← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 45

Sashe 9

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mahmud yayi mishi ruk'iyya inaga yad'an samu matsala ne,daroya sosai manosh yakeyi harya shiga gida,mum da miher se binshi da kallo sukeyi,miher tace the prince lfya kuwa,yace wlh maryam ce take haukatani uama manta mum nashi tana palon,ai take ya seta kanshi yace mum dama kina nan ne,yad'an sosa k'eya,tace nidai inaso akawomin maryam d'innan inga mai sunana kuma sirikata,miher tace dama yau nake so inje in bro ya yadda zuwa jibi kuma se inje mu taho tare. Manosh yace a'a ki bari dai jibin se driver ya kaiki ku taho tare,miher bata so hakanba amma tasan manosh magana d'aya yakeyi dan haka ta sanar da maryam cewa baza samu zuwaba se jibi,maryam bataji dad'iba dan batayi zaton manosh zaik'iba. Da yamma su manosh sukaje gaisuwa gun surukansu tun daga gun mahaifin ameena suka fara har na zahida sannan suka wuce gire mota 3 masu zafi. Kyakkyawan k'arb'a aka musu dama ansan da zuwansu. Koda sukaje gidansu rashida da samira sannan suka wuce batare dasunyi hira da 'yan matanba. Bayan sun komane ya kira maryam se fushi takeyi waidan ya hana miher zuwa. Babu irin rarrashin dabai mataba amma tak'i tanata fushi. Yace am sorry apple zan kawota jibi da kaina kinji,tace banso indai kai zaka kawota bazaniko inaba,yace to shikenan bazan zoba zan kiraki anjuma pls zan d'auki wani kiran kinji,tabace komaiba ta katse wayan shi kuwa ya d'auki wayan oganshi. Kamar yadda manosh yace yau miher ta shirya driver ya kaita gun maryam,mirna sosai maryam tayi bayan sun gaisa da mamane se suka wuce d'akinta,ita kanta miher d'akin ya burgeta dukda dai ita 'yar masu akwai ne. Hira sukayi kad'an maryam ta cikawa miher ciki da abin mak'ulashe sannan tace bari in yiwa mama sallama semu tafi dan in dawo da wuri koh,tare suka mik'e sukai mata sallama tace a gaishesu sannan suka tafi. After dress ce red a jikin maryam tayi kyau sosai taga sun tsaya a wani katafaren gida. Koda aka bud'e gate se taga ashe cikin yafi wajen had'uwa,bayan sun k'arasane taketa ganin flawers kala kala masu kyau sosai. Miher tana rik'e da hannunta se gaisheta gards din sukeyi har suka k'arasa palo, me zata gani...hoton miher da manosh ne da kuma iyayensu,jikinta yayi sanyi tanata fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tabbas maryam bazata tab'a mance fiskan wannan mutumin da take tunanin shine mahaifin manosh ba,acikin ranta kuwa tace wlh bazan tab'a b'oyewaba koda hakan zaisa in rabu da manosh peach d'inaba. Miher tace yanaga kina ta kallon hotonmu da iyayenmu nadai fi bro manosh kyau,murmushin kawai tayi tace nidai bance komaiba,miher ta kaita d'aya palon sannan ta zauna tace ina zuwa bari na kira mum sannan ta wuce wani kofa,ita kuwa tana zaune kanta a sunkuye tana tunani. [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd Dedicated 2 FIDDY G MUH'D 25-26 Mum da miher sun fito a tare kan maryam a sunkuye, tayi saurin durqusawa qasa ta gaishe da mum din manosh cikin fara'a da sakewa sosae mum ta amsa mata gaisuwa tare da tambayanta ya mutanen gidan, sun dae gaisa sosae amma kan maryam a sunkuye yake. Mum tace ki saki jikinki fa , nan kaman gida ne haka dae sukaci gaba da hira mum ta kama hanya ta tafi ta barsu