Sashe 43
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
manish da kuma mahaifiyarsa agun dad d'in marwan sunje dubashi ana zaune ana hira se sukaji sallaman marwan. Wani ajiyar zuciya dad d'in marwan ya sauke lokacin dayaga d'an nasa ya rame sosai kamar wanda yayi ciwo. Bayan yayi musu sallamane ya wuce gunda mahaifinsa yake kwance ya tsuguna tare da rik'e hannunsa yace sannu dad,ya jikinnaka,dan Allah dad kayi hakuri karka ce komai,kawai nayi abinda nake tunanin shine mafita agareni shiyasa,amma dan Allah kayafemin? Dad nashi ya shafi kansa yace bazance komaiba marwan,domin bakayi laifiba hakan da kayi shine daidai domin na fahimceka d'ana Allah ya maka albarka,sanyi marwan yaji a ranshi yayi nurmushi tare da cewa ameeen dad nagode,toya jikinka? Dad yace nayi sauki ai yanzu dana ganka kusa dani,ko kuma ince tun dawowan abokinka na fara samun lfy,abokanka sunyi k'okari dani sosai sedai muce Allah ya saka musu da alkhairi Allah ya masu masu musu suma, aka amsa da ameen. Amma zuciyar marwan tana nanata abinda mahaifinsa ya fad'a wai tun bayan dawowan abokinka,yace dad prince ya dawone? Yace eh ya dawo yau kwanansa d'aya kenan da dawowa. Tsantsan farinciki marwan baisan sanda ya rungume mahaifinsaba yana cewa Allah sarki abokina Alhamdulillah,ina yake dad? Dad d'in manosh yace suna can gida. Sallamar dr muh'd ne ya katse su,shima ya tsaya kallon marwan cikin mamaki yace dama zaka dawo ashe? To ai ka koma domin bana bukatar dawowanka. Marwan yace haba dr kuyi min uzuri dan Allah,muh'd ya mik'awa dad maganinsa sannan ya kalli marwan yace uzurifa kace? Ai babu wani sauran uzuri kuma domin kanuna mana cewa bamuda muhimmanci agurinka har zaka iya mana haka. Dad d'in manosh yace yanzu dai tunda ya dawo kuma yasan yayi laifi toku mishi uzuri. Muh'd yace dad gaskya semunyi zama danba haka kukeba run yaranta amma gashi alokaci d'aya ya canja mana tsarinmu dan haka dole semunyi zama shima yasan hakan. Babu wanda ya sake cewa komai haka marwan ya gaidasu dukkansu sannan ya nemi gafaran mahaifiyarsa sannan suka fito shida muh'd inda suka wuce office nashi yana cewa waime hakane muh'd? Amma ai a tunanina ban d'auka zakumin hakaba tunda kunji dalilin yin hakan nawa. Muh'd yace sosai munji dalilinka amma kuma ai abinda kayi bashine mafitaba kuma kanuna mana cewa mu abin baishafemuba kenan sekai kad'ai. Marwan zaiyi magana muh'd yace nazo bawa dad maganinsane dan haka zan koma idan mun had'u dukkanmu semuyi magana. Marwan yace shikenan muje ka saukeni agida,tare suka fito suka shiga motan muh'd amma babu wanda yace komai har suka iso gidan marwan ya fita shima muh'd ya wuce gidansu manosh inda suketa hira. Bayan marwan yayi wanka yaci abincine suka sake fitowa shida rash suka kawowa dad abinci. Se marwan yace zaibar rash a hospital d'in bariyaje gunsu manosh ya dawo. Suna hira amma hankalin manosh gabad'aya yana india saboda har yanzu su yah ibrahim basu kira kowaba. Slm marwan ya fad'a tare da k'arasawa ciki inda suka amsa salamarsa suna kallonshi cikin mamaki dan sam muh'd baigayamusu cewa marwan ya dawoba. Abdallah yanadaga jijin babanshi yace oyoyo uncle marwan sannu da dawowa,marwan ya k'arasa gun manosh cike da murmushi manosh ya mik'e suka rungume juna suna farinciki abdallah se kallonsu yakeyi yace daddy dama manyama suna rungumar junansune? Dariya sosai manosh yayi tare da sake marwan yace sosaima kuwa musamman idan sun dad'e basu had'uba. Marwanma dariya yakeyi sannan ya d'aga abdallah sama yace ina alfiya? Yace tayi bacci tun d'azu ko sallan isha batayiba,marwan yace haba to idan ta tashi gobe ka tabbata tayi gashi? Abdallah yace insha Allah zatayi,marwan ya ajiyeshi yace jeka ka kawo min abin tab'awa kaji? Da sauri abdallah ya fita sannan ya mik'awa sauran hannu suka gaisa harda muh'd. Yace koku had'a fiskokinku koku sake dai ina cikin farin cikin dawowar prince,saboda haka bazan biye mukuba sannan kuyi hakuri kumin uzuri akan abinda nayi muku... babu wanda yace dashi komai acikinsu,se manosh da yake binsu muh'd da kallo dan yaga duk sunyi shuru suna danna wayoyinsu. Murmushi manosh yayi yace waito me kuma hakan magana yake muku fa? Muhsin yace dan Allah malam babu ruwanka aciki kawai kayi shuru,manosh yace kamar inyi shuru bayan kunyi shuru kowannenku yana danna waya hakuri yakebaku tunda yasan yayi laifi aise ku mishi uzuri. Muh'd yace idan kaine hakan ya faru dakai mezakayi a wannan lokacin dakasan komai? Manosh yace gaskya kusan yadda marwan yayi nima hakan zanyi,amma dai bazaiyu ace na b'oye nukuba tunda mun zama d'aya babu wata boyayya a tsakaninmu ai koma akan menene,amma pls ubar maganan haka ya isa kawai marwan baka kyautaba da abinda kamusu semu kiyaye gaba inaga maganan ta k'are. Muhsin yace bata k'areba prince wannan wulak'ancine ai amintakarmu yazama bayi da ma'ana kenan wai har ace bamusan inda d'aya daga cikinnu yakeba wannan abun kunyane wlh laifikam kayi "dude" kawai dai abar maganar haka nan. Marwan yace nasan nayi laifin ai shiyasa nake so mufahimci juna ai,majid ya mik'e yace to nidai prince kacewa miher ta taimaka tazo mu tafi dan yau bazan barta ta kwana agidaba jiyama da kyar nayi bacci wlh. Muh'd yace kaikuma ana magana ka tashi,majid yace eh ai maganan naku bata shafenibane shiyasa domin nibamma san waya shigo nanba. Bugu manosh yakaiwa majid ta yadda ya isa hargun marwan harya bugeshi,marwan yace me hakane wai baka ganine? Majid yace eh aikasan ni makahone,dariya manosh da marwan sukasa inda majid yakaiwa marwan duka yace wlh sa'a kaci d'an iska albarkacin dad baida lfyane kawai zamu d'agama kafa dabadan hakaba wlh dase kaci kwakwa-kwakwa kamar yadda mukayiwa captain a baya... Hahahaha sukasa dariya dukkansu,manosh yace ai wlh kune kuka dena kulani amma muna waya da marwan ab'oye lokacin. Muhsin yana dariya yana kallon marwan yace to ashe kaine d'an iskan daka karya mana doka tun'a wancan lokacinma bamusaniba,dariya sukeyiwa junansu sosai inda inda manosh yake kallon muh'd yace kodai in fad'i nakane abokina? Muh'd yace ohonka idanka tonama ai kanka ka tonawa... hakadai suketa hira cikin hara da dariya. Can se wayar marwan ta fara ringing,kodaya duba numbern waje yagani hakan yasa yayi saurin amsawa yace hello,muryan yah ibrahim yaji yace marwan,marwan yace yane mutanen india kun isa lfy? Yace lfy lau wlh yawanci numbernku baya tfy kaima da kyar na sameka wlh ka dawo daga tfyarnaka ne? Marwan yace eh wlh yau na dawo yasu mama ya aunty da lubna? Ibrahim yace suna lfy lau wlh auntynema bata jin dad'i wlh zazzab'i taketayi tunda muka bar nigeria wlh. Subhanallah ya jikinnata to? Yace da sauki inasu muh'd,yace kowa lfy kun samu masauki mai kyau ko? Yah ibrahim yace alhamdulillah wlh,manosh yace banishi mugaisa pls? Ibrahim yaji kamar muryan manosh,shi kuwa marwan baisan cewa babu wanda sukayi waya da 'yan india ba shine mutum na farko. Manosh ya karb'i wayan yace hello yah ibrahim,ibrahim ya kira sunanshi cikin mamaki yace manosh dakai nake magane? Manosh yayi mirmushi yace nine wlh ya kun isa lfy ina apple d'ina? Yah ibrahim yaji dad'in aranshi yace Alhamdulillah bari na kaimata kozata ji sauk'i gaskya nayi farincikin jinka captain Allah abin godia. Shima manosh dad'in yajin a ransa mara misaltuwa yanata so yaji muryan apple nashi,yah ibrahim yayi sallama a d'akin da aunty take kwance lubna ko sallah ko takeyi mama da baba kuwa suna can d'akinsu ko kuma ince masaukinsu yah ibrahim lfy kaketa sauri haka? Yace barima in had'a da gudu aunty kashi zakuyi magana,batare datasan wayeba ta karb'a dan atunaninta ma dad d'in manosh ne. "Tace Assalamu alaikum" wani sautin saukan numfashi taji"sannan akace "wa'alaikumus salam _my one nd only apple_. Wayan ta cire daga kunnenta tana karewa wayan kallo sannan ta sake mayarwa kunnenta tace peach...? Sautin sauk'an kiss kawai taji akunnenta har cikin ranta taji wani ni'ima mara misaltuwa take ta fara hawayen farin ciki tace peach kaine kodai mafarki nakeyi? Manosh ya mik'e daga inda ya zauna kusada marwan ya shige d'akinsa su kuwa sebinshi da kallo sukeyi suna taya abokinsu murnan jin muryan matarsa... [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas 97-98 "Peach yanaji kayi shuru?" "Apple how are u" "Ya jikinki my luv?" Alhamdulillah peach kaine dagaske?" "Nine apple,Allah ya dawo dani tare da taimakon addu'oinku agareni." "Murmushi tayi tace yaushe zakazo india peach,ina shaik'in son ganinka my luv" Karki damu *aunt* zanzo insha Allah kema kinsan nafiki son inganki ko?" Dan haka inaso ki kwantar da hankalinki yanzu haka k'ok'arin da naketayi kenan wlh. Dariya tayi maicike dajin dad'i tace kai Alhamdulillah Allah abungodiya peach nayi matuk'ar farinciki wlh Allah,ina fata dai kana lfy?" "Dariya yayi tare da cewa i'm fine aunt kikwantar da hankalinki lfyata lau jealousynah." Ya k'are maganar yana mata dariya Itama dariyar tayi tace ka fara koh? "Apple yasu mama da fatan duk kuna lfy,ina kuma sisterna lubna?" Shuru tayi nad'an lokaci sannan tace kowa lfya sis lubna ma tanata murnan dawowarka gata tadameni waisedai in bata wayan,amma bazan bataba dan nima bangaji dajinkaba tukun." "Manosh yayi dariya yace toki gaishesu,sannan kicewa sis lubna kawai nagaisheta yanzu bana son jin kowa se apple d'ina,dan haka tayi hakiri senazo magaisa." Dad'i aunty taji,farin ciki ya kasa k'auracewa fiskanta tama mance da yah ibrahim yana tsaye agefe se shagab'a da kalaman soyayya kala-kala suke jefan junansu dashi abin ban sha'awa... Marwan yana duba account nashi seyaga 0.00 "Yace lallai captain wato seda ka tabbatar wayan ta gama amfani kafin ka dawomin da ita koh?" Manosh yace sorry luv ne yayi nisa nama d'auka ko muna tarene ashe awaya muke. Dariya suka sa dukkansu muhsin yace shiyasa naga kamar ma seda kayi wanka kafin ka fito. Hahhhhhh! "Washe gari aka sallami dad d'in marwan dayake ya samu lfy. Gida aka wuce dashi inda mahaifin manosh da sauran 'yan'uwa suka bashi hakuri akan ya maida matarsa wato hajiya khadija mahaifiyar marwan "Cikin saukin kai kuwa ya maidata inda marwan yaketa murna." Sedai hajiya iya tana kwance ba lfy,tunda abun ya faru itama take jinya kad'an kad'an dan tak'i barima asan bata da lfyan se yanzu da ciwon yacigaba sosai. Hakadai aketa faman jinya dan dad d'in marwan ya d'aukota daga girei ya dawo da ita gidansa inda take samun kyakkyawan kulawa daga gun mum d'in marwan. "Manosh kuwa anata kan masa magani akan abinda ya sameshi gameda lfyanjikinsa akan abinda shukrah