← Book details Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 83

Sashe 46

Ciki Da Gaskiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******
Da sallama yashigo, haryanzu Aysha Na kwance Ammah ta hanata tatshi, yak'araso da saurinsa, gaban kujerar ya durkusa saitin fuskar Aysha, idonta Na a lumshe yasaka hannu yana shafa kwantaccen gashin goshinta, ahankali ta bud'e shanyayyun idanunta, wad'anda ciwo yasakasu komawa k'ananu kuma sunyi d'anja.
Sassanyan murmushi yasakar mata, sannan ya sumbaci goshinta, ta kuma lumshe idanunta tabud'e ahankali bisa fuskarsa.
"Babiena ya jikin?".
Cikin mamakin sunan daya kirata dashi, muryarta can k'asa tace, "Alhmdllh."
" masha ALLAH, bara kiga acire ruwan tunda yak'are" kanta ta jinjina masa kwai.
Yacire ruwan sannan ya taimaka mata tatashi zaune, daidainan Ammah tafito daga kichin d'aukeda kula k'arama. Sannu itama tama Aysha, sannan tazauna gefenta tana tambayarta ina kemata ciwo yanzu?.
Aysha tace babu komai, saidai bakinta d'aci.
"Karki damu shima zai daina watarana?".
Nanma kanta kawai ta d'agama Ammah.
Ya khaleel yad'an murza hannunta dake cikin nasa, tajuyo ta kallesa. Gira d'aya yad'age mata, yace, " mizakici yanzu to?".
Janye idanunta tayi daga kansa, tad'an jingina kanta da gefen hannunsa, Dan zaman yafara gundurarta, cikin dadishewar murya tace, "dama zan samu dafaffen gyad'a".
Murmushi yayi yace, " saikuma mi?".
"Shikad'ai ya isheni ya Sadauki".
Yashafe fuskarta da hannunsa Na haggu, " haba my Sholy kidai fad'i wani abun bayan gyad'an, kinsan bakici komaiba".
Ta d'ago idanunta tana kallonsa, fuskarta a yamutse tace, nidai gyad'an is OK, idan kuma za'a samu zogale ahad'amin dashi to".
Ammah dake kallonsu cikeda sha'awa dajin dad'i tace, "Abu mai sauk'ima kuwa, bara ajenan gidansu Ameenu arok'o zogalan tunda sunadashi, barama dakaina zanje aii".
"Yauwa Ammah jar wuya, shiyyasafa nake yinki akoda yaushe, dolene nasiya miki motafa".
Baki ammah tawashe. "Lah iro gaske ko wasa?".
" ahaf aii dagaske nakeyi ammah, amma sai nanda k'arshen shekara idan ALLAH ya kaimu, yanzu abubuwa sunmin yawa".
"Yo konanda shekara biyune aii zanhak'ura iro, kaidai kawai kacika alk'awari idan munkai daranmu".
"Insha ALLAH zancika ammah".
Ammah tafita anata washe hakwara ya khaleel zai saya mata mota.

Tana fita ya khaleel yamaida kallonsa ga Aysha yana murmushi, A'eesha kinfaji Ammah tsohuwa, ko INA ita INA mota?".
Murmushi Ayshan tayimasa, tace, " Yaya kacika alk'awari kawai".
Harar yazuba mata.
tace, "o, sorry sadauki, tayi maganar tana rufe bakinta da hannu.
guntun murmushi yayi, sanna yamik'e da Aysha ajikinsa yana fad'in muje kiyi wanka, kafin Ammah takawo zogalan ko, tunda kinsan saita dafa tukunna.
Cikin 6ata fuska Aysha tace, "to gyad'anfa kuma?".
Yatsansa guda d'aya yasaka ya d'alli bakinta.
Zafi yasakata dafe bakin da sauri.
Shikuma yay murmushi yakaita toilet d'in Ammah.
Dak'yar ya yarda yafito tayi wankan da kanta bayan yahad'a mata ruwa maid'an zafi, amma da ya dage saiya mata wankan dakansa.
Ganin shagwa6ar datake zuba masa zata sakashi ya narke, yasakashi hak'ura yafita.

