Sashe 13
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
pecking d'in yatsan nashi yana mata murmushi tare da cewa ya jikin,tace naji sauk'i sosai wlh,manosh yace alhamdulillah zuwa gobe za'a sallameku insha Allah nizanyi tfy kuma zankai 1week kafin in dawo su dad zasuje gun baba dan asa mana rana kinji? Sam maryam bataso tfyan manosh ba haka kurun tad'an canja fiska,shi kanshi ya lura da hakan seya sauya muryanshi yace "apple r u aokey?" Tace yes am fine ina zakaje? Yace zanje kaduna ne,karki damu kinji zan dawo insha Allah addu'arki nake buk'ata apple,kallonshi takeyi tare da tausayin kanta tace Allah ya kare min kai,yace ameen suna kallon junansu ciki so sannan tayi saurin kawar da kanta gefe tana kallon flower daya kawo mata,manosh bazai iya jurewaba dan haka ya mik'e tare da cewa nizan tafi apple ga wannan,ya ajiye mata kud'i a gefen gadonta sannan ya nufi kofar fita. Har yakai gun k'ofan kanta na kallon flowern,seya juyo yana kallonta sam taqi kallonsa har ya gama kallonta sannan yaja k'ofa ya fita harzai kulle kenan seta d'aga kanta suka had'a ido cikin tausayin junansu yace _i love you so much apple_ _tace i love you too manosh_ Harda d'an kwalla a idonta sannan yaja kofar da sauri ya rufe,ita kuwa hawayene suka zubo mata kona menen oho.... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated to mom sudais* *(awans 35-36 Hankalin maman maryam ya kasa kwanciya,seta kira baban maryam a waya tana tambayanshi ko maryam ta iso? Baba yace a'a bata isoba,hankalinta ya sake tashi tace malam yaci ace ta iso ai,shi kanshi hankalinsa ba'a kwance yakeba,amma seyayita kwantar mata da hankali da daddad'an kalamai yana cewa kinsan fa maryam da taimako da kuma tausayi,zaiyu wani abinne ya tsaida ita a hanya amma bari nabi sawunta. Mahaifin maryam ya rufe shop nashi yabi hanya ai ko seyaga almajirai sunata d'iban abinci a k'asa kuma ya tabbatar da cewa wannan kulan abincinshine. Wayansa ya d'auka ya kira matarshi ya tambayeta cewa me kika dafa minne yau,tace shinkafa da miyace mai had'e da wake,katse wayan yayi ya kama fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tare da duduba guraren kozai hango maryam amma sam se *rivom* nata daya hango wanda shida kanshi ya sayo matashi. Hankalinshi ya tashi sosai,ya kira number'n maryam yanata ringing amma ba'a d'aukaba har kusan sau biyar. Haka ya wuce gida a rud'e inda ya had'u da yah ibrahim da abokanshi suka gaisheshi ya amsa amma suna ganinshi sunan akwai abinda ke faruwa,ibrahim yace baba lfy kuwa,yace lfy lau ka biyoni gida. Haka suka juya abokanshi suna tsaye daga waje su kuwa suka wuce gida. Mama tana jin sallama ta fito tare da cewa malam lfy,nan ibrahim ya gaisheta sannan baba ya gaya musu duk abinda ya gani a hanya sannan yayita kiran number'n maryam shuru. Addu'a suketayi dukkansu tare da tunanin to ina maryam take? Ibrahim ya kira rashida da sameera a waya suka ce mishi sam maryam bata zoba,ya sake kiran zahida da amina suma sukace bata zoba,nan ya wuce gidan hajiya iya nanma batanan,koda hajiya iya taji lbrn hankalinta a tashe harda kukanta dan yadda take son maryam a ranta. Nan tayi lullub'i ta wuce gidansu maryam inda mahaifiyarta taketa addu'a tare da kwalla a idonta. Duk wanda yaji yasan ba lfy bane domin maryam bata tab'a yin hakaba,ga kuma rivom da mahaifinta ya gani agun yasan lallai akwai matsala sosai. Bayan anyi sallan