← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 45

Sashe 4

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi dariya yace kaida ka sani kuma,marwan yace aaah "congrats dude" kadai samomin friend nata ko,dariya sukayi dayake suna iya jiyo abinda marwan yake cewa,muhsin yace muma da mukaje bamu samuba bare kuma kai,dariya marwan yayi yace to ai abin rabone,muh'd yace sosai to har yanzu dai rabon namu bai rantseba tukunna kaga majid dayake d'an iskane se dariya yake mana waishi ai yana da miher,marwan yace rabu dashi ba laifinshibane captain ne ya b'atashi ai tunda yace ya bashi miher tun da wuri,any way se kun iso ya banji muhsin bane,muhsin yace abokina aure kawai nakeso nima shiyasa ka jini silent,dariya sukeyi sannan marwan ya katse wayar yana dariya. Mahaifin maryam seda ya rabawa makwabta abin alkhairin dasu manosh suka kai,sannan ya rabawa yaran da suka shiga da kayan sannan ya koma shop d'inna. "Maryam tace sannu baba,yace sannu 'yar baba bak'in da sukazone yasa banzo da wuriba sunzo neman izinine akanki. Shuru maryam tayi dan kunya daya kamata tace baba zan iya tfy gida,yace eh jeki,sannan ta bashi kud'in cinikin seta tafi tana mai jin kunya. Koda ta is a gida mahaifiyarta ta gaya mata komai tare da alkhairin da suka kawo. Murmushi kawai tayi tana bin kayan da kallo,wayar tace ta soma ringing,koda ta duba number'n manosh ne seta tashi ta shige d'akinta tare da d'aukan wayan tace assalamu alaikum,wa'alaikumus salam AUNT,murmushi tayi dan tasan shine setace na'am kun isa lfy,yace lfy lau ya muka barki,tace lfy mun godefa Allah ya saka da alkhairi,yace amin,tace inasu majid,yace duk sun wuce gurin aiki dama akan aikinsu na tattarosu,tace eyyah,yace bazaki tambayeni sunanaba,murmushi tayi tace to ina sauraro,yace a'a ai baki tambayeniba,shuru tayi tana murmushi a hankali,manosh ya sake kiran sunanta AUNT,tace na'am ina sauraon sunanka,yace sunana maryam,dariya tayi wanda shima ya sashi dariyan sannan yace eh mana,tace maryam ai sunan mata ne bana mazaba,yace sunana muh'd manosh mu biyune agun iyayenmu nida k'anwata miher,sannan ni SOJA ne amma friends d'ina suna kirana da prince wannan shine lbrna a tak'aice. Dariya sosai maryam tayi dan yadda yayi bayaninshi da sauri sauri tace masha Allah yanzu kai d'in soja ne,yace banyi kama da sojaba ko,tace gaskya kam,yayi murmushi yace to ai k'aramin sojane ni ba babba ba shiyasa,murmushi tayi kawai batace komaiba,yace aunt ya kikayi shuru kona dameki ne,tace a'a bakomai,yace to kefa,tace sunana maruam ni kad'aice agun iyayena na gama secondary skul muna jiran result,manosh yace ok to Allah yasa muga alkhairi,tace ameen,yace suwaye friends naki na kusa, tace rashida muh'd,amina babale,samira jauro da zahida abba,ya e duk a girei suke,tace rashida da sameera suna gireizahida tana jimeta,amina kuma tana yola. Yace ok kuma ku 5 kenan,tace eh,yace to duk ki gaishe min dasu pls,tace zasuji nagode,yace ok byee,tace byee tare da katse wayan ta sauke wani ajiyar zuciya tana murmushi. Miher taji dai bro manosh yana waya kuma tasan da mace yakeyi,abin ya dameta sosai seta kira LUBNA a awaya tace k'awata gaskya kina sanya dewa kuma wlh na hango matsala,lubna tace kamar ya matsala,miher tace ina tunanin bro manosh ya fad'a soyayya da wata dan kamar naji suna waya ya kamata kiyi mishi magana yanzu gaskya kar asamu matsala. Hankalin lubna ya tashi tace da gaske kikeyi miher,miher tace wlh kuwa,lubna tace pls miher ki tambayi majid tunda saurayinkine pls kinsan babu yadda zanyi in tuntub'i bro marwqn da irin wannan zancen amma tunda ke budurwan majid ne pls miher,miher tace bakomai zan tambayeshi amma dukda haka "you have to do somethin friend" lubna tace sosai ma kuwa zanyi nagode byee. Bayan sun gama wayane lubna ta ciza baki tace ina wlh bazai tab'a yuwaba,duk wanda tayi k'ok'arin shiga tsakanina da manosh wlh sena d'auki mummunan mataki a kanta ko 'yar gidan uban wayece ita. Yaune manosh zai tafi abuja yana sanye da kakin sojojinshi yayi matuk'ar kyau ya fito da 'ayar k'aramar kit d'inshi a hannu ga kuma bindiga a aljihunsa yace mum zan wuce a mana addu'a,tace to Allah ya kare ka kula da ibada sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake,miher da take gefe tace mum kullum sekin gaya mishi haka aiya zauna a kanshi,tace to ai addu'ace kuma d'an adam azijine,manosh yace amin mum rabu da ita yarantace,miher tace wlh bro niba yarinya bace "am a big gal"dariya sukayi suka rakoshi har waje driver yaja suka tafi air port. A hanyane ya kira maryam yace aunt kin tashi lfy,tace lfy lau ya mutanen gida,yace lfyansu lau yanzu na barosu ina hanya zan tafi abuja sannan zanyi 1week kafin in dawo karkiga shuru banzoba,tace ok Allah ya kiyaye hanya Allah kuma ya bada sa'an tfy,yace ameen aunt thankyou so much,tace wlcum,yace ki kulamin da kanki kinji,tace to nagode,yace ok byee sannan ya katse wayar. Ita kuwa maryam seta tsinci kanta dason sake ganinshi dan ad'an lokaci kad'an da had'uwansu amma se taji tana sonshi sosai a ranta,dan tunda take babu wanda ya tab'a zuwa yace yana sonta sedai taji yara suna cewa aunty ai wane yace mana kece matarshi ko kuma wane yace mana ke zai aura, amma babu wanda ya tab'a sallama a gidansu se manosh. Lubna ce kwance a d'akinta daya sha kayan duniya tana tambayan miher a waya toya ake cikine,miher tace wlh da gaskene amma nima majid yak'i gayamin mum ne na tambaya take cemin wai ai har sunje neman izini a girei yarinyar take. Ran lubna se tafasa yakeyi tace shikenan nagode,miher tace bro manosh yayi tfy yau kuma zai jima dan haka ki shirya yana dawowa sekizo,tace insha Allah miher nagode sannan sukayi sallama. Hankalin lubna in yayi dubu ya tashi setace wlh dolene in fara shige shige gun malamai dan samo kan manosh kota halin k'ak'a koma wacece wannan yarinyar zan ganta ai kuma zanga dame tafini,kyaune ko gashi ko hasken fata ko kuma dukiya koma dai menene zakici ubanki wlh tunda kika shiga tsakanina da masoyina. Manosh yana isa ya kira mum nashi sannan ya kira maryam,yace aunt na iso lfy,kunya taji sosai dan bata kirashiba tace to Alhamdulillah,yace baki damu danibako aunt,gashi ko kirana bakiyiba,tace am sorry bahaka bane,yace to menene,tace kayi hakuri zan gyara,dad'i yaji sosai yace toba komai I LUV U,kunya taji tayi shuru tana jinsa,ya kira sunan aunt,tace na'am,yace bakiji abinda nace bane,tace "me too" tare da katse wayan dan kunya dataji, shi kuwa dariya yakeyi yanaji sonta na k'aruwa a ransa... [7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNT'YN YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd 11-12 Auntyn yarane take koya musu karatu a cikin gidansu dan har black bord babanta ya mata dan koyar da yara,gidan nasu d'an daidaine ba wani gidan masu hali bane,amma dai koda yaushe gidan tass yake. Tsakar gidan flour ne na silinti se'a shinfid'a katuwar taburma ana karatu. Marwan ne a hanya zuwa girei duba abokinsa da bayaida lfy,ya kira manosh a waya amma yayita ringing bai d'aukaba. Bayan yaje sund'an tab'a hirane se yayi mishi sallama ya kama hanyan koma,kiran salla yaji muryan k'aramin yaro nan danan imani ya k'ara ratsa marwan yace kai bari dai na k'arasa kawai nayi la'asar tunda an kira. Har gun masallacin ya isa ya paka motarshi ta gefe seya hango wani yara,ya k'ara gun masallacin yayimasa sallama yaron ya amsa tare da cewa salla zakayi,marwan yace eh wanene ya kira sallah yanzu,yaron yace nine,marwan yace masha Allah amma kana da murya mai dad'i menene sunanka,yace sunana ABDALLAH,marwan yace suna mai dad'i gaskya inaso mu kulla abota dakai,abdallah yace to shikenan ya sunanka,yace marwan,abdallah yace kaima sunanka da dad'i ga buta kayi alwala a nan girei kake,yace a'a ina jimetane,abdallah yace ayyah nikam anan girei nake kagama gidanmu can ba nisa,marwan yace to ashe zan dinga zuwa kana koyamin k'ira'a,dariya abdallah yayi yace sedai kaje gun Auntyn yara ta koya maka itace malamata,yace waye kuma Auntyn yara,abdallah yace itace malamata kokuma ince malamar yaran unguwannan harma dana nesa. Marwan yace bari dai muyi sallah ko semuyi hira,yace to sega yara sun fito daga gidansu maryam mata sun wuce gida maza kuma sun nufi masallaci. Kowannen sallama yayiwa 'yan masallacin sanan suka hauyin alwala,marwan yana ta ganinsu abun ya burgeshi sosai. "Bayan an idar ne marwan yace da abdal muje can muyi hira se in tafi. Bayan sun k'arasane yace ina jinka kagani na mijine kuma babba kanaga auntyn yaran zata koya min karatun, yace a'a kam kayi girma sedai in zaka dinga zuwa masallacinnan daga magrib zuwa isha kullum ana karatu da kuma litattafai masu yawa. Dad'in hirannasu sosai marwan yakeji yace to yaran can da suka fito daga gidancan fa kodai koyarwa ake acan,yace eh auntyn yara ce mai koyarwa bayan azahar zuwa la'asar,biyanta akeyi,abdallah yace a'a fisabilillah dai ai auntyn yara kowa natane kuma kowa ya santa babba da yaro babu wanda zai iya gaya maka halinta don ta cika goma cip cip. Dariya sosai marwan yayi yace matar aurece,abdallah yace a'a budurwace kuma kuma kasan me,marwan yace a'a,abdallah yace auntyn yara macece mai tarin ilimin addini dana boko gata da son mutane sam bata da kyamar d'an adam aduk yadda ta ganshi,kuma tana son taimakon dan adam,gata kyakkyawa sosai amma kuma 'yar karamace. Dariya sosai marwan yayi yace kai abdallah duk ita kad'ai kodai ka kara da nakane,yace wlh da gaske ko inkirata ku gaisa ne,marwan yace a'a kace mata me?abdallah yace ince mata tazo abokina yana so su gaisa,marwan yace zata fito,yace eh zata fito bari inje. Maryam tana sanye da aldoguwar riga jah ta nad'a gyalen akanta tana k'okarin fitowa,se abdallah yayi sallama ta amsa tare da cewa abdalla rashida fa ta shirya kuwa,abdallah yace wlh ban saniba zaku fitane,tace eh zamuje jimeta duba zahida ba lfy,yace to muje dama gunki nazo zaku gaisa da abokina. Mamaki ya kama maryam tace aboki kuma,yace eh,tace to muje se suka fito a tare. Marwan ya zubawa budurwan kallo har suka k'araso tayi mishi sallama ya amsa sannan suka gaisa,tace to abdallah mun gaisa nizan wuce,abdllah yace to ai shima jimeta zaije abokina ka sauketa dan Allah. Marwan yace tobakomai abokina auntyn yara muje,batayi mamakin jin sunata a bakin marwanba,se tace a'a wlh da wata k'awata zamu tafi yanzuma gidansu zanbi kafin mu wuce,abdallah yace abokina yayatace bari naje na kirata yana juyawa sema ga rashidan tahowa,yace kama ganta,murmushi maryam tayi tace daga yin aboki se kuma a d'aura
Chapter 4 · 0% Book details