Sashe 6
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
no bahaka bane,yace toya akayi kika sani,tace kowa ya shaidi soja baya wasa kuma ba dariya,manosh yayi murmushi yace to ai ni k'aramin sojane,manya ne suke hakan kuma sud'inma ba dukka bane. Sameera tace ina fata dai zaka rik'e mana friend namu da kyau,yace base kin fad'a samira "because i luv her over" dariya tayi tace to Allah ya barku tare musha biki,yace ameen nagode sosai,tace yawwa ga rashida. Rasha tace captain zance nece kodai prince manosh dan sunan naka na larabawane,dariya yayi sosai yace duk wanda kika kira,tace captain d'in dai ina wuni,yace lfy ya kuke ya apple d'ina,tace lfyanta k'alau ya aiki,yace alhamdulillah,tace to Allah ya sanya alkhairi adai rik'e mana ita amana dan kaine mutum na farko data amshi soyayyarshi,yace insha Allah rash bazaku samu wata matsala daga gareniba dan nima itace mace ta farko data fara shiga jinina,rash tace jini gabad'aya, yace "yes ina ji da ita sosai pls ku kula min da ita sosai" rash tace to gaskya munji dad'i Allah ya barku tare,yace ameen nagode da addu'arku,tace bakomai gata nan. Maryam tana murmushi tace hello,yace eeeeh aunt ya akayine,tace babu,yace friend naki suna da kirki sosai wlh kun burgeni gaskya saura zahida da amina ki turo min number'nsu dukkansu kinji,tace ok mungode,yace banace miki bana son godiya ba,tace ai ya zama dole,yace nidai banaso,tace to shikenan byee yace byee. Yaune manosh ya dawo daga abuja,nan kuma dad nashi ya dawo daga tfy. Manosh yaje har palo ya gaida dad d'insa sannan ya gaya masa ra'ayinshi akan maryam,dad yace a ina take,yace a girei ne,k'irjin dad nashi ya buga amma seya ce to badamuwa zanyiwa iyayen abokanka magana semuje,manosh yace yace to dad nagode,dad yace Allah ya sanya alkhairi yace ameen sannan ya wuce d'aki ya shirya da sauri cikin kananan kaya yasha turare sannan ya d'auki kits d'in tsaraban maryam yayiwa mum sallama yace zanje girei ne,tace to Allah ya kare,yace amin ya fita. Miher ta bishi har waje tace bro gun yarinyar ne,yace ke sunanta maryam ba yarinyaba, tace to ka gaisheta,yace yawwa k'anwata barima in baki numbernta ki dinga kiranta kuna gaisawa kinji, mihar tana son bro manosh sosai dan yana sonta kuma yana kulawa da ita sosai sam bayaso yaga an b'ata mata rai,dan haka itama taga ya dace taso abinda yake kauna dukda dai ita tasoshi da k'awarta lubna amma hakan baiyuba. Shida muhsin da marwan da muh'd suka tafi danshi muhsin yana gun zahida,hakama majid yana gun miher. Wayanta ya kira yace aunt gani a waje,tace yaushe ka dawo daga abujan,yace d'azu,mamaki sosai tayi dan bai sanar da itaba,tace to ina zuwa. Munbern rashida da samira ta kira tace pls kuzo yanzu,ba jimawa sukazo ta d'aya kofar bayan,duk himarne a jikinsu suka fita. Salam,suka amsa wslm,bayan sun gaisa ne manosh yace dama bakisan marwan ba toshine wannan,tace eyyah sannu,yace yawwa maryam ya kike ya hakuri damu,tace bakomai,yace to idan yayi badaidaiba ki sanar dani zan hukuntashi,dariya sukayi sosai,muh'd yace zamu hukuntashi dai,maryam ta gabatar da rashida da kuma samira, sannan suka fara hira,manosh yace aunt yane,tace bakomai,yace muje daga can kinji su marwan zasu damemu,muh'd yace gara dai kam,tana dariya suka d'an matsa gefe. Hannunsa a aljihu yace baba yana gidane,tace eh,yace yasan munzo,tace eh nagayawa mama kuma nasan ta gaya mishi,yace ok kinsan bana so kiyi laifi,murmushi tayi tace ya k'anwarka,yace miher lfyanta k'alau tamace in gaisheki,sannan na bata numbernki,tace eyyah ina amsawa,yace tun bata gankiba amma tana sonki sosai. Maryam tayi dariya tace nagode ina majid da muhsin,yace suna hira gun zahida majid kuma na barshi a gida gun miher,tace tofa,yayi dariya yace kinga marwan da muh'd ma sun biyonine dan su fahimci juna dasu samera kinga in Allah yayi se ayi bikinmu rana d'ara d'aya,dama akwai wani abokina YUSUF AHMAD shima sojane ya tab'ayin aure matarsa ta rasu agun haihuwa ita da bbyn dukka se bai sakeyin aureba,shine na had'ashi da amina. Maryam tace eyyah Allah ya jikansu,yace ameen kinga shikenan za'ayi bikin abokai da kuma k'awaye ko? Murmishi tayi tace to Allah ya tabbatar,yace ameen meyasa bakya son yin magane, tace bakomai,yace kinaso nima inyi shuru ne,tace a'a se wayansa ya fara ringing,bak'uwar numbern ce ya d'auka tare da cewa hello,muryar mace ce tace yah manosh lubna ce, yace ok lubna ya kike ya gida,tace lfy lau ka dawo lfy,yace lfy lau wlh yasu mama,tace lfyansu lau dama na kirane in maka sannu da dawowa,yace to nagode sosai numbern ki kenen,tace eh shine,yace ok thankyou,tace ok seda safe sannan ya katse wayar tare da saving d'in numbern a wayanshi maryam tanata satankallonshi da yake hasken wayan yana haska fiskanshi. Gaskya manosh ya had'u take fad'a a ranta,seya katseta da cewa kina satan kallona ko,kunya taji sosai dan batasan ya gantaba,tayi mirmushi tace a'a,yace eh mana aina ganki,meyasa zakiyi sata bayan ni nakine,dariya tayi wanda ya baiyana fararen hakwaranta,yace nima bari na haskaki to,wayanshi ya haska fiskarta tayi saurin juya kanta,seyace to shikenan na dena,sannan ta juyo yace inga wayarki,ba musu ta mik'a mishi,yanata danne danne ashe numbernshi yake dailing dan yaga wani suna tasa mishi, ita kuwa tanata kallonshi tana k'ara jin sonshi a ranta. Yace "PEACH & CREAM" gaskya sunan yamin dad'i sosai apple thankyou,murmushi tayi tare dajin kunya tace wato dama sunan dana samishi ya duba, wayan ya mik'a mata ta karb'a tare dajin kunya se wayanta ya fara ringing,dubawa tayi taga UNCLE IBRAHIM,d'auka tayi tace slm uncle ibrahim ina wuni,yace lfy lau aunty ya gida ya fama da yara,tace lfy lau ya aiki,yace alhamdulillah muna kai,tace Allah ya taimaka yace ameen yasu mama da baba,tace lfyansu lau wlh, yace dama na kira mu gaisane,tace nagode sosai tana mirmushi shi kuwa manosh se kallonta yakeyi. "Bayan ta gamane manosh yace kar inyi laifi amma waye wannan? Tace brothern rashida ne brothernmu dukkanmu, tun muna primary yake mana lesson a gida har secondary, da shine yake koyar damu a gida tare da sauran yara,bayan tfyan shi NYSC ne yace indinga koyar da sauran yaran,kuma duk yan unguwan uncle ibrahim muke kiranshi. Manosh yace ok,amma akwai wani abu kuma bayan wannan? Tace a'a meyasa ka tambaya,yace to ai naga ya kirakine kuma da dare,murmushi tayi a zuciyarta kuwa tace wato dai kishi kake, tace ai duk muna waya dashi hardasu sameera bawai ni kad'ai bane,kuma ya zama kamar d'an gida dan hargun mama yana shiga su gaisa sannan ya tafi. Manosh yayi magana a zuciyarshi yace gaskya akwai atsala,afili kuma yace ok tobakomai apple zamu wuce kar'in rik'eki dewa, tace to mungode Allah ya kiyaye hanya ka gaida miher,yace zataji insha Allah sannan suka k'arasa gunsu marwan. Manosh yace to muje guys,muh'd yace amma baka kyautaba danka gama hiranka sekace muje,yace to ai ahikenan nima ba gamawa nayiba kawai dai hakura nayi dan haka kuma ku hakura,marwan yace to rashida nagide sannan yace aunty maryam mun gode sosai semun sake zuwa dan yanzu kam ni kad'ai zan dinga zuwa prince yana takura mana,dariya sukayi lokacin manoah ya fito da k'aramar kits a mota yace to shikenan nima hakan yafimin kowa yayi zuwanshi,manosh ya mik'awa maryam kits d'in batare dayace komaiba tasa hannu ta karb'a tare dayin godiya sannan ya mikawa samira wani leda yace ga tsarabanku,godiya sukayi sosai sannan sukayi sallama suka tafi. Ahanyane manosh yake ce musu akwai matsala gaskya dole su dad suzo da wuri ayi tambaya dan ban yarda da uncle ibrahim d'innan da apple ta gayaminba. Dariya su muh'd sukasa tare da cewa soja da tsoro,yace a'a kunsan fa bana zama sosai,shi kuwa yanzu idan ya dawo daga NYSC ai suna tare kenan 24 gaskya da sake. Marwan yace tobase ke hakuraba tunda ya zama sirikina zan nema maka wata ai,duka manosh yakaiwa marwan yace d'an iska wlh zanyi maganinku bazaku sake biyoniba,hakadai suketa hira da hara har suka isa gida lokacin muhsin ya dawo dagun zahida nan dai sukaita tsokanan manosh wai gaskya seka dage tunda ku biyu masoyanta. Nima dai sad-nas nad'an tayasu kad'an [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Writeen by sad-nas & Hama gee muh'd 17-18 Washe gari miher ta kira maryam a waya suka gaisa sosai take ce mata iher ce k'anwar captain manosh,murmushi maryam tayi sannan suka sake gaisawa,miher tace dan Allah ki rik'e min bro na da kyau dan ina sonshi sosai banaso ya shiga cikin damuwa ta dalilinki pls auntyna,maryam tace insha Allah hakan bazai faru ki kwantar da hankalinki,dad'i sosai miher taji sukaita hira sannan sukayi sallama. Mahaifin manosh kuwa tunda yaji cewa a girei d'ansa yake neman aure se hankalinsa ya tashi,amma dai dukda haka ya gayawa aminansa sunce,zasuje nemawa manosh aure dan yana son ayi biki da wuri,amma se iyayen,sukace abari tunda AZUMI yazo se bayan sallah se suje tunda su marwanma sun sami nasu matan,dan haka aka yanke shawara za'aje bayan sallah. Soyayyan abokai da k'awaye dai yana tafiya yadda ya kamata abin gwanin ban sha'awa. Sannan abinda zaifi burgeka a soyayyarsu shine soyayya mai tsafta sukeyi,bakamar irin soyayyar da akeyi a zamanin yanzuba,seka budurwa da saurayi suna kissing d'in junansu wasuma har huging kai wasuma har tab'a jikinsu suke bari namiji su aganinsu hakan shine wayewa ko kuma iya soyayya amma fa ku sani bakomai bane se sab'on Allah da kuma ragewa kanki mutunci a idon saurayin. Wlh mafi yawancin maza suna son tab'a jikin mace,wasu sunayi yin hakan dan nasu manufarne wasu kuma sunayin hakanne dan su gwada macen,idan kika yarda yaci gaba da tab'aki to wlh wani daga ranan bazaki sake ganin ya dawoba dan zai d'auka duk samarinki haka suke miki tunda yasan halin mazan. Amma idan kika taka mishi birki dole ne zaiyi respecting naki sosai kuma bazai tab'a rabuwa dakeba sedai in dama ba aurenki yake sonyiba. "Amma zamanin da muke ciki yanzu sedai addu'a" se kaga budurwa ta nemi yaro k'arami kona makotanta ta goyashi sunce hospital wai tanaso tayi planing dan ta bada tazara,su kuwa doctor ko nurse ba tare dasunyi bincikeba sesu sama duk kalan planing d'in da take buk'ata shikenan budurwa ta maida yaro taje ta samu saurayinta wanda dama shine ya bata wannan shawaran waidan ya kai sadakinta gidansu yana ga ai yanzu kam shikenan kin zamat tashi,shiyasa taje tayi planing domin su shek'e ayarsu kafin suyi aure ya santa tun a waje,kuma bazai tab'a aurenkiba tunda ya