Tanayi tana hutawa, haka tagama wankan, saboda jikinta duk babu k'wari, ga ko INA ciwo yake mata, musammanma mararta wlhy.
Koda tafito abakin gadon Amman ta iskeshi zaune, yabud'emata hannayensa alamar tazo gareshi.
Akunyace tak'arasa tashige kuwa, ya rungumeta tareda gyara mata zama acinyarsa, ahankali ya sumbaci goshinta, murya k'asa-k'asa cikin kunne yace, " nizan shiryaki ko? Tunda kin hana namiki wanka".
"kai ya khaleel wai bakajin kunya? Ammah fa zata iya shigowa ta ganmu".
Hannu biyu yasaka ya tallafe kumatunta, sai raba idanu yakeyi a fuskarta, itakam takasa kallon cikin idonsa, saikawai ta lumshe idanu, ganin haka yayi murmushi tareda d'ora bakinsa akan NATA yashiga abubuwa.
Tun tana k'ok'arin kwace kanta harta hak'ura ta mik'a wuya. Saida ya sumbaceta San ransa sannan yacire bakinsa suna sauke numfashi.
Kunya ta lullu6e Aysha, tayunk'ura ahankali zata tashi Yakuma rik'eta da k'yau, "kinga Izamanki, bara Na shafa miki man, nasan jikinki babu kwari sosai".
Dole Aysha tahak'ura ya shafa mata man, amma idonta arufe akayi komai.
Kwantar da ita yayi agadon Ammah yace, " kwanta kihuta inazuwa".
Ta gyad'a masa kai tana wani lumshe idanu, jinta takeyi wani fayau da ita yau d'inan wlhy.
Fitar ya khaleel babu dad'ewa saiga Anty Ama.. Tashigo, k'arasowa tayi Indaa Aysha take tana mata sannu, Aysha ta amsa kanta tsaye, harda cema Anty Ama wai mi doctor yace yana damunta?".
'Yar dariya Anty Ama tayi, tace, "ya khaleel nasan aii zai fad'a miki, yasan kin tashine?".
Aysha ta gyad'a kanta ahankali, kamar wata k'adan garuwa..
Babu dad'ewa ya khaleel yakawoma Aysha da doguwar riga Arabian gown, Anty Ama tatashi tafita.
Yanzuma dakansa yasakama Aysha kayan, duk kuwa kunyarsa ta gallabeta, harzai d'auketa tace, "please Anty Ama batatafiba fa".
Yad'an d'age gira yana ta6e baki, harya mik'o hannu zai d'auketa yajiyo sallamar Anty mamie a falo.
Dole ya dakata, yadai taimaka mata tamik'e zaune, dad'an rangajin rashin kwarin jiki ta isa falon, Anty Mamie tayi saurin tararta tana mata sannu, a kujera doguwa ta zaunar da ita ta jinginata da jikinta, yanzu ina ke miki ciwo?".
"Wlhy Anty Mamie dukdai banajin dad'in jikina, gakuma bakina d'aci".
"Sannu, Duk zasu daina kinji."
Ya khaleel kallonsu yakeyi cikeda sha'awa, saiyaji inama momyce kebama matarsa kulawa haka? kwallah suka cika idanunsa, karo Na farko dayafajin d'acin rashin kulawar Momy akansa, da k'yar ya maida kwallan, saidai tuni Anty Mamie tagani, ita kanta saida ranta ya sosu, Dan koba'a fad'aba tasan mi khaleel keyima kewa, (kulawar mahaifiya), amma yaza'ayi, haka ALLAH ya tsara masa.
Sallamar da Ammah ta doka yasakasu duk maida hankalinsu kanta, Anty Ama...tamik'e ta kar6i kayan hannunta tana mata sannu, "a'a Ammah mi'aka samomana kuma?".
" uhm mizan samo nikuwa, zogalene da gyad'a, wai Indo kesonci".
"Kai Ammah waye indo kuma?".
Da hannu Ammah ta nuna Aysha, "matar iro mana".
Mi Anty Mamie kuwa zatayi inba dariyaba, ya khaleel kam 6ata fuska yayi, Amma baice komaiba.
Zogalan Aysha tafaraci, babu laifi ansamu ya zauna, harma tad'anci gyad'ar.
Daganan akaita shigowa dubata, mama ma tazo, hakama bak'in 6angaren Momy da Anty shukurah tamusu jagora, Amma banda Aleeya da Anty zuwairah da kubrah, dama mufeedah ba'a sakata a lissafi, su Hasnah kuwa suna makaranta.