ita da miher. Miher ta kawo mata kayan maqolashe kala kala, maryam bata iya cin komai ba in banda ruwa da tasha. Suka dan yi hira kadan daedae lokacin dad din manosh ya shigo yana kiran miher da sauri tace naam dad, sannan ta fita taje wurin dad dinta, yace ke da wa kuka shigo?? Tace nida wanda bro manosh zae aura ne. Tazo gaida mom ne nan dae tace dad bari tazo ta gaishe ka, tayi sauri ta koma taje ta kira mrym da sauri ta fito kanta a sunkuye ta durqusa har qasa ta gaishe da dad shima ba laifi cikin fara'a ya amsa. Koda suka gaisa ya wuce dakinshi ita kuwa maryam tana kallonsa a nitse ta sake tabbatarwa wannan shine mutumin da nan da bazata taba mantawa dashi ba a rayuwarta. Jiki sanyaye ta koma falo suka zauna dae, ita kanta miher ta lura da sauyi daga gareta amma bata ce mata komai ba. Maryam ta dan zauna na kusan 30 mins tace to gaskiya zata tafi saboda batason dare yayi miher tace bazaki tafi ynxu ba dole se bro manosh ya dawo dan shine zai maida ke gida maryam tace aa ni bamuyi haka dashi ba dan allah ki tashi ni zan koma gida. Miher taga dae da gaske takeyi dan haka ta kira bro manosh a waya ta sanar dashi bada jimawa ba yazo daedae lokacinda suka fito tayi sallama wa mum zata tafi, mum ta hada mata goma ta arziki ta rako ta har kofar falo sannan ta juya , shi ko dad daman ya riga da ya fice. Ko da ta iso wurin mota tana tsaye shi ko manosh ya danno shi da marwan kallonta yakeyi tun daga sama har qasa saboda kayan ya bala'in mata kyau murmushi kawae takeyi tare da gaishe da marwan bayan sun gaisa ne manosh ya matso kusa da ita yace wato bazaki gaishe ni ba kenan?? Shuru tayi batace mishi komai ba tace nidae ka kaini gida yace ae ba ni na kawo ki ba wanda ta kawo ki saeta maida ke,maryam ta maida kallonta gun marwan tace marwan kaji abinda yace ko,marwan yace rabu dashi muje in maidake,duka manosh ya kaiwa marwan tare da cewa ina ruwanka acikin hidimata,marwan yace da ruwana mana aunt muje in kaiki gida kinji tare da dannan keyn mota ya bud'e mata gaba ta shiga ta zauna sannan manosh ya karb'e keyn a hannun marwan yace zaka zauna a baya kenan,marwan yace eh ba matsala,maryam tayi mirmushi yayinda miher tasa mata goma na arzikin da mum ta had'ota dashi sukai sallama manosh yaja mota suka tafi. Tunda suka fara tfy manosh da marwan ne suketa hira itakam tayi shuru tana ta tunani a ranta. Manosh ya lura cewa akwai sauyi tattare da ita,yace kira sunanta a hankali apple,juyowa tayi suka had'a ido sannan ta mayar da kanta gefe,shuru yari bai sake cewa komaiba har suka iso girei,marwan yace jirani abokina bari naje gun rash a tsatstsaye yanzu zan dawo. Bayan marwan ya tafine su kuwa suna zaune a cikin mota manosh yace apple meyake damunki? Murmushi tayi tace bakomai,yace no apple karmu fara haka dake pls ki gayamin dan nasan akwai wani abu,tace gaskya naji dad'in yadda aka karb'eni a gidanku mum naka tana sona sosai nagode sosai tana murmushi tare da kallon kyawawan idanunsa,shima idanun nata yake kallon yayi da yakejin shaid'an yana zugashi da cewa kayi kissing nata manosh,maryam taga kallon da yake mata ya fara wuce gona da iri dan haka tayi saurin kawar da kanta tare da cewa zan shiga gida. Manosh ya dawo hayyacinsa yace bakomai apple kin cancanci a k'aunaceki domin kina da halayya na