← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 45

Sashe 39

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da wani akayiwa hakan da sunanmu ya gama b'aci,yanzu haka kunyan had'a ido dasu nakeyi wlh mungode sosai Alhaji zamu tafi,yana kaiwa nan ya fito suka biyoshi a baya,bai k'arasa gun motaba ya yanke jiki zai fad'i da sauri su majid suka tallafoshi aka sashi cikin mota ida muhammad yaketa faman dubashi yace ai jininsane yahau sosai. Subhanallah ake ambato agun,da sauri suka shige se jimeta inda akayi hospital dashi. Dad d'in marwan baida hawan jini sam,amma yau gashi dr yace hawan jinine ya kamashi sosai. 'Ya'yan nashi sunyi iyakan k'ok'arinsu agun dan kula da mahaifin abokinsu. "Shi kuwa mahaifin manosh,yana cikin damuwa wanda har yake jin ciwon kai mai zafi,amma haka ya daure yana nan akan abokinsa. "Su maryam kuwa fitowa sukayi daga d'aki sukazo gun hajiya iya kamar yadda babansu ya umarcesu. Dan tun lokacin dataji abinda ya sami d'an nata shikenan aka rasa gane kanta. Hakuri aketa bata,itama hajiya khadijan sam ta kasa sakewa,hakan yasa tace zata komar da hajiya iya gidansu can na jimeta tunda akwai masu girki,ita zata tafi asibiti gun mijinta. Haka aka rakosu har waje suka tafi. Maryam sebin motar nasu da kallo takeyi har sukayi nisa sannan lubna ta kamo hannunta tace aunty kidenasa damuwa aranki pls komai ya wuce kamata yayi ace kina murnan samun k'anwa. Jiki sanyaye ta juyo suna kallon junansu tace lubna,bakya jin komai gameda abunda ya sami daddynkine? Lubna tace daddyn bro marwan dai. Maryam ta dafa kafad'arta tace lubna har gobe har jibi shima daddynkine sannan inaso ki nuna damuwarki sosai akanshi kamar yadda kike nunawa akaina inhar kinasona da gaske. Jikin lubna yayi sanyi ta wuce gida tasa himar nata har k'asa tace mama baba zanje duba daddy,babu wanda ya hanata,seda tazo dabda maryam tace zanjene saboda ke saboda kuma shi daddy bayi da laifi sansan zanjene dan bro marwan bayanan,nasan koba komai zan d'ebemasa kewa. "Maryam tanata bin lubna da kallo harta dena kallonta zata shiga gida kenan setaji ana kiran sallan la'asar,koda ta juyo dan ganin mai kiran sallan seta wannan tsohonne dai wanda ta taimakawa a farkon littafin... "Marwan ahankali yake tfy harya isa gun abokinshi yace kaini masaukina. Bamusu ya kaishi batare dayace mishi komaiba,saboda yadda yaga marwan yasan bazai samu kowace amsa daga bakinshiba. "Bayan ya saukeshine marwan ya fita yace nagode,abokinsa yace yaushe zanzo to?" Dan numberka kona kira bana samu. Marwan yace zan kiraka sannan ya shige. Rashida tanata safa da marwa setaji nocking,da sauri taje ta bud'e kofa taga marwan atsaye kansa a sunkuye dukya galabaita yayi wani iri kamar maiyin azumi. Hakan ya tabbatar mata da cewa baici komaima,kallonta yakeyi cikin tausayi ga kwalla dasuke yawo a idanunsa. Tausayinshi ya kamata,ta rungumeshi sam ajikinta tana kuka tana cewa waime yake faruwane luv,dan Allah ka sanar dani bana son yadda nake ganinka ahakannan pls luv, baice da ita komaiba se kwallan da yake zubarwa,ahankali ta cire masa kayan jikinsa itama haa ta jashi zuwa toilet inda ya zama kamar jariri haka ta wankeshi tas sanan itama ta wanke jikinta ya d'auki towel itama haka suka fito a tare,yasa kaya tasake janshi wuza gun cin abinci amma sam yakici da k'yar tasashi yaci kadan sannan ya koma gado ya kwanta. Bayan ta gama komaine tazo inda yake tana tsunbatan sassan jijinsa a hankali tana kallonshi har cikin ido. Shi kuwa sam hankalinsa baya jikinsa,lips nashi ta far kissing