Sashe 15
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*dedicated 2 miemie bee* 33-34 da sauri maryam ta share kwallanta dan kar azo a ganta. Manosh kuwa wani iri yaji a ranshi sam baiso ya bartaba amma babu yadda zaiyi,awaje ya samu muh'd sukayi sallama ya sake jaddada mishi cewa ya kula mishi da apple shidasu majid. Manosh ya isa kd lfy,yana isa maryam ya fara kira,taji dad'i sosai suka d'an tab'a hira sannan sukayi sallama. Hajiya iya dake zaune a gefen maryam tace surukin nawa kenan shine ba'a tab'a kawo minshiba,dariya maryam tayi tace saurin me kikeyi hajiya ai dole zaizo ya gaisheki dan kece babbar k'awa. Dariya sukayi dukkansu maman rashida tace to maryam mudai zamu wuce Allah ya baki lfy,tace ameen mama nagode. Hajiya tace ni wannan mota naki semun rabata gaskya,ya zaiyi ya kawo miki bai kawomin,rash da maman maryam sunata dariya,maryam tace karki damu wai yasan ke baki da k'afane bazaki iya tuk'iba kinga ni se inyi ta kaiki duk inda zakije ko? Nanma dai dariyan akayi daidai lokacin samira zahida da ameena suka shigo da sallama. Bayan an gaisane su maman rash suka fita inda yah ibrahim ya mayar dasu a motar maryam. Maryam da k'awayenta se hira sukeyi tare da tayata murnan samun mota. Sosai maryam take samun jama'a harda malaman islamiyyansu se zuwa gaisheta akeyi dayake ita mai jama'a ne sosai. Daga masu kawo mata fruits se masu bata kud'i,su kansu doctors da nurses d'in sunata mamaki har tambaya sukeyi wai maryam d'innan 'yar wayece a garinnan dan yadda jama'a suke sintiri agunta. Shi kanshi dr muh'd yaji mamaki sosai,dan haka ya kira manosh yace gaskyaka samu mata wlh ka rik'eta da kyau sannan mu dami su dad akan ayi maganan aurennan da wurifa. Dad'i sosai manosh yaji yace insha Allah. Maryam ta samu sauk'i sosai koma ince ta warke. Da yamma miher da mum nata sukazo inda miher ce tayi driving nasu gwanin sha'awa. Lokacin maryam ta idar da sallan la'asar kenan tana addu'oi setaji bud'e kofa tare da sallama,mamantane ta amsa musu dan rash ta koma gida. Koda maryam ta idar,kunya sosai taji da ganin mum d'in manosh. Kanta a sunkuye tace sannu da zuwa,mum tace yawwa maryam sannu ya jiki,maryam tace da sauki ina wuni,tace lfy lau ya kika k'ara ji da jikinki,tace da sauki,mum tace to Allah ya k'ara lfy Allah kuma ya yaye miki,maryam tace ameen gabad'ayansu sannan mum ta zauna kusa da maman maryam akan carpet dake shinfid'e a k'asa,ita kuwa miher ta zauna a gefen maryam tana zolayarta matar bro kin samu lfy se kuma magan aurenku da bro,ahankili tayi maganar cikin zolaya tana dariya. Maryam data kasa sakewa dan kunyan mum murmushi kawai takeyi,miher tace wlh ki dena jin kunyan mum dan bata da matsala sam wlh garama ki saki jikinki bro yace in kawo miki wannan,flower ne d'an k'arami maiban sha'awa,amma maryam taqi karb'a dan kunya,miher se dariya takeyi tace idan bakya so shikenan se in gaya mishi yanzunnan,muntsinin miher tayi ta cinyarta batare dasu mum sun ganiba. Daroya sosai miher takeyi tace shikenan nifa wasa nakeyi kar anjuma inji kin cijeni,mirmushi sosai maryam tayi tajin kalmar miher amma sam taqi tayi magana,mum ma ta lura da cewa maryam a takure take dan haka tace miher mu tafi ko donmu barta ta huta. Murmushi maryam tayi miher ta mik'e,maryam tace mun gode Allah ya kare,mum tace ameen sannan tayi gaba itada maman maryam. Ai suna fita maryam ta karb'e flowern tace wlh sena had'aki