← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 45

Sashe 7

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

samu abunda yake so,koda kuwa ya aureki tofa bazai dinga ganinki da mitunciba kuma wulak'anci kala kala zai dinga miki bayan zunibin da kika kwasa wa kanki. Hmmm 'yan uwana mu kula mu dinga yiwa kanmu fad'a mu kare addininmu da kuma martabarmu ALLAH YASA MU DACE MUFI K'ARFIN ZUCIYANMU AMEEN. Addininmu ya koyar damu addu'oi iri iri,zamanin yanzu seda addu'a. Ina masu yara,ko k'anne ko jikoki dadai sauransu mu tsaya tsayin daka dan nemowa yaranmu ilimin addini kafin mujega na zamani,kuyi k'ok'ari kusa yaranku a ISLAMIYYA. Mu kasance masu yiwa yaranmu addu'oi da fad'in alkhairi akansu idan sun b'ata mana rai bawai muyi musu bakiba. Wannan addu'a tana kore komai,tana kare komai a fad'in duniyannan dan haka mudinga yiwa yaranmu safe da yamma. Fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD (S A W) yace koda sabon gida mutum yayi tofa wannan addu'a ita kad'ai zakayi batare dakayi sauk'an QUR'AN ba ko kuma yanka, addu'a ce mai kyau sosai. AUZU BI KALIMATILLAHI TAMMAT,MINSHARRI MA FALAK3 sannan shine yace adinga yiwa yara sau 2 a rana ma'ana safe da yamma so uku2. Allah ya gafarta mana kurakurenmu ameen. Lokacin musabak'a yayi. Kuma auntyn yara itace aka d'auka a girei local gov, inda aka shiryashine a mubi local gov. Duk wani malamin sunna ya halarci wannan musabak'an amma banda manosh sakamakon yanayin aikinsu,amma friends nashi duksun halarci gurin inda maryam muh'd Attah kokuma ince aunty'n yara zata karanta SURATUL BAK'ARA. K'ira'a kakeji yana tashi masu imani se zubar da kwalla sukeyi,dole abin ya birgeka mai sauraro da kuma mai kallo. Koda akazo kan maryam ana kiran sunanta jama'a suka d'au kabbara ALLAHU AKBAR kaje ji yana tashi a wannan gurin, himar d'inta milk colour har k'asa mai hannu sannan tafiya takeyi cikin nutsuwa harta k'arasa ta k'arb'i abin karatu ta fara da korar shaid'an sannan ta fara karatu . Ba iyayen maryam kad'aiba,harda wandama basu santaba seda suka zubda kwalla da murya da Allah ya bata mai dad'i sauraro,su majid masuji dad'i muryantaba se a yau da take karatu,kowa da abinda yake fad'a a ranshi akan maryam. Miher kuka takeyi sosai dajin karatun maryam tana mai jin haushin kanta data fifita karatun boko sama dana addininta. Har aka tsaida maryam sannan ta tsaya suma kansu malaman badan sunsoba sedan lokaci yayi nata kamma harya wuce. Kabbara kawai akeyi da k'arfin gaske su muhsinma da muryansu sosai suke kabbara yayinda manosh yake jiyowa daga wayansa da miher ta kirashi yanata sauraro,wani k'aunartane na susamman yake shigansa wanda shi kansa bazai iya baiyyanawa. ALLAHU AKBAR, dan Allah FANS kuma kuce ALLAHU AKBAR!nasan ku kanku maryam ta burgeku,k'ilama baza'a rasa masu zubda kwallaba danjin haushin kansu na rashin neman ilimin addini,tofa ku sani lokaci mai k'ure mukuba ba'a tsufa da neman ilimi Allah ya bamu ilimi bar albarka damu da 'ya'yanmu ameen. [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Writeen by sad-nas & Hama gee muh'd 19-20 Bayan an kammalane ake kiran wanda sukazo na d'aya, a suratul bak'ara maryam itace tazo na d'aya. Koda aka kirata kuka takeyi harta isa inda *sheik malam balalau* ya bata kyautarta masu sayawa tanata hawayae ta k'arb'a harda key'n mota, jama'a suna ta kabbara. Hakadai aka gama taron miher ta k'ara gurinta ta rungumeta tana tayata murna tare da murmushi sosai a fiskarta. Itama maryam d'in rungumeta tayi sannan k'awayenta su su 4 d'in suka rungumeta kowa yana tayata murna su muhsin suka k'araso gunta suna tayata murna dad'i taji sosai ga abokan arziki dukdai se zuwa akeyi ana tayata murna. Bayan tad'an nutsu ne se miher ta mik'o mata waya tace bro na zaiyi magana dakai, karb'a tayi tare da komawa gefe tace slm. "Wslm my appale congratulatoins" tace "thankyou"ya aiki,yace ki bari kawai kawai wannan aikin namu baiyiba gadkya dayasa nayi missing taro kamar wannan,am verry sorry my apple,tave bakomai wlh wa'yanda ka turoma yayi wlh naji dad'i sosai Allah yabar k'auna,yace ameen apple gaskya bansan mezan ceba wlh dan lokacin da nakejin karatunki ni kaina bansan yanayin da nakeji ba,murmushi tayi tace dama kaji,yace yes miher ta kirani naji tun daga farko har k'arshe. Tace eyyah nagode zamuyi waya anjuma kaji,yace ok wait,tace to menene,yace *I LUV U* murmushi tayi tace *minfu mi yid'ima* sannan ta kashe wayar yanata dariya tare dajin dad'i a ransansa da samu mace kamar maryam. Duk kyautan ta rabar da wasu,mota *honda civic ce* ash ta samu dan haka ta mallakawa mahaifinta shi kyauta. Ranan auntyn yara tana tafiya zataje kaiwa mahaifinta abinci seta ga wani mutum jikinsa duk jini yana buk'atan taimako,da sauri ta k'arasa tace subhanalillah lfy bawan Allah,yace wlh wanine ya bugeni da mota ko tsayawa baiyiba,kwalla ne kawai maryam ta fara dan yadda yaji rauni tace amma mutane sam babu imani a wannan zamanin, nan ta tsaida wani mai mashin tace dan Allah ka taimaka mishi,ba musu ya taimaka zai kaishi asibi,tace Allah ya kare Allah ya baka lfy,yace ameen 'yan mata nagode gaskya kina da hali mai kyau,murmushi tayi tace bakomai d'an'uwa amma a maimakon godiyan da zakamin,inaso idan kasamu dama kataimaki mutane uku a rayuwarka,suma kuma kace su taimakawa wasu ukun,yace insha Allah,sannan mai mashi yace yaja suka tafi. Maryam tana tafya tana tuanin mahaifin su rashida k'awarta,shima wanine ya bugeshi da mota amma sam yak'i tsayawa wanda hakan shine sanadiyan rasuwanshi dayake uazo da k'aran kwana. Hajiya iya tana zaune a palonta tanata zubda hawaye ita kad'ai,tana cewa yah Allah ka yafemin da irin wannan zalinci da son zuciya irin nawa,Allah ka bani mafita akan wannan abi dana aikata tun kafin inbar duniya. Lokaci yata ta tafiya yau azimi saira sati, bayin Allah sunata raba abinci wa talakawa, manosh da abokansa suka had'a kayan abinci sosai buhu sugar shinkafa gero gyad'a da dai sairansu suka raba a jimeta da gidan marayu sannan suka aika da sauran wa gidajen surikansu. Su kuwa 'yan matan sayayya na musamman suka musu na kayan azumi. Azumi saura 3days uncle ibrahim ya dawo, murna agun yara ba'a magana, shima yayi kewarsu sosai nan dai akaita ihun da tsalen dawowansa. Ibrahim mutum ne mai kirki ga hankali da nutsuwa bafulatanine baida hanke sosai amma kyakkyawane. Suna kama sak da albdallah,rashine kawai tayi kama da mamansu amma sukama babansu marigayi suka d'auko. Lokacin maryam tana gidansu rashida ita da samira,dan haka suka fito sukaje gunshi suna mishi sannanu da dawowa. Kallonsu yakeyi cike da kewarsu ya e sannunku na sameku lfy,sukace lfy lau sannan suka k'arb'i kayansa suka wuce mishi dashi gida. Bayan isha ibrahim yazo gidan su maryam kamar yadda ya saba. A tsakar gida maryam ta shinfid'a masa taburma,bayan sun gaisa da mamane yana zaune suka gaisa da maryam suna ta hira dai daga nan mama ta wuce d'aki. Ibrahim yace ya bayan rabuwa,tace alhamdulillah gaskya munyi kewarka sosai ,yace to ai nima haka kuma alhamdulillah yanzu kam na kammala se muka aiki ayita tayamu da addu'a. Maryam tace to Allah ya baka mai albarka yace ameen result naku shuru ko,tace eh wlh har yanzu,yace naji ana cewa soon zai fita,tace to Allah yasa muga alkhairi,yace ameen ya fama da yara,tace bakomai aina saba yanzu suma kullum sesun tambayi yaushe zaka dawo,yace eyyah ai sunce tunda na dawo yanzu to auntyn yara seta huta ka karb'eta,murmushi maryam tayi tace hakadai suke fad'a tun kafin ka dawo. Yace hakan za'ayi ai dan kina k'ok'ari abubuwan suna miki yawa aunty,tace wlh bakomai har yanzu ni aunty ce,yace eh mana har gobema,dariya tayi shima haka sunata hira har isha suna jiyo miryan abdallah mai dad'i yana kiran sallah,se yace bari na tafi seda safe ki gayawa mama na tafi,yace to a huta gajiya,yace tonagode sannan ya tafi. Lubna kuwa abun duniya ya dameta taji ance bayan sallah za'aje tambayan aurensu manosh,gashi tasan maryam ce yarinyar da manosh yake so. Hankalinta a tashe tuni ta dena kiran maryam bayan zagi kala kala da takeyiwa maryam, harta hakura ta dena dan sam maryam bata kulata. Wasu 'yan iskan maza y'an iska ta nemo y'an shaye shaye tace tanaso su sace maryam sannan su watsa mata *acid* a fiskanta ta biyasu kud'i sosai tare da basu address d'in maryam da kuma nuna musu hotonta,amma tace su bari se bayan azumi ma'a dai bayan sallah da kamar sati d'ati d'aya sesu d'auketa. Yau aka d'aiki azimi maryam tana gun hajiya iya suna hira, hajiya tace maryam kiyita sani a addu'a kinji,maryam tace insha Allah hajiya. Azumi yanata tfy,maryam sunayin abincin masallaci ita da mahaifiyarta sannan wasu sukan shiga dan su tayasu aiki dab magrib se'a fita dashi kofar masallaci ayita rabawa bayin Allah irin qanda gwamnati take rarraba a unguwannin nan. [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd 21-22 Azumi yanata tafiya,abdallah se samun kayan sallah yakeyi agun jama'a. Dan shine mai kiran sallah a masallaci gashi da shiga rai. Ranan manosh manosh da marwan sunje girei se marwan yace aboki abdallah zoka gaisa da abokina wanda zai auri auntyn yara. Abdallah yazo suka gaisa cikin fara'a yace dama kaine kake neman auntynah,manosh yace eh nine,abdallah yace to Allah ka rik'eta da amana karka cutar da ita dan Allah dan ance soja suna dukan matansu. Dariya sosai su manosh sukayi sannanya rik'o hannun abdallah yace har abada abdallah,karka sa ranni zan wulak'anta maryam domin ina k'aunarta fiye da yadda nake k'aunar kaika kuma wlh bacika baki nake makaba kaji? Abdallah yace alhamdulillah naji dad'i sosai Allah ya tabbatar muku da alkhairi,sukace ameen,sannan yace auntyn yara ta aikeni bari aje aje na dawo,sukace to seka dawo sannan ya tafi. Abdallah yaje gunda uncle ibrahim yake da friends nashi yamusu slm tare da gaisuwa sannan yace yah ibrahim gurinka nazo an aikoni,ibrahim yace to ina jinka,se kuma abdallan yayi shuru,ganin shurunne ibrahim ya mik'e yace to muje gefe ka kaya mun. Bayan sun koma gefene abdallah yace yah ibrahim auntyn yara ce ta aikoni gunka,dad'i sosai ibrahim yaji da akace auntyn yara yana sonji menene aikan. Abdallah yace tace wai tayita kiran number'nka amma yak'i tafiya,wai inzo ince maka tayi bak'i kuma tana so gu gaisa dasu. Ibrahim yace bak'i wani iri maza ko mata?abdallah yace maza wanda yake nemanta da kuma aunty rashida. K'irjin ibrahim ya buga sosai yace abdallah dama zance danaji da gaskene kenan akan auntyn yara? Abdallah yace eh yaya hakane
Chapter 7 · 0% Book details