ahankali cikin nutsuwa,shi kuwa idanunsa arufe yana jin yadda take mishi,kamar a mafarki yaji muryan manosh yana cewa marwannnnn Azabure,ya mik'e rash tace lfy luv,yace my luv manosh naji yakirani wlh ahine. Rash ta mik'e tace manosh fa kace,to a ina yake? Allah yasa dagaskene luv dabanda zaikai aunty farinciki maza muje muduba,bamusu yanufi k'ofa ita kuwa tasa himar ta fito,se juye juye sukeyi suna duba kofofin d'akinan ko zasuga fitowarsa koma suji muryanshi. Can yasakejin marwannn,ai kuwa yana juyawa seyaga manosh yana k'ok'arin fitowa daga wani d'aki amma sam j'afarshi baya motsi kaman an manda da superglue. Da gudu suka k'arasa gun,amma ina take kofan ta kulle kanta. Bugawa marwan yakeyi kamar zai b'alla kofan amma ina,sunan manosh yaketa kira yanacewa prince gani ka bud'e kofan pls kaida waye? Shuru babu amsa,seyaga k'ofa ta bud'u da kanta,dasuka shiga shiga amma babu alaman mutane acikin d'akin. Marwan yace ina bazai yuba wannan duk sharrin shukrah ce,duk yadda akayi suna nan,lallai bazan bar nanba senagano captain,nan suka zauna sunata addu'oi,ita kuwa rash tsone ya kamata sosai dan tabbas itama taga manosh da idanunta... " aunty kuwa koda tsohonnan ya idar da kiran sallah,gunshi ta k'arasa tace baba,murmushi yayi mata yace inatayaki murnan samun 'yar'uwarki. Murmushi tayi mai had'e da tsoro tace nagode,nakuma tuna da abinda ka gayamin a yanzunnan. Yace masha Allah maryam zan tafi,tace baba dan Allah mijinafa,kokasan inda shukrah takai min shi? Dan Allah baba kataima. Baba yace wacece shukrah? Jikin maryam yayi sanyi tace baba aljanace ita,ta rabani da mijina tsawon kusan wata hud'u kenan ba'asan inda yakeba. Baba yace ta ita maryam bansan komaiba akan wannan kimana tausayamiki sosai,Allah ya bayyana miki shi,kuci gaba da addu'a maryam babu wani abu dazai gagara,sannan kisa a ranki cewa Allah zai dawo miki da mijinki,karki dogara da wani kinji? Jikinta sanyaye tace to baba nagode tare da kwalla a idanunta. Ahankali tabar gun masallacin tayi hanyar komawa gida saboda mutane sun fara zuwa sallah,kan ta karasa kofar gida ta juya amsam bataga baba ba,kuma babu alamarsa tagurin. Mamaki,sosai tayi tayi da gudu ta shiga gida tana kuka ,hankalin iyayenta a tashe suke tambayanta ko lfy,tace gamo tayi da aljani. Iyayen suka tsaya kallon junansu,mahaifinta yace maryam wani irin gamo? Nan maryam ta basu lbr tun daga farkon had'uwansu da baba stohonnan har kuma taimakon daya mata a jejin yankari lokacin da saddam ya harbeta da bindiga a hannu da kuma abinda tsohon ya gaya mata akan lubna. Mamaki sosai iyayen sukayi,babanta yace maryam anya kuwa lfyanki lau? Tace wlh baba lfyta lau yanzuma shinagani shine wanda kukaji muryanshi ya kira sallah. Baba yace ajani ya kira sallah kuma maryam? Tace eh wlh baba nasan bazaku yaddaba amma wlh shida kanshi yagayamin shiba mutum bane aljanine. Baba yace to Allah ya karemu dadukkan 'yan'uwa musulmai,suka amsa da ameen sannan ya fita zuwa masallaci yanata kalle kalle tare da tambayan jama'a ina wanda ya kira sallah yanzu? Wanine yace tun d'azu yabi tacan,baba yace shibazai tsaya yayi sallan bane? Yaro yace oho mishi tsohone kodai zaije ya dawone oho mishi. Haka dai su baba suka idar da sallah amma wannan wannan tsohon bai dawoba,baba kuwa ya jinkirta yanata karatun qur'an a masallaci harya isar amma baiga kowaba haka ya wuce gida. Lokacin suna cin abincine se maryam tace baba har yanzu lubna shuru kodai sun wuce gidane itada yah ibrahim,mama tace kirasu kiji,bamusu ta d'auki wayarta ta kira lubna,cikin nuryan kuka lubna ta d'auka tace aunty zan dawo anjuma kad'an,maryam tace ya jikinnashi? Lubna tace da sauki yana bacci,maryam tace yanaji muryanki kina kuka lubna? Lubna ta share kwalla tace aunty daddy ya saki mummy. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....... [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas *To you readers! They say LIFE is a mirror: if you frown at it, it frowns back: if you smile, it returns the greeting*. *Is that true?* 87-88 Sakifa kikace lubna,tace eh sannan ta katse wayar. "Maryam ta kalli iyayenta tace baba wai daddyn marwan ya saki hajiya khadija" duk basuji dad'in lamarinba,amma babu abinda zasu iyayi akai haka suka gama cin abinci suka wuce dan k'arasa shirye shiryensu. Kusan 10:00pm yah ibrahim ya kawo lubna gida,idan suka dad'e suna magana da baba kafin ya tafi. Ranan dai basuyi wani baccin kirkiba dan gobe zasuyi tfy. Maryam kuwa tama rasa meke mata d'ad'i. "Washe gari da safe mahaifin maryam ya sanar da tfyan da zasuyi a masallaci don yiwa maryam aiki,sannan kuma yasake rokon jama'a ayita addu'a wa surukinsa wato manosh Allah ya bayyanashi. Addu'a sosai aka musu awannan lokacinma. Da misalin 9:10am yah ibrahim yazo ya kwashesu a mota inda suka wuce hospital suka gaida mahaifin marwan sannan suka wuce airpot. 10:20am jirginsu ya tashi abuja,suna sauka dama komai ya zama ready yah ibrahim ya gama komai suka wuce suna zaune zaman jiran tfya india. Marwan kuwa suyita addu'a har rashida ta fara bacci,shine ya d'agata yakaita d'aki ya kwantar da ita sannan ya koma yayita zama harya gaji sannan ya dawo shima hakadai suka wayi gari. "Bayan sunyi breafast ne marwan ya sake komawa d'akin amma bakoai aciki" mamaki sosai yakeyi abu kamar a drama?" Rash ce ta biyoshi hakadai suka sake dawowa d'akinsu inda take ce mishi itata sayi waya kuma tayita kiran numbern 'yan gida baya shiga dan haka ya bata numbern su majid,sam marwan yak'i yama karb'e wayan. Nan rash tayi fushi tace waime kake nufine kakawoni nan ka ajiyeni babu wani bayani jiya haka ka fita ka barni bakaika dawoba seda lokaci ya kure waima ina kajene marwan? Cikin mamaki yake kallonta yau sunanshi ta kira kai tsaye. Yace luv yau nine kuma marwan? Sannan zargina kike kome dakike min wannan tambayoyin? Tace eh zarginka nakeyi saboda abirkice ka dawo jiya kamar wani bugagge idan ka gaji da zama danine nikam kamaidani gidanmu gabad'aya kacanja kadena bani hakkina idan ka sau matan banza awaje toka sallameni intafi gidanmu nan ta fashe da kuka. Shi kuwa marwan maganganun nata sun mishi zafi sosai gashi dama yana da damuwa,baice da ita komai yafita yabar mata d'akin tanata kuka. Shukrah waike wani irin muguwace haka? Hahahha lallai kam manosh ka samu baki,wlh indai bazan samekaba tofa sedai in hallakaka itama maryam d'in ta rasaka tunda kai taurinkai kakeji dashi,danka samu na sake maka bakinka ko,tokamin bankwana manosh semun had'u a kiyama.............. Ihu mai k'arfi manosh yasa,awannan lokacin kuwa su yah ibrahim zasu tafi dama wayoyinsu akashe yake. Juyowa yayi yana kallon aunty se faman kuka takeyi tana tsaye,gunta yazo shida lubna sukace lfy aunty muje mana? Kuka ta fashe dashi tace sam bazatajeba ta fasa,mutanen gun suka tsaya suna kallonsu,da k'yar mahaifinta yashawo kanta ta yarda se waige waige takeyi har suka wuce tana kwalla. Yah ibrahim ma kwallan yakeyi dan yana mugun tausayawa aunty sosai. Haka suka wuce cikin jirgi tana tsakiyan mamanta da kuma lubna jirgi ya tashi.. Rash kuwa
Chapter 39 · 0% Book details