da captain kinata sani magana bayan kinsan bazan iyaba ko,miher tayi dariya tace nima ai zan gayamishi harda muntsinin da kika min,dariya sukasa dukkansu sannan tace miher mungode sosai ku bakwa gajiya da d'awaiyinane pls bana buk'atar wani abu kuma dan Allah ya isa haka mana,miher tace dani kikeyine,kallonta maryam ta tsayayi tace ni kike mannawa hauka ko,miher tace "am sorry our wifey" ban isa in manna miki haukaba wlh amma wlh mum bazata tab'a yarda inzo dubaki empty hand bane nizan tafi nabar mum tana jirana zamuzo gobe nida *my majid* kafin a sallameki *apple* tate dajan lallausar kumatun maryam. Dariya sosai maryam takeyi yayinda miher ta fita da sauri tana mata byee,ita kuwa murmushi takeyi tare da cewa tonagode Allah ya kiyaye hanya. Maman maryam ta bud'e ledojin kayan tea ne manyan gwangwanaye da kuma fruits. Mama ta kalli maryam tace sude basa gajiya wlh,mamansu tana da kirki wlh gata da sauk'in kai kamar ba matar mai kud'iba kuma naga soyayyarta akanki sosai wlh. Maryam tayi murmushi tace wlh mama hakama miher tana sona sosai wlh gaskya ba laifi Allah yasa su d'aure a haka,mama tace ameen sannan sukaci gaba da hiransu irinna *uwa da 'ya*. Yau aka sallami maryam,babantane ya d'aukesu a motarshi inda sukaitawa dr muh'd godiya, cikin girmamawa yace wlh bakomai baba Allah ya bata lfy,suka amsa da ameen sannan maryam tace nagode fa sosai da k'ok'arinku Allah yabar zumunci,murmishi yamata tare da cewa ameen aunty bakomai semunzo girei,tace wlh na hutar daku hakama yayi wlh sannan ta tafi yana musu Allah ya kiyaye. A girei ma tinda maryam ta dawo zuwa ake ana gaisheya. Bayan kwana biyu ne miher tazo da drivernsu da kula sabuwa babba a hannunta peppe chikeen ne a shike. Murna sosai maryam tayi da daginta suna d'an tab'a hira sannan ta mik'e tace zan tafi dan akwai inda zanje wlh sannan ta bud'e zip na jakanta ta ciro flower tace inji camtain. Murmishi maryam tayi tace nagode bari in wanke kulan ki tafi dashi,mihe tace no wlh danke kawai na sayi kulan dan haka shima nakine. Gidiya sosai maryam tayi tare da rakota har waje sukayi sallama. Bayan tfyantane samira da rsha sukazo sukaita hira,maryam ta d'ibo musu kazan sunaci suna hira inda maryam take sanar dasu cewa gobe za'azo tambayarsu. Washe gari da misalin 10:00am na safe iyayen manosh dasu marwan sukazo girei domin tambayan auren 'ya'yansu. Dama baban maryam yasan da zuwansu dan haka shima ya nemo mahaifin samira da kuma 'yan unguwa dan shine uban maryam da rashida dukka. Koda sukaga mahaifin manosh masu ji mamakiba dan yah ibrahim ya musu bayanin komai kuma yace ya yafe harma da maman rash,amma baban maryam yace dole za'a sanar dashi kodon yasan yayi kissa kuma *azumi sitti* yahau kansa. Zuwan manya sukayi da iyaue su majid,dan seda sukayi tambayan zahida da amina sannan sukazo girei. Karb'a na musamman aka musu inda aka gaggaisa kuma aka fahimci juna ansa aure nanda 3month. Bayan an gamane sukayi godiya sannan suka tafi. Bayan sun koma gidane mahaifin maryam ya kira mahaifin manosh yace dama inaso muyi wata magana mai muhimmancine akan wani bawan Allah daka tab'a bugewa akan hanya girei shekaru biyu da suka shige,idan baka mantaba akwai wata yarinya dataketa bin motarka a wannan lokacin tana kuka. Jikin mahaifin manosh yayi sanyi dan baizai tab'ance wannan rananba. Baban maryam yace to wannan mutumin bakowabane illa mahaifin rashida wanda marwan