← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 45

Sashe 23

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*dedicated to mmn adnan* (babby) 51-52 zama sukayi sunta kuka sosai,hiransu na d'azu kawai taketa tunowa a zuciyarta da kuma dariya yayita sasu ita da manosh lokacin da sukaje ganin gida,nan ta sake fashewa da kuka tana cewa ashe daman bankwana muketayi dakai d'an aunty,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un suketa nanatawa tare da cewa Allah ya jik'anka abdallah yasa ka huta. Yah ibrahim ne da friends nashi seke fitowa da gawan abdallah bayan sun gama mishi sutura. Koda suka fito daga d'akin ya ibrahim kuka sosai jama'a keyi,da sauri maryam ta d'ago da kanta ai kuwa setaga gawan a hannunsu suna zuwa gun mama dashi,tunda yah ibrahim ya had'a ido da aunty seyaji hawaye yazo mishi ido amma ya daure ita kuwa kuka sosai sukeyi ita da rash. Mama ta matso tayita mishi addu'a,rasha da maryam ma suka matso se kuma baban maryam d'in tunda shine matsayin ubansu dukkansu. Haka aka d'auki gawan aka fita dashi yayinda jama'a suketa kuka akai mishi sallah,batare da b'ata lokaciba aka kaishi gidansa na gaskya hardasu manosh wato "the 5 emms" dan yah ibrahim ya tura musu texs d'in rasuwan k'aninshi abdallah kuma d'an autansu. Yah ibrahim ya kasa barin kabarin se hawaye yakeyi akan kabarin,friends nashine taredasu marwan suka d'agashi jiki sanyaye suka dawo gida inda aka zauna kab'ar gaisuwa. Hmmm!rayuwa kenan,yau kaine gobe bakaibane. Kuduba dai kuga irin mutuwar da abdallah yayi,ran friday,kuma koda yabar gidansu maryam ya wuce gida hira sosai sukeyi da mama da yah ibrahim rash kam tuni ta koma bacci dan ko wani sallama basuyiba,in banda gaisuwa daya mata na safiya tace ya jikin,yace wlh na samu lfy. Koda suka gama hira dasu yah ibrahim alwala yayi yayi sallah sannan yace mama tea zansha,ta had'a mishi yasha ya ajiye cup d'in yaci gaba da addu'oinshi bayan nan seya kwanta akan sallayan a d'akin yah ibrahim dama tare suke kwana,tofa kwanciyan kenan dabai tashiba. Yah ibrahim kuwa yana gum mama suna hira,bayan sun gamane ya dawo d'akin yace abdallah a k'asa kuma,tashi ka kwanta akan kafifar mana,shuru bai tashiba,kuma kowa yasan abdallah sam bayida nauyin bacci,hakan yasa ibrahim tab'ashi amma seyaji baya numfashi. Salati ya kamayi tare da girgiza abdallah amma babu abdallah ayau ya rigamu zuwa gidan da duk wani musulmi seyaje dazanar lokacinmu yayi. Allahu akbar,Allah yasa muyi irin rasuwan abdallah ameen. Ana zaune agun makoki kowa juki yayi sanyi,idan aka tuna da karatunshi na asuba cikin suratul muh'd. Kai jama'a duniya ba komai bace wlh,Allah ya gafarta mana kurakurenmu ameen. Manosh se kallon hotunanshi yakeyi a wayanshi yana tsaye tagun pool ya d'aga yatsan hannunshi d'aya wato ALLAH WAHID. kwalla manosh yaji a idonshi amma sam yaqi zubar dasu,dan bayaso azabtar da abdallah,domin shi kuka ga mamaci azabace ake k'arawa mamacin. Jama'a sosai abdallah ya samu kowa alkhairai kawai kakeji abakinsa akan abdallah,hakan yasa yah ibrahim farinciki sosai,domin shaidar duniya itace zata bika har lahiranka. 