Sashe 22
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ki kula da kanki ki kuma ji tsoron Allah aduk inda kike,tace to mama nagode sannan tafito. Tace nagayamata,yace ok muje harda abdallah,nan abdallah ya bud'e mata gaba yace auntynah kishiga,murmushi tayi tace kaidai ka shiga nizan zauna a baya,haka kuwa akayi suka kama hanyan jimeta,shi kuwa manosh wayansa ya d'auka yayiwa maryama texs nan ta duba kamar haka tagani. _Hi my jealousy_ _I love you so verry much_ _Kuma ki dena wahalar dani pls,saboda ni manosh nakine ke kad'ai batare da kowaba,kwanaki kad'an suka rage in mallakeki apple jealousynah_. Murmushi sosai taketayi bayan ta gama karantawa,shi kuwa yanata kallonta ta mirrow yana tayata murmushin. Tun daga nesa abdallah yake gango wani had'add'en gida mai penti cream da kuma d'an army green yace gaskya gidancan ya had'u,manosh yace ko,abdallah yace sosai wlh koba hakaba aunty? Maryam ta kalli gidan tace hakane k'anin aunty. Daidai gidan manosh ya tsaya,dama maigadi yana baiwa flower ruwa ata wajen gate dinne,da sauri ya ciro remote a aljihunsa ya danna se gate d'in ta bud'u sannan suka shige ciki,daga maryam har abdallah bud'e ido sukayi sosai suna kallo.. [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTU'N YARA Written by sad-nas *dedicated to nurcee lurv* 49-50 Bayan sun fitone manosh ya rik'o hannun abdallah kamar wani yaro k'arami yace muje d'an gaban goshin aunty. Murmushi abdallah da maryam sukayi,ya kalli apple yace muje _jealousy_ tare da mata gwalo ya kashe mata ido d'aya wanda ya bata dariya tana biye dasu. K'ofa ya bud'e suka shiga palon farko babbane sosai wanda yasha wll peper army green mai tsadan gaske da labule ga kujeru da standart AC,can gefe kuwa daining ne shima komai army green ne harda frdje d'in. Akwai d'aki babba komai white ne a ciki,se kuma d'ayan d'akin blue amma bakomai daga gani kasan d'akin boys masu zuwane. Se katon kichine da store wanda farin tiles ne kota ina ansa gas da frezer ne kawai. Abdallah ya kalli aunty yace abokina white d'akinnan na wayene,yace nawa ne,blue d'in kuma na yaran aunty maza masu zuwa nan gaba,hhhh abdallah yayi dariya ita kuwa kunyane ya kamata. Sama suke hawa wanda palo 2 ne a saman,dama da hagu,na dama shine na manosh komai *milk colour ne* na hagu kuwa na maryam ne komai *peach colour ne*. Woooo! zanso ace kunga gidannan,kowannesu da daining nashi colourn palonshi,sannan a palourn maryam akwai wani ki hine da store komai light blue ne sedai bayi da girma kamar kichin d'in k'asa. Agefen maryam akwai d'akinta da toilet a ciki,daga gefe kuma d'akin bbynsu mace ce mai ziwa bayan sunyi aure ba'asa komaiba dai amma wall peper pink ne. Se kuma d'akin baki da toilet a ciki. A palon manosh kuwa dainingne se kuma d'akinsa da toilet. Gaskya tsarin gidan ya burgeni mu samman idan ka haura sama, palour 2ne a gefenka ga peach ga kuma cream. Manosh ya nuna musu ko ina tare da musu bayani. Abdallah ya dad'e yana addu'a a cikin gidan sannan ya yabawa manosh da irin k'okarin dayayi a wannan gidan nashi,dan base na fad'a. Drinks masu sanyi ya d'auko musu daga frdje,mamaki sukayi lokacin daya bud'e fridje d'in a cike yake da drinks da kuma faro water. Maryam dai taki shan komai,abdallah ne yasha abinshi shida manosh,yace nifa banga d'aki naba,manosh yace d'akinka uana daga gefen flour ata waje,yace yawwa bari naje na duba,manosh yace to muma gamu fitowa. Shuru maryam tayi gashi palourn yad'au sanyi,dan tun shigowarsu ya kunna AC. Tashi yayi daga inda yake zaune ya dawo inda take yace tashi muje ki zauna a palo na kafin mu tafi dan nacewa su marwan sekin fara zama akan kujerun kafin su zauna. Ba musu ta mik'e suka k'arasa a 3seta ya zauna,ita kuwa a 2,yace tashi ki dawo nan,sam tak'i tace a'a nanma na zauna ai,yace pls apple kizo zan mana pic ne anan,amma sam kunya ya hanata tashi,haka ya yashi yace inda take ya zauna batare da jikinsu ya had'uba ya musu pic. Thankyou yace da ita tare da nuna mata pic d'in,murmushi tayi tare da karb'an wayan dan sunyi kyau sosai,yace amma fa kin fini kyau dan haka zanyi deleting,tace a hakan pls ka barshi wlh kama fini kyau,yace to shikenan tare da mik'ewansu a tare. Kallon juna suka tsayayi,take ta kawar da kanta gefe tace gida yayi kyau sosai Allah yasa mu shigo a sa'a Allah kuma ya k'ara arziki ya karemu daga dukkan....hannunsa taji acikin nata yasa ta kasa k'arasawa,shi kuwa yace ameen aunt. Hannunta take k'ok'arin gwacewa daya lura da hakan seya sake mata hannun yace sorry apple haka kawai naji cewa in