azahar ne mahaifin maryam yayi bayani a masallahi akan a tayasu da addu'a. Duk wanda yaji seyayi addu'a dan base na gaya muku daliliba. Cikin k'ank'anin lokaci magana ya baza ko ina a garin girei. Ibrahim ya kira manosh a waya amma yanata ringing bai d'agaba,hakan yasa ya kira number'n marwan bugu d'aya ya d'auka bayan sun gaisane yake ce mishi manosh fa,domin yayita kiranshi amma bai d'aukaba,marwan yace wlh ni ina office ne maybe baya kusane. Ibrahim yace ok dama wlh maryam ce aketa nema tun d'azu taje kaiwa mahaifinta abinci har yanzu shuru babu ita babu lbr,ahanya akaga kulan abincin a zubar a k'asa sannan an tsinci rivom d'inta har haryanzu babu wani lbr. *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* marwan yaketa nanatawa tare da mik'ewa yayi gun manajer'nsu bayan sunyi magana marwan ya d'auki motarsa se gida. Miher ya gani a tsakar gida zata fita,nan dai suka gaisa yace ina prince,tace yana bacci bayajin dad'i kanshi yana ciwo. Marwan yace ok sannan ya wuce d'akin miher tanata binshi da kallo dayya taganshi tasan ba lfy,haka kawai taji ta fasa tfyan dan tana so taji menene da sauri tabi bayan marwan ta lab'e daga bakin kofa inda taji marwan yana cewa "dude" "dude" ahankali manosh ya bud'e ido yana mamakin ganin marwan a wannan lokacin. Marwan yace sorry na tashe ya jikin,yace alhamdulillah lfy? Marwan yace ka kashe wayar kane,manosh yace no a silent nasa dan ind'anyi bacci wlh ya akayi,marwan yace "dude" akwai matsala baga'a apple ba tun 11:40am yanzu gashi har 3:20pm,kuma duk inda ake tunanin tana zuwa anje bata nan sannan........da sauri manosh ya mik'e tare da d'aukan wayanshi yaga miss call din baban maryam dana ibrahim dadai wasu daban,number'n apple ya kira yanata ringing amma sam bata d'agawa. Kamar zaiyi kuka ya sake kiran wayan yanata cewa "pls apple pick d call okey" where are you apple,wurgi yayi da wayan seda screen d'inshi ya pashe ya shige toilet da wuri,shi kuwa marwan ya d'auko wayan amma ina ba'a ganin komai taci screen. Manosh ya fito ya shirya suka fita ko mum nashi bai sallamaba,daya ga miher yace miher maryam ta kiraki?miher da jikinta yayi,sanyi tace a'a,yace kiyita kiran numbern ta sannan ki gayawa mum cewa ba'aga maryamba nina fita. Hawaye miher ta fara dan yadda taga bro nata ya hargitse a lokaci d'aya. Basu wuce ko inaba se girei,inda suka isa har parlon mahaifinta yana zaune da mutanen unguwa,sukayi sallama tare da gaisuwa sannan manosh ya farayiwa baba tambayoyi kamar ba surukinsaba,shi kanshi baba yasan manosh a rikice yake,manosh yana gama jin komai ya musu sallama suka wuce gurin yayita dube dube amma baiga komaima. Abokinsa *faruq* ya kira wanda yake aiki a *mtn office* yace faruq matar da zaura an d'auketa wayanta a kunne yake inaso kabin min line nata pls insan a ina take da sauri dan Allah. Da sauri faruq ya fara neman line na maryam amma baiga komaiba da tana inda babu netwrk,nan ya sake duba kira na k'arshe daya shiga wayarta ba'a d'aukaba yaga lokacin tana *gurore* sannan yanzu baya iya ganin inda suke. Faruq ya kira manosh yace captain d'azu kaine ka kirata last kuma ya shiga lokacin tana gurore. "Whats! Gurore fa kace faruq? Faruq yace tabbas captain karka damu zanci gaba dabin line d'in inga suna inda ba netwrk ne. Katse wayan manosh yayi yace ina tausaya musu wlh tunban kamasu kowaye yayi miki wannan aikin "he will pay for it