*****
Momy kuwa sai bayan magriba ta farka, bayan k'arin ruwan yak'are Aleeya ta cire mata.
Ya khaleel baije wajenba saida yadawo sallar isha'i, yatarar Momy zaune akan gadonta ta jingina da fuskar gadon, shayi takesha Wanda Hasnah ta had'a mata.
Yazauna kusada ita gefen k'afafunta, " momyna ya jikin?".
Ahankali tace, "da sauk'i Ibraheem, kana ina nafarka tun d'azun ban gankaba?".
" naje sallah ne, kinsan kuma itama Aysha babu lafiya, nad'an lek'ane naganta shine nawuto nan, bammasan kin farkaba."
Batace komaiba dangane da Aysha, Dan bak'aramin sosuwa zuciyarta keyiba idan tatuna da cikin jikin Aysha, gakuma babban bak'incikinta Na mufeedah, babu abu mafi hassala ranta sai idan tatuno wai Habeeb ne ya lalata mata rayuwar yarinya, yaron datasanshi afagen iskanci, babu nau'in zina wadda za'ace habeeb baiyitaba, wai shin yama akayi yashiga rayuwar mufeedah?, bayan kobarinsu zuwa gidan hajia khaltum batayi, saboda tasan gidan tamkar rezane da katifa awajen had'ari, wasu zafafan kwallan suka gangaro bisa kumatunta, ita kanta batasan kuka takeyiba.
Ya khaleel yasaka hannayensa yana goge mata cikin tausayawa, muryarsa a raunane yace, "haba Momy, Dan girman ALLAH ki kwantar da hankalinki, kinsandai bakida isashshiyar kafiya, yaufa bak'aramin hawa jininki yayiba, ALLAH ne kawai ya taimakemu Doctor Faisal yazo kawo magungunan A'eesha, Amma da kafin mukaiki asibiti ansamu matsala, kicire batun mufeedah aranki, kid'auki hakan amatsayin k'addara, kuma bawai na k'yale baneba, dolene nad'auki mataki akansa".
Jin jina masa kai kawai Momy ta iya, Amma itakad'ai tasan irin tafarfasarda zuciyarta keyi, aii wannan yak'in natane, dolene tad'auki mataki da hannunta, Dan habeeb bai Shata abanzaba, tsorontama ALLAH yasa baida wata cutar dazai zubama mufeedah batajiba bata ganiba, saikawai tarushe da kuka data tuno lalacewar rayuwa irinta Habeeb.
Ba ya khaleel ba, hatta inna jummai mahaifiyarta kukan d'iyarta yad'aga hankalinta, sukai cirko-cirko suna kallon yanda ya khaleel ke lallashinta, dak'yar yasamu tayi shiru.
Bayan tagama shan shayin da ya khaleel ya lalla6ata, ya 6alle magungunanta yabata tasha, baffahma yashigo yadubata, kusan mintinsa 30 sannan yafita, hakama su mama duksun shigo sun dubata, dukda dai k'in amsamusu tayi, danji take kamar takashesu tahuta Dan bak'in cikin sanin sirrinta dasukayi, saidai babu damar hakan kuma.🤪

***********

Kusan 10pm ya khaleel Yakoma 6angaren Ammah, ya tarar Aysha hartayi barci, Ammah ma zaune take tana kallo da gyangyad'i, Amma dan k'unata tak'i taje ta kwanta, wai film take kallo, gashima ba Hausa akeyiba bare ace tanajin misuke fad'a, kamarma yaren Germany akeyi.
Cikin sand'a yawuce tabayanta yashiga bedroom d'inta, Aysha Na kwance a gadon ta k'udundune da k'aton bargon Ammah, barci takeyi, saidai dagani kamar batajin dad'in barcin, yakwanta ahankali ta bayanta, mannata da jikinsa yayi, yasaki sassanyar ajiyar zuciya, idonsa alumshe ya sumbaci wuyanta yana shinshinar k'amshinta, yasan Aysha dabance a fagen tsafta, ko 'Yar ahekara 100 taganta tabari, gabanta yadawo, yasumbaci goshinta da la66anta data ta6e kamar zatayi kuka, murmushi yayi yana zagaya la66an da d'an yatsansa, kamar tasan miyakeyi tagyara bakinta yakoma normal, wani murmushin yasaki, sannan ahankali yad'ora bakinsa, kad'an yay kissing d'inta yajanye bakinsa, saboda motsi data fara.
Maganar Ammah yajiyo sama-sama, dasauri yatashi Yakoma bakin gadon ya zauna, addu'oi yayma Aysha ya tofeta dasu, jiyake kamar karya barta wlhy, Dan yana buk'atar jinta ajikinsa, amma yasan jarabar Ammah bazata yardaba, gwara yabarta nanda kwana biyu saiya lalla6ata tabashi ita.
Ammah data shigo tarik'e kunkumi👯‍♀, "kaikuma yaushe kashigo saikace wani Aljani?".
" kinacan kina gyangad'i yazakisan Na shigo".
"Kajimin d'an jakar uba, yo bakaida matarka bane kuka jamin, tunda safe bakubar uban kowa yayi barciba, nitashi katafi saida safe".
" ko bakicebama zantafi aii Ammah, saidaifa ga amanata nan, nabaki kirik'e gam-gam, karki saki baki kita barci taita shan wahalar ciwo cikin dare".
"Ank'i kar6ar Amanar taka, tashi kafita kafin nakira ubanka nasanarmasa".
"A'a aiba'azo nanba Jar wuya, kinga saida safe, nasanki jar wuyace, dolene nayi shakkarki"..
''Kaidai kasani fitsararre dogon banza".
Haka taita mitarta ita kad'ai, saida tayi mai isarta sannan ta kwanta tayi musu addu'a, Dan Ammah akwai kulada addini, shiyyasa ta tsaya tsayin daka jikokinta suka samu ilimin addini, gashinankuwa kowa yanacin ribarsa.
Damma zakkar mufeedah dasuka fitar.

Nace, " itama Jamata akayi aii🤷🏽‍♀".

_____________________________

*_Washe gari_*
Chapter 46 · 0% Book details