rik'e hannunki,kanta ta d'ago suna kallon juna atsarge tace muje,murmushi yayi tare da cewa to muje,gaba tayi yana biye da ita a baya,sedaya kashe komai sannan ya fito harta fita waje. Sunanta ya kira aunt,juyowa tayi tare da kallonshi,yace zo muje gida flower naki,da murna taje suka bi gefe sam takasa b'oue farincikinta sebin flower d'in takeyi da fararen hannunta hakwaranta tas a waje shikuwa se pic yake mata batare data saniba. Can kuma ta hango wani guri mai kama da swiming pool,amma kuma taganshi a rufe da wani glass kana iya ganin cikinsa,sosai taji dad'i tare da kallonshi tana murmushi,gwalo yayi mata da harshensa tare da dannan gefen pool d'in seya bud'u. Sam ta kasa boye murnanta tace thankyou so much peach,mirmishi yakeyi tare dajin dadin yadda yaga tana farinci seyaji dad'i sosai har cikin zuciyarshi yace Always my jealousy . Yake ta b'ata rai tare da mik'ewa tayi hanyan komawa gun mota,da sauri harda gudunshi yasha gabanta tare da had'a hannayenshi gu d'aya yace _pardon me apple_, k'itayi zata wuce ta gefenshi se yayi saurin rik'o yatsan hannunta guda 2 yace inyi tsallen kwad'o? D'aga kanta tayi alaman eh,aiba b'ata lokaci ya saki yatsunta yahau yin tsallen kwad'on se dariya takeyi sannan tace ya isa haka shikenan har a yanzu dariyan takeyi,shi kuwa se kallonta yakeyi yana mirmushi. Daidai nan abdallah yazo yace gaskya d'akina yayi kyau sosai nagode,manosh yace bakomai d'an aunty kafi haka aguna. Abdalla yace naga swiming pool amma na ganshi a rufe kuma na kasa bud'ewa,manosh yace na rufene saboda bana so kowa ya fara shiga se auntynka,amma muje in bud'e maka tunda ta tab'a ruwa,murmushi abdallah yayi suka tafi acan manosh yayi ta mishi pic sannan sukayi tare,maryam taga shuru yasa ta lek'asu taga se selfi sukeyi,abdallah yace auntyna kizo muyi tare,amma sam tak'i,dole abdallah yasa taje manosh yanata d'aukansu sannan suka kama hanyan komawa girei bayan sayayyan da sukayi a shop. Godiya sosai abdallah yayi dan kayayyaki masu tsada manosh ya sake saya mishi. Maryam ma ta tayashi godiyan sannan sukayi sallama ya tafi ita kuwa taje tanata baiwa maman lbrn gidan manosh. Dad'i sosai mamaji tare dayin addu'a. Washe gari alhamis su miher harsun fara shirye shiryen biki lubna ce mai tayata. Su rash sukace sam su dole ayi biki amma maryam tace babu abunda zatayi. Bayan isha abdallah yazo sunata hira da maryam yace wlh aunty kaina ciwo yake min kid'an kamamin mana,nan ta kama mishi kan da addu'a har mama tana cewa toga paracetamol d'an aunty ka daure kasha,yace a'a kamun da aunty taminma naji dad'i seda safe,aunty tace to Allah ya sauwaka yace ameen. Da asuba yau jumma'a bayan an idar da sallan asuba,abdallah yayita karatun qur'ani mai girma da daddad'an muryansa mai k'arawa mai sauraro imani. Yakai 1hr yanayi sannan akayi wa'azi aka watse,gidansu maryam ya shigo suka gaisa tace kaji karatunka na yanzu a wayata nayi recording,mirmushi yayi yace kai aunty keda ma naki yafi nawa shine kiketa tara muryana a wayarki,tace eh har gobe kiran sallanka yana cikin wayan manosh,dariya yayi yace Allah yabarmin ke auntyna,tace ameen nima Allah yabar min kai,babane ya shigo yace abdallah ya jikin dai,yace ai naji sauk'i baba,baba yace Allah ya kara lfy,yace ameen. Seyace aunty naji su aunty rashida sunce zasuyi biki sosai ina fata dai banda ke ko? Tace eh bandanikam walima kawai su captain zasuyi,yace kin kyauta aunty irin wannan karatun zanyi a wannan ranan Allah ya kaimu lokacin kawai aunty,tace ameen sannan ya fita. 8:40am mama tazo d'akin maryam tana cewa maryam yau kuma kece mai baccin safe,toki tashi maryam *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* da sauri ta farka tace mama lfy,mama tace maryam yau kuma munyi rashin ABDALLAH seta fashe da kuka tare da rik'e maryam gam. Maganan kamar a mafarki tajishi,amma yadda taga mamanta ta riketa ta kuka tasan cewa ba mafarkibane gaskyane, *innalillahi wainna ilaihirraji'un*itama take furtawa tare da kallon mamanta tace wani abdallan kenan mama kina nufin abdallah nah? Da sauri ta mik'e bata jira amsar mamaba ta zurma himar nata tayi waje. Jama'an data gani a wajene tun daga bakin masallaci har k'ofar gidansu abdallah yasa ta k'ara fashewa da kuka tana wuce mutane batare datasan cewa wandon sleeping dress bane a jikinta,harta k'araso k'ofar gidan dakyar ta samu hanya ta shige ciki. Kukan rash ta fara jiyowa dana mamansu,rash ta mik'e ta rungumeta tana cewa shikenan abdalla yatafi yabarmu maryam innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas