← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 45

Sashe 2

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sukaita hira nada'an wani lokaci sannan suka fito kowanne ya shiga motarsa ya tafi. Miher tace bro manosh k'awata tana sonyin magana da kai amma kuma idan kun had'u seta kasa saboda kunya. Manosh yace wata k'awarkin kenan,tace LUBNA nama bro kaima kasan banida da k'awar data kaita duk duniya,manosh yace to to ai bata cika maceba kenan tunda tana tsoron na miji,miher tace bafa tsoro takejiba kunyane da kuma tunanin disgin da zaka mata,manosh yayi murmushi tare dajan hancin miher yace wani irin disgi kuma luvlyn sis,tace bro SONKA fa takeyi wlh amma takasa gaya maka nace ta bari in sanar dakai amma tak'i tace wai ita zata sanar dakai kuma wlh bazata iyaba pls bro ka amin....shiii sis karki k'arasa pls kedai ki bari tunda bata sakiba harse lokacin dataga ya dace seta sanar dani kinji,miher tace hakan ya nuna kaima kana sonta kenan? Manosh yace nop ina dai sonta a matsayin k'anwan abokina kin gane yana mata murmushi,miher tace dat why nake so ku fahimci juna tunda k'anwar marwan ne. Manosh yace zomuje palo mu zauna,bayan sun shiga sun zaunane yace miher akwai abinda baki saniba inaso ki nutsu ki saurareni kuma bance ki gayawa kowa,miher tace haba bro kasan akwai sirri mai karfi a tsakaninmu kuma babu wanda yake sani se mutum d'aya,manosh yace wa kenan? Tace zuciyana mana tana dariya wanda yake kara mata kyau,shima dariyan yayi yace to kina jina Ita dai LUBNA ba k'anwar marwan na jini bane, iyayen marwan suna son bby girl tun farkon aurensu tunma ba'a haifemuba,se Allah ya basu d'a namiji marwan kenan,sunyi farin ciki sosai kuma ke kanki kinsan yadda suke sonshi,amma ita mahaifiyarshi tanata so ta haifi mace gashi kuma bata sake haihuwaba shine sukaje gidanmarayu suka d'auko lubna tun tana jaririya suka riketa tamkar 'yar cikinsu. Mamaki sosai mihertayi dajin wannan lbrn da bro manosh ya bata,tace bro da gaske kake?murmushi yayi yace na tab'a miki karyane,tace wlh abun yaban mamaki amma to itama lubnan batasan da hakaba ko? Manosh yace bata saniba amma duk iyayenmu sun sani damuma,shiyasa banaso kiyinunakin sani kema. Miher tace to amma shine dalilin da yasa baka sonta kenan,manosh yace bahakabane sis yana jnkumatunta yace ai lubna yarinyar kirkice gata kyakkyawa duk namijin daya ganta zai sota amma kuma nid'in ban shirya neman mace bane yanzu shiyasa,ya kare maganar yana murmushi tare da barin palon ya d'auko key'n motansa ya fito yana cewa me,zan sayo miki sis,binshi kawai take da kallo tace bro ina zakaje kuma,yace gurin OGA na zanje yana nemana daga nan kuma zanje a rage min gashin kaina dan yana damuna sosai,miher tace pls kar'a rage dewa domin gashin yana maka kyau ai adai gyara maka shi,to luvlyn sis byee,itama hannun ta d'aga mishi guards d'insa sun mik'e da sauri yace no ni kad'ai zanfita karku damu,ok sukace dashi sannan mai gadi ya bud'e gate ya fita. Auntyn yara har an gama abincinne,eh baba an gama ya rana ya kasuwan? Alhamdulillah yau na samu ciniki sosai se hamdala,murmushi tayi tace to madallah baba kaci abincin idan anzo saya se in sayar,to 'yar baba nagode ya maman naki,lfyanta k'alau tace in gaidaka,yace to ina amsawa yau kind'an dad'e yar baba,tace wlh baba wlh mutum ne farfad'iya ta kamasa akan titi ya fad'i shiyasa kaga na dad'e, yace Allah sarki 'yar