11:00am su manosh suka shiga cikin gidansu rash,inda suke zaune a rana suka shigo da yah ibrahim sukayiwa mama gaisuwa dakuma rash harma da maryam,dan dole agaida maryam saboda indai kasan abdallah tofa dole kasan maryam dan kowa shaidane akan k'aunar da take tsakaninsu. Rash da maryam basu iya amsa gaisuwanba banda kuka da sukeyi har'yanzu,haka suka fice tare dayiwa baban maryam gaisuwa sannan suka tafi. Haka dai akayita zuwa gaisuwa mutane ma'a magana. Yau monday yaune uku dan haka su manosh da iyayensu sukazo hardasu dad,akayi addu'an sannan sukayi musu gaisuwa suka wuce. Da hantsi su mum d'in manosh danasu marwan harda miher da lubna sukazo gaisuwa. Kukan da rash takeyi yasa duksuma suketayi. Miher tace ina yah ibrahim muyi mishi gaisuwa,samira ce ta kirashi yazo suka gaisa harda lubna,tausayinshi ya kamata setaji sabon k'aunarshi yana shiganta a hankali saboda wannan shine ranar farko da suka fara ganin junaeye to eye,dukda dai dama tayi mishi gaisuwa a waya kuma tagayamishi cewa zasuzo ranan uku. Yace mun gode sosai Allah ya bada lada,sukace ameen sannan ya gaida mum nasu ya fita waje. Rayiwa kenan yau wenesday bikin su maryam saura 2dys kawai. Manosh ya kira maryam a waya haryau kuka takeyi,yace pls apple kiyi hakuri kibar kukan,batace mishi komaiba se dan Allah ina neman alfarma a d'aga bikinmu se zuwa wani lokaci pls? Shuru yayi yace ok apple zanyiwa baba magana kinji,tace nagode sannan ta katse wayar. Manosh ya sami mahaifinshi da zance amma se mahaifinshi yace munyi maganan da iyayensu amma sunce baza'a d'agaba tunda an sanar,sannan mamacin bazai dawoba sedai idan akwai wani biki da zakuyi to duk kuyi canceling nashi saboda rasuwan. Manosh yace to dad mungode sannan ya tafi tare da sake kiran apple ya gaya mata,aise fashe da kuka sosai wanda ya d'aga mishi hankali da sauri ya katse wayan cike da damuwa ya kira marwan suna magana,marwan yace eh wlh ibrahim ma cewa yayi kawai ayi bikin baza'a d'agaba kuma wlh nima naso a d'aga. Manosh yace to yaushe zamuje girei,marwan yace anjuma ba,manosh yace dama ba'yi musu jeren kichineba kud'in nake son bawa apple ta sayi kayan kichine sannan suje suyi jere amma yanzu komai ya tsaya kenan,marwan yace sedai muba su mum kawai su k'arasa mana dan kaga ba time yanzu gaskya. Haka kuwa akayi a ranan mum da 'yan'uwansu sukayi sayayyan kayan kichine abin se wanda ya gani aka shirya komai tas zuwa 8:pm suka gama komai aka rufe gidan. Ran alhamis da safe bayan an gama yiwa miher lalle tasa driver yakai mai zanen lallen har girei dan ayiwasu maryam rash da samira. Dayake tana sauri nan danan ta musu ta gama zuwa azahar ta gama musu,maryam tace nawane kud'inki,mai lallen tace an riga da'an biyani zan koma,nan driver ya maidata gidansu miher aka biyata kud'ade masu yawa aka kaita gun zahida da amina ma ta musu. Bayan la'sar angwaye sukazo harda yusuf angon amina. Amare suka fito amma sam babu wata walwala a fiskarsu,angwayen basu damuba dan sunso a d'aga auren amma sam ank'i. Bayan sun gaisane kowanne yaja fefe da matarsa suna magana,yayinda majid da muhsin da yusuf suke gu d'aya da yah ibrahim suna magana. Manosh yace apple,shiru tayi dan sam setaji bata son auren. Yace babu wani abu da kike buk'ata,tace babu komai tare da kwalla a idanunta,ledan hannunsa ya mik'a mata dan dole ta karb'a yace kije gida zamu tafi muma amma pls kibar wannan kukan,batace komaiba ta wuce gida batare data musu sallama ba. Manosh jikinsa a sanyaye yace wlh ibrahim aurennan da d'agashi akayi se nan da 2month,gabad'ansu baso sukeyiba wlh mutuwar abdallah kamar yau akayi suke jinta a jikinsu,muma kuma haka wlh,muhsin yace wlh kuwa. Ibrahim yace haka Allah yayi karku damu Allah yayi mishi rahama,suka amsa da ameen sannan suka tafi. Bayan isha manosh ya kira apple,tace kayi hakuri pls da abinda nake maka ba laifina bane,yace don't worry apple am okay with everything kinji,wlh naso abar auren amma hakan baiyuba,tace