Sashe 16
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated 2 billylosh* 37-38 hankalin manosh a taahe ya kalli d'aya daga cikin sojojin yace ina tausayawa duk wanda yayiwa maryam haka wlh. Miher ce zaune ita da mum nata a palo suna jimamin abinda ya fari da maryam se wayanta ya fara k'ara da sauri ta d'aga tare da cewa hello lubna,lubna tace miher ya gida naji bro marwan yana cewa anyi kidnaping maryam d'in da bro manosh zai aura? Miher tace wlh kuwa lubna,lubna tace subbahanalillah yanzu su waye sukayi wannan aikin,miher tace wlh har yanzu dai shuru tukunna amma ansan inda maryam d'in take yanzu haka,lubna tace haba alhamdulillah a ina aka sameta,miher tace bawai an sametabane fa,andai gano inda take a *numan ne*. Lubna tace har numan aka kaita kai Allah ya tona asirinsu zanzo gobe insh Allah,to sekinzo nagode. Koda lubna ta ajiye wayan miher se ta kira wani tace hello *saddam* ya akayi har su bro suka gane cewa maryam tana numan,aikinka baiyiba saddam domin yanzu haka su captain suna numan dan haka kuyi gaggawan d'agata daga numan ku k'ara gaba da ita zan tiro maka da kud'i yanzu a account naka saddam idan asirinmu ya toni zansha wuya agun bro marwan wlh seya kusan kasheni pls indai da gaske kana sona tokayi wani abu plss saddam. Murmushi yace karki b'ata bakinki bbynah, yanzu zamubar adamawan ma kwatakwata karki damu sweetheart zan nuna miki cewa da gaske nake k'aunarki bari na nemo wani abokina,lubna taji sanyi a ranta tace nagode sena jika. Maryam kuwa dama ta kashe wayan gabad'aya tasa a cikin pant nata. Yadda aka ajiye mata abincin haka sukazo suka samu,yace wato bakici abincin bako,bai jira jin abinda zata ceba ya toshe mata baki da hanci da wani hankachif fari take ta mance inda take seya d'auketa cak se mota suka kama hanya,cikin ikon Allah kuwa ba'a tsaidasuba har suka bar numan. Tfy sukeyi hankalinsu a kwance suna dariyan mugunta yana cewa *captain manosh* zanga iya kwarewarka kafin in shiga hannunka kuwa sena gama lalata budurwan naka tukunna dan nasan idan na shiga hannunka tofa tawa ta k'are shiyasa nima zanyi abinda nakeso tunda dama banida iyaye se kawai in bisu bayan na shana hhhhhhh... Manosh se kiran line na maryam yakeyi amma shuru, seyayi tunanin kodai tana tare da mutanenne shiyasa bata bud'e wayanba. Nan dai yace bari yad'an k'ara jira. Anan ne muhsin ya kirashi yace "dude" na raba hotunanta kota ina yanzu haka ma ana haskawa a gidan *TV GOTEL* , *NTA* da kuma *ATV* duk anta haska hotunanta,manosh yace nagode abokina pls kuyita tayamu da addu'a sannan kuyita bada sadaka Allah ya bamu sa'an gano inda take,muhsin yace ka kwantar da hankalinka abokina insha Allah zamuga maryam cikin k'oshin lfy dan maryam tana da halayya masu kyau. Iyaye maryam kuwa hankalinsu yad'an dawo jikinsu da sukaji lfyarta k'adau amma dai har'a yanzu suna cikin tashin hankali sosai. Duk girei seda akaji zance sace maryam auntyn yara,dan haka aketa addu'oi babba da yaro kai harta almajirai idan sukaji lbrn tofa suna komawa gun malaminsu suka gaya mishi,yace musu kwarai yaji a radio dan haka kota ina addu'oi maryam take samu. Hajiya iya kuwa tafi kowa tashin hankali ana zaton,ko menene dalili oho? Kuka takeyi safe da dare tare da addu'an Allah ya baiyana maryam. K'awayen maryam sun zama abin tausayi musamman rashida data tina kalmomin