baba Allah ya rayamin ke Allah ya miki albarka,Allah yasa kiyi kyakkyawan karshe a rayuwarki. Tace ameen baba harda kai da mama da dukkan 'yan'uwa musulmai. Tun daga nesa ta fara jin muryan yaran makaranta sunata cewa oyoyo auntyn yara2,da sauri ta fito daga cikin gidan FLOWER tana murmushi tare da tafa hannun tana cewa oyoyo kannen aunty suka rungumeta dukkansu yaran amma banda d'aya, seda suka gama oyoyon sannan d'aya yaron yace sannu auntyn yara,tace sannun Abdallah nah ya makarantan,yace alhamdulillah sannan ya gaida baban auntyn nasu,yaran sukace aunty mutafi gida to, tace to baba ka gamane? Babanta yace na gama kuje yana murmushi,suka mishi sallama tare da addu'an Allah ya kawo kasu mai albarka suka tafi. Dad'i yakeji a ransada samun 'ya kamar maryam gashi tana da marrin jini kowa yana sonta manya da yara... [7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by Sad-Nas & Hama gee muh'd 5-6 Maryam ko kuma ince auntyn yara suna tfy suna hira da yara se bata lbrn makaranta sukeyi ita kuwa tanata dariya dayake ita d'in akwai fara'a ga kowa. Abdallah yace auntyn yara wai yaushe uncle ibrahim zai dawone,tace yadai kusa akwai wani abune,yace kawai dai naga nauyin ya miki yawane,tayi murmushi ta e aiba komai koda ya dawoma ai aiki zai kama tunda bautar k'asa ya tafi,abdallah yace har inaso in girma da wuri kodon indinga taimakawa kamar ke,dariya tayi tace insha Allah burinka zai cika abdallah. Haka dai suketa hira da yaran unguwansu suna tafiya jama'an dake wucewa sunata d'agawa auntyn yara hannu tare da gaisuwa maza da mata kowa ya santa a garin girei. Maryam ita kad'aice agun iyayenta suna sonta sosai fiye da ransu gashi sunyi sa'an yarinya tunda ta taso da son mutane take musamman yara k'anana kowa nata duk gireim ana alfahari da ita tun tana primary ita take zuwa na d'aya har secondary kuma ko'a islamiyama haka gata da murya mai dad'i musamman idan tana karatun Qur'an kyaututtuka sosai garin girei ta samu dukta dalilin maryam har gasan Alqur'ani mai girma tana zuwa state state kuma ita take zuwa na d'aya kona biyu ta hakanne takai iyayenta makka da kyautar kujeran da take samu agun MUSABAK'A,dayake ta samu kujeran sau dewa dan haka aminan mahaifintama dukta basu kyautar su uku kuma itama taje amma sam bata hakorin makka ba. Maryam tana da son yara sosai, dan haka take koyar dasu acikin gidansu bayan yaran sun dawo daga makara,duk fanni arabic da boko tana koyar dasu daidai iyawarta,dan tana da ilimi sosai. Ayanzu dai sun gama secondary suna jiran result kenan, yaranma suna sonta sosai dan tana kula dasu sosai komai k'azartar yaro bata kyamarsa gashi ta iya sayomusu abin wasannin musamman balobalo da ice cream na dela kananan nan,indai ta shiga gari toseta sayo musu shiyasama bata rabuwa da katon din biski da su sweet a d'akinta. Wannan daliline yasa ake kiranta da auntyn yara babba da yaro dan yanzu ba'ama ganeta da maryam sedai kace AUNTY'N YARA,itama tana jin dad'in sunan da ake kiranta dashi. K'awayenta su hud'u ne kuma kansu a had'e yake dukkansu, rashida muh'd,amina babale,zahida abba,da kuma samira jauro. Sune k'awayen maryam tare suka gama makaranta kuma duk y'an girein ne,abdalla shine k'anin rashi muh'd yarone mai hankali da nutsuwa ga son addini kuma yana da ilimi sosai yaron yana da shiga rai sosai shiyasa duk cikin yaran maryam tafi sonshi,saboda mahaifinsu baya raye suda