Sashe 21
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
4 zaiyi kenan yana neman wata...? Da wannan tunanin ta koma girei,bayan ta ajiye aiken da mamanta tamatane seta wuce d'aki ta kwanta har yanzu manosh bai kirataba ita kuwa ta kasa hakura seta kirashi. Hello apple kiyi hakuri wlh am busyne shiyasa ban sake kirankiba,tace busyn me kenan,yace ki bari kawai hidiman dewa pls kimin hakuri zan kira pls,tace bakomai se'anjuma,yace ok tnx luv u,shuru tayi tare da katse wayar. Abin ya d'an dami manosh amma dayake yana da abinyi sosai sebai sake kirantaba. Har la'asar bai kiraba,ita kuwa maryam abin yana cinta sosai a rai,manosh bai kirataba harse bayan magrib yace da ita am so sorry apple zanzo bayan sallan isha kinji,shuru tayi mishi,ya sake nanata tace sekazo tare da katse wayar,sake kiranta yayi ta d'auka batare datayi magana ba,yace apple are you okey? Tace ues am fine,yace amma naji muryanki wani iri,tace bakomai sekazo... Abun ya dami manosh sosai dan haka suna idar da sallan isha suka taho shida muh'd da marwan. Kamar kullum muh'd da marwan sun tafi k'ofan gidansu rash da mota shi kuwa manosh suna zauren gidansu maryam inda ta shinfid'a mishi k'aramin carpet tare da kawo mishi fruit kamar yadda ta saba dantasan yana son fruit sosai shiyasama bata rabuwa dashi a gida. Manosh yaga canji sosai tattare da ita hakan yasa ya ajiye wayarsa a gefe ya maida kallonshi gareta,ita kuwa kanta na kallon cikin gidansu kyakkyawar gefen fiskanta yake kallo tare da b'akin takalmin dayayiwa kafarta kyau yace apple lfy kuwa,tace lfy lau batare data kalleahiba. Yace toyana ganki haka kodai bakya jin dad'i ne,tace a'a lfyta k'alau,yace tomeyasa tunda nazo yau baki kalleniba kuma gashi sam baki sakeba kamar namiki laifi? Juyowa tayi suna kallon juna har cikin ido sannan tace kwarai kuwa kamar ka sani,seta sake mayar da kanta gefe, murmushi yayi yace pls apple ki bari fushin bai karb'ekiba wlh tomenayi nikuma yau? Ta sake kallonshi da kyau sannan ta juya,murmushin ya sakeyi yace kidena min wannan kallon kina bani tsoro wlh,shuru tayi batace komaiba,yace wai dagaske kike yine aunt,to pls ki gayamin laifina so that in nemi yafiyarki kinji,tace bakomai zan shiga gidane, yace ok to jeki mana yau harse kin nemi izinin shiga gida? Tace ina nufin zanje in kwanta bacci nakeji,shuru yayi yana kallonta cikin mamaki seyace ok badamuwa bari inji kosu marwan sun gama,nanya kira marwan tare da sawa a handsfree yace ya kun gamane mu wuce? Marwan yace kaji gayennan fa danka gama muma semu gama,manosh yayi murmushi yace bahakabane bata jin dad'ine shiyasa,amma shikenan bari na shiga masallaci nima inji karatu idan kun gama seku tab'ani,marwan yace ok ka gaisheta pls,yace zataji. Manosh ya kalleta yace apple zan tafi kije kiyi baccin kinji,mik'ewa tayi batare datace komaiba zata shige yace tsaya ki tafi da carpet d'in. Cak kuwa ta tsaya ya nad'e tare da d'aura mata tiran friut d'in danko d'aya bai shaba yau,tausayinshi ya kama maryam se kuma bataji dad'in abinda ta mishiba,matsowa yayi kusa da ita inda suke jin kamshin turaren junansu yace gashi,friut d'in ta kalla sannan ta kalli idonshi wanda shima idon nata nake kallo cike da tausayi ta kawar da kanta gefe tare da karb'a ta wuce da sauri batare datace mishi komaiba yanata binta da kallo harta tafi sannan shima ya fito ya shiga masallaci amma shi kad'ai yasan abinda yake damunshi hakama ita maryam d'in koda ta shiga gida friut d'in tasa a gaba tanata kallo tare dajin kwalla yana zuba a fiskanta. 9:30pm su marwan sukayi hon wa manosh wanda har ita maryam taji hon d'in kuma tasan sune zasu wuce,sam bataji dad'in abinda tayiwa manosh ba. Manosh yace musu yau sam banganewa apple ba,akwai wani abu amma tak'i gayamin. Muh'd yace kodai jikintane to,manosh yace sam bahakabane akwai dai wani abu daban dan sam tak'i sakemin yau kamar wanda nayi mata wani laifi kuma tak'i cewa komai. Abin ya d'aure musu kai sosai haka suka koma gida yayita kiran wayanta amma sam tak'i d'agawa yayi texs shima shuru bata amsa mishiba hakan ya tabbatar mishi da cewa fushi takeyi dashi. Washe gari tun asuba yake kiran numberta amma tak'i d'auka abin ya dameshi sosai dan sam jiya bai samu yayi bacci gashi kuwa yau zaiyi tfya zaije lagos ama 2days kawai zaiyi,haka yayi sallama dasu mum da marwan sannan ya tafi. Koda yaushe seya kira number apple amma sam bata d'auka daga karshema ta rufe wayan nata gabad'aya. Abun yayiwa manosh ciwo sosai,bayan abunda ta mishi ranan shi baiyi fushiba,bai kuma san laifin daya mataba dan haka shima yasa a ranshi cewa bari dai yad'an kyaleta na 2days maybe kafinnan zata huce. Da magariba maryam ta bud'e wayanta amma ga mamaki bataga texs d'in manosh ko d'ayaba. Hakan yasa tad'an damu kad'an tanata zaman jira har bayan isha shuru. Manosh dai bai sake kiran maryam ba harya gama 2days nashi a lagos ya dawo gari. Kuma so da yawa idan suna tare dasu rashida yakan kirasu su gaisa amma sam ya dena kiranta,hakan yasa ta damu sosai kuma tana matuk'ar son ganinshi. Yau wenesday bikinsu manosh saura 9days kawai,abun ya dami maryam sosai tanata tunani aranta. Bayan ta idar da sallan azaharne sega wani yaro yazo yace auntyn yara ana kiranki a waje,tace wanene,yace wanda yake zuwa gurinkine,nan taji dad'i a ranta dajin cewa manosh ne, tace to jeka kace ina zuwa. Atamfa tasa d'inkin riga da siket tare da himar kalan atamfar peach colour tayi kyau sosai. Tunda take fitowa yake kallonta harta k'araso da sallamarta,ua amsa tare da cewa kin kyauta apple da kika maidani haka,fiskanta a had'e tace kaima ai ka kyauta. Yace menayi,kalonshi tayi har cikin ido tace bansaniba,yace ni kikema wannan kallon ko, wlh appale idan kika shiga hannuna ko hmmm. Kunya sosai taji tare dayin mirmushi tace ina wuni,lfy ya mama,lfyanta k'alau,ya rashin kirkinki,tace muna fama dukkanmu,mirmushi yayi yana danna wayanshi. Tace ka fara ko,nifa bana so mun magana kana tab'a waya,kallonta yakeyi harda dakewanta,wayan nashi ya d'ago yace kalli nan,juyowa tayi tana kallonshi inda ya nuna mata wayan,mamaki sosai tayi da ganin pic nata akan wayan lalli kuwa wato dama d'auka hoto kakeyiko,murmushi yayi yayinda pic nata suketa wuce akan screen nashi kala kala,mamaki sosai tayi wato duk lokacin da suke tare pic yaketa mata yana k'are mata kallo. Katseta yayidan ya sauke wayanshi k'asa yace tun randa mukazo shop din baba nakeda pic naki har ranan yau. So duk lokacin da nake tare dake muna hira ina kallon ki a wayana,tace oh shiyasa ni kake cemin in dena kallonka ko,yace eh mana ni bana so ana kallonane shiyasa,murmushi tayi tace ina miher,yace oho ban saniba,tace haka kace ko,yace eh nima yau na dawo daga lagos kwanana biyu acan dana dawo ban sameta a gidaba taje gun k'awarta. Maryam tace baka gari? Yace yes ai kece kika cazamin kai shiyasa nima na tafi,kuma nayi iyakan k'okarin in sanar dake kink'i picking call nawa bansan wani irin laifi nayimikiba. Tace lallai ka kyauta,yace wlh bani da laifi apple kece da laifi dan haka kibani hak'uri,murmushi tayi tace bashakka kuwa ai kamin laifine shiyasa,yace to amma idan na miki laifi bazaki gayaminba apple sedai kiyita wulak'antani dan kinsan ina sonki ko? Tace hmm su so manya,kallonta yakeyi sosai yace bakiyardaba kenan,tace dakam ina sane da wannan son,amma ayanzu kam bansaniba konice ko kuma ita. Kallon juna sukeyi yace me kikace apple? Tace eh aikaji abinda nace. Yace pls ki gayamin ban ganeba,tace wata yarinyace na ganku da ita ranan kana tsaye dab da ita marwan yana gefe,harka bud'e mata k'ofa kuka tafi kuka bar marwan agun,kuma na kiraka alokacin amma sam kaki kirana da sunan daka saba gayamin sema cemin kayi wai zaka kirani anjuma shine baka kiraniba harse bayan magrib shine kukazo kaida muh'd da marwan. Tabbas manosh ya gane komai dan haka ya shiga yin dariya sosai kamar bashiba,yace kardai kicemin shine dalilin dayasa kika min wannan horon,shuru tayi tana kallonshi rai ab'ace shi kuwa dariya sosai yakeyi yace haba aunt gaskya bakimin adalciba dama ashe kina da kishi apple,dariya sosai manosh yakeyi wanda hakan ya tfyar da hankalin maryam ta tsaya kallonshi tana murmushi,dariyanshi yana mugun kasheta dan wani kyau na musamman yakeyi,manosh ya lura da irin kallonsa da takeyi wanda ita kanta basan tanayiba,hakan yasa ya dena dariya shima ya tsaya kallonta tare da juyawa yaga ba mutanen sam a inda isuke,hakan yasa yace mata zonan aunt,se yanzu ta dawo saiti tace nak'i,yace pls ki matso apple,tace meyasa,yace toki dena pls kallona banso saboda kina tafiyarmin da hankali aduk lokacin da kike kallona wlh. Shuru tayi tare da kallon wani girin gabad'aya kunya ya kamata shima ya lura da hakan dan haka ya kira marwan a waya yace abokina gani agun aunt,marwan yace kace komai ya daidaita kenan?manosh yayi murmushi yace zai daidaita dai kasan meyasa take fushi dani,marwan yace seka fad'a menen wai? Yace randa dad ya aikemu muka fito se muka tsaya a gefen gidan man su muhsin. Marwan yayi dariya yace kardai ince taganka kaida lubna lokacin da nake mata fad'a? Dariya manosh yayi yace to wlh fushin da takeyi dani kenan waita d'auka budirwatace. Dariya sosai sukeyi marwan yace haba aunt har kina sa ran abokina zai iya hango wata bayan ke,murmushi tayi tana sauraronsu,marwan yace wlh lubna ce k'anwata kuma laifi tayi yasa nake k'okarin hukuntata shine abokina ya shiga tsakaninmu yace muje mu maidata gida,danace bazan jeba suje shine yace da lubna tota dawo gaba ta zauna se suka tafi ni kuwa ina jiranshi yadawo wannan shine gaskya aunt,ai wlh ki kwantar da hankalinki mu sam iyayenmu zamu gada mata d'aya kawai is okay,manosh yace a'a nidai 2 zanyi dan nama gaya mata kuma tsarin gidanama na mata biyune,nagode daka wankeni marwan sena shigo,yace ok a gaisheta,manosh yace zataji amma gaskya na canja mata suna daga *apple zuwa jealousynah*, ba marwan kad'aiba harda ita maryam dariya sosai tayi wanda harshi marwan yana jiyowa. Bayan sun gama dariyanne manosh yace *jealousynah* ina so mufitane bazamu jimaba kije ki sanar da mama kinji? Tace nifa bana son wannan sunan,yace okay apple,murmushi sukayi tare tace inane zamuje? Yace cikin jimeta amma yanzu zamu dawo kinji,tace to bari inje in gayamata,ok yace da ita sega abdallah yazo gunshi. Mama tace to maryam