi.
Momy kasa hak'uri tayi, tace, ''to isashshiya bazasu tafi d'inba, kedai tafi ga hanya nan, ko akwai Wanda ya rik'ekin........
Shigowar su ya khaleel ya katsema momy bayaninta, sarai kuma ya khaleel yaji da Aysha momy take, amma koda suka had'a ido da ayshar saita sakar masa murmushi mai kashe zuciya.
Shima baisan sanda ya maida mata murtaniba.
Duk hakan nafaruwane akan idon momy da Aleeya.
Aikam bak'inciki tamkar zai karsu awajen.
Har suka tafi momy na antayama Aysha harara.
Itakam Aysha na sakarma momy murmushin k'ular da zuciya🤣🤣🤣🙀🙀.
Sai bayan sallar isha'i wannan suka tafi, sukabar Aysha da kewa, ita dama akwai saurin Sabon tsiya da mutane, shiyyasa 'yan ciki da gaskiya fans suka maidata k'awarsu😜😜😜.

*_Monday morning_*

Around 11am ya khaleel yasaka aka kawo masa mai aikin hajia khaltum har office.

Daka ganta kasan a tsorace take, ya khaleel na zaune saman kujerarsa yana duba wasu files, Mahfouz yashigo da yarinyar, matsashiyar budurwace, bazata wuce shekaru 19 ba a duniya.
Cikin daka tsawa Mahfouz yanuna mata kujerar gaban table d'in ya khaleel, bai d'ago ya kallesuba, yana cigaba da aikinsa, Mahfouz yace, ''sir! Ga yarinyar".
Batareda yad'agoba yace, ''ok, zaka iya tafiya".
Saida yayi, salute nashi sannan yafita.
Kusan mintuna 10 yanata aikinsa, baisake bin takan yarinyarba daketa zare idanu, sosai tsoronsa ya shigeta, dan tsaf tagane ya khaleel d'in, tunda tana zuwa gidansu idan hajia khaltum ta aiketa, taga kuma hotunansa a jikin abubuwan bikinsa da hajia khaltum tabuga, suma har aka babbasu.
Fuskarsa a d'aure yad'ago yana kallonta, bayan yahad'a files d'in gabansa waje d'aya ya ajiye.
Bindiga ya nuna mata, kinsan wannan komiye aii🔫?".
Atsorace ta gyad'a kanta.
"Baki zaki bud'e kimin magana".
"Im.....Im..bindiga Ce".
"Minene aikinta?".
" harbi".
"Idan aka harbi mutum da ita a ciki ko kansa, ko k'ijinsa, mike faruwa?".
" idonta cikeda kwallah tace, "zai mutu yalla6ai".
" thanks god dakikasan aikinta, to inhar baki bani amsar tambayar dazan mikiba, saina tarwatsa kwalwar kanki da ita".
"Wlhy insha ALLAH zan fad'a maka komi kake buk'ata, inhar nasani".
"da k'yau 'yar gari".
"Miye sunanki?".
" sunana Sakina................✍

*_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_

*_part 2_*
(littafi na biyu📕)

