Sashe 11
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dedicated 2 *billy tabacco* 29-30 Maryam tana komawa gida ta wuce d'akinta dama mamanta bata dawoba,ta kwanta tana kuka sakamakon tunawa da kalmomin rash agare. Dan bata tab'a zaton cewa wani abu zai shiga tsakaninsuba. Wayartace ta fara ringing kodata duba se taga manosh ne,haka tak'i d'aunkan call d'n nashi har sau 3. Bayan azahar ya sake kiranta seta d'auka hello,yace apple ina kiga shiga haka,tace sorry bacci nakeyi dan kaina da yake ciwo,ya kake yasu mama,yace eyyah sorry apple ya jikin naki,tace da sauki sosai,yace zanzo da yamma kinji,tace to nagode sekazo. Dab la'asar manosh yazo abdallah yana kiran sallah,alwala yayi yayi sallah sannan suka zauna hira da abdallah inda yake tambayarshi ina marwan,makosh yace yana gun aiki,nan dai sukai ta hiransu manosh se dariya yakeyi seda aka watse sannan maryam ta fito babu ko fara'a a fiskanta. Ta k'arasa da sallama,suka amsa sannan abdallah yace auntyn yara yanaganki haka babu ko murmushi, tace bakomai abdallah banajin dad'ine,yace sannu Allah ya baki lfy,tace ameen sannan ya kalli manosh yace toni zan tafi seka sake zuwa,manosh yace to bari na baka sako,yace to,sannan manosh ya bud'e motarshi ya fito da leda da gani kayayyaki ne a ciki yan kanti ya mik'awa abdallah. Abdallah ya karb'a yace wazan kaiwa?manosh yace nakane na baka kyauta,godiya sosai abdallah yayi yace auntyn yara ki tayani godiya,mirmushi tayi tace mungode Allah ya saka da alkhairi suka amsa da ameen sannan abdallah ya tafi. Maryam tace ko zamu shiga cikin gidane,yace yau kuma,tace eh ko kuma muje zaure in shinfid'a maka taburma wlh bana jin dad'ine,manosh yace amma kinje hospital ne,tace banjeba dan ko su mama basu saniba,yace tomeyasa,tace babu komai,kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa sannan ya d'auki wayarsa ya kira muh'd ya gaya masa cewa inda hali yazo girei ya duba apple nashi sannan ya katse wayar tare da cewa to muje zauren karki fad'i min anan,murmushi tayi sannan ta wuce gaba shi kuwa ya fito da sayayyan fruits daya mata da sauran abubuwan kwad'ayi yabi bayanta lokacin taje d'auko taburma da karamin carpet ta shinfid'a mishi carpet din ita kuwa ta zauna a taburman. Sam tak'i kallon manosh dukda dai tana son ganinsa dan yau red top ne a jikinsa da black jeans se kamshi yakeyi. Shi kuwa kallonta yakeyi sosai,can dai tace meyasa ka kira muh'd ai naaha magani,shuru yayi kamar baijitaba yana ci gaba da kallonta,da taga yayi shuru seta d'ago da kai tana kallonshi suna kallon juna,murmushi tayi tace nika dena min irin wannan kallon bana so,yace tobase ki hananiba,mik'ewa tayi taje ta yanko mishi kankanan daya kawo mata dasu apple ga greves dadai sauransu tayi jerensu a tirai kamar fiskan manosh sannan taje ta ajiye mishi ta yadda zai gane fiskanshi tayi drawing. Mamaki sosai yayi yanata kallon drawing d'in danya burgeshi sosai harya bashi sha'awan ci,amma kuma bayaso ya b'ata drawing d'in,kawai setaga ya d'ako wayanshi yanata d'aukan pic din friut d'in. Bayan ya gamane yace fiskan waye kenan wannan,tace na wanda zaisha,dariya yayi wanda ya k'ara mata sonshi azuciyarta,yace haka fiskana yake kenan? Tace eh amma dai fiskanka yafi wannan kyawun gani. Dad'i sosai yaji amma baice mata komaiba,wayansane ya fara ringing ya d'auka ok bari na fito. Kallonta yayi yace bari muh'd ya shigo kuma ki tabbata kin gayamishi abinda yake damunki kinji ko, mamaki sosai tayi har mh'd yazo kenan,tace to sanna ya fita suka shigo tare. Muh'd yayi sallama ta amsa sannan suka zauna tace ina wuni,yace lfy lau aunty ya jiki ashe bakiji dad'i ba,tace eh amma da sauki,manosh yace ba wani sauki wlh dairewa kawai takeyi danko a gida basu saniba. Muh'd yace haba aunty pls kidena wasa da rashin lfyanki karki sawa kanki ciwo kinji,mirmushi tayi tace kainane fa dama kuma nasha paracetamol,manosh yace towayace kisha? Murmushi tayi tare da kallonshi cikin zolaya sannan ta taahi ta wuce gida. Manosh yanata binta da kallo,muh'd yace haba prince irin wannan kallo haka,manosh yace wlh bata da lfy daga ganinta daurewa kawai takeyi pls ka gwadata sosai. Muh'd yace "calm down dude" zata samu lfy insha Allah. Faro mai sanyi ta kawo musu sannan ta zauna,muh'd yace mungode amma wannan fiskan yamin kyau kamar fiskana. Dariya sukayi dukkansu,manosh yace a'a kaje can samira ta maka naka wannan fiskan nawane kuma bazaka ciba,dariya mh'd yayi tare da d'aukan inibi d'aya yasa a bakinsa yace shikenan zanen ya b'aci. Manosh yace gaskya baka kyautaba,memakon ka jira in fara sha kafin kasha,mikewa maryam tayi ta sake d'auko inibi tazo ta mayar inda mh'd ya cire sannan tace shikenan magana ya k'are. Dariya sukayi sannan manosh ya far sha cikin nutsuwa take satar kallonshi,dan bai tab'a cin wani abu suna tareba se yau. Muh'd yace nagode aunty gaskya abin ya burgeni nima zance samira ta dinga min. Manosh yace copy copy,murmushi sukayi sanna muh'd yace aunty meke damunki ne? Tace wlh ciwon kaine kawai,k'irjinta yana mata ciwo amma sam tana jin kunyan cewa harda k'irjinta. Muh'd yayita tambayoyinta tana bashi amsa sannan yace ok ina zuwa bari inje inzo,manosh yace akwai wani damuwane,yace no bakomai sena dawo sannan ya tafi. "Manosh yace kin tabbata abinda kike ji kenan?" "Tace eh kanta na kallon wani gefen" "Manosh yace apple bana so ki b'oyemin komai imma kina jin kunyan muh'd toki gayamin tunda baya nan" Maryam taga bazata iya b'oyewaba dan yadda take jin k'irjinta,setace da k'irjina yana min ciwo sosai. "Kallonta yakeyi cikin damuwa,dan yana lura da yanayinta yasan tana jin ciwo tadai k'i fad'ane kawai. "Sunanta ya kira a hankali yace apple? Kanta ta d'ago ta kalleshi har idonta yayi jah tace na'am tare da sunkuyar da kanta,yace se kuma inane yake miki ciwon? Tace shikenan....bata gama k'arasawaba taji cikinta ya kame kamar an soka mata wani abu,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un taketa nanatawa a zuciyarta. Manosh yace ya kikayi shuru,tace bakomai ina zuwa,bata jira mezaiceba ta mik'e ta wuce gida yana binta da kallo. Koda ta k'arasa gun mamanta ta wuce a d'aki ta cire doguwar himar nata ta fad'a kan gado tana cewa mama cikina ya kameni sosai yana min ciwo. Hankalin maman ya taahi sosai tayi kanta tana mata sannu tare da tofa mata addu'oi,tace bak'on ya tafine? Cikin jin ciwo take magana tare da kame cikinta tace basu tafiba suna zaure. Mama ta rasa yadda zatayi seta d'auki wayanta ta kira baban maryam ta gaya mishi komai,shima hankalinsa a tashe ya kira number yah ibrahim yace lallai yaje gida. Bada b'ata lokaciba yah ibrahim yazo a zaure sukaci karo da manosh. Su gaisa sannan yace ina maryam d'in? Manosh dabaisan komaiba yace ta shiga ciki,yah ibrahim yace kasan bata da lfy,yace eh na sani harma abokina ya dubata yanzu. Kan yah ibrahim ya d'aure seyace bari in shiga ciki dai dan yanzu babanta ya kirani yake cemin bata da lfy sosai cikinta na ciwo,a razane manosh ya mik'e yace ciki kuma,tacewa yanzu kenan ko,ibrahim yace eh sannan ya wuce ciki akabar manosh cikin damuwa sosai. Maryam se juyi takeyi tana addu'oi,har ya ibrahim yayi sallama,mama ta fito tace bari na fito da ita sannan ta koma tasawa maryam himar,shi kuwa yah ibrahim da sauri ya kira rash a waya yace tazo yanzunnan kuma cikin shiri. Bada b'ata lokaciba sega muhammad yazo sakamakon wayan da manosh yayi mishi. A tare sukazo da rash ta gaishesu sannan ta wuce ciki,maryam ta fara hangowa babu yadda take mama tana rik'e da ita ita maeyam bata iya ko mik'ewa tana sunkuye kuma rik'e da cikinta. Da sauri rash ta k'arasa ta riketa sosai tana mata sannu. Hankali mama a tashe tace gaskya zan biku muje asibitin nan dan hankalina zaifi kwanciya,waya tama baban maryam,sannan ibrahim yaje ya sanar dasu manosh komai,se manosh yaba ibrahim keyn motanshi yace ya d'auki su mama a ciki shi kuma zasu tafi da muh'd. Haka kuwa akayi su manosh suka tafi shida muh'd sannan ibrahim ya bud'e musu motar, da sauri abdallah yazo dan yadda yaga mama da rashida suna rik'e da auntyn yara,baice komaiba ya karasa yace lfy mama,tace wlh maryam ce ba lfy zamuje asibiti. Subhanallah nima zan biku, ibrahim yace shiga baga to,abdallah ya shige gaba su mama kuwa suna baya suka kama hanyan jimeta. Asibitin da muh'd yake aiki sukaje, aka wuce da ita kai tsaye. Ae a lokacinne manosh da muh'd suka gaida mama sannan muh'd ya wuce duba maryam. "Yana shiga rashida ta fito ta wuce gunsu mama,shi kuwa manosh kunya sosai ya kamashi gaahi k'ananan kayane a jikinshi,nan ya kira su majid cikin k'ank'anin lokaci suka zo dukkansu ukun. Marwan majid da muhsin sukaje suka gaida mama sannan suka gaisa da ibrahim. Rashida tana gefe ita da abdallah sannan marwan ya k'araso suka gaisa ranta a b'ace,amma seya d'auka kodan rashin lfyan maryam ne. Muh'd ya fito su manosh suka k'arasa da sauri donjin meke damunta harda yah ibrahim d'in da abdallah. Mama da rash kuwa suna tsaye a gefe guda. Muh'd yace *ulcer* kawai babu wani abu, kuma dole zata zauna a asibiti dan se'an k'ara mata ruwa har leda biyar. Sannan yayi mata allura yanzu dan har tayi bacci ma, ibrahim yace to mun gode kayi duk wani abunda ya dace pls yanzu medame ake buk'ata? Muh'd yace haba aiba komai wlh already nasa mata ruwan karka damu babu wani abu da ake buk'ata kudai tayamu da addu'a kawai. Godiya sosai ibrahim yayi sannan yace bari naje na sanar da mama dan hankalinta a tashe yake,muh'd yace muje inyi mata bayani. Bayani sosai muh'd yayiwa mama tare da cewa ta kwantar da hankalinta maryam zata samu lfy insha Allah. Godiya mama tayitayi sannan ya tafi gunsu manosh. Manosh yace zan iya ganinta,majid yace jeka ka kanga inba hakaba ai bazamu gane hankalinkaba ad'an lokaci kad'an kashi harka fita hayyacinka kamar ba sojaba, dariya sukayi baima kulasuba ya wuce d'akin tana kwance babu himar a jikinta se atamfa d'inkin doguwar riga daga sama ya bada shape amma k'asan a bud'e yake. Karon farko kenan da manosh yaga maryam babu himar ajikinta,mara ce sosai gata 'yar karama bata da jiki sam,amma k'irjinta a cike suke. Bai k'arasaba ya janyo k'ofar ya koma gunsu majid yace muje ko,dan muma mamanta damar shiga, haka sukayi musu sallama suka wuce yacewa ibrahim ya rik'e key din motarsa dan zirga