hakane nagode,yace kidena min godiya apple am sorry for d lost of our abdallah,shuru tayi hakan ya tabbatar mishi da cewa kuka takeyi,yace apple are you okey? Tace "yeah am fine" cikin muryan kuka tace peach gobene fa abdallah zaiyi karatu a walima,ashe fad'a kawai yakeyi...manosh yace pls stop it apple,babu abinda zai canja zauyi walimar kuma karatun abdallah zamu saurara agun insha Allah. Tace thankyou so much peach,yace "anything for apple" _i love you so much_,tace me too. Dad'i yaji yace ki huta kinji gud nyt,tace thankyou. Lubce agun doctor da safiyar friday taje ayi mata gwajin jini ko tana d'auke da H I V. Amma sam babu komai Allah ya kareta,murna sosai tayi tare dayiwa Allah godiya,bayan ta kira yah ibrahim ta gaya mishi komaine,seta kira maryam ma. Murna sosai maryam tayi tace shikenan barka lubna,tace nagode maryam bazan manta dakeba sannan ina tayaki murnan zama matar bro manosh,maryam cikin hawaye tace nagode. Bayan sallan juma'a aka d'aura auren masoya 6 a babban masallacin jumma'a dake jimeta,inda angwaye sukasa jallabiya ash da lullub'i irin na larabawa,sunyi kyau sosai kuma suna cikin wani ni'ima mara misaltuwa amma dukda haka manosh da marwan akwai damuwan rashin abdallah sossi a fiskansu,bare kuma da suka san halin da matansu suke ciki a yanzu haka kuka sosai sukeyi an kasa rarashinsu dan ansanma bajin rarrashin zasuyiba dan haka akabarsu suyi mai isarsu.... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muhd *dedicated 2 iman muh'd alee* 53-54 Hankalin manosh ya kasa kwanciya seya sake kiran maryam,daidai lokacin da yapendo ladi tayita mata nasiha har tayi shuru sannan ta barta. Wayan ta d'auka tare dayi sallama,yace aunt ina fata kin dena yin kukan,tace eh,yace gud pls kiyi hak'uri komai ya wuce da akwai yadda zanyi inganki yanzu dana zo,tace bakomai,yace inatayamu kasancewa miji da mata yau,murmushi tayi tace nima haka,dad'i sosai yaji yace gaskya an cika sosai dayake kuma jumma'a mun samu jama'a harda wanda ba'a gayyacesuba,mirmushi tayi tace to Alhamdulillah ina gaida angwaye,yace apple,tace na'am,yace i luv u apple,wani iri taji yadda yayi maganan tace me too. Yace semunzo anjuma ko akwai abinda kike bukata,tace eh akwai yace menene,tace flower,murmushi yayi yace zan kawo miki anjuma idan nazo d'aukan matata,tace da kanka,yace yes ba matatabace,tace eh amma ai da manya zamu,zauna a motan,yace a'a nidai dagani seke,dariya tayi tace a'a nidai manya nafiso,ok bakya son inkaiki ko,toshikenan nibazan zobama nayi fushi. Tace haba fushi kuma dani,yace yes se anjuma bari mu gaisa da friends na dad,tace ok pls karka manta da flowernah,yace indai bazan manta dakeba to hakama flowern,murmushi tayi shima haka sannan sukayi sallama. Nasiha sosai akayiwa amare harma da angwaye musamman manosh ance dole yabar maryam taci gaba da karatunta,yace dukya amince harda sa hannu kuma ya rubuta cewa maryam itace matarsa ta farko kuma ta karshe babu k'arin aure tare dasa hannunsa dana mahaifinsa akabawa babanta takardan da kuma malamanta se kuma iyayen manosh d'in. Da dare bayan sallan isha aka had'a walima ta maza agu d'aya, inda akasa karatun abdallah ne kawai yake tashi agun ga malamai da angwaye da abokai dadai jama'a sosai,masu kuka sunata kukansu,harda su maryam dan angwayen sun kirasu a waya donsu saurari walimar. Karatun abdallah yakai awa daya sannan malam balalau yayi musu wa'azi sosai tare dayiwa abdalla addu'oi akaci abinci maiji da lfy aka sha aka k'oshi sannan aka rufe taro da
Chapter 23 · 0% Book details