yake neman aurenta,tun daga wannan lokacin daga bugeshi ko minti goma bai k'araba Allah yayi mishi rasuwa. A wannan lokacin akwai wanda ya ganka shine da kukazo girei yace lallai kaine wannan mutum, yanzuma na gaya maka hakanne dan kasan cewa azumi yahau kanka,sannan yana da kyau ka nemi gafarar iyalansa,wanda ya gankan bakowa bane illa d'an cikinsa wanda yazo ya gaisheku mai suna ibrahim wato yayan rashidan kenan,amma sunce sun yafe har abada sun d'auki kadda. Mahaifin manosh ya sauke ajiyar zuciya yace nagode sosai alhaji Allah yabar zumunci,kuma wlh naji dad'i sosai da yadda kamin magana a sirrance Allah ya saka da alkhai kuma insha Allah gobe zanzo gun iyalan marigayin,wlh tun wannan lokacin nima bani da sukuni kuma na koma girein na tambayi wani matashi akan wani da aka buge da mota nan ya tabbatar min da cewa Allah yayi mishi rasuwa,wlh tun daga wannan lokacin na kamu da hawan jini kuma nayi azumina sittin,sannan nayi aike zuwa ga iyalan wannan mutumin a wannan lokacinma sedai na hana abayyana sunan,kuma nasan nayi kuskure sosai wanda hakan shiyasa na gyara halayyata da dama alhaji nagode sosai kuma insha Allah gobe inanan zuwa girei da safe. Mahaifin maryam ya tuna da randa akazo da abinci da kaya da kuma kud'i har *dubu d'ari uku* wai a baiwa iyalan marigayi,kuma sunyita tambaya daga gun waye aiken yazo amma sam basu samu amsaba. Kamar yadda mahaifin manosh ya fad'a da safe yaje shida mahaifin marwan da kuma drivernsu,inda suka samu mahaifin maryam a gida dan baije ko inaba tunda yasan da zuwansu. Shiya musu jagora har cikingidansu yah ibharim suka gaida da iyalinsa sannan suka bada hakuri tare da musu gaisuwan rashin. Suka amsa tare da cewa cewa ai kwananshine ya k'are dan haka bakomai sun yafe wlh,godiya sosai mahaifin manosh yayi tare da musu alkhairai sosai sannan kuka fito tare da yah ibrahim yana rakasau da baban maryam. Bayan fitowansune mahaifin manosh yake tambayan ibrahim akan aikin da yakeyi,nan ibrahim ya gaya masa cewa bai dad'e da gaba NYSC nashiba yana jirane tukunna,nan mahaifin manosh ya bashi *card*nashi yace ya same ran monday.godiya sosai ibrahim yayi dan yasan kawai aiki za'a bashi. Lokaci yanata tafiya angwaye se himma suke bayarwa wajen aikin ginin gidajensu da zasu tare da amarensu. Manosh kusan kullum seyaje girei tun bayan dawowarshi,ranan suna hira yake tambayar apple wani irin gida take so,dadai tak'i gaya mishi,amma da taga zai b'ata rai tace ita dai ranta nason gidan sama,sannan ya kasance *milk da d'an army green*. Murmushi manosh yayi yace shikenan nagode. Itama murmushin tayi tace amma pls karka takura kanka danni kai nake so ba gidaba dan haka kakyi komai d'an daidai pls,dad'i sosai yaji yace shikenan apple zanyi d'an daidai *mata 4* dariya sosai tayi tace bakomai tunda dai nice *uwar gida* Soyayyarsu abun burgewa wlh domin mai tsafta ce. Maryam ce zata kaiwa babanta abincin a shop nashi tana cikin tfy se wata bak'ar mota ta tsaya,da sauri suka fito maryam bata zata gurinta zasu nufoba kaiwai suka big'e abincin hannunta ya zube a k'asa,kan tace wani abu sunsa mata hanki a hanshi mai d'auke da magani take ta mance inda take sukayi saurin jefata cikin mota suka fizgi motar a guje. Adaidai wannan lokacin iyayen maryam sukaji gabansu ya fad'i atare suka hau fad'i *Hasbunallahu wani'imal wakim* suketa nanatawa... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: