Sashe 10
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wayarka,yace ai devio d'aya kika tab'a turamin na wanda ya buge mahaifina ko? Hawaye ya sake zubowa a fiskarta tace eh shi,yace eh har yanzu yana wayana ai,tace bakowa bane wannan mutumin illa mahaifin manosh yah ibrahim. What! Mahaifin manosh kikace,tace eh shine na tabbatar da hakanne yau danaje gaida mahaifiyarshi yah ibrahim bazan iya b'oye makaba dannima mahaifinka mahaifinane sannan mun dad'e muna nemanshi se gashi kuma ashe shine mahaifin manosh,kukane yaci karfin maryam take ta katse wayar. Hankalin ibrahim ya tashi sosai ya rasa meyake mishi dad'i musamman dayaji maryam tana kuka,don ya dad'e dasa son maryam a ranshi tun mahaifinshi yana raye ya sanar dashi,amma se mahaifinshi yace karka damu ibrahim ka gama karatunka tukunnan maryam 'yace aguna nima zafin samun kwarin gwuiwa idan ka gama karatu ka samu aiki se inyiwa mahaifinta magana tunda amininane. Hakan yasa ibrahim ya hakura yabar abin a ranshi amma kash *muna namu Allah yana nashi* hankalin ibrahim atashe ya wuce gidansu maryam..... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd Dedicated 2 *ANEELURV* 27-28 Uncle ibrahim yana isa yayi sallama,maryam ta fito tare da amsa sallamar,tunda ganin fiskarta ya tabbatar tayi kuka. Kallonta yakeyi mai cike da kauna,yace ina mama,miryarta k'asa ba tare data kalleshiba tace tana d'aki. Ibrahim yace aunty meyasaki kuka,shuru tati ta kasa cewa komai,ya sake cewa aunty pls banaso in sake ganin hawaye a fiskarki wlh na yafewa mahaifin camtain amma saboda kece kawai wlh dabadan keba danayi k'aransa,aunty kin wuce duk yadda kike tunani aguna sannan babanki ya rik'emu kamar uba tun bayan rasuwan mahifinmu dan haka ki wantar da hankalinki kinji wlh komai ya wuce zan samu baba anjuma muyi maganan. "Maryam ta d'ago da kanta tana kallonshi tace nagode sosai yah ibrahim,basan dame zan biyakaba a duniyannan Allah yabar zumunci. Murmushi yayi mata tare da cewa ameen aunty pls kicire komai a ranki karki nunawa captain wani canji sannan karki sanar dashi kinji,to tace dashi yace to ai seki murmushi dan fishi bai kamacekiba,dariya takeyi wanda yake kara mishi kaunarta a ranshi nan sauyin kallon da yake mata ya canja,wanda ita ita da kanta ta lura da hakan,take jikinta yayi sanyi,shi kuwa juyawa yayi ya tafi batare daya sake cewa komaiba. Tunani sosai maryam ta shiga akan yanayin yah ibrahim tace kodai sona yakeyi to? Kai a'a da sona yakeyi aida ya dad'e da fad'a kawai dan kila dan kokarinane yasa yake sona haka amma kuma meyasa yakemin wannan kallon da manosh yake min sannan ya tafi babu sallama? Wayanta ta d'auka ta kirashi bugu d'aua ya kayse ya kirata ta d'auka da sanyin murya tace yah ibrahim katafi babu ko sallama? Yace am sorry aunty bazan iya tsayawa inaci gaba da kallonki bane,tace todai ai semuyi sallama koh kamar dai yadda muka saba. Murmushi yayi yace tokiyi hakuri aunty nayi laifi,murmushin ta mayar mashi tace ba komai ya wuce dama shiyasa na sake kiranka. Yace tona gode aunty ina so in miki wata tambaya pls ki gayamin karkiji kunyana,tace to inaji, "you love camtain right?" Shuru tayi dan bata tab'a tunanin jin wannan tambayan daga garesaba,yace aunty kinyi shuru,tace yah ibrahim yana da wani haline mara kyau kodai kasan wani abu mara kyaune game dashi? Yace "aunty" namiki tambaya kimin tambaya,cikin sanyin murya tace yah ibrahim bazan iya b'oye maka komai a duniyannan ba "yes ina sonshi" amma wlh idan yana da wani aibu kagayamun ko kuma baba,tunda dama ai nace kayi bin ike akanshi. Ibrahim yace hakane aunty wlh bayi da wani aibu ko hali mara kyau kawai dai na tambayekine,tace tomeyasa kamin tambayan? Yace yanzu nayi laifi kenan,yace bakayiba nima ina so ka gayamin me dadilin tambayan? Yace idan muka sake had'uwa zan gayamiki yayinda nake kallon fiskarki kinji,tace toshikenan nagode,yace ok bye sannan ya katse. Maryam dai da tunanin maganansu ta kwana a rai kuma daahi ta tashi. Rashida ce taje gun maryam,lokacin tana zaune a gaban *computer* tana sanye da blue jeans da kuma jan top mai dogon hannu ta nad'e kanta da *light brown* gyale k'arami,rashida tace kai amma kinyi kyau a kayannan bari in miki *picture* ai kuwa maryam tayi dariya fararen hakwaranta suka bayyana rash ta dauka tare da cewa gaskya ki turawa captain wannan pic din dan yayi kyau sosai wlh. Murmushi maryam tayi tare da kab'ar wayan rash tana ganin pic din, nan suka koma kan k'aramin gadonta tana shirya books nata rashida se d'aukata takeyi,maryam tace ke ya isama mana. Dariya rash tayi sannan suka fara hira nanne maryam take gaya