2⃣8⃣

"Sakina kinsan miyasa aka d'akkoki aka ajiye anan harna tsawon kwanaki hud'u?".
"a'a yalla6ai".
"Inason wasu bayanai awajenkine, miye alak'arki da gidan Alhaji mustapha Adamawa?".
"ni mai aikice agidan yalla6ai".
"Aikinmi kikeyi?".
" sharan d'akunan masu gidan, saikuma falo dadai sauransu".
"Uhm, atunanina Wanda ka yarda dashi kake sakarwa shiga lungu da sak'o Na gidanka, danya gudanar da irin aikinki, da alama kema masu gidan sun amince dake kenan?".
Cikin in ina tace, "ha...hakane yalla6ai, amma nima duk sanda zanyi wannan aikin, musamman Na bedrooms nasu saiwani d'an gidan yatsaya akaina harna gama, sannan mu fito tare".
Shiru ya khaleel yayi yana kallonta, yakoma jikin kujera yana lilawa ahankali, hannunsa rik'eda bindiga yana sosata akan kwantaccen sajensa zuwa baki.
Sakina dai atsorace take sosai, tunda take bata ta6a ganin bindiga ido da ido hakaba, saidai ta 'yan sanda, itama daga nesane.
Kusan mintuna biyu baisake cewa komaiba, sai zuwa can yajeho mata tambayar data gama rikita dukkan illahirin halittar jikinta.
"Hakan yana nufin basu yarda dakeba kenan kema? Dukda tsawon shekaru Biyar dakika d'auka kina aiki agidan? Shin wacecema talatuwa agidan?".
Tsoro, razana, kad'awar ciki data zuciya duk suka riski sakina lokaci d'aya, takasa cewa komai, sai zufa dake keto mata takowacce ga6ar jikinta.
Cikin daka tsawa yace, "nace wacece talatuwa agidan dakike aiki?!!".
"yalla6ai fad'ata tamkar salwantar rayuwatane narantse maka, sannan bansan miyasa basu yarda dani d'inba".
Wani murmushin k'asaita yayi, tareda fad'in ''dak'yau yarinya, anzo wajen".
"Ki fad'amin, kokuma kafin ki koma wajensu su kasheki, ni zansaka alburushin bindigata acikin kanki, saidai akai musu gawarki su tambayeta".
Hawaye masu zafi suka fara zarya akumatun sakina, tace, " yalla6ai zan fad'a maka, amma Dan ALLAH karufamin asiri karkace nina fad'a".
Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanu, amma baice komaiba.
Tace, "shekaruna kusan biyar ina aiki agidan, lokacin da'aka kawoni banwuci 14 ba, kuma talatuwace ta d'akkoni daga k'auyenmu Na boza a fika Local Government, jihar yobe, mahaifina da hannunsa yabadani wajenta, bayan tabashi mak'udan kud'ad'e, ina kuka mahaifiyata Na kuka aka taho dani. Koda aka kawoni Abuja wani gida aka kaini, agidan akwai 'yan mata dayawa, k'anana da manya, kuma kowanne irin yare dake Nigerian zaka samu, hardama 'yan Niger dawasu k'asashe makwaftan Nigeria, banfahimci abinda yatara wad'annan mata agidanba aka d'akkoni aka dawo dani gidan Alhaji mustapha, nikaina bansan dalilin yin hakanba, amma daga nanne nacigaba da aiki agidan, Alhaji mustapha ba mazauni baneba, shiyyasa gidansa yazama k'ark'ashin mulkin matarsa, dukda dai nakanji masu gidan sukan tattauna akan hajia khaltum tanada kishiya, kuma alhaji mustapha yafi zama a can, yalla6ai satar amsa 1 zan baka, nasan kaid'in kwararrene Dan nakanji firarka awajen yaran gidan, suna yawan yabama kwazonka saboda soyayyar da baby take maka".
Da Sauri ya khaleel yataso daga jikin kujerar, ''kinga fad'amin wace satar amsace?, bar batun wancan shirmen".
Sakina ta jinjina kanta tace, " yalla6ai mafi yawancin masu zuwa gidan wajen hajia khaltum, namiji ko mace zaka samesu dawani tambarin hoton tarttu na 🦂kunama a damtsen hannunsu Na haggu, tabbas wannan shine tambarinsu, wannan kawai Na iya fahimta tartare dasu yalla6ai, wlhy iya gaskiyata nafad'a maka, Dan ALLAH karka kasheni, kuma karkace Nina fad'a".

Kwantar da hankalinki, zansa a maidaki yanda bazasu fahimci komaiba, da sauri yad'auki ☎waya yayi kiran office d'in Mahfouz da Basheer.
Babu dad'ewa saigasu sunzo kusan atare, saida suka k'ame, tareda salute nashi, sannan ya khaleel yace, "Mahfouz! Amaida yarinyarnan, amma yanda za'a iya fahimtar saceta akayi".
"OK sir"
"Kibishi kuje, inhar ina buk'atar k'arin bayani zansa akuma d'akkomin ke".
''To yalla6ai ngd, tayi maganar tana hawaye, Dan bata fatan akuma kawota wannan wajen".
Saida aka d'aure idonta kamar yanda aka kawota sannan aka fita da ita.
Ya khaleel yamaida hankalinsa akan Basheer dake zaune, ''Basheer ina buk'atar hotunan gawar David".
" OK sir!, bara na kawo, amma akwai Na binciken k'arshe da akayi suna hannun Oga Joseph ".
Jin jina kai khaleel yayi, yakira Joseph akan yakawo masa file d'in binciken mutuwar David.
Babu dad'ewa saiga Joseph ya iso, kar6a khaleel yayi yafara bincike, zuwa can yad'auki wani hoto da David ke shinfid'e a table doctors nata aikinsu akan gawar, damtsen 💪🏻hannunsa ya khaleel ya kalla, cikin zare ido yace, "Joseph hoton miye wannan?".
Kar6ar picture d'in yayi yana kallo, sir! Inhar hasashena yayi dai-dai wannan kunama ce🦂, dukada ba'a gani dak'yau".
Da sauri ya khaleel yamik'e yana fad'in Joseph inason ganin gawar David yanzunnan.
" OK sir!, idan ka shirya saimuje".
Chapter 40 · 0% Book details