gari masu kyau daban sha'awa,dad'i taji tace ai kaima haka,dan azamanin yanzu da kyar asamu namijin da baya iya tab'a koda hannun budurwansa shiyasa kullum nake k'ara sonka manosh nasan cewa kana min so na gaskyane kuma mai tsafta. Jikinshi yayi sanyi dajin kalaman maryam,yayi hamdala a cikin zuciyarsa yace Allah nagode maka danafi k'arfin shaid'an a wannan lokacin Allah ka k'ara kareni akan sha'awar da nakeyiwa maryam ameen. Ta katseshi da cewa ya naga kayi shuru,yace bakomai kawai bana so ki tafine harse marwan ya dawo,murmushi tayi tace toshikenan kamin hira,yace kedai zaki min,tace ni nawa sun k'are ai,yace to mata biyu nake sofa in aura dake da kuma wata kin amince? Murmushi tayi tace eh na amince mana ai halal ne kana iya yin hud'uma,dariya sosai manosh yakeyi,wanda yake burge maryam dan manosh ya had'u wlh sedai sam bai fiye yin dariyaba wanda ta lura hakanma dan itace yakeyi se kuma dasu marwan ko miher. Manosh ya tsargu da irin kallonsa da maryam takeyi yayi sauri tsayawa da dariyan nashi yace "apple why are looking at me like that?" Kunya sosai taji dan batama san ya akai taketa kallonshi hakaba,kuma aduk lokacin take kallonshi sha'awarta tane kawai yake kamashi. Maryam tace ina son ganinka aduk lokacin da kake dariya dan kanamin kyau sosai manosh,jiyayi kamar ya rungumeta dan yadda yake ji,amma seya daure yayi d'an murmushi tare da d'aukan wayarsa ya kira marwan yace ganinan zuwa mutafi sannan ya katse wayar maryam tana kallonshi,shi kuwa bai sake kallontaba hannayenshi suna kan siterin mota yace apple am goying,mamaki taji amma setace tonagode Allah ya kiyaye hanya yare da bud'e kofar mota ta fita se nanne shima ya fito tare da d'aukan abubuwan da mum ta bata yake mata har zauren gidansu ya ajiye. Tace nagode tana murmushi,kallonta yayi batare dayayi murmushi yace *minfu miyatti* sannan ya wuce motarshi ya shiga yaja yana mata bye,ita kuwa murmushi kawai take mishi daga k'arshe ta d'aga masa hannu sannan ta wuce gida. Maman maryam tayi farin ciki sosai dajin yadda aka k'arb'i maryam hannu bibbiyu,ga kuma zannuwa da less masu tsada ga sarka da turare da mum din manosh ta bata. Maryam ta koma d'aki tana kwance se kuma ta tashi ta bid'e kit nata ta d'auko memori tasa a wayarta ta sake tabbatar da cewa lallai wannan shine mahaifin manosh,hawayene suka fara zuba a idanunta se taji wayanta na k'ara,koda ta duba *peach &cream* ne seta d'auka tare da share hawayenta tace hello,manosh yace apple mun tafi,tace to Allah kare nagode,yace ameen *i luv u* murmushi tayi tare da cewa *she luvs u 2* dad'i yaji yace thankyou apple,tace always *peach* wayyo Allah manosh kamar zaiyi hauka yana mirmushi ya katse wayar yatana lumshe ido,marwan yace bari in karb'eka dan naga kamar ka gaji,dariya sukayi dukkansu sannan manosh ya fizgi motar kamar zasu fire sama,marwan yace a'a mudaije a hankali kaga dukkanmu tuzuraire hhhhhh Maryam kuwa wasu zazzafan hawayene suke zub'o mata tinda ta ajiye wayar. Tace inason sosai manosh,yanzu ya zanyi kenan? Wayarta ta d'auka ta kira uncle ibrahim bayan sun gaisa tace dam inaso miyi magane in baka cikin mutane,yace ok bari na kiraki. Bayan ya katsene ya sake kiranta yace yes aunty ina jinki,tace ka tuna da wannan vedion dana tura maka a
Chapter 9 · 0% Book details