← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 45

Sashe 20

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk wanda ya ganta zesan akwai wani abu. Sun isa palo inda taga mahaifiyarta na zaune tana kallo,sallamarsu shiya juyo da fiskanta gunsu... Maryam tace hajiya khadeeja,hajiya khadeeja tace maryam tare da mik'ewa ta rungumeta sema a lokacin ta lura da lubna a gefe data tsaya tana kallonsu. Mum d'in lubna ta saki maryam tare da k'are musu kallo dukkansu,suma kallonta sukeyi dan sun tsorata sosai da irin kallon da take musu. Maryam tace hajiya dama lubna 'yarkice,kuma kece mum d'in marwan? Hajiya jikinta a sanyaye tace eh nice dama kunsan junane keda lubna? Tace a'a ta had'u da tsautsayine machine ne ya bugeta ni kuma ina sayya lokacin senaji ta fad'o ta jikina,to dai naga ta k'asa mik'ewa shine na rakota gida. Mum d'in lubna tace subhanalillah tare da zuwa gun lubna tanata dudduba jikinta tana mata sannu to Allah ya kare na gaba yanzu inane yake miki ciwo? Lubna tace k'afatace mum da k'yar nake takawa,tace sannu ai dole muje a duba miki kafan agun masu duban kafa koma kinyi targad'e waya sani. Shuru lubna tayi yayinda mum ta zaunar da ita tace sannu maryam ki zauna bari in kawo miki abun sha,ashe kuma haka ya faru,maryam tace eh wlh,mum tace to Allah ya kare na gaba Allah ya toni asirinsu,maryam ta kalli lubna tace ameen sannan mum ta wuce. Maryam tace nizan tafi idan kinga period naki seki gaya min,koma dai me ake ciki zamuyi waya dan yanzu kin zama k'awata lubna,murmushi tayi tace nagode maryam kin zama kamar 'yar'uwata na jini wlh bazan tab'a mantawa dakeba,wlh a tsorace nake har yanzu,maryam tace ki dena tsoro mudai jira tukunna nayi miki alk'awarin zanyita tayaki da addu'a Allah ya bamu mafita akan wannan lamarin,lubna tace ameen. Sega mum ta shigo da abin tab'awa kad'an maryam taci tace nizan tafi hajiya nagode sosai da hidimar da kikayi a gidanmu,mum tace bakomai maryam kigaida mutanen gidan dukka,tace zasuji,mum tace bari insa driver ya maidake,tace a'a wlh dasu yah ibrahim mukazo idan mun gama zaidawo ya d'aukemu yanzu kasuwan zan koma,tace eh to bari drivern ya maidake kasuwan,tace to hajiya nagode sannan ta kalli lubna tace to Allah ya sauwaka ya kiyaye nagaba,lubna tace ameen nagode. Mum d'in lubna ta rakata hargun mota sannan suka tafi. Hankalin mum d'in lubna a tashe tare da tunani mai zurfi a cikin ranta ta shige gun lubna tana mata sannu. Maryam se taji dad'i sosai a ranta tace dama hajiyace mahaifiyar marwan da lubna,gaskya sunyi sa'an iyaye domin hajiya khadija macece mai kirki sosai sannan tason maryam ita. Wayan maryam ne ya far k'ara ta duba taga samira ce,tace hello samira kuyi hakuri ganinan na kusa isowa,samira tace okey. Bayan ta ajiyene call d'in manosh ya shigo ta d'auka tare dayin sallama,ya amsa sannan yace Alhamdulillah apple mun kama saddam,k'irjinta ya buga sosai tace haba peach,yace wlh kuwa yana can gurin horo,tace tokun saki wannan mutumin,yace karki damu bazan cutar dashiba,gobe zan sakeshi insah Allah,tace to nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,yace ameen apple kin gama sayayyanne? Tace eh nagama amma yah ibrahimma ya shigo jimetan kawai zamu koma tare,yace ok toshikenan ki gaishesu senazo kinji,tace yaushe zakazo,yace sedai zuwa gobe insha Allah,tace har gobe kwana d'aya fa kenan ban gankaba,dad'i yaji data nuna damuwarta agareshi,yace kinaso inzone,tace eh amma bakomai yau da goben duk d'ayane,yace to lnagode zanzo gobe da safe kinji,tace Allah ya kaimu,yace ameen aunt ki gayamin wani abu,tace *i luv u* tare da katse wayar dan kunya dataji. Dariya yaketayi tare da sauke wani ajiyar zuciya yace *i luv u 2 apple* yusuf yace tofa ai bata jikaba sedai ka sake kiranta,manosh yayi murmushi yace waya gayamaka taji mana,dariya sukayi tare da wucewa.. Maryam tayiwa drivern godiya ta tafi gunsu rash tayi d'an sayayya kad'an sannan suka kira yah ibrahim yazo suka wuce gida a motar da manosh ya sayawa maryam. Kowa gida ya wuce maryam taje ta watsa ruwa tare da alwala tayi sallah tayi addu'oi sosai. Abdallah ne ya shigo sunata hira da auntyn shi har magrif sannan ya tafi masallaci. Anata zuwa yiwa maryam da iyayenta barka harda malamai manya. Koda yaushe suna waya da lubna tana tambayarta akan shiga ruwa zafi,tace eh tana shiga sosai dan yanzu kamma tfya normal takeyi. Dad'i sosai maryam taji kuma sam bata gayawa kowa komai akan lubna,hakama shi saddam duk azabar da ake gana mishi yace shine kawai yayi ra'ayin sace maryam wabu wanda ya sashi,hakan yasa suka kaishi gidan yari aka kulleshi acan,shi kuwa d'ayan tuni an sakeshi har gidansu maryam yazo yayita mata godiya tare da tabbatar mata da cewa daga yau ya zama mutumin kirki ya dena d'aukan abun tsakaninshi da mutane sedai taimako. Dad'i maryam taji sosai tare dayiwa Allah godiya... *** Bayan wata d'aya lubna taga period nata yazo kamar dai yadda ta saba. Murna sosai tayi tare dayiwa Allah godiya sannan ta kira maryam ta gaya mata komai, murna sosai itama tayi tace shikenan lubna nagode,lubna tace nice da godiya damuwa d'ayane yanzu shine idan nayi aure,maryam tace inga kawai ki gayawa mahaifiyarki danki samu mafita,lubna tace sam bazata fad'aba,maryam tace to shikenan duk yadda ake ciki zamuyi waya se'anjuma. Maryam tana kwance a d'akinta wajen 10:pm seta kira yah ibrahim a waya,yayi mamakin ganin kiranta amma seya d'auka yace hello aunty lfy dai koh? Tace lfy lau kayi hakuri na tasheka,yace bakomai akwai wani abune? Tace dama shawara nake nema agunka akan wani abu daya dameni wanda bazan iya gayawa koda mahaifiyata bane bare kuma wasu amma haka kawai naji zuciyata ta raya min cewa na gaya maka yah ibrahim. Yace to aunty ina sauraronki,tace yah ibrahim wata baiwar Allah ne ta had'u da jarabawa kuma se muka had'u da ita a wannan lokacin da abun ya sameta. Nan dai maryam ta kwashe lbrn da lubna ta bata tun farkon had'uwansu da saddam har zuwa fyad'en daya mata ta gaya mishi tas sedai bata gayami ko wacece yarinyarba kuma bata gayamishi abunda lubna da saddam suka mataba kawai dai lbrn shak'uwar saddam da lubna ta bashi batare data gaya mishi sunayensuba. Shuru ibrahim yayi dan yama rasa mezaice,yace amma meyasa tak'i sanar da iyayenta,aunty wannan babban maganace wanda dole se manyanta sunsan dashi,dan haka kigaya mata ta cire wani tsoro a ranta ta sanar da iyayenta tunda ba laifinta bane wannan shine kawai shawaran da zakibata. Maryam tace yah ibrahim wlh nayi iyakan k'ok'arina dan in fahimtar da ita amma seta nunamin cewa garata gudu koma ta kashe kanta akan ta sanar dasu. Yah ibrahim yace aunty wanene wannan yarinyar? Tace kayi hakuri yah ibrahim bazan iya gaya makaba domin nayi mata alk'arin zan b'oye sirrinta. Shuru yayi yace to aunty gaskya shawaran da zan iya bata kenan dan shine kad'ai mafita agareta. Maryam tayi shuru tace yah ibrahim zan gayamaka kowacece amma inhar zaka taimaketa,yace wace irin taimako kuma ni zanyi mata aunty? Maryam ta gyara murya tace yah ibrahim taimakon da nakeso kamin shine ka amince zaka aureta. Shuru yayi tare dayin murmushi yace in auretafa kikace aunty? Tace kwarai yah ibrahim,a rayuwata babu wanda nake k'auna da burin ya zamanto mijina irinka yah ibrahim,jira nakeyi ka dawo daga bautar k'asa se'in sanar dasu baba, amma muna namu Allah yana nashi segashi su manosh sunje gun baba batare dana saniba sun nemi izini kuma baba ya amince musu,hakan yasa na amincewa manosh na kuma cigaba da addu'a wanda hakan yasa naji ina son manosh har cikin raina kai kuwa na maka matsayin " *soulmate*" d'ina, yah ibrahim wlh kaina fara so a raina kuma har gobe kai *soulmate* d'inane... Maryam bata k'arasa maganaba ta fara kwallah,yah ibrahim kuwa wani zazzafar k'aunarta yake shigansa,yace aunty kidena pls ya isa haka kinji? Tace yah ibrahim dan Allah ka amincewa buk'atata wlh yarinyar tanada hankali gata fara ce kyakkyawace sosai bugu da k'ari zaka ilmartar da ita sosai tafannin addininmu. Yace shikenan aunty na amince koda mummunace ita tunda dai ke kika zab'amin ita na yarda zan aureta kidena kuka kinji aunty, "i will do anything just for you aunty" shikenan? Bazan iya misalta muku farincikin da maryam ta shigaba,bata san lokacin datace "i love you so much uncle" dad'i yaji yace to wacece ita yarinyar? Tace sunanta lubna k'anwar marwan ne wanda zai auri rashida. Mamaki sosai yayi yace to shikenan ki kwanta kiyi bacci zanzo da safe kinji,tace to nagode sosai seda safe... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas *dedicated to mace tagari* 47-48 Washe gari da safe yah ibrahim yaje suka gaisa da mama sannan sukayi hira sosai da aunty harta bashi number lubna dan dama tun a jiyan ta sanar da lubna komai,dukda dai lubna taji kunya sosai,amma setaga koba komai ai asirinta zai rufu tunda shi yah ibrahim yasan halin da ake ciki kuma ya amince zai aureta a hakan. Lokaci yanata tfy,ibrahim da lubna suna waya sosai dan ta turo mishi da pic nata ta whatsapp shima kuma ya tura mata amma bai tab'a zuwa gidansuba. Koda yaga pic d'in lubna mamaki sosai yasha dan kawai seyaji k'aunarta na k'aruwa a cikin ranshi tare da addi'an da yakeyi akanta. Itma lubna ta yaba sosai dan yah ibrahim ba irin mazan da mata zasu k'ishi bane. Hakanan suketa soyayyarsu,wanda har abdallah yasan lubna suna gaisawa sosai. Ita kiwa maryam seta tsinci kanta cikin farin ciki da kwanciyan hankali mara misaltuwa. Ranan taje jimeta aike tana cikin keke nape seta hango manosh tsaye da wata budurwa wanda sam bataga fiskartaba saboda yana tsayene dab gabanta. Kuma ta tabbatar da cewa manosh ne dan taga motarshi sannan kuma ga marwan a gefe yana tsaye rai abace,se taga manosh ya bud'ewa budurwa kofar motarshi na baya harta shiga se kuma ta sake fitowa ya bud'e mata gaba ta shiga. Maryam ta kira number manosh dan tabbatarwa,ai kuwa seta ya d'auka tare da cewa hello,tace ya kake,yace lfy lau zan kiraki anjuma kinji,tace meyasa kana wani abune? Yace eh kiyi hakuri zan kira kinji,tace ok sannan ta kashe wayar tanata binsu da kallo setaga shima ya shiga mazaunin driver yaja suka tafi yayinda marwan yake tsaye agun rai a b'ace. Hankalin maryam ta tashi sosai ta rasa meke mata dad'i,tace wato dama da manosh yake cemin mata 2 ko
Chapter 20 · 0% Book details