Sashe 38
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suzo akwai magana kamar yadda hajiya iya ta sanar dashi. Hakama d'an nata wato mahaifin marwan harma da dad d'in manosh dayake aminaine duk aka taru agidansu *auntyn' yara* inda lubna take zaune kusada aunty tana kallon hajiya khadija da kuma hajiya iya dan taga ta ina zasu fara. Mum d'in marwan dai kanta a sunkuye ta kasa sakewa sam dan batasan mezai biyo bayaba,duk dai ana zaune a palon baban maryam kowa kuma ya damu yasan dalilin wannan taron. Sallaman muhsin da majid da kuma muhammad ne ya katse su,bayan sun samu guri sun zauna ne aka fara gaishe gaishe,koda muhsin yace aunty ina wuni,seta amsa cikin muryan kuka saboda ta tuno da mijinta,kowa kuma yasan dalilin hakan,lubna ce tayita rarrashinta sannan hajiya iya ta d'ago kanta idonta jajur,kowa ya d'auka akan b'atan manosh ne zatayi magana,inbanda lubna datasan dalilin taron. Hajiya ta fara magana kamar hakaaaaaa... [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas 83-84 "Bakomai yasa na had'a wannan taroba sedan wata magana mai girma ko kuma ince na taramu ananne saboda in tonawa kaina asiri akan abinda na aika". Hawayene yasa hajiya iya tsayawa tana mai goge kwalla,inda d'an nata wato mahaifin narwan ya shiga damuwa. Hajiya iya tacigaba da magana cikin muryan kuka ta kwashe lbr tun daga farko har k'arshe kamar yadda mahaifiyar arwan ta bashi lbr dalla-dalla. Tun bata k'arasaba kowa ya kama fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un",hajiya iya tace dan Allah kuyi hakuri karkuce komai harsenaga. Taci gaba da cewa nasan zakuji wani iri kilama bazaku yaddaba sakamakon yadda na muku bayanin amma wannan shine gaskyan lamari. Dan Allah kugafarceni kuyafemin wannan laifi mai girma dana aikatashi cikin jahilci da kuma sonkai irin nawa..... Tunda hajiya iya ta fara magana idon aunry yake zubar da kwalla kamar pampo har kuma yanzu,nanne take tunanin kodai mafarki takeyine,amma sam ba mafarkibane wannan gaskyane,amma kuma anya abinda hajiya iya ta fad'a gaskyane? Lubna ce ta katse maryam da maganan zuci da takeyi,tace aunty kida shakku akan abinda ta fad'a domin babu k'arya ko kad'an aciki fase gaskya zallah. Shine dalilin dayasa naje gidanta nake gaya mata maganganu ranan,sakamakon bazan iya gayawa kowa abinda mahaifiyata da kuma kakata suka aikataba shiyasa na rik'e abun a raina dan banaso sunansu ya b'aci dukda dai nagane gaskyan amma hajiya khadija ta rik'e tamkar 'yar cikinta hakan yasa nayi shuru ban gayawa kowaba,sannan wannan shine dalilin dayasa bro marwan ya k'irk'iro da tfyarsa wanda ko aminansa basu san dalilin wannan tfyanba saboda kunyan abinda familynsa suka aikata baisan ta yadda zai fiskanci mutaneba.......Aunty ce tasa hannunta akan bakin lubna tana kwallah sosai idanunta sunyi jah,ta kalli hajiya khadija da hajiya iya sannan tace hajiya shin dagaskene...? Atare suka d'aga kai ma'ana ehh gaskyace" hajiya khadija ta k'ara da cewa maryam nasan bamu cancanci yafiyaba amma dan Allah kuyi hakuri wannan shine dalilin dayasa muke k'aunarki sosai aranmu nida hajiya iya,shine dalilin dayasa bamaso ace yau munganki cikin kinci dan musan bamu kyauta mikiba dan Allah alhaji kuyi hakuri mun yadda da duk wani hukunci da zaku yanke mana amma fatanmu shine kusan gaskya akan cewa lubna 'yar cikunkuce k'anwa ga maryam..... Su baba dai kasa cewa komai sukayi hakama su dad d'in manosh. Shi kuwa dad d'in marwan jiyake kamar ya tsaga k'asa ya shiga dan kunyan abinda mahaifiyarsa da kuma matarsa suka aikata,ga kuma 'ya'yan cikinsa su majid,"oooh" wannan abin kunya dame yayi kama? "Maryam tanakuka ta kalli iyayenta inda kansu yake sunkuye dan basusan me zasuceba,musamman baba,yana ganin girman hajiya iya sosai,bazai iya yin komai akaiba illa yafiya. Maryam tagane komai akan halin da iyayenta suka shiga,hakan yasa ta matso kusa da iyayenta inda kowa yake binta da kallo,tace baba mama,nidai har abada hawaye sosai takeyi,inda hajiya iya taji zuciyarta na bugawa sosai,maryam tace nayafe musu har abada baba,kuma ina sake baku hakuri akan kuyafe musu,lallai marwan yayimin wani magana kafin ya tafi ya kuma nemi yafiyanmu tun kafin inji wannan lbrn,seyanzune nagane meyakenufin da wannan kalaman nashi,sannan yanzu haka bamu san w ani hali suke cikiba baba,dan lokacin da marwan yabar k'ofar gidannan gabad'aya baya cikin hayyacinsa,dan Allah baba kayafesu kaida mama domin ceto rayuwar marwan da rashida danko numbernsu baya shiga,seyanzu na gano dalilin ciwon marwan baba dan Allah baba ka yafe musu..... tana kaiwa nan ta mik'e zuwa d'akinsu tana kuka ita kuwa lubna kallonsu takeyi cikin tausayawa,tace baba kayi hakuri a yafe musu kodon rik'eni dasuka babu kyama babu wulakantawa se d'inbin soyayya da suka nuna min fiye da d'ansu bro marwan,ta sake juyawa ta kalli dad d'in marwan tace daddy har gobe bazan dena kiranka da sunan daddyba,haka kuma kema mummy ina k'aunarku har gobe,nagodewa Allah daya had'ani da 'yar'uwata dukda kun rabamu,kuma cikin k'ankain lokaci nayi koyi da halayenta nagari,daddy samun 'yar'uwa kamar aunty abin alfaharine agareni. Yau zan gayawa kowa abinda baku saniba,daddy nayiwa aunty mugunta har halakata naso nayi sakamakon son zuciya irin na hajiya iya,lokacin da aka nei aunty aka rasa nice nasa akayi kidnaping nata har zuwa jejin yankari,amma cikin ikon Allah aunty ta dawo gida lfy,kuma ita tasan cewa nice nasa a saceta saboda kar ayi aurensu da bro manosh dan k'aunarshi danakeyi acikin raina. Amma hakan baiyuba kuma tak'ita gayawa kowa abinda ya faru harda iyayenta ta b'oye musu saboda bata so ta b'ata tsakanin iyayenu da kuma aminantakar dake tsakanin bro manosh da bro marwan,haka kuma wanda nasa aikin ya yaudareni ya b'ata min rayuwata ta hanyar yimin fyd'e wanda duk alhakin auntyne ya kamani,shiyasa ban gayawa kowaba se ita auntyn,saboda ina tsoron fad'a muku agida daddy,sannan aunty itace kawai wanda ta fad'o min araina wannan lokacin,bayan na kirata nagaya mata komaine,sam batasa komai a rantaba tazo har inda na mata kwatance itata staftaceni ta rufamin asiri ta hanyar had'i aure da yah ibrahim dan tasan zai rufamin asiri zai kuma zauna dani zuciya d'aya..... Lubna ta tsaya anan tana shehshek'an kuka inda hajiya khadima taketana kai har kusan duk wanda yake palon seda yayi kwalla dajin lbrn da lubna take bayarwa. " lubna tace wannan sirri dana gaya muku yau babu wanda yasan dashi dagani se aunty,koshi yah ibrahim d'in baisan komai akan sace auntyba,amma dai yasan abinda saddam yamin ya kuma amince ya aureni. Nabaku lbrn nanne badan komaiba sedan innuwa hajiya iya da mummy cewa Allah yasa mana k'aunar junanmu tunba yauba nida aunty,sedai shaid'an yayi tasiri akaina har nake neman halakata dan soyayya,amma duk kukuka janyo hakan,dabaku rabamuba da tare zamu tashi inji jina kusa dani...kin cuceni hajiya kun tarwatsa min rayutawa nidai bazan tab'a yafewaba wlh.. mama ce ta kamota tana rufe mata baki tareda goge kwallan idanunta tace lubna ya isa haka tashi kije gun 'yar'uwanki kinji? Bamusu ta mik'e ta fita nata kuka,su yah ibrahim ma fita waje sukayi dukkansu 4 sukayi zugum a waje babu wanda ya iya cewa komai acikinsu.... "Jirginsu marwan ya sauka a abuja, inda suka sauka a hilton. Tun da marwan ya fita bai dawoba rashida ta shiga damuwa gashi wayarsu duk ya karb'e ya cire sim. Saukowa tayi dama da kud'i a hannunta sosai,taje ta sayo k'aramin waya da sabon sim mma tama rasa waye zata kira,hakan yasa tafara kuka ko abinci bataciba. Marwan kuwa tunda ya fita da motan wani abokinsa da yake aiki acan din yaketa tfy,baima san ina yake zuwa. Gabad'aya hanklinsa atashe yake,halinda ake ciki yanzu agida yola,sannan ko wani hukunci dad nashi zai yanke akan mum oho,yanzu abokansa sunsan komai,gashi babu lbrn aminsa dazai iya gayawa damuwarsa wato manosh. Kuka yakeyi sosai kamar k'aramin yaro,baya ko kallon gabanshi hakan yasa wata mota k'ok'arin kaucewa marwan amma sam yagagara saboda yadda marwan yake sake dososhi,se alokacin hankalin marwan ya dawo jikinsa ya fara fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ya kauce da sauri tare da tsyawa a gefe shima wancan din ya tsaya yana zagin marwan,shi kuwa se hakuri yakebashi amma sam se faman masifa yakeyiwa marwan,dak'ar dai ya hakura ya tafi. Shi kuwa marwan zama yayi acikin mota yana zubda kwalla..... [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas 85-86 "dad d'in marwan yakasa cewa komai sabida bayida abin fad'a akan mahaifiyarsa". Mahaifin manosh ne yacewa mahaifin maryam dan Allah alhaji kuyi hakuri da abunda muka aikata muku,dukda dai mahaifiyarmuce dukkanmu tunda ta haifemu" amma tabbas sunyi kuskure mafi girma arayuwa,babu da wani abu da zamu iyace cewa sedai muyita baku hakuri daku yafemana sannan 'yarku dama tadawo hannunku tunda tana auren d'anka ibrahim. Za'a iya sanar da dangi amma ataimaka ab'oyewa mutanen waje. Mahaifin maryam yace bakomai alhaji wannan yawuce,sedai fatan Allah yasa mukiyaye gaba,Allah yasa wannan ya,zama darasi akan wasu,saboda munbarwa Allah komai wlh nafe duniya da lahira,amma fa idan da wanine aka mishi haka tofa bazai yafeba,sannan dole se hukima ta shiga shicin zance wanda hakan zai iya janyo wata babban rigima tsakanin familys harma yakai gidan yari. Amma alhamdulillah yazo gidan sauki tunda duk gashi Allah ya had'a zuri'a a tsakaninmu" bazamu iya cewa komaiba se Allah ya kare nagaba,sannan nagode da kulamin da yarinyata da kukayi,nagane manufar hajiya iya da kuma dalilinta. Sedai ba haka ya kama a bullowa lamarinba,ita a tunaninta lokacin ina fama da talauci ta yadda bazan iya rik'e koda yarinya d'ayaba,se kuma gashi Allah yabani kyauta biyu a lokaci guda,tofa musani Allah baya d'aurawa bawa abinda bazai iyaba,tunda shiyabani su toshizai bani hanyar da zan renosu,alokacin bani dashi,yanzu kuma ina iya rike mutanen daba jininabama,kamar yadda kuka rikemin lubna. Bakomai hajiya Allah ya yafemu gabad'aya. Har k'asa hajiya iya ta sauko tana kuka tare dayin godiya,hakama mahaifiyar maryam tace tayafe bakomai. Nanne dad d'in manosh yayi magana kansan a sunkuye dan kunya,yace mungode sosai alhaji Allah yabar zumunci,wani lokacin mata basu da tunani,duk abinda zuciyarsu ta rayamusu shi kawai sukebi tabare dasunyi shawara da kwakwalwarsuba,aduk lokacin da zuciya ya raya maka abu maikyau ko mara kyau tofa ana so mutum yayi shawara da kwakwalwarsa domin zuciya zata kaika ta baroka,yanzu kai dakayi hakuri wlh inda wanine bazai hakura,kuma kaduba abinda lubna tayiwa maryam,da maryam ta fad'a awannan lokacin toda abu ya lalace tun daga wannan lokacin se daga baya kuma za'aji kunya,kuma dukkune sanadin faruwar hakan. Hajiya da girmanki amma ki aikata irin wannan abu haka babu dad'inji,sannan kuka b'oyemin akan tsintota akayi wannan wani irin tunanine haka?