mata cewa mahaifin manosh ne ya buge mahaifinta kumata gayawa yah ibrahim,hankalin rashida ya tashi sosai ta mik'e tsaye tace mahaifin manosh fa kikace,maryam tace eh wlh wlh shine kinsan jiya naje gaida mum nashi acan naganshi. Rashida tace wlh bazai yuba,ya rabani da mahaifina shikenan aahe manosh bai sami mahaifi nagari wlh tunda har zai iya yin kissa sannan kuma ya gudu mugu mara imani wlh Allah ya isa mana. Maryam tace dan kiyi hakuri rash kidena fad'a haka,rash tace ai wlh ba mutumin kirki bane tunda haka yake Allah yasa camtain karya d'auko halinsa dan wlh indai halinsu d'aya to ina tausaya miki m aryam. Maryam tanata bata hakuri amma ina rash se kuka takeyi harta fara cewa to yanzu kinsan hakan tome kuke ciki da captaim maryam? Maryam tace kamar ya rash? Rash tace har yanzu kina son captain, maryam tace rash wani irin magane haka kuma pls kiyi hakuri ki nitsu pls,rash tace in nutsu,hakan ya nuna har yanzu kina tare da captain kenan maryam mahaifina fa mahaifinkine,kuma har zaki iya ci gaba da soyayya da d'ansa,lallai nagode danke mahaifin na raye shiyasa keto marwan d'inma daga yau bani bashi tunda shi abokin manosh ne koma ince amininsa dan haka kema daga yau *bani bake maryam* tana kaiwa nan ta ta fice tanata kuka sosai. Mamakine sosai ya kama maryam dajin kalaman rash,dan tunda suka taso ko musu bai tab'a shiga tsakaninsuba kowa ya sansu kuma yasan shak'uwarsu sannan maryam tana son rash sosai fiye da sauran k'awayenta dan haka se abin ya dameta sosai, dama mamanta ta tafi angiwa dan haka ta rufe gida tabi bayan rash. Kuka sosai rash takeyi itama mamanta bata gida dan yare suka fita da maman rash d'in sunje barkan haihuwa. Maryam tace haba rash yau har zaki iya furta cewa *bake bani* akan manosh,rash nasan ina son manosh amma wlh soyayyar da nake miki yafi wanda nakeyiwa manosh,domin shi zan iya rabuwa dashi amma ke na d'aukeki tamkar k'anwatace da muke ciki d'aya meyasa zakice haka dan Allah? idan rash jajur dan kuka tace wlh karyane maryam dakam nasan kina sona amma banda yanzu dan haka ki fita kibar mana gidanmu ki fita bana bukatan in sake ganinki dake da kowa nakima ki fita anan da k'arfi ta hank'e maryam har waje se jinta tayi ta mannu da mutum ta bayanta. Da sauri ta goge hawayen idonta tare da juyowa se sukayi ido hud'u da yah ibrahim take hawaye yaci gaba da gangarowa a fiskanta ta juya tana kallon rashida da tsoro ya gama kamata dan ganin yah ibrahim datayi. Wucewa maryam zatayi da kukanta se yah ibrahim yayi saurin rik'o hannunta yace auntyn kiyi hakuri meya had'aku? Karon farko kenan danamiji ya rike hannu maryam bata iya cewa komaiba se kokarin fisgan hannunta takeyi agun yah ibrahim tace dan Allah ka sakeni yah ibrahim zan tafi gida,yace no aunty dan Allah ki tsaya yana rike da hannunta ya juya rai a b'ace yana kallon k'anwarshi rash yace ke meya faru,jiki na rawa ta gaya mishi,ya e shine yau da hannunki harkin iya hankad'e maryam rash? Ina ruwanki azan,yana rik'e da hannun maryam harya isa gun rash *belt* d'in jikinshi ya zaro rash ta fara kuka tare da cewa dan Allah yah ibrahim kayi hakuri wlh bazan sakeba. Rash ta tsorata sosai dan tasan halinshi sarai, kukda dai bai tab'a dukantaba tunda take. Maryam tayi saurin shiga tsakaninsu tana hawaye tace dan Allah ya ibrahim karka dake pls,tsawa ibrahim ya dakawa maryam wanda dukkansu seda suka tsorata yace aunty ki matsa! Rash ta rike maryam sosai tana bashi hakuri. Maryam tace kayi hakuri yah ibrahim amma sedai ka dakemu dukkanmu tana kuka sosai. Jikinshi yayi sanyi dan yadda yaga maryam take kuka haka ya sake *belt* din a k'asa rash kuwa da gudu ta fita ta wuce d'akin mamanta ta kulle da key. Maryam ma tazo zata wuce amma seya tareta,kuka takeyi tace yah ibrahim zan tafi gida,yace *aunty am sorry pls akan abinda rash tamiki*,maryam batace komaiba tace pls kaban hanya in wuce,yace sekin share hawayenki,bai jira me zataceba yasa hannunsa yana share mata,tayi saurin kawar da kanta gefe tare da buge hannunsa daga kan fiskanta,amma ina seya sake mayarwa tare da rik'e hannunta yace pls aunty ki dena kuka wlh har cikin raina nake jin kukanki sabo da yadda nake *k'aunarki tunda dad'ewa*. Da sauri maryam ta d'ago da kanta suna kallon junansu sosai har cikin ido,hakan ya sake rikitar da ibrahim sosai aise ya tsinci kanshi da fara matso da fiskarshi dedai nata da niyan kissing nata. Idanunta ta zaro tare da bigeshi gefe tayi saurin barin d'akin da gudu ta wuce gida,shi kuwa wani ajiyar zuciya ya sauke huuuuuh! tare da nadaman abinda yake son aikatawa... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd