← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 45

Sashe 34

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

lubna da suke tsaye akanta tun ihunta na farko sune suka rik'eta sunta rarrashi dan sunji dukkan hiran maryam da manosh d'in. Yah ibrahim da babane suka shigo dajin muryan kukan maryam suna tambaya ko lfya? Nan lubna ta gaya musu komai,inda mamaki ya kamasu sosai. Yah ibrahim yayita kiran numbern amma sam baya shiga,maryam dai se kuka takeyi tana ta surutai kamar wanda ta zare tana cewa baba manosh yace in samu miji inyi aure yana nufin ya sakeni kenan baba,menayi mishi dazai min haka baba,nagaya mishi halin da nake ciki amma koya kula baba,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Lubna tana rungume da yarta itama kuka takeyi sosai,sam bata son ganin naryam cikin damuwa musamman ma datasan cewa yartace uwarsu d'aya. Hakadai ranan lubna bata koma gidantaba shi ibrahim d'inne ya koma saboda mahaifiyarsa ita kad'aice se mai musu girki. Daga baba har mama abin ya basu mamaki ganin yadda lubna takeyida maryam,bayan iyayenta sun rarrashetane se suka barsu a d'aki ita da lubna. Yah ibrahim kuwa tunani iri iri yakeyi a zuciyarshi,ga kuma damuwan halin dayaga maryam aciki yau ya tausaya mata sosai harma yake tunanin inama dashine ya aureta da shikenan maryam bata da damuwa sam,amma ina haka Allah yake tsarawa kowa rayauwarsa. Wayarsa ce tayi k'ara number manish ne,mamaki yayi sosai tare da d'auka da sauri yace slm,wslm yaji muryan manosh,basu gaisaba manosh yace na kirane don inji cewa dagaskene za'a fitar da aunt india? Ibrahim yace eh hakane,manosh yace to shikenan idan kun dawo ka sama mata miji ka aurar da ita dan nikam bazan dawo garekuba na zab'i in zauna anan domin ceton apple zan iya jure komai ibrahim shiyasa nafiso ace kaika auri aunt ba waniba pls ka auri aunt nasan zaka kula da ita kamarni. Ibrahim yace mekake fad'ane captain insha Allah zaka dawo kuma kadena sa ran cewa wani abu zai same aunty babu abinda zai sameta da yardan Allah zaka dawo kushi gaba da zamanku munata addu'a kuma shukrah setasha wahala wlh muguwa...tsawa maikyau ibrahim yaji akunnensa ana cewa wlh k'arya kake ibrahim wahala kam sedai auntyn yara amma badai niba,kuma zanga yadda zaku karb'o my manosh daga hannuna dama kai kad'aine mai taka min birki kuma ina so kasan cewa my manosh yabarku kenan har abada bazaku sake ganinshiba,sannan ka gayawa mahaifin maryam ya kiyayeni wlh su dena b'ata lokacinsu waisu suna so suga bayana to wlh idan bai dena shiga gonataba sena tozarta maryam d'in da kuke ji da ita. Hhhhh ibrahim yayi dariya yace dama ashe kece shukrah,kece kika ari muryan captain kike so ki b'ata tsakaninsu da aunty,to Allah ya tona asirinki muguwa,ina so kisan cewa aunty tafi k'arfinki shiyasa har yanzu kika kasa mata komai shine kika b'ullo mata tasan muryan mijinta koh,tota Allah ba takiba wannan kad'ai bai isheki shukrah,komai kikayi seya warware hakan yana nufin bazaki tab'a samun nasara akanmu bane kuma mahaifintama yafi k'arfinki hatta shi captain yafi karfinki wlh kawai dai jarabawace Allah ya sauko mishi dashi kuma insha Allah zamuci wannana jarabawan muzuba dake shukrah *QUR'AN* yana sama da komai acikin duniyan kuma dashi zamu karb'o captain agurinki idan kuma kin isa toki hanamu d'aukoshi daga gareki kawai lokaci muke jira kekanki kisan duk duniya babu wanda captain zai bud'ewa zuciyarshi ta shiga ta zauna se *aunty* . Haushi da takaici yasa shukrah katse wayar Yah ibrahim ya tsinci kanshi dayin murmushin tare dajin dad'in sanin cewa ba manosh bane yayi magana da aunty shukrah ce. Take ya kira baba a waya ya gaya mashi komai,baba baiyi mamakiba dan yasan babu abinda aljanu basayi, take yaje ya sanar dasu maryam dan hankalinta ya kwanta. Ai kuwa dad'i sosai taji tare dayin add'ua Allah ya kare mata mijinta ya kuma dawo dashi garesu. Marwan kuwa yana kwance ne kawai amma yakasa bacci dan irin abubuwan dayaji yau da kuma gani. Tun bayan barin su lubna gidan yaketa tambayar hajiya iya kakarsa meke faruwane danshi kansa yasan akwai wani abu dayasa lubna tayi mata hakan amma sam hajiya iya tak'i cemishi komai se kukan nadama da taketayi babu sassaushi. Haka marwan ya gaji ya tafi gida gun mum nasu,koda ya gayawa mum nasu abinda lubna tayiwa hajiya iya sam mum batayi mamakiba,shima marwan d'in ya lura da yanayin mum d'in nashi wanda yasashi tambayar mum nasu yace wai meke faruwane mum nakasa fahimtar komai tabbas akwai wani abu dayake faruwa mum dan Allah ki gayamin. Marwan ya kamota suka zauna yana share mata kwalla. Mum ta dubi marwan tace zan gaya maka marwan amma sekamin alk'awarin bazaka bari mahaifinka ya d'auki mummunan mataki akainaba, cikin rashin fahimta marwan yace banganeba mum? Mum tace marwan dad naka yana k'aunarka fiye da komai a duniya,idan yasan abinda na'aikata tonasan zamana dashi yazo k'arshe, kaine zaka iya hanashi rabuwa dani d'ana saboda k'aunarka da yakeyi. Marwan ya sauke ajiyar zuciya yace namiki alk'awari mum har abada bazan bari ku rabu da dad ba. Mum tace nagode marwan, sannan ta fara bawa marwan lbr kamar haka... [7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNRY'N YARA Written by sad-nas *dedicated to AUNTY SIS*
Chapter 34 · 0% Book details