mamansu kawai suke zama uncle ibrahim shine babban yayansu. Bayan sallan la'asar baban maryam ya dawo gida,daga maryam har mamanta sunyi amakin ganinsa,yace kuna mamaki ko wlh flower dai kad'an ya rage duk an saye yanzuma cikin JIMETA zan shiga in sayo wasu. Maryam tace baba yanzu duk sun k'are,yace wlh addu'arkuce ta d'azu ta karb'u kinsan bakin yara wani mutumine yayi sabon gida kuma yana so ya shuka flower shine ya sayi fiye da rabi,sukace Alhamdulillah baba ka kawo inje tunda nima nasan gurin kaika huta a gida,yace to 'yar baba gashi. Nan da nan maryam ta shirya cikin after dress bak'i ta d'auki pos d'inta tace sena dawo,sukace to Allah ya kare tace ameen sannan ta wuce titi tana isa kuwa ta samu mota se jimeta. Koda ta isa kekenape ta hau ta k'arasa gurin, amma sai mai keke yace bashi da canji,tace toya zamuyi kenan tana ta waige waige seta hango manosh yana rabawa masu bara sakadan 200 sabbi gal,ta kalli mai nape tace malam dan Allah kayi hakuri bari inje can in nemo canji,yace to bakomai. Nan ta nufi gurin manosh yanata raba musu kud'i tayi sallama tare da cewa bawan Allah,d'agowa yayi da sauri danjin muryan Apple ya kalleta batare dayin maganaba,tace sannu dai dan Allah canji zaka taimakamin dashi, ya kalli k'udin hannunta dubu d'aya,amma seyace wannan dai sadaka nake rabawa sannan banida wani canjin,tace to dan Allah ko 200 d'inne ka bani gashi ka rike 1000 d'in zan biya mai keke ne. Juyawa yayi yana kallon napen seyace rik'e dubun seya mik'a mata 200 d'in,tace nagode sannan taje tabiya mai nape ya bata canjin 150 seta dawo tace to kayi hakuri bari na shiga gun flower'nnan sena baka kud'inka,yace to se tayi saurin wucewa ciki yanata binta da kallo. Da yake sun santa tana shiga dama sun h'ada komai tunda babanta ya sanar dasu a waya dama. Bayan su gaisa se d'aya yace tokije ki nemo mota mana, tace akwai motoci anan muje kawai,suka bita dashi taga wani mota tace girei zaka kaini da wannan flowers d'in. Manosh yana ganin haka yama drivernshi waya take yazo da HILOX fara,yace kaje ka kaso flowers d'in can kasa a mota, har an fara sawa seya zo yace oga yace oga yace asa miki a mota,tace waye kuma oga,yace gashican shine mai gurinnan gabad'aya. Shuru tayi suka kwashe suka zuba dukka a hilox d'in setacewa mai motan data tsayar dan allah malam kayi hakuri,yace bakomai yarinya karki damu,tace nagode sannan ta k'arasa gurin manosh tace dama kaine mai nan gurin? Eh yace da ita tare da cewa kuje a kaiki gida koh,tace nagode sosai ga 200 d'inka,yace karkimin godiya,arayuwa idan kin samu dama toki taimaki mutane uku,suma kuma kice musu su taimaki wasu ukun ya k'are maganan yana murmushi,dad'i taji sosai har cikin ranta tana binshi da kallo harya shiga motarsa ya tafi. Gun hilox d'in ta nufa driver ya bud'e mata ta shiga ya rufe tace nagode sannan suka kama hanya yace ina zan kaiki,tace girei,yace ok sannan yaja suka tafi tana mai farin cikin jin kalaman manosh. Suna cikin tfy wayan driver yayi k'ara ya d'auka tare da cewa hello sir,se kuma yace eh nan girei ne sannan yace ok sir seya saka wayan a aljihunsa har suka k'arasa kofan gidan flower'n babanta sannan tace anan zamu tsaya,yace ok tare da tsayawa,dama babanta yana jiranta a shagonsa,drivern ya gaida baban maryam sannan suka kwashe flowern tare. Maryam da babanta sukayi godiya sannan ya tafi. Maryam taba babanta
Chapter 2 · 0% Book details