wlh" dan bazan barshiba. Marwan yace muje gida mu shirya manosh,manosh yace no karka damu ka koma kawai yanzu motarmu zaizo zamu bi bayansu,marwan yace ok "dude but pls becarefull,daidai nan motan sojojin ya iso wani ya fito daga gaba manosh ya shiga sannan shi ya shiga baya suka tafi,sega majid yazo suka wuce girei gun iyayen maryam,koda marwan ya gaya musu inda maryam take mamaki sosai sukayi,mahaifiyarta kuwa kuka sosai takeyi,makota sunata bata hakuri. Abdallah yana zaune a masallaci tare da samari da sauran yara anata karatun qur'an amma abdallah hawayene kawai yakebin fiskanshi. K'awayentama duk sunzo sunata kuka Manosh ya kira muhsin yace pls zan tura maka pic na apple kai gidan TV da radio dake adamawa dukka duk wanda yaba da wani bayani akwai babban kyauta ageshi,mihsin yace ok "dude" pls ka kwantar da hankalinka insha Allah za'a sameta cikin k'oshin lfy,manosh yace Allah ya amshi addu'anmu tnx "dude" sannan ya katse wayan. Maryam ta fara bud'e idanunta tare dayin addu'a harta gama bud'esu dukka tana k'arewa d'akin da take kallo. Katiface kawai a d'akin da wani zanin gado se tsami yakeyi ga akwati da tarin taba wiwi dasu totolin sune kawai a wannan d'akin. Nan danan taji gabanta ya fad'i tanata addu'a tare da mik'ewa ta murd'a kofan amma setaji a kulle yake,nan ta tuna da wayanta datasashi cikin pants nata tun lokacin da suka bige mata abincin babanta. Da sauri tasa hannunta akan pants d'in cikin ikon Allah taji har yanzu wayan yana jikinta,hamdala tayiwa Allah sannan ta ciroshi da wuri dama a silent yake,kodata duba missed calls babu adadi a cikin,da sauri ta kashe wayan gabad'aya dan ganin 7:00pm ne ko sallan azahar batayiba. Kofan data gani ta bud'e taga toilet ne amma babu kyan gani sam a cike yake da k'azanta,hancinta ta d'aure da d'ankwalinta ta shiga da yake akwai ruwa ga kuma morning fresh da izal nan da nan ta wanke shi tas sannan tayi alwala wayanta yana cikin pants nata ta shinfid'a d'ankwalinta tayita biyan sallolinta. Tana cikin yin sallanne se taji ana bud'e kofan tare da shigowa. Daga jin muryanshi kasan d'an giyane,yana cewa daga zuwanki har kin fara mana kashi ko kashi kin bud'emu da wari kota ina,koda yake shinkafa da wake kuka dafa a gidanku yau shiyasa,ga abinci nan idan kin gama sallan sekici,bayan ya ajiyene ya d'auki kwalin sigari sannan ya tafi. Bayan maryam ta idar da sallolintane tare,dayin addu'in neman tsari sannan ta dubi abincin daga gani a resturant aka sayo,amma sam bata ciba seta tashi tasa sakatan d'adkin ta ciki sannan tashiga toilet ta kunna wayanta tare da kiran number'n mahaifinta bai d'aukaba dan yana tlband'aki,dan haka ta sake kiran mahaifiyarta bugu d'aya ta d'auka tare da cewa maryam,maryam tana magana a hankali tace na'am mama sannan,ta fara kuka tana cewa mama ya kuke ku kwantar da hankalinku ina halin lfy amma bansan a ina nakeba...bata k'arasaba taga call d'in manosh,tace mama zan sake kiranki bari inyi magana da manosh,to maryam Allah ya kareki zan sake kiranki bayan kunyi wayan kiyi k'ok'ari kozaki gane inda kike dan azo a taimaka miki su waye suka d'aukeki? Maryam tace wlh mama har yanzu bansan komaiba ina kullene a wani d'aki banga kowaba har yanzu. *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*suketa nanatawa ita da mamanta suna hawaye amma ita maryam daurewa takeyi kar ajita tana waya azo a karb'e. Banyan maryam sun gama