data dinga gayawa maryam ranan,dan haka ta dinga kuka tare da kewar aminiyarta. Hakama abdallah ya shiga wani hali sosai dan ganin maryam yakeyi kamar yarsa da cike ciki d'aya,yah ibrahim nema yake lallashinsa dan kowa yasan irin k'aunar da take tsakaninsu hakama ita maryam d'in tana ji da abdallah fiye da,sauran yaran. Manosh baiga kiran maryam ba har 12:00pm dan haka yasan cewa akwai matsala,kuma shi yasan babu wadda ya gayawa cewa maryam tana numan daga iyayenshi se iyayen maryam se kuma friends nashi,dan haka abin ya dameshi sosai gashi faruq yace mishi wayan maryam a kashe yake bazai iya gane inda takeba dole se wayanta yana kunne. Da misalin 2 na dare suka isa wani jeji tare dabi cikin jejin daba kowa se wani d'an k'aramin gini daba'a k'arasashiba nan suka tsaya suka fitar da 'yan kayayyakin da suka taho dashi suka dai kimtsa gurin se suka kwantar da ita akan bargo sannan suka zauna a gefe. Saddam ya kira lubna yace hello bbynah mun iso lfy,tace sannu da hanya a inakuke yanzu? Yace muna jihar bauchi cikin gefe da *jejin yankari* ido lubna ta zaro tace har bauchi,yace yes bazasu tab'a tunanin zamuzo bauchiba,dad'i taji har cikin ranta tace nagode bbynah aikinka ya gyaru,murmushi yayimata yana busa sigarinshi yace bbynah gaskya bazan kyale yarinyarnanba dolene sena tab'ata fa,hankalin lubna ya tashi tace no bbynah kafa cemin ni kad'ai ce yarinyar da kake so taya za'ayi kashe min haka kuma,wato dama kana cin amanata kenan ko? Saddam yace wlh ba haka bane bby shikenan wlh bazan mata komaiba amma kinsan ked'in kince dole semunyi aure kafin muyi wani harka kuma gaskya ni a matse nake wlh,lubna ta murgud'a baki tace karka damu idan mun gama wannan aikin zakasha mamaki da irin gift d'in dazan baka wlh bbynah,nan saddam yaji dad'i yace okey my luv shikenan sekin jini,tace ok but pls karka mata komai indai har kana sona,yace wlh bazan mata komaiba karki damu bbynah. Maryam bata farkaba har asuba,ta jita ak'asa nan ta tashi da sauri tana addu'oi tare da k'arewa gurin kallo setaji hawaye a fiskan,kukan tane ya tashi mutum guda d'aya da yake kwance daga gefe dan sauran kam duk sun shiga gari neman abinci. A gigin baccin yazo inda take yace ke 'yanmata yane? Kallonshi takeyi tare da cewa bawan Allah inane nan kuma? Yace nan jihar bauchine ta gefen jejin yankari. *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* maryam taketa fad'i sannan tace karfe nawane yanzu? Ya duba wayanshi yace 5:30am,tace ina zan samu ruwa nayi sallah,nan ya d'auko pure water ya mik'a mata tare da ciro bindiga a aljihunsa yace kinga wannan,wlh idan kikayi wani kuskure sena pasa kanki dashi,jikinta na rawa tace to alwala kawai zanyi inyi sallah. Komawa yayi ya kwanta ita kuwa jiki na rawa ta koma gefe tana alwala. Bayan nan ta koma cikin ginin tare da lekashi taga dai bacci na damunshi sosai,dan haka ta ciro wayanta ta kunna tare da da turawa manosh texs sannan ta kashe wayar tahau yin sallah. Manosh daya kasayin bacci yana zaune a mota a numan seyaji texs ya shigo wayanshi,da sauri ya duba _hello peach,sun d'aukeni daga numan zuwa jejin gefen yankari dake jihar bauchi gurin babu kyan gani a tsakiyar jeji muke cikin wani kango da babu ko rufi asaman pls peach do something ka kulamin da iyayena plss da kuma abdallah nah byeee_..... Manosh ji yayi kamar zaiyi hauka dan yadda yakejin k'irjinji yana tafasa. Kwana d'aya kawai amma dukya fita hayyacinsa haka ya juya ya koma girei ya dad'a baiwa iyayen maryam hak'uri tare da kwantar musu da hankali,sannan yasa aka kira mishi abdallah yace kayi hakuri abdallah maryam tana cikin jarabawane amma komai zai wuce ina tabbatar maka da cewa auntynka zata dawo insha Allah kuma dukda halin da take ciki sam bata mance da kaiba tace ingaisheka abdallah. Rungume manosh abdallah yayi yana zubda kwalla shima manosh daurewa kawai yayi sannan ya kalli yah ibrahim yace ka kula dashi dan sak'on maryam kenan akanshi. Manosh ya shige mota ya wucegida a galabaice,toilet ya shige ya watsa ruwa sannan ya fito yasa jaket maroon da black yana k'ok'arin fitowa sega mum nashi da miher,nan ya koma lallausar gadonshi *milk colour* yad'an jingina yana kallonsu. Kuka miher ta farayi tare da ciro wayanta ta d'aukeshi hoto taje har kusa dashi tace kalli yadda ka zama fa bro, kwallan idonshi ya share tare da kamo hannun miher yace karki damu zan koma normal ne bayan na samo apple d'ina. Mum tanata kallonsu tare da tausayawa d'an nata tace Allah ya baka sa'a *son*, yace ameen mom nina tafi sena dawo,har waje miher ta bishi tanata kuka harya tafi.... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated to Hasiya Ahmad & Maryam Adamu Girei* (TAHIRA) 39-40 Bayan maryam ta idar da sallah ne taketa hamman yunwa,dan tunda ta baro gida bata sake cin abinciba se ruwa data sha,gata da *ulcer*. Lek'owa tayi taga har yanzu bacci yakeyi,dan haka taje inda yake tanata crwa 'bawan Allah 2' ahankali ya bud'e ido tare da tasowa ya zauna! Kallon juna suka tsayayi domin sun tabbata akwai inda suka tab'a had'u dukkansu d'in. Can maryam ta tuna shine mutumin da mota ta tab'a bigeshi a hanya harta taimaka mishi yahau mashine aka kaishi hospital tabbas shine wannan. Wani sanyi taji a ranta tare dayin mirmushi tace bawan Allah dama kaine ka rabani da iyayena? Shuru yayi yana kallonta cikin mamaki yace dama kece yarinyar da aka d'auke? Kallonshi ta tsaya yi tana mamaki tare da cewa aka d'auke ko kuka d'auke bawan Allah. Bayansa yaketa waigawa sannan ya mik'e tsaye cikin hanzari yace banina d'aukekiba abokin aikinane,maganar gaskya nidai ba mutumin kirki bane wannan ranan da muka had'u dakema sata naje nayi aketa bina tare da fasamin jiki,dak'ar nasamu na gudu shine na b'ullo ta girei har muka had'u dake kuma na miki k'arya kika tausaya min tare da taimakona. Maryam tayi shuru tana sauraranshi tace to bawan Allah dan Allah ka gayamin abu guda d'aya wanene yasa a kamoni? Shiru yayi yace bazan gaya mikiba sedai in taimakeki in baki wayana ki kira duk wanda kike buk'ata indar har kinaga za'a iya taimaka miki,shuru maryam tayi tace to ai nabar wayata a gida ban kuma san numbern kowaba sena iyayena da k'awayena. Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toki gayamin numbern iyayenki,nan ta gaya mishi numbern babanta yasa ya kirashi,bugu d'aya ya d'auka lokacin suna tare da dad d'in manosh yaje yi musu jaje. Maryam tace baba nice yanzu haka ina jihar bauchi cikin jejin dake gefen yankari,baba yace to wannan numberfa? Tace baba karka damu lfyata lau babu abinda ya sameni sedai ina jin yunwa sosai har k'irjina ya fara min ciwo,subhanallah maryam haka suka barki da yunwa